Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » CIKIN BAURE: Babi na shaɗaya

CIKIN BAURE: Babi na shaɗaya

 • Ku latsa nan dan karanta babi na goma

   

  Wani irin masifaffen son shi ne ya cigaba da azalzalarta a zuciya, sake sumbatar hoton ta yi kafin ta yi save. cigaba da gamsar da zuciyarta ta yi da kallonsa, a fili ta ce "Mutumin nan ya had'u", a ranta ta 'karashe fad'in "In dai na mallake shi ba zan bar wata kofa da wata mace zata sake shigowa rayuwarshi ba."

   Fitowa daga dp d'in ta yi bayan ta gama ba idanunta abinci, kai tsaye cikin chat ta shiga, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ta aje mashi "Salam", fitowarta ke da wuya nutsastsen 'bangaren zuciyarta ya tambaye ta "Kanki d'aya kuwa?", domin ko da bata son Abbas, amma ta san neman magana dawani namijin bai halatta a gareta ba, da yake ta makance a soyayyar gaibu sai ta kawar da wannan tunani, ita in dai tana ganin motsinsa toh bu'kata ta biya. Fitowa ta yi a contact d'insa ta shiga group d'insu na mata zallah, sosai take son group d'in, dan ana tattauna abubuwa masu muhimmanci. Sallamar da wata Maman Huda ta turo a sticker da yaren larabci ce ta amsa, aikuwa suna gaisawa Maman Huda ta ce muje Pc, wata da ke online a group din ta ce "A yi maganar public mana", daga 'karshen maganarta ta turo emoji mai d'auke da gwalo, wanda ke nuna da wasa ta yi maganar, reply Maman Huda ta yi ma waccan da "Abin sirri ne ai", dariya suka yi. Asma'u kuwa tuni ta fice a group d'in, tick biyu ta gani a sallamar da ta aje ma Nas, da sauri ta shiga chat d'in, sai ga shi online, dubawa tick d'in ta yi ta ga ko ya bud'a, amma sai ta ga basu zama blue ba, uzuri ta yi mashi tunda yanzu ya zo.

  Bayan ta baro shi ne ta ga Sallama da new number, sanin Maman Huda ce ta yi saurin bud'ewa. Gaisawa suka 'kara yi, daga bisani Maman huda ta rubuta mata "Kamar ke ce a group d'in matan 'kwarai ki ka nemi maganin zubar da ciki ko?", Asma'u ba ta yi mamakin tambayar ba, don tun kafin ta amsa sallamarta ta duba profile d'inta, a nan ta ga suna cikin groups har had'u, wanda duk ta dalilin link suka shiga. Amsa Asma'u ta ba ta "Eh kuwa ni ce, kina da maganin ne?", cewa ta yi "Eh", Asma'u ta ce "Da gaske?", had'e da tura emoji mai dariya, "Eh dagaske, amma dan Allah me zai sa ki zubar da cikinki?".

  Ba tare da dogon nazari ba Asm'au ta danna voice button, sai da ta nad'e irin matsayin Abbas a ranta, da kuma shirin rabuwa da shi da take kana ta sakar ma Maman huda, aikuwa tana gama sauraro ta turo mata emoji mai kuka, sannan ta biyo bayanshi da gajeren typing mai d'auke da "Matsalarmu d'aya", cike da tausayin kansu Asma'u ta yi mata typing da "Wayyo, Allah ya kawo mana mafita", Maman Huda ta turo mata stciker mai dauke da "Amiin."

  Labarinta ta ba Asma'u cewar itama auren dole aka yi mata, sakamakon wani Alhaji da ya zo ya zuba ma waliyyinta ruwan kud'i, tana ji tana gani aka raba ta da wanda suke soyayya tun ta yarinta, sosai ta zayyana mata irin 'kuncin da ta shiga, wanda ko kusa Asma'u bata samu kanta a irinshi ba, saboda har ga Allah ita Asma'u auren gata ne aka yi mata, sai dai nisa da ta yi a makauniyar soyayya ya hana ta gane haka.

  Idanun Asma'u na fitar da hawayen tausayin Maman Huda ta tambaye ta" Amma ina mahaifanki da har waliyyinki ya samu damar cutar maki da zuciya?", Maman Huda ta ce "Ni marainiya ce ai, tun ina 'karama na rasa mahaifina, toh bayan mamana ta yi aure a Yola ne na koma hannun kawuna, wanda dama lokacin babana na raye a gida d'aya muke zaune, hakan ne fa ya ba shi damar yin yadda ya ga dama da zuciyata", Asma'u ta ce "Allah ya ji'kan mahaifinki", Maman Huda ta ce "Amiin."

  Za'ke Asma'u take ta ji makomar auren Maman Huda da Alhajin da aka ri'ka 'kara mata ruwa da jini saboda 'kin shi, don haka ne ta jefo mata tambaya ta hanyar typing "Amma har yanzu kuna tare da Alhajin?", Maman Huda ta ce "Eh muna tare", Asma'u ta ce "Ta'b, na ranste idan ni ce ba zan zauna ba, duk yadda zan kashe auren nan in samu 'yanci sai na yi", emoji mai d'auke da murmushi ta turo ma Asma'u, sannan ta d'ora typing da "Hmm!, idan na kashe auren in tafi ina? Kada ki manta fa ni marainiya ce", Asma'u ta ce "Yoh wurin mamanki mana", Maman Huda ta ce "A'a, in dai ina son Mamana ta zauna lafiya a gidan aurenta ba zan je can ba, wannan Alhajin dai gidanshi ne wurin zamana duk da mai 'kaunarshi ma bana so, na san Allah ba zai bari na wula'kanta ba, kuma Alhamdulillah, duk wani gata da mace ke so ina samunshi a gidan, ga tukuicin 'Yata Hudah da 'kannenta twins duk maza da Allah ya ba ni, kin ga idan na bijire na yi ma Allah butulci, kuma shi kanshi kawuna idan na bijire ban mashi adalci ba, dan shi ya yi d'awainiya da yarintata har zuwa auren da nake kira na dole", sai da Asma'u ta d'an jinjina kana ta ce "Hakane", duk da a ranta bata jin zata iya ha'kurin Maman Huda.    

  Sun sha hira sosai, wata a voice, wata da typing, daga 'karshe Maman Huda ta ba Asma'u shawara a kan ta yi ha'kuri ta haife cikinta, dan bata san me zata haifa ba, mai yiwuwa ya zama silar farincikinta a duniya da lahira, idan ya so daga baya sai ta san na yi tunda Asma'u ta fad'a mata ba zata iya ha'kurin zama da Abbas ba, da yake Asma'u ta san bayan haihuwa akwai raino sai ta nuna mata ita dai gwara cikin ya 'bare, hakan zai bata damar kutsa kai cikin neman cikon burinta, voice Maman Hudah ta yi mata da "Toh ni dai ba zan so ki jefa kanki a lalura ba 'karshe ki yi kuka da ni, zubar da ciki ba 'karamar illa gare shi ba, gwara ki bari ki haihu, idan ya so kina tafiya wanka sai 'ki dawowa, abin da kika haifa kuma ai ribarki ce ko da baki tare da babanshi", godiya Asma'u ta yi mata duk da bata gamsu da shawarar ba.

   Save d'in numberta Asma'u ta yi, kana suka yi sallama. Wurin Nas da ke 'kasan ranta ta nufa, gashi dai online, amma bai bud'a chat d'inta ba, hakan sosai ya tab'a mata zuciya, gaba d'aya ta ji WhatsApp d'in duk ba dad'i, fitowa ta yi, bata zame ko ina ba sai wani app dake had'a pics, wani tsalelen hotonta ta da ta yi cikin wata golden din atamba, frame mai guda biyu ta samu ta had'a hotonta da na Nas, shi yana sama ita tana 'kasa "Parfect match" ta fad'a a fili, domin ba 'karamin kyau had'in ya yi ba, sai dai bata yi save d'in hoton ba, don Abbas gwanin d'aukar wayarta ne. Hoton Nas d'in ma dake wayarta goge shi ta yi domin gudun abin kunya.

  Batun Sallamar da ta yi ma Nas har washe gari bai bud'a ba, ta yi zarya a WhatsApp kuwa ya fi a 'kirga, kuma duk lokacin da zata je takan yi sa'ar yana online, ta so 'kara jibga mashi wata sallamar amma zuciya ta hana ta, wannan lamari ne ya sanya ma zuciyarta nauyi. Da yamma Abbas na dawowa ya same ta tsakar gida ta had'a tagumi a kan kujera taya ni gulma, d'an rusunawa ya yi, lokaci d'aya kuma ya janye mata duka hannayen daga kumci, idanunsu sark'e da juna ya tambaye ta "Ya dai, me ke damunki?", tsanarsa da kuma ba'kincikin watsi da chat d'inta da Nas ya yi ne suka taru wurin ingiza ta fad'in "Kai ne damuwata Abbas", tare da fizge hannunta, Ras! gaban Abbas ya fad'i, dan babu alamun wasa a maganarta, cike da mamaki ya mi'ke daga du'ken da yake "Kamar ya ni ne damuwarki Asma'u?", amsar da bai ta'ba zato ba ta ba shi, cewar "Da ka shigo rayuwata mana har na aure ka, ka tab'a ganin alamar sonka a tare da ni?", tana rufe baki ta mi'ke tana ta huci.

  "Haba Asma'u, wace irin magana ce wannan, dan Allah ki gaggauta dawowa hayyacinki tun kafin na rasa nutsuwata", ya fad'a kamar zai yi kuka, "Toh sai me idan ka rasa nutsuwarka", sai da ya girgiza kai sannan ya ce "Sai ba komai, kuma kam ban tab'a ganin wata alamar so na a tare da ke ba, kawai dai ina danne ma raina ne, domin ke d'in ta daban ce a rayuwata", shiru na wucin gadi ya yi yana kallon yadda take tsinano baki, kafin daga bisani ya d'ora da fad'in "Asma'u me ye manufar fad'a mani wannan magana, ina nufin me kike so na yi ne?", "Ka yi duk abin da ya dace in dai ka gamsu bana sonka", tamkar mashi maganarta ke sukar zuciyarshi, murya a disashe ya ce "Okay, ki bani lokaci toh", bai bari ta sake magana ba ya juya, da kallon tsana ta raka shi har ya fice daga gidan, tsaki ta yi tare da fad'in "Ina dalilin zama da wannan 'karangiyar."

  Shi kam "InnaliLlahi wa Inna ilaihi raji'una" ce bakinsa kawai ke furtawa, yadda yake mata son gani kasheni bai tab'a ba ransa akwai ranar da irin haka zata fito bakinta ba. Wata irin juwa ce ta shiga d'aukarsa, jin zai fad'i sai ya yi maza ya dawo soron gidan, kwantar da bayansa ya yi ga bango, idanunsa a lumshe ya ce "Ashe Asma'u bata so na", aikuwa sai muryarta a can tsakar gida ta 'kara jadadda mashi tsananin 'kinta a gare shi, inda ya jiyo tana fad'in "Duk Aunty ce ta ja mani wannan ala'ka'kan, ba tare da ta tambaye ni wa nake so ba ta tashi ta aura mani shi, Ya Allah ka raba ni da Abbas, kana ka had'a ni da zab'in rayuwata." Wannan magana tata da 'karar kwana na kusa, da Abbas ya mutu, domin wata irin bugawa da zuciyarshi ta yi sai da komai na shi ya tsaya, sallallamin dai ya cigaba da yi cikin sautin da ya kai mata, don soron bai da wata tazara tsakaninshi da tsakar gida, hakan ne ya sanya bakinta yin gum.

  Da ace 'kafafun Abbas za su iya d'aukar shi, toh da ya bar unguwar, toh ba zai iya ba, dan haka ya jawo 'kafafun da'kyar ya shigo gida. Falo ya same ta tsaye tana duba WhatsApp, hannunsa na kyarma ya kar'be wayar, fad'uwa gabanta ya yi, don cikin contact d'in Nas take, kuma a tsammaninta ya gani, "Bani wayata", ta fad'a cikin fad'a, "Zan baki Asmy, amma dan Allah ki zauna mu yi magana", sai da tab'ata mashi lokaci sannan ta zauna a hannun kujera, inda shi kuma yake zaune kan kujera suna fuskantar juna.

  Asma'u ki sani, fitina a kwance take, Allah kuma bai son mai tadar da ita", lallashinta ya shiga yi, tare da tabbatar mata sonta ba zai barshi ya iya rabuwa da ita ba, "Kambala'I, toh shikenan", abinda kad'ai ta iya cewa, zuciyarta a 'kule ta mike ta nufi bedroom, can ya bi ta yana 'kara nuna mata illar furucinta, domin idan mahaifansu suka ji abin ba zai yi ma kowa dad'i ba, da yake ta yi nisan da bata jin kira, sai ta yi kunnen uwar shegu da maganganunsa, dan yanzu ta kai ma'kurar da bata tsoron fushin kowa.

  Wannan yanayi na damuwa da'kyar ya iya barin Abbas fita masallaci, ana gama sallar magrib ya kira Abdul tare da shaida mashi abinda Asma'u ta yi mashi, Abdul bai yi mamaki ba, sai dai duk da haka dole ya kwantar ma abokinshi da hankali, don sanyin muryar Abbas kad'ai sun tabbatar mashi da yana cikin matsananciyar damuwa. Shawara ya ba Abbas cewar ya tsiri sabuwar kyautata mata, maiyiwuwa hakan ya sa ta sauko, tunda mace rauni gare ta.  

  Ko da Abbas ya dawo gida, bai samu fuskar yi ma Asma'u magana ba don gaba d'aya hankalinta na kan waya tana aikin kallon Nas a online duk da bai bud'a sa'konta ba, bare ta sanya ran reply, tana gama zaman gawon shanun ta tashi fuu ta shige bedroom, ba tare da Abbas ya samu ko da arzikin ruwa daga gare ta ba. 

  Ta 'bangarenshi ko da ta kawo mashi ruwan ma ba zai iya sha ba saboda babu sauran wani 'kawa zuci a tare da shi, shi tunaninshi yadda zai shawo kanta. A wannan dare dai bai iya rumtsawa ba, da asuba kuwa zazza'bin da ya kwana da shi bai bari ya je massalaci ba. Bayan gari ya waye ne ya same ta a falo ta kwantar da kanta a bayan kujera, sosai yanayinta ya tabbatar mashi da itama akwai abin da ke nu'kur'kusar mata zuwa.

  "Asma'u", ya fad'a bayan ya zauna gefenta, hannunsa ya d'aura a kan cinyarta lokacin da ya 'karashe maganar, sosai zafin hannunshi ya shiga jikinta, dagowa ta yi suka had'a idanu, tausayi ya bata, sai dai wanda ba zai iya janye ta a kan bakanta ba.

  Bai wani 'bata lokaci ba ya ce "Asm'au, tsakanin jiya zuwa yau ji nake kamar zan mutu, ki tausaya mani ki mayar da maganarki ta jiya wasa, kiyayyarki a gare ni azaba ce wadda bazan iya jura ba a duniyar nan", yana rufe baki siraran hawaye suka gangaro mashi a kumci.

  Kai ta girgiza tare da fad'in "Bana jin zantukana zasu zama wasa, kawai ka taimaki rayuwata ka yi abin da zai sama mun da farinciki mai d'orewa", sosai ya ga tsanarsa a cikin 'kwayar idonta, lallashinta ya shiga yi da raunanan maganganu, amma fafur ta 'ki sauraron shi, da ta ga magiyar da yake mata bai mai 'karewa bace, sai ta mi'ke da nufin barin wurin, ru'ko hannunta ya yi ta baya, cike da dakiya ya ce "Asma'u, fad'a mun me zan maki wanda zai sanya ki farinciki?", ba tare da tunanin gaba ba ta ce "Saki, saki nake so Abbas".

  Tsabar kad'uwa bai san lokacin da ya mik'e tare da matse mata hannu gam ba, shiru ya yi ha'de da lumshe idanu, take Allah ya taimake shi ya samu mafita, a hankali ya bud'e idanunsa da tun jiya suka 'kan'kance "Toh shikenan Asma'u, zan yi maki abin da kike so, amma ina da sharad'i.."

  INA YI MABIYA WANNAN LITTAFI BARKA DA SALLAH, DA FATAN ALLAH YA KAR'BI IBADUNMU, ALLAH YA SA MUNA DA RABON GANIN TA BAD'I LAFIYA AMIIN.

  SANNAN DAN ALLAH KU RI'KA YI MANI COMMENTS DA LIKES, DA SHI NE BAKANDAMIYA ZASU BIYA NI HAR NA SAMU ZARAFIN CIGABA DA KAWO MAKU LABARIN. 

  Babi na Shabiyu

Comments

3 comments