Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » KULA DA KAYA: Gajeren Labari

KULA DA KAYA: Gajeren Labari

 • Cike da kaɗuwa nake bitar takardar da na kasa gazgata baƙin saƙon da take ɗauke da shi. Jiki a mace na juya akalar ganina zuwa ga mijina da muke tsaye a tsakar gida, "Menene haka Aminu?", a taƙaice ya ce "Saki biyu ne". Haƙiƙa zuciyata ta jijjiga bisa ga amsar da ya ba ni, domin ba tun yau yake razana ni da saki ba. Jiƙaƙƙun idanuna na lumshe, don na san da wahala Aminu ya juri zama da ni, kasantuwar na daɗe da lalurar ciwon sanyin da na kasa yaƙar sa, saboda makaman yaƙin suna hannunsa.
  Kuma halinsa na rashin ba mace ƴancin faɗar albarkacin bakinta ya sa ba zan iya faɗa mishi rashin siya mani audugar mata na tsawon shekaru biyar ne ya haifar mani da ciwon ba, domin bai taɓa ba ni gudunmuwar da zan tarbi baƙona na kowane wata ba, a cewarshi, ba zai iya adashen da ba ranar kwasa ba. Ni kuma ba sana'a bare na riƙa siye, sai dai na riƙa amfani da tsumma wanda shi ne sanadin lalurata.
  Tsaurin halin Aminu bai hana ni gwada sa'ata akan ya ƙara haƙuri na cigaba da neman magani ba, amma sai ya ce "Ni fa ina a kan bakana, aure ma zan yi". Yana rufe baki ya maida takunkuminsa a fuska, wanda nake DA yakinin yana sanya shi ne domin to she hancinsa daga shaƙar ƙarnin ruwan da nake fitarwa a dalilin ciwon sanyi.
  Gaskiya yau kishi ya kai haƙurina a magaryar tiƙewa, sannan ya ƙara hasko mani matsalolin Aminu da sun fi shurin masaƙi, domin yadda yake sarrafa mace kai ka ce ba mai ilima ba. Kodayake, mu daina alaƙanta tauye haƙƙin mace da rashin ilimi, akwai marassa aiki da iliminsu irin Aminu, waɗanda basu ɗauki mace mutum ba.
  Duk wani cigaba gami da samuwar ƴanci gani yake shi kaɗai ya shafa, shi ya sa har yanzu ban mallaki katin zaɓe ba, a faɗarshi ba abin da zan yi da shi.
  Bayan ficewarsa ne na haɗa kayana gami da kama hannun tilon ɗana Salim muka nufi gidan Kakata Hajja, wadda ita kaɗai ta rage mani. Sosai ita da surukarta da suke a gida ɗaya suka jajanta mani. Kawuna Lamis kuwa zakkarsu ya fita. Daga tsayen da yake a tsakar ɗaƙin Hajja ya dube ni cikin fushi "Kin kashe aurenki kawai don ki ɗora mana jidali".
  Hajja ce ta shigar mani faɗan, inda ta ce "Kai Lamis! Ko ni tsohuwa ba zan iya haƙurin da Luba ke yi a gidan Aminu ba, don haka ka shafa mata lafiya".
  "Shikenan Hajja! Ni dai bani da ƙarfin ciyar da ita, kuma dole ta maida mishi ɗanshi tunda ita kaɗai muka ba shi".
  Kawu Lamis na da ƙarfin faɗa aji saboda shi ke ɗaukar ɗawainiyar gidan, shi ya sa Hajja ta kasa hana shi ɗaukar Salim da nufin maida ma Aminu. Da gudu na bi bayanshi har waje ina faɗin "Don Allah Kawu Lamis ka dawo mani da yarona", ko kusa kukana bai sa ya tausaya mani ba, sai ma ya jefe ni da mugun kallo tare da burka mashin ya tafi.

  Mutane na kiran dare da mahutar bawa, toh gaskiya ni gajiyar da ni ya yi, domin duk ƙwarewar bacci a sata, amma a dararen makon bai samu sa'ar sace ni ba. Kwana nake kukan kewar Ɗana da bayan shi ban sake ko ɓatan wata ba.
  Ƙasa da mako biyu ciwo da yunwa suka sauya kamannuna, gashi Kawu Lamis ya kasa ciyar da ni, bare na sa ran magani a wurinsa.
  Zaune nake a ɗakin Hajja kaina haɗe da guiwa, shigowa ta yi ta zauna gefena duk da ƙarnin da nake, "Luba, jikin ko garin?", a hankali na ɗago kaina da ke ɗauke da kayan damuwa.
  Sai da na matse ƙwallan da ke cike da idanuna sannan na yi mata tambayar da ke ta nuƙurƙusar zuciyata, "Hajja! Ta ya bazawarar da bata da abin yi zata kula da kanta?", a dagule ta ba ni amsa, "Ta hanyar neman na kanta", na ce "Wace hanya ce?", ta ce "Hanyoyin biyu ne".
  "To a ciki wacce zan bi?", domin yunwa da ciwo ba su da dangantaka da kowa, bare na sa ran rangwamen su, "Ki nemi halal ko da ƙarfinki zai ƙare". Lallashi da shawarwari ta ba ni, hakan ne ya rage zafin wutar da ke ci a cikin zuciyata.
  Hannuna ta kama muka fito. Matar Kawu Lamis da ke zaune a ƙofar ɗakinta tana ganin mu ta haɗe rai, kasantuwar itama abinci da lalurata sun haɗa mu faɗa. Hakan kuwa ya ba ni ƙarfin neman na kaina.
  Wankin kuɗi na fara, kuma daidai gwargwado kuɗin da nake samu suna biyan buƙatuna har na siyi audugar mata, don aganina audugar ce matakin farko na yaƙar ciwon sanyi kafin na ga likita. hakan ya sa wankina ya fi ƙarfi a ƙarshen wata.
  Akwai matar da ke yawan ce mani na daina wankin kuɗi saboda rama da kuma ciwon jikin dake yawan damuna. Ni kam idan akwai abin da ya fi wanki wahala zan yi domin rufin asirina, ce mata na yi "Idan ban yi wanki ba da me zan tarbi baƙona na kowane wata?".
  Cike da zaulaya ta ce "Kai ni har zawarawa sun fara karakaina?.
  Fahimtar da ita azancina na yi cewar jinin al-ada nake nufi, sake cewa ta yi "Na me ki wahalar da kanki da siyen auduga alhalin ba ƙarfi gare ki ba?".
  Labarta mata tsaka mai wuyar da rashin amfani da auduga ya jefa ni na yi. Sosai ta fahimce ni, amma sai ta nuna mani amfani da audugar ma yana da matsala madamar ba tsafta. Hanya ta ɗaura ni mai sauƙin kashe kuɗi, ina komawa gida na samu zannuwana da basu ji jiki ba na farke. Kowane wata da waɗannan ƙyallaye nake amfani, ina gamawa zan yi musu wanki na musamman gami da goge su na adana. A nan na fahimci baƙon kowane wata tsafta ya fi buƙata.
  Zawarawa kuwa ko da na fahimci farautar mutuncina ke kawo mafi yawansu, sai na rage kula su, domin zawarci sai da taka tsan-tsan.

  ****
  Kwanci tashi asarar mai rai, domin har na cika wata goma a gida. Rayuwar kuma sai godiyar Allah, saboda ba kowace rana ce Juma'a ba. Salim kuwa sai da ya cika shekara ɗaya sannan Aminu ya kawo shi. Wannan zuwa na Salim ne kuma ya ba Aminu damar kutso kai a cikin rayuwata, saboda kullum sai ya kira ni a waya wai na ba yaronshi, ni kuwa na daɗe da gane idan kare na son ɗaukar takalmi da shinshinar sa yake farawa.
  A ranar da ya zo ɗaukar Salim har cikin gida ya shigo muka gaisa, sosai na yi mamakin yadda ya zarce ni rama.
  Da daddare ina cikin shafe jikina da man zafi kiransa ya shigo wayata, ɗaga kiran na yi, muna gaisawa ya fara surutan da suka sa jikina karkarwa, Tambayar shi na yi "Ina Amaryarka da zaka ce sukuninka na hannuna?", a marairaice ya ce "Tana gidansu", na ce "Ka zama auri saki", ya ce "A'a Luba, ita ɗin ba matar rufin asiri ba ce", na ce "Ashe?", duk da na san ƙarfe ɗaya baya amo shi kaɗai.
  Muna gama wayar na faɗa ma Hajja ƙudurinsa, ce mani ta yi "Ai wuƙa da nama na hannunki", na ce "Hajja kome! koma ma halinka fa?", ta ce "Aa toh!".
  Bayan mako ɗaya, dayyamma ina zaune a tsakar gida sai ga wayarshi wai na fito. Rakuɓe na same shi a soro kamar zakaran da ruwa ya daka. Bayan mun gaisa ne na faɗa mishi ba fa zan koma gidansa ya ƙarasa kashe ni ba. Guiwa biyu ya durƙusa yana faɗin "Ki taimake ni Luba! Na miki alƙawarin nemo miki lafiyarki da na zama silar raba ki da ita, kuma zan ba ki kariyar da ba zaki sake rasa ta ba", kallon sama da ƙasa na yi mishi na ce "Kamar da gaske".
  Magiya ya shiga yi, sai da na ga ƙwalla a idanunsa sannan na yi mishi alamun ya tashi, "Toh zan yi nazari".
  Cikin gida na dawo, tun kafin na zauna wani yaro ya biyo ni da babbar leda in ji Aminu. Audugar mata ce a ciki guda goma shabiyu.
  Gaskiya ina son Aminu! Sai dai tsoron koma ma halinka nake. Shawara Hajja da sauran mutane suka ba ni akan na koma ko don Salim. Amincewa na yi, sai dai kafin nan sai da muka je asibiti ni da Aminu akan ciwon sanyi.

  Lallai na taki sa'ar kome, domin Aminu ya ba ni ƴancina. A fagen shawara ma ya daina cewa me na sani a rayuwa?.
  Batun audugar mata kuwa ni na ce ya rage siye tunda na iya amfani da tsumma, kai ya girgiza, "A'a Luba, rashin uwa ke sa a yi uwar ɗaki. Kuma kula da kaya ai ya fi ban cigiya ko?", na ce "Haka ne".
  Ya ce "Toh siyen auduga ba fashi, fatana ki kula mani da kanki", na ce "Insha Allahu mijina".

  Hadiza Isyaku
  @Hazaka writers association
  Ƙarshe

Comments

4 comments