Makalu

Sabbin Makalu

View All

CIKIN BAURE: Babi na Hudu

 • Asma'u na cikin saƙawa da kwance yadda zata sake guje ma Abbas a wannan karon ne ta ji dawowar sa daga sallar la'asar. Zumbur ta miƙe tare da kabbara sallar ƙarya a kan carpet, saboda yana shigowa ɗakin zai fara cika ta surutansa da ta tsana. Wani shashe na zuciyarta ne ya ankarar da ita cewar "Idan fa ya ga kina sallah to zai ƙwallafa rai a kanki", ranta ba daɗi ta lumshe idanu, lokaci ɗaya kuma ta kawar da kai ga tunanin zuciyar ta cigaba da sallah, domin ta fi gamsuwa da hakan.

  Sallamar da Abbas yake yi ma Asma'u ta sha ban-ban da wadda yake yi ma game garin mutane, domin ruhinsa da ƙarƙarshin zuciyarsa sun gama gamsuwa da ba ɗaya take da su a wurinsa ba. Cikin tattausan salo mai kama da farkon waƙa ya yi sallama a cikin ɗakin kamar yadda ya saba, wani irin farinciki ne ya mamaye shi lokacin da idanuwansa suka dira a kan Asma'u yayin da ta yi sujuda.

  Kafe bayanta ya yi da idanu, har a lokacin yana tsaye a bakin ƙofa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, wadda take tattare da kusancin cikar muradinsa a matsayinsa na sabon ango.

  Asma'u kuwa duk da zuciyarta ba a natse take ba, amma jikinta na bata kallon ta yake, cike da tsanarsa ta miƙe daga tahiyar farkon data gama, ɓangare ɗaya kuma ƙasan ranta cike da ƙuna akan wasa da sallar da take, wadda kuma tsananin ƙiyayyar Abbas ce sila. Takunsa ta ji ya wuce bedroom, daga can ta tsinkayo muryarsa mai cike da nishaɗi yana waƙar Ado Gwanja ta kujerar tsakar gida, kuma lallai ta san ganin tana sallah ne ya sa shi wannan waƙar, ƙwafa ta yi a fili gami da cigaba da sallah, lokaci ɗaya kuma tana ta saƙe-saƙen yadda zata kufce mashi.

  Tana cikin tahiyar ƙarshe ne ya fito falon ya zauna, sai dai bayan da ta ba shi ne ya sa bata iya tantance kalar zaman da ya yi ba har sai da ta sallame tare da yin addu'a kana ta juyo.

  Zaman da za'a iya kamanta shi da kwanciya ya yi a kan kujerar one seater, kansa da ke kwance a bayan kujerar ya ɗago lokacin da ya ji alamun ta gama sallar, idanunsa dake lumshe ya buɗe gami da gyara zama, lokaci ɗaya kuma ya sakar mata ƙayataccen murmushi kafin ya ce "Har kin gama?", fuskarta dama a murtuke take, cikin ɗacin rai ta ba shi amsa "Umm", lokaci ɗaya kuma ta yakice hijabin da ke jikinta, take cikakkiyar surarta mai rikita tunanin Abbas ta bayyana. Wani irin shauƙinta ne ya fizgi Abbas ɗin, kallo mai ɗauke da zallar son ta ya cigaba da yi mata. Ita kuwa kallo na ɗaya daga cikin abin da ta tsana,
  don haka ne ta ƙara shan mur ta bi ta gabansa zata wuce, ji ta yi ya riƙo hannunta mai taushin gaske tare da ɗan matsa shi da ƙarfi, a fusace ta juyo da nufin yarfa shi, sai dai tana ganin idanunsa sun sauya ta kasa magana saboda faɗuwar da gabanta ke yi, "Ina zaki je?", ya tambaye ta cikin sarƙewar murya.

  Amsa ta ba shi da "Hijabi zan kai a ciki", kallon hijabin dake ɗayan hannunta ya yi sannan ya maida dubansa ga fuskarta da ba annuri ko kaɗan a cikinta "Ok, ina jiran ki", ya faɗa bayan ya sakar mata hannun da take ta son ƙwacewa, da idanu ya raka ta har ta shige bedroom ɗin.

  A hankali ya ɗauke kansa gami da sake kwantar da shi a bayan kujera, rufe idanunsa ya yi, cikin ransa kuma yana hasaso yadda zai kasance tare da ita.

  A ɓangaren Asma'u kuwa zama ta yi turus a gefen gado, "Anya wannan hanyar ta kwana-kwana zata fidda ni?", tambayar da ta yi ma kanta kenan, don ko shakka babu ramin ƙaryarta ya ƙure, a can baya ta hana Abbas kanta ta hanyar yin ƙaryar period, toh yanzu kuma da ta yi mashi ƙaryar ɗaukewar sa wace ƙarya zata yi mashi idan ya buƙace ta?.

  Da zuciyarta ta saba magana, don haka ne wani sashe na cikinta ya ce "Kawai ki fito fili ki bayyana ma Abbas ba kya son shi, ta haka ne kawai zai shafa maki lafiya".

  Kai ta girgiza, domin Abbas na da kwarjinin da ke sakar mata da guiwa a duk lokacin da ta so yi mashi rashin mutunci, kuma ta wani ɓangaren bayyana mashi ƙiyayya a zahiri ba zai yi ma Aunty da ta ɗauka tamkar uwa daɗi ba, sai dai kuma a ganinta wannan hanyar ce kaɗai burinta na son rabuwa da shi zai cika.

  Cikin ɗacin rai ta kwanta a gefen gado domin samar ma kanta mafita.

  Ƙaddara kenan! Da ace da Nas ta haɗa ta, da yanzu wani labarin ake ba wannan ba. Kowace mace burinta shi ne ta auri wanda take so kuma yake sonta ta yadda za su ba juna kulawa ta musamman, to ita ta samu kulawar, sai dai ba a wurin wanda take so ba, don tun kafin ta auri Abbas ta fahimci shi mai kulawa ne, sai dai kasancewar sa ba shi ne zaɓinta ba ya sa ta kasa gamsuwa da kulawar da yake bata. .

  A ranta ta ce "Me ya sa ƙaddara ta nufe ni da haka?", don yadda take jin tsanar Abbas a ranta ko ta ce zata ɓoye ta san dole wata rana ta fito fili, bare ma ba zata iya ba. Lamo ta yi a kan gadon, lokaci ɗaya kuma tana jiyo muryarsa a falo yana waya, "Banza" ta faɗa a ranta, don ta san bai ƙi ta fito falon ba.

  Bayan ya gama wayar ne ta ji yana kiranta "Asma'u", shiru ta yi kamar mai bacci, aikuwa sai ga shi ya shigo bedroom ɗin, daga bakin ƙofar da yake tsaye ya ce "Baccin yamma?", sai da ta turo baki sannan ta ce "Eh", sake cewa ya yi "In zo mu yi tare?", ta san zaulaya ce, amma don ta nuna mashi bata ra'ayin shi ta ce "A'a", dariya ya yi wadda kullum take sa ta tambayar kanta "Anya Abbas na fushi?", domin ta gwalashe shi sau ba adadi, amma bai taɓa nuna mata rashin jin daɗinsa ba.

  Idanunsa akan cikakkiyar surarta ya shigo ɗakin ya zauna a kan side locker sannan ya ce "Kada ki yi bacci yanzu, anjima ki kasa na dare".
  "Toh me ye ruwanka idan na kasa", ta faɗa a ranta, a zahiri kuma gyara kwanciyarta ta yi ta juya mashi baya.

  Ya ji ba daɗi a ranshi, amma sai ya basar ya ce "Ni kuwa ko na yi laifi ne ake fushi da ni?", duk da ba yau ta fara yi mashi irin haka ba, tamkar kurma ta koma mashi, murmushi mai sauti ya yi "Ok, toh fita zan yi yanzu tunda ba kya son magana. Ko na turo maki Zulaiha ta taya ki hira kafin na dawo?", idanunsa akan hips ɗinta ya ƙarashe maganar. Duk ƙannen Abbas ba wanda Asma'u ta tsana kamar Zulaiha, saboda yarinya ce mai surutu, ita kuma Asma'u yadda take jin ta a ƙuntace bata buƙatar duk abin da zai takura ta "A'a" ta faɗa a taƙaice.

  "Uhm!", ya ce, daga bisani ya kuma cewa "Mu je ki rakani toh", hararar shi ta yi duk da baya ganinta ta ce "Ni fa bana jin daɗi, kawai a sauka lafiya".

  Ba tare da ya ce komai ba ya juya, har ya kai bakin ƙofa kuma ya dawo, duƙar da kansa ya yi saitin kunnenta ya ce "Ƙirar jikinki na ƙayatar da ni. Ki ƙara gyara shimfiɗa kafin na dawo", bai jira jin me zata ce ba ya juya ya tafi, ƙasan ransa kuma cike da jin ba daɗi a kan rashin walwalarta.

  Kai tsaye wurin da suke siyar da block ya nufa. Wuri ne babba da ke cikin wata sabuwar unguwa da yanzu mutane ke ta gine-gine acikinta, filin da suke sana'ar na babban abokinsa ne mai suna Abdull, amma jarin na su ne su biyu suka haɗa guiwa domin cigabansu, kuma daidai gwargwado suna samun customers saboda babu ha'inci a block ɗinsu.
  A gefen yashin dake tule a wurin ya faka mashin ɗinsa saboda ba rana a wurin, kai tsaye rumfa ya nufa, inda Abdull yake zaune yana jiransa.

  "Ango ka sha ƙamshi", Abdull ya faɗa cikin sigar zaulaya, dariya Abbas ya yi gami da faɗin "Tukunna dai",

  A kan ƙatuwar tabarmar da Abdull ke zaune shi ma ya zauna, hannu suka miƙa ma juna, bayan sun gaisa ne Abdull ya dube shi a tsanake, "Na ce ango ka sha ƙamshi, kai kuma ka ce tukunna dai, anya Amarya bata yi maka rowa ba?"

  Dariyar Abbas ya yi "Wai da gaske haka na ce?", Abdull ya ce "Zan maka ƙarya ne", ɗan shiru Abbas ya yi, daga bisani ya sa hannu ya ɗan bubbuga kansa, lallai damuwar son kasancewa da Asma'u ta fara fitowa fili, "Wallahi ban san haka na ce ba", dariya su duka suka yi. Abdull bai tambaye shi ya zamansa da Amarya ba, amma dai ya gargaɗe shi da ya sanya ma bakinshi linzami.

  Ita ko Gimbiyar tana jin tashin mashin ɗin Abbas ta taso ta garƙame gidanta da Key. Tana komawa cikin gidan ta yada zangonta a falo, maganar "Ki ƙara gyara shimfiɗa" da Abbas ya faɗa mata ce ta so hana ta saƙat, sai dai tana tuna Nas ta manta da wannan magana, kwantar da kanta ta yi a hannun kujerar da take zaune ta cigaba da tunanin sa mai kashe mata jiki. Tabbas Asma'u ta gamsu da cewar an halicci zuciyarta ne kawai don Nas, shi ya sa take ambatar sunansa a kowane bugawa da take.

  Bubbugar da ake ma ƙofa ce ta yi mata buƙulun karɓar zazzafar kiss a wurin Nas, lokacin da zuciya ta hasaso mata gatanan ta rako shi a bakin gate ɗin gidansa. Ran Asma'u a ɓace ta fita don yadda ake buga ƙofar kai ka ce raba ta da garkuwarta za a yi.

  "Waye?" ta tambaya cikin ɗaga murya, daga can Zulaiha ta ce "Ni ce", kamar zata maƙaro ta ce "Kuma shi ne ba kya iya knocking a hankali, ya aka ce?", daga can ta ce "Ba komai", Asma'u ta ce "Toh je ki yi wasa".

  Maimakon muryar Zulaiha sai ta ji muryar babba tana cewa "Amarya baƙi ne fa, ko angon na ciki mu koma inda muka fito?".

  Ras! Gaban Asm'u ya faɗi, don duk wanda ya ji yadda ta yi ma Zulaiha magana zai fahimci bata son yarinyar, buɗewa ta yi, suna yin arba da matashiyar matar ta shiga naɗe tabarmar kunya da hauka, inda ta dubi Zulaiha da ke ta maƙyaftai ta ce "Ke haka ake knocking kamar za'a ɓalle ƙofa?", matar da shekarunta ba zasu wuce ashirin da biyar ba ta bata amsa cikin zaulaya, "Ni ce fa na buga ƙofar, saboda idan kun yi bacci ke da angon ku farka", wayancewa Asma'u ta yi tana dariya, don tun ba a je ko ina ba ta ji matar ta shiga ranta, cewa ta yi "Wane bacci kuma da yamma, bayan angon ma tuni ya yi ficewarsa". Cikin gidan suka shiga suna dariya.

  Iso Asma'u ta yi mata a ɗan ƙuƙut ɗin falonta, cikin ranta kuma tana ganin yadda matar take ƴar gayu zata iya raina mata, zama suka yi a kujera suna fuskantar juna, Zulaiha kuma a bakin ƙofa ta ja tunga, cike da kulawar ƙarya Asma'u ta dube ta "Nan zaki tsaya?", girgiza kai ta yi, "Ai tafiya zan yi", ɗan cira kai Asma'u ta yi "Ok", matar ce ta ce ma Zulaiha "Toh ki saki labulen kafin ki tafi, kada sauro ta shigo musu ɗaki.

  Ciki Zulaiha ta shigo ta tsaya a hannun kujerar da matar ke zaune, kallon ta Asma'u ta yi, lokaci ɗaya kuma ta maida dubanta ga matar, cikin ranta tana jin kamar ta kora Zulaihar.

  Gaisawa suka yi, anan matar ke faɗa ma Asma'u tana ɗaya daga cikin maƙwabtansu, gidanta ne a farkon layin, na Ams'u ne kuma na huɗu, Abin da ya sa bata zo walima ba itama bikin ƙanwarta aka yi, kuma Abuja aka akai amaryar, basu su dawo ba sai jiya.

  Allah ya sa Alkhairi Asma'u ta yi ma matar, daga nan kuma ta shiga tunanin gidan farko a layin, ta san gidan sosai saboda shi ya zama zarra a cikin gidajen layin, gate ɗin gidan kaɗai abin kallo ne, bare kuma cikinsa, kuma a yadda matar ta ci Leshi ta tabbata daga gidan ta fito. Asma'u na son tarayya da mutane masu kuɗi, don haka ne ta ƙara sakar mata fuska suka yi ta hira kamar sun san juna, cikin ƙanƙanen lokaci Asma'u ta ji damuwarta ta ragu.

  Zulaiha ce ta katse musu hirar inda ta dubi matar ta ce "Aunty Zainab na tafi", sai a lokacin Asma'u ta san sunan matar, bayan Zulaiha ta fita ne Asma'u ta dube ta "Sunanki kuwa ɗaya da mamanmu, amma ta rasu", cike da jimami Zainab ta ce "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata".

  Kafin Asma'u ta ce Amiin wayar Zainab ta ɗauki ruri, Idanun Asma'u akan wayar mai masifar kyau lokacin da Zainab ta dubi fuskar wayar ta ce "Abban Khalil, ba dai ka dawo ba".

  A kunne ta kara wayar, daga can cikin wayar aka riga ta magana "Zee na dawo fa", daga inda Asma'u take tana jin maganar.

  Ɗan marairaice fuska ta yi "Oh, yanzu na fito fa Abban Khalil", daga can ya ce "In dai kun gaisa da amarya ai shikenan, ko kin fi son na zauna ni kaɗai kamar maye", dariya Zainab ta tuntsure da ita, cikin zaulaya ta ce "Toh miye idan ka zauna kai kaɗai?", daga can ya ce "Au haka kika ce, bari na koma toh", dariya ta yi "Sorry, ganinan Abbanmu".

  Yadda ma'auratan suka yi waya cike da nishaɗi ne ya birge Asma'u, a ranta sai ta ji da ma ita, toh ƙaddara ta haɗa ta da wanda bata marari bare su sanya juna nishaɗi, da Nas ne kuwa abin da ya fi haka ma sai sun yi.

  Tashi Zainab ta yi da nufin tafiya. Chinchin Asma'u ta ce ta jira ta kawo mata, Cewa ta yi "A'a" saboda yaron cikin da ke gare ta, har bakin ƙofa Asma'u ta raka ta, a wannan karon bata rufe ƙofa ba saboda gudun sake tafka abin kunya.

  Tamkar da farincikinta Zainab ta tafi, a kan rijiya ta zauna tana jin ba daɗi a ranta, a fili ta ce "Allah ka sani bana son Abbas, don tsarkin mulkinka ka raba ni da shi tun kafin ƙiyayyarsa ta sa na saɓa maka".

  Tana nan zaune har magarib ta doso, banɗaki ta shiga ta kimtsa jikinta, tana fitowa ta shige ɗaki tunda ba sallah take ba.

  Wayarta da har yanzu bata rabu da ɗaurin gaba da robalee ba ta kalla, a zahiri ta ce "Da Nas nake aure ai iPhone zan riƙe ba wannan jagwal ɗinba", domin wayar Zainab ce ke ta yi mata gizo a idanu.

  Tana cikin jujjuya ta ne ta kufto ƙasa ta watse, aikuwa da ƙyal ta gano M card da sim ɗinta da suka ɓuya a ƙarƙashin kujera, tana haɗa komai kuwa ta yi wurgi da ita akan kujera.

  Abbas na dawowa ya tambaye ta "Lafiya wayarki a kashe?" duban wayar ta yi ta ce "Toh faɗuwa ta yi fa", daga tsayen da yake ya miƙa hannu ɗauki wayar, yana danna power ta kawo kuma ta ɗauke. Dudduba ta ya shiga yi, lokaci ɗaya kuma ya ce "Wannan waya rabuwa da ita shi yafi, Insha Allah zan chanja maki mai kyau ƴar yayi", idanunsu sarƙe da na juna ya ƙarashe maganar, kasantuwar akwai wutar Nepa. Waya na ɗaya daga cikin burikan Asma'u, murmushin jin daɗi ta yi wanda har ya bayyana a fuskarta, Abbas ya ji daɗin haka, wayarshi ya fiddo aljihu ya miƙa mata "Aunty ce dama ta kira zaku yi magana".

  Karɓar wayar ta yi tare da kara ta a kunne, don har ya yi dialing number, tashi ya yi nufi kitchen, ita kuma cike da jin daɗi suka yi waya da Aunty, anan kuma Aunty ta ƙara yi mata nasihar ta yi ma mijinta biyayya, domin Aljannarta na ƙasan ƙafarsa. Da Aunty ta san yadda Asma'u ta yi nisa a ƙin Abbas da bata ce ta yi mashi biyayya ba, bayan sun gama warya ne a ranta ta ce "Hanyoyin Aljanna na da yawa, idan ban same ta a ƙafar Abbas ba ai zan same ta a ƙafar Nas", domin tuntuni ta tsara irin biyayyar da zata gwada mashi.

  Abbas na dawowa ɗakin ta bashi wayar, hannunta da wayar ya riƙe "Wato kin ji muryar Aunty sai farinciki kike ko?", ranta sal ta ce "Toh na yi kewarta ai", ya ce "Tun yanzu", ta ce "Eh mana", ya ce "Kina da aiki, toh kuwa ke da zuwa ganin ta sai kin shekara".

  Dariya ta tuntsure da ita, ita da ba zama ta zo yi gidansa ba wace shekara kuma, bayan ya gama tsokanar ta ne ta miƙe da nufin kawo mashi abinci, ledar da ya manto a cikin but din mashin ɗinsa ya tuna, cewa ya yi ta bar abincin ya yi masu tsaraba.

  Ita kuwa daɗi ta ji, don abincin da ta yi ba wani daɗi ya yi ba, saboda ba wani girki ta iya ba, da rana ma da ƙyal suka ci abincin saboda miyar ta ƙone, kuma matsalar rashin iya girkinta sai da Aunty ta ce taje ta koyi girki, amma ta ƙiya saboda bata ɗauki Abbas miji ba.

  Nama ne da fura ya yi masu tsaraba, sosai suka cika cikinsu, suna gamawa Abbas ya zauna gefenta a kan kujera two seater. Wayarshi ya ɗauka tare da kunna musu film ɗin jarumi Prabhas, wanda Algaita records suka daɗe da fassara shi da sunan (Mai taɓargaza), sosai film ɗin ya daki zuciyar Asma'u har ta yi kuka, shi ma Abbas jikinsa ya mutu liƙis, saboda mutuwar da mahaifiyar jarumin ta yi ba tare da sun haɗu da juna ba, kuma abin da ya fi sosa musu zuciya da labarin film ɗin ya kasance da gaske.

  Duban Idanun Asma'u dake ta fitar da ƙwalla Abbas ya yi "Da ma baki kalla ba ko?", ya tambaye ta cikin raunin murya, kai ta ɗaga tamkar ƙaramar yarinya "Uhmm", sai da ya haɗe wani abu marar daɗi sannan ya kai hannunsa ga fuskarta ya cigaba da goge mata hawaye, lokaci ɗaya kuma ya na faɗin "Rashin uwa ba daɗi, shi ya sa nake tausayinki, don ma Allah ya maye maki gurbinta da Aunty", sosai wannan maganar ta ƙara karya zuciyar Asma'u, tabbas Aunty tamkar uwa take a wurinta, amma haɗa ta aure da Abbas ya sa lokutta da dama tana jin haushinta, sai dai girmanta da take gani ne ya sa ba zata iya nuna mata ba.

  Abbas kuwa daga sharar hayawe ya ji yana neman rasa nutsuwarsa, itama ta lura da haka, aikuwa cikin ƙanƙanen lokaci hawayen Asma'u suka yi ɗaukewar famfo.

  Gabanta na wata irin faɗuwa ta zame jikinta daga nashi ta miƙe, ruƙo hannunta ya yi tare da tambayar ta cikin shaƙaƙƙiyar murya "Ina zaki je Asmy?", kamar zata yi kuka ta ce "Zan je in kwanta", cewa ya yi "To mu yi wanka mana", kai ta girgiza "A'a", bai wani matsa mata ba, duk da wankan nata na da kyau. Bedroom ta koma ta kwanta cikin doguwar rigarta ta bacci, cikin ranta kuma tuni ta samu mafitar da zata ji da Abbas, domin ƙaryarta ta ƙare.

  Abbas kuwa cikin ƙanƙanen lokaci ya yi wanka gami da shirinsa na bacci. Cike da farincikin yau zai kasance ango ya maido Asma'u a jikinsa bayan ya kwanta a bayanta, Asma'u bata bari ya yi nisa ga abin da ya soma yi mata ba da dakatar da faɗin "Period fa nake".

  Take kuwa ya wartsake ya ce "Me?", don zuciyarsa na faɗa mashi ba daidai ya ji ba, amsa ta bashi da irin maganar da ta yi da farko.

  Sake tambarta ya yi " Dama bai ɗauke bane?", girgiza kai ta yi "A'a sabo ne na fara", ya ce "Wancan fa?", kasa bashi amsa ta yi, sake cewa ya yi "Asma'u kin yi shiru".

  Shawarar da tuni ta yanke ta faɗa mashi, cewar ƙarya ce ta shirga mashi, don ba wani period ɗin da take a can baya.

  Tamkar zai yi kuka ya ce "Saboda me Asma'u, me na yi maki da kika yi mani wannan horon?", aranta ta ce "Aure na da ka yi shi ne laifin", a fili kuma ta yi shiru, jijjigata ya yi "Na ce me na yi maki?", da ɗan faɗa-faɗa ya ƙarashe maganar, wanda hakan ya haifar mata da tsoro a zuciya, kamar zata yi kuka ta ce "Ni fa tsoro nake ji", ya ce "Tsoron me Asma'u?" duk da ya fahimci manufar maganarta, hannu ya sa ya dafe kai, cikin ranshi yana jin kamar ya yi kuka. Tabbas ya yi jan shiri a daren aurensu, amma son zuciya na Asma'u ya wargaza mashi, take ya fara tuna yadda take ta nuna mashi halin ko in kula, zuciya ce ta ce mashi "Ko dai bata son auren?" da sauri ya girgiza kai, don yadda yake mutuwar son ta ba zai yi wannan fata ba, ita kuwa sai maƙyaftai take a cikin duhu, ji ta yi ya kamo hannunta cikin duhun "Asma'u ki nutsu, ki cire tsoro a ranki, insha Allah zaki same ni mai tausayawa a gare ki" sosai ya danne fushin dake ransa ya cigaba da lallashinta.

  Komawa suka yi suka kwanta, sai dai a wannan karon bai raɓi jikinta ba, duk yadda ya so yin bacci amma ya kasa. Itama neman baccin ta yi ta rasa, don bata san ya zata yi ba.

  Gani ta yi ya sauka akan gadon ya koma falo, baki ta taɓe ta gyara kwanciyarta.

  Shi kuwa tunda ya zauna a kan kujera yake ta ƙwafa a ransa, domin baƙincikin da Asma'u ke son cusa mashi ya fara tasiri a ransa, tsawon kwana biyar kenan da aurensu, amma ya fahimci ko kusa bata son ya raɓe ta, tun bai jin komai a ransa, har ta kai ga ya fara ji, kawai dai yana ɓoye mata ne don baya son ƙorafi.

  Amsar da ta bashi ce ta dawo mashi a rai wadda ta ce "Tsoro nake ji", tambayar kansa ya yi "Tsoron me?", saboda ya san ba ango bane kaɗai ke mararin ranar daren farko ba, wani sashe na zuciyarshi ne ya fara cusa mashi yi ma Asma'u uzuri saboda ƙarancin wayewarta da kuma yarinta, da yake shi mai sauƙin kai ne sai ya karɓi uzurin da zuciya ta kawo mashi, ta haka ne ya rage jin haushinta, ɗaukar ma ranshi ya yi zai cire mata tsoro da kalar na shi salon wanda yake ji kamar ya tashi a yanzu ya fara gwada wa.

  "Toh yanzu ma me zan mata?", ya tambayi kanshi, saboda ya san da wahala ta bari ya raɓi jikinta, shi kanshi a yadda yake yanzu ba zai iya zuwa inda take ba, tunda ko ya je ba zai samu abin da yake so ba, zamewa ya yi ya kwanta a kan kujerar.

  Haka a kwanakin ya riƙa nesa da Asma'u don baya son ransa ya ɓaci, abin mamaki sai ya lura hakan na sanya ta nishaɗi, sosai ya shiga ruɗanin da ya hana zuciyarsa saƙat, har ta kai ga ko fita ya yi baya iya taɓuka komai saboda fargabar kada ace Asma'u bata son shi.

  Ita kuwa a ranar gama period ɗin ne ta kira babbar ƙawarta Khadija a waya, nan ta ke labarta mata komai da kuma neman mafita, don har a ranta bata ƙaunar Abbas ya kusance ta, maimakon Khadija ta bata shawarar da take so, sai ta shiga yi mata faɗa akan kada ta yi ma kanta asarar nagartaccen miji, domin a wannan zamanin samun miji mai natsuwa da tsoron Allah kamar Abbas sai an tona, sannan kuma ta tsoratar da ita faɗawa cikin fushin Allah, domin duk matar dake hana mijinta kanta to tana cikin tsinuwar Allah da ta mala'ikunsa, aikuwa da yake Asma'u na tsoron Allah sai jikinta ya yi laƙwas. Sosai ta ɗauki nasihar, amma ita da son Abbas har abada, kuma batun zama da shi bata yi wannan alƙawarin ba.

  A nashi ɓangaren ma dawowa ya yi da sabon salon kula ta a daren, tun tana zamewa har ta kai ga ya samu abin da yake marari a wannan dare mai albarka a wurinsa..

  DA FATAN ZAKU GAFARCE NI BISA GA JINKIRIN DA AKA SAMU, HAKAN YA FARU NE SANADIN SAUYIN DA LABARIN YA SAMU, INDA SALON LABARIN YA TASHI DAGA HANNUN ASMA'U YA DAWO WURIN MARUBUCIYA. Da fatan zaku gafarce ni

  @Hadiza Isyaku

  @HazaƙaWriersAssociation

Comments

1 comment