Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » KISHIYAR KATSINA: Babi na Biyu

KISHIYAR KATSINA: Babi na Biyu


 • Caa! Matan dake cike da falon suka yi ma Aysha, wanda mafi yawansu danginta ne da kuma na Khamis. Kalmar rashin kyautawa ce ta riƙa fitowa a bakin mafi yawansu, domin ba haka ake siyasar karɓar kishiya ba.

  Aunty Rahama wadda ƙanwa ce ga Khamis ta ce "Aysha kina tare da wahala, tunda har ki ka ƙallafa ma ranki baƙin kishi".

  Duk mutunta junan dake tsakanin Aysha da dangin Khamis bai hana ta murje ido tare da duban Aunty Rahama ta ce "Ji Aunty Rahama da wata magana, to wallahi ku kuka ga wahala ba ni ba, kuma amarya da danginta basu ga komai ba tunda har suka shigo gonata".

  Shewa falon ya ɗauka, ɓangare ɗaya kuma duk aka bi ta da kallon mamaki, wasu na faɗin ta kyauta, wasu kuma na faɗin ta kwafsa.

  Aunty Rahama kuwa ɗan taɓe baki ta yi tare da faɗin "Maida wuƙar ƙanwata, na san wutar kishi ce ke ruruwa azuciyarki, don haka dole mu yi maki uzuri kafin ki gane babban kuskuren da kika tafka"

  Aunty Rahama na rufe baki wata daga cikin dangin Ayshar ta ɗora da "Yo Rahama kishi hauka ne, in banda sakarci da ɗaukar zugar ƙawaye me zai sa ta wannan katoɓarar?".

  Faɗa sosai suka yi mata, suka nuna mata girman kuskuren da ta aikata, wanda ko shakka babu ya zubar mata da ƙima a idon Amarya da danginta. Sannan suka nuna mata kishi fa ba hauka bane, iyaka tsakanin ta da amarya duk wadda ta iya allonta ta wanke.

  Duk surutun da suke yi Aysha bata ɗauki ko ɗaya ba, asali ma gani take suna faɗin haka ne don ba su aka yi ma kishiyar ba.

  Miƙewa ta yi tare da duban Zuzee da duk ta sha jinin jikinta, saboda ta lura da kallon tsanar da dangin Khamis ke jifarta da shi. Bakomai kuma ya ja wannan kallo ba sai fahimtar da suka yi ita ce babbar ƙawar Aysha, kuma duk rashin mutuncin da Ayshar ke yi da sa hannunta a ciki.

  "Zuzee ta shi mu je ciki" Idanun Aysha a kanta ta faɗi haka.

  Amsa Zuzee ta bata da "Ki je zan shigo", saboda bata son su zarge ta, Aysha bata yi tunanin komai ba ta yi gaba, Zuzee na ganin ta shige ta ɗan riƙa sa baki ana tsigar Ayshar.

  Aunty Rahama ma babbar ƙawarta mai suna Hajjo na zuwa ta bar falon. Ɗakin Amarya suka shiga, aikuwa suka taras ana ta zagin Aysha, kuma ganin su bai sa an fasa ba.

  Rahama ta ji ba daɗi, sai dai tunda Ayshar ce ta ja ma kanta ba yadda ta iya.

  Matsawa suka yi a gefen gadon da Amarya ke zaune, Aunty Rahama ta ce "Maryam ga ƙawata ku gaisa".

  Cike da kunya Maryam ta ɗan yaye mayafin da ke kanta tare da gaishe da Hajjo.

  Amsawa ta yi sannan ta yi musu Allah sa Alkhairi. Bayan sun fito Hajjo ta tambayi Aunty Rahama "Ni kam wacece mutanen can ke cewa ta rako mata?".

  Aunty Rahama ta ce "Waa ce fa idan ba Aysha ba, ai ta gama bamu kunya". Abin da Ayshar ta yi ta labarta ma Hajjo.

  Ran Hajjo a ɓace ta ce "Kanta ta wulaƙanta, amana kuma ko ta karɓa, ko kada ta karɓa duk ɗaya, tunda aikin gama ya gama", ɗakin Aysha suka nufa, lokaci ɗaya kuma suna tattauna maganar cikin ɓacin rai.

  A ɗakin Amarya kuwa yadda zata zauna da Aysha suka shiga kitsa mata, don sun fahimci mugun abu ne ke cike da ran Ayshar, wanda kuma idan ba tsaye suka tashi ba, to ƴarsu zata sha wahala.

  Da yake Amaryar ba kanwar lasa bace ta ce "Ai wallahi ta gama yawo tunda har na auri mijinta, baƙin kishi kuma mu zuba ni da ita". Daga yara har tsofaffin dake wurin ba wanda ya kwaɓi Maryam, sai ma ƙara zuga ta da suke akan ta yi ƙoƙarin zama tauraruwa a wurin Khamis, basu suka fara shirin tafiya ba sai da suka ga zamanta ya daidaita akan dokin huɗubar da suka ɗaura ta akai.

  Yamma na bada baya waɗanda ke a Katsina suka tafi, waɗanda ke a nan garin kuma sai da suka ji motsin shigowar ango sannan suka kama gabansu.

  Khamis kuwa ɗakin Aysha ya fara shiga, inda ya same ta akan sofa tana ta danna waya. Gefenta ya zauna tare da faɗin "Uwar gida baki yi bacci ba?".

  Rufe data ta yi sannan ta ɗan sauke ajiyar zuciya "A'a, sai na raka ka ɗakin Amarya tukunna zan kwanta", Idanunta a kan fuskarsa ta ƙarashe maganar, ganin farinciki kwance a fuskar ya sa ta ji zafin dake a zuciyarta ya ƙaru, "Yanzu wannan farincikin duk a kan wata ne ba ni ba", cike da ƙunar zuciya ta faɗi haka a ranta.

  Ido ya ɗan zaro tare da faɗin "Da gaske ki ke?", don bai taɓa tsammanin jin haka daga bakinta ba, saboda ya ji labarin katoɓarar da ta yi a ɗazu.

  Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Wallahi da gaske nake", sannan ta miƙe don ta tabbatar mashi, hannunsa ta ɗan ja ta ce "Mu je".

  Kasa tashi ya yi, sai ma ya kafe ta da idanu, cikin ransa kuma yana kallon tsantsar damuwar da ta kasa binnewa a akan fuskarta. Jikinsa ne ya ɗan yi sanyi, saboda in dai zata ajiye damuwa a ranta, toh kuma matsaloli ne zasu biyo baya, tunda gashi ɗazu ta fara zuba wulaƙanci.

  Ɗan matse hannunta dake cikin nashi ya yi, sannan ya yi magana cikin cigar zaulaya, "Ki zauna in baki kazar uwar gida tukunna, idan kin gama sai ki raka ni".

  Ido Aysha ta lumshe tare da girgiza kai alamun "A'a", don idan ta buɗe baki kuka ne zai fito ba magana ba.

  Sosai ya lura da kukan da take son yi, amma sai ya share ya ce "A'a sai kin ci ko muna fita".

  Ido ta sake lumshewa tare da haɗiye kukan dake shirin fitowa ta ce "Allah kuwa na hutar da kai, ka ga dare ke yi, na san Amarya na can tana jiran ka", sake jawo hannun sa ta yi alamar ya tashi.

  Ɗan shiru ya yi kamar mai tunanin wani abu, daga bisani ya ce "Toh shikenan, ni dai na fita haƙƙinki". Bai jira jin me zata ce ba ya maida dubansa ga Haneef da ya baje akan gado yana bacci, tambayar ta ya yi "Ina Haneefa ta ke ne?".

  Cewa ta yi "Tare da su Hafsat suka tafi",

  "Okay" ya ce, sannan ya ya zare hannunsa daga cikin nata, ledojinta ya ware mata a gefe sannan ya miƙe.

  Mayafi Aysha ta yafa gami da zura takalma, sannan ta karɓi ledojin da ke hannunsa suka fita.

  Ba da son rai Aysha ta tsiri wannan rakiyar ba, sai don kawai ƴan'uwanta sun matsa mata, wai a ganinsu hakan duk neman matsayi ne a wurin miji "Matsayin banza", ta faɗa a ranta a daidai lokacin da suka zo ƙofar ɗakin Amarya.

  Duban Khamis da ke ta washe baki ta yi, sai ta ji kamar ta maƙure shi don takaici. Shi kuwa bai san tana yi ba, don duk a zuciyarta take ta wannan hauragiyar.

  Ɗakin Amarya kuwa ya sha wani irin gyara, don kafin danginta su tafi sai da suka daidaita komai a muhallinsa, sannan suka turare ɗakin da turarukan wuta masu sanyaya zuciya.

  Hannun Aysha cikin na Khamis suka shiga cikin ɗakin. Wata irin faɗuwar gaba ce ta samu kanta a ciki, wadda bata rasa nasaba da ƙayatuwar Amarya duk da bata ga fuskarta ba.

  Zama suka yi a gefen gadon, Khamis ya dubi Amarya da kanta ke ƙasa ya ce "Amarya, ga uwar gida ta kawo maki angonki".

  Baki Aysha ta taɓe tare da ɗauke kanta ta cigaba da raba idanu a ɗakin.

  Ita kuwa Maryam bata so ganin Aysha ba, don a halin yanzu ba wanda ta tsana kamar ta, murmushin yaƙe ta yi a cikin mayafin tare da cigaba da jujjuya zoben dake hannunta.

  Ɗan taɓo Aysha Khamis ya yi, saboda gaba ɗaya hankalinta na ga wasu ƙayatattun frames dake manne a bangon ɗakin, bayan ta maido hankalinta gare shi ne ya yi mata alamar ta yi magana.

  Ƙaƙaro murmushi ta yi ta ce "Amarsu ta ango, toh ga amanar mijina na kawo maki, da fatan zaki kula mani da shi".

  Ba don idon Khamis ba, da sai Maryam ta maida martani akan rashin mutuncin da ta yi musu ɗazu.

  Nasiha Khamis ya yi musu akan su zauna lafiya, kuma su riƙe juna da Amana, jin shi kawai suke, amma kowa da irin nata ƙudurin akan ƴar'uwarta.

  Tashi Aysha ta yi da zimmar tafiya, Khamis ya ce "Tun yanzu?".

  Ta ce "Eh mana, gwara na barku ku kwashi Amarci".

  "Umma ta gaida Aysha" Maryam ta faɗa a ranta, don ji take kamar a kanta Ayshar take zaune.

  A bakin ƙofa Khamis ya raka ta, sallama suka yi ya dawo tare da sanya ma ɗakin key.

  Cike da zaƙuwa ya ƙaraso kan gadon tare da yaye mayafin da ke kan Maryam a hankali.

  "Masha Allah" ya furta a lokacin da ya yi arba da kyakkyawar fuskarta.

  A hankali ya lumshe idanu tare da buɗe su, cikin ransa kuma yana jin wani irin nishaɗin da sai idan suna tare ne yake jin shi.

  "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya hallici surarki Maryam, sannan godiya marar adadi agare shi bisa ga mallaka mani ke da yayi a matsayin abokiyar rayuwa" cikin wata irin kasalalliyar murya Khamis ya faɗi haka, lokaci ɗaya kuma ya riƙe mata dukkan hannaye yana wasa da su.

  Ita kuwa kunya ce ta mamaye ta bisa ga irin kallon da yake mata, a ɓangare ɗaya kuma tana jin wasan da yake mata da hannu har a cikin ƙwaƙalwarta.

  Yunƙurin zame hannun ta yi, amma ta kasa, sai dai ta lumshe idanu tana cigaba da sauraren kalmominsa da ke nutsar mata da zuciya.

  Bata wani ankare ba sai jin saukar numfashinsa ta yi a fuskarta, ba shiri ta buɗe idanun, sai ta ga yana yi mata wani irin mayataccen kallo mai wuyar fassarawa.

  Ɗan baya ta yi da kan suka cigaba da kallon junansu, kowane yana jin kamar ya haɗiye ɗan'uwansa saboda kyawun da suka yi.

  Khamis da ƙamshin jikinta ya sakar mashi da duk wata lakka ta jiki ya ce "Maryam ina sonki" tare da ɗan sumbatar ta a gefen kumci.

  A yadda yake jin kansa, zai iya aiwatar da komai, toh ganin basu ci komai ba ya taimaka mata suka sauko a ƙasan capet ɗin da ke shimfiɗe a bedroom ɗin.

  Abubuwan da ya shigo da su ya riƙa bata a baki, duk da ƙudurin Maryam na yi ma *kazar Amarya* cin gilla amma ta kasa, saboda tsoron da ya cika mata zuciya, don ta ga dai abin ba na wasa bane.

  Sai da Khamis ya ɗan sha fruits sannan suka yi wanka da Alwala.

  Suna fitowa suka gabatar da sallar godiyar Allah, saboda burin kowanensu ya cika, musamman Khamis da ke matuƙar son ta, son da ida ba ita bace, da tuni ya haƙura da auren don samun farincikin Aysha, amma sai ya riƙe wuta tare da ɗaukar ma ransa haƙuri da duk wani ƙalubale in dai zai mallaki Maryam.

  Haka abin yake a wurin Maryam, danginta ba su son ta auri mai mata, amma ta ce ta ji ta gani saboda idan ta rabu da Khamis, da wahala ta sake samun namiji mai nagartarsa.

  Addu'a Khamis ya yi mata akai, sannan suka yi shirin kwanciya.

  Maryam na jinta a jikinsa ta fara kyarma, da yake gwani ne sai da ya fara rage mata wannan tsoro da maganganu, a cikin kunnenta ya riƙa faɗin "Ki yi baccinki a natse, ni kuma zan kwana a gefenki ina gadinki". Ta ji daɗin maganar, aikuwa ta ƙara ƙanƙame hannunsa dake zagaye da ita.

  Sai dai ba a jima ba ta ji wasa ya canja salo, tsoron da take ji bai hana ta karɓar saƙonnin da yake aika mata ba. Shi kuwa sai da ya ga ta yi liƙis sannan ya tabbatar mata da ta zama matarsa.

  Wahalar da ya bata a wannan dare ba ta bari su duka sun runtsa ba.

  Kamar yadda tsananin kishi bai bar Aysha itama ta runtsa ba. Ji ta riƙa yi kamar ta je ta banka ma ɗakin Maryam wuta, sai dai kuma ba wannan dama.

  Da safe Haneef ya tambaye ta "Mammy wai ina Daddy ya kwana?", saboda har goman safe Khamis bai fito daga dakin Maryam ba, "Ban sani ba", ta ba shi amsa a fusace, shiru ya yi, don tsaf zata iya huce haushinta a kansa.

  Khamis kuwa, yana can ya susuce wurin wurin Maryam da ke ta shagwabewa tana kukan kissa, lallaɓa ta ya yi sannan ya kimtsa jikinsa ya fito.

  Kai tsaye ɗakin Aysha ya nufa yana ta washe baki, ko kusa bai lura da yadda ta yi ramar dare ɗaya ba, saboda ƙagare yake ya koma wurin Maryam. Bayan sun gaisa ne ya ce "Aysha ki hanzarta gama girki saboda Maryam bata ci komai ba sai ruwan Tea".

  Kallon sama da ƙasa ta yi mashi, sannan ta ce "Shi ruwan Tea ɗin wa ya girka mata shi a ɗazu?".

  "Ni na girka mata" ya bata amsa a taƙaice, saboda ya lura da biyu ta yi maganar.

  "Toh yanzu ma sai ka shiga kitchen ka girka mata na rana, don ni ba zan yi ba.

  Idan aka ce Aysha na da wani ɓoyayyen hali marar kyau Khamis ba zai yadda ba, amma sai gashi ta nuna mashi zahirin rashin mutuncin da take ɓoye da shi, wanda idan shima ya fito mata da nashi, abin ba zai ma kowa daɗi ba.

  Cikin ƙunar rai ya dube ta "Aysha, butulci ne abin da zaki saka mani da shi ko, toh nagode", bai maida hankali akan abin da take cewa ba ya fice daga ɗakin.

  Sababi ta riƙa yi ita kaɗai, daga bisani nemi malamarta Zuzee a whatsApp, Vn mai ɗauke da tabbacin ta yi abin da ta ce ta aje mata. Saboda a jiyan dangin Ayshar sun ce ta yi ma Amarya girkin kwana bakwai, amma Zuzee ta ce bai yiwuwa ta kwanar mata da miji, kuma don daɗi ya mata yawa a yi mata girki.

  Zuzee na zuwa ta yi mata reply da "Kin mani daidai Tawan"..\u270d\ud83c\udffc

Comments

0 comments