Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » CIKIN BAURE: Babi na shabiyu

CIKIN BAURE: Babi na shabiyu

 • "Ban damu da duk wani sharad'i naka ba, in dai bu'katata zata biya", cike da gadara ta 'karashe maganar, tare da yi mashi kallo mai cike da tsangwama. Murmushin da ya fi kukan da yake ciwo ya yi, lokaci d'aya kuma ya girgiza kansa da ya yi jingim.

  Hannunta ya kama "Mu zauna toh", domin ji yake kamar zai fad'i saboda jiri, bayan sun zauna a kujera two seater ne ya fuskance ta, domin ya fahimci za'ke take ta ji sharad'in, "Zan rabu dake Asma'u, amma ba yanzu ba..", a zabure ta yi mashi mugun kallo, ta bud'e baki a tsiwace zata yi mashi magana ne ya yi saurin dakatar da ita "Yana daga cikin sharad'in, ki bani dukkan nutsuwarki har lokacin da zan ba ki damar magana, idan kuma ba haka ba zan koma ciki in kwanta, idan kin shirya sai ki tashe ni mu yi maganar", yadda ya yi maganar cike da mazantaka ne ya sa ta yin la'kwas, domin duk inda namiji yake yana da wani kwarjinin da idan ya motsa yake firgita zuciyar mace, toh wannan kwarjinin ne ya bayyana 'karara a fuskar Abbas, duk da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba.

  Turo baki ta yi tare da hard'e hannu a 'kirji, massarafan sautinta ta baza tana jiran maganarsa, ko da ya fahimci haka sai ya cigaba da fa'in "Kin ga dai yanzu ciki gare ki, ko da mun rabu a 'ka'ida ta addinin Musulunci a gidana zaki yi idda, idan kuma ya kasance saki uku ne, to akwai cutuwa ki koma gidanku da yaron ciki, domin za ki yi zaman rainon cikin, bayan kin haihu kuma ki raini d'an, don haka sharad'ina na farko shi ne sai kin haife mun d'ana, idan ma ba zaki iya shayar da shi ba, sai ki ba ni shi, Allah ba zai hana wadda zata shayar da shi ba, tun da mahaifiyarshi ta gaza."

  "Kam bala'i", ta furta a fili, domin bata kai sharad'in a nan ba, kuma da ya san plan d'in da take shiryawa a kan cikin, da bai zo da wannan shad'i ba, "Toh idan kuma cikin ya 'bare fa, sharad'i ya zo 'karshe ko?", sosai tambayarta ta sare mashi guiwa, saboda idan ya ba ta amsa da "Eh", toh zata iya zubar da cikin, ta maza ya yi wurin bata cikkiyar amsa da "Eh, amma kafin shi akwai sharad'i na biyu.", Fad'a mata ya yi cewar dole d'an zaman da ya rage musu ta bashi kulawa ta musamman, cike da rashin fahimtar zancenshi ta ce "Kamar ya kulawa ta musamman?'', ya ce "Ina nufin ki tarairaye ni irin tarairayar da ki ka yi ma masonyinki tanadi, ma'ana mu yi zama mai cike da soyayya da 'kauna ta yanda...", bata bari ya 'kartashe maganar ba ta ce "Ba zai yiwu ba", tana rufe baki ya ware hannu tare da fad'in "Ashe ba ranar rabuwa a tsakaninmu", dubanta ya yi sosai kana ya ce "Na rantse babu wasa a maganata, idan kin bi sharad'ina zan baki cikakken 'yancinki ki je ki auri wanda kike so, idan ki ka bijire mani kuma sai dai mu yi ta zaman ba'kin ciki ni da ke, wanda ya cuci wani a tsakaninmu Allah ba zai barshi ba", yana kaiwa nan ya ta shi ya shige bedroom ya kwanta, don ya fahimci idan ba true colour d'inshi ta gani ba, ba zasu wanye lafiya ba.

  Iya 'kuluwa kam Asma'u ta yi ta, kuka take son yi, amma ta kasa saboda cunkushewar da zuciyarta ta yi, babu wata 'kofa da hawaye zasu samu sararin fita. Yo ta ya ma zata iya gwada ma Abbas soyayya, kuma ma dan had'ama irin wadda ta yi ma Nas tanadi?, "Na rantse ko wa ya tsaya maka ba zan bi sharad'inka ba", a fili ta yi maganar, sai dai cikin sautin da ba lallai ne ya jiyo ta ba, ba tare ta matsa daga inda take zaune ba ta shiga tunanin yadda zata yi da cikin, domin shi ne ala'ka'kan da zai kawo mata tsaiko. Shawara ta fara da zuciyarta cewar zata je asibiti a cire cikin, tana tuna shi ke raka ta ta ja tsaki, wani shashe na zuciyarta ne ya ce "Toh dole sai kin fad'a mashi zaki je asibiti, me zai hana ki yi 'karyar za ki je suna a familyn babaku, daga can sai ki wuce", sosai ta gamsu da wannan, shu'umin murmushi ta yi tare da mi'kewa itama ta nufi bedroom. Tsaye ta yi a saitin kansa ta ce "Kana ji na?", a hankali ya bud'e idanunsa ya ce "Eh", sake lumshe su ya yi, domin kunne ke ji ba ido ba, ta kuma ji haushin haka, amma dole ta danne ta ce "Na gamsu da sharad'inka, amma muddin ka 'ki saki na duk abinda na yi maka kai ka ja." Ba shiri ya bud'e idanun, domin tarkon da ya had'a mata ya kama ta, ya tsiro sharud'd'ansa ne domin ya samu damar cusa kanshi a zuciyarta, ta yadda da kanta zata yi watsi da maganar saki, danne dariyar muguntarshi ya yi a rai kana ya ce "Toh madalla. Ki sani kuma babu gardama, duk abinda nake so zaki yi mani, da fatan kin ji", a ta'kaice ta ce "Na ji", a ranta itama tana yi mashi dariya, domin itama ta gama shirinta da take zaton bai san da shi ba.

   Juyawa ta yi, har ta kai bakin 'kofa ya dakatar da ita, zaune ya tashi tare da kallon fuskarta da ta yi kicin-kicin "Sharad'in zai fara daga yanzu", dara-daran idanunta ta watso mashi, hakan ne ya ba shi damar fad'in "Ki saki fuskarki, ta yadda ko wani ya shigo ba zai fahimci kina da damuwa ba, na maki al'kawali zan rabu dake, ko da hakan zai yi sanadin ajalina", sosai maganarsa ta 'karshe ta sanya ta farincikin da ya bayyana a fuskarta, domin an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

  "Ko ke fa" ya fad'a yana dariya, umarnin tafiya ya ba ta, bayan ya jiyo motsinta tsakargida ya ya d'aga hannu sama "Allah ka san yadda nake son Asma'u, ina ro'konka da kada ka jarabce ni da rabuwa da ita, domin hakan zai iya zama ajalina." Addu'oi sosai ya kwararo, bayan ya gama ya koma ya kwanta, bai d'auki lokaci ba baccin da bai yi daren jiya ba ya d'auke shi.

  Ita kuwa kitchen ta shiga, amma tunanin yadda zata iya gwada ma Abbas 'kauna ko da na wuni d'aya ne ya mantar da ita abin da ta je yi, fitowa ta yi tare da jingina da bangon kitchen d'in, "Mutumin da ban ta'ba jin son shi a raina ba ta ya zan kula da shi?, Dole ma na yi gaugawar zubar da cikin nan tun kafin 'kiyayyarsa ta halaka ni", tamkar a kunnen 'dan tayin da ke cikinta ta yi wannan magana, domin sai da ya yi motsin da bai ta'ba yin irinsa ba, dafe cikin ta yi da duka hannayenta, maimakon ta ro'ka mashi albarkar Allah, sai ta shiga ro'kon Allah ya 'barar da shi, ko dan ta huta da masifar 'kin Abbas. 

  Ta da'de tsaye a wurin, da ta ji 'kafafunta sun fara nauyi ne ta koma kitchen d'in ta had'a musu breakfast. Ta so had'a tea d'inta ita kad'ai, sai dai tuna shara'in ne ya hana ta. A flask ta juye ruwan zafin ta kawo falo, bayan ta had'a sauran kayan tea d'in ta nufi bedroom, yanzu ma 'ki'kam ta yi a kansa, murya a disashe ta ce "Ka ji.?" 

  Ya ji ta kam, domin falkawarsa kenan, amma sai ya yi shiru saboda akwai darasin da yake son koya mata, jin ta d'an buga filon had'e da sake fad'in "Ka ji" ne ya sanya shi bud'e idanu suka kalli juna, sosai yadda take son 'boye 'kunar dake ranta ya kusa sanya shi dariya, amma sai ya gimtse ya ce "A'a ban ji ba", cewa ta yi "Kuma ka amsa?", ya ce "Eh", ta ce "Toh ka tashi ga breakfast can", ma'ke kafa'da ya yi, aikuwa ta juya a hasale, ru'ko hannunta ya yi "Yanzu haka ya kamata ki tashi masoyinki?", ta ce "Toh ya kake son na yi?", ya ce "Yadda kika yi buri wa masoyinki da ke shirin raba ni dake, na san ai kin yi tanadin kyautatawa mai cike da salo na musamman a gare shi ko.?"

  Kashe mata baki maganarshi ta yi, hakan ya ba shi damar cigaba da magana "Yana da kyau ki gyara, domin ni ma na samu damar cika maki al'kawarinki", yana kai wa nan ya sakar mata hannu.

  Idanun Asma'u cike da 'kwalla ta nufi falo, bata jima ba ya fito falon shi ma, ganin tana goge hawaye da bayan hannu ne ya ta'ba mashi zuciya, a gaggauce ya 'karasa gabanta ya tsugunna, hannayensa biyu ya sa ya share mata hawaye, "Sorry! Ki dena yi mana asarar hawayenki ni da future...", kasa 'karasa maganar ya yi saboda wani irin kishi da ya turnu'ke mashi zuciya. Shiru na wucin gadi wurin ya yi, daga bisani ya lallashe ta har ta dena 'kwallan. Black tea kad'ai ya iya sha saboda salaf d'in da bakinsa yake.

  A wannan rana dai bai fita ba, kuma daidai gwargwado Asma'u ta kula da shi, amma ba a son ranta ba, sai don cikar muradinta na rabuwa da shi, hakan kuwa ya faranta ransa sosai har ta kai ga ya nemi zazza'bin ya rasa. Da daddare kuwa bayan ya fita ne ya siyo musu gasasshen nama da fura . Da kanshi ya d'auko plate da cups a kitchen ya kawo kan tabarmar da take zaune a tsakar gida. sau biyu ya d'auki naman ya kai mata a baki, ita kuwa sagale ta yi da hannu tana kallon shi, marairaice fuska ya yi shi ma ya kalle ta, haushi had'e da dariya ya ba ta, d'auka ta yi ta sanya mashi a baki, zata janye hannu ya ri'ke shi, cikin hasken wutar nepar da ya game tsakar gidan ya ri'ka yi mata kallo mai cike da so, sadda dda kanta ta yi a 'kasa, domin abin da take ji ya sha banban da wanda shi yake ji. Ya dauki lokaci a haka, daga bisani ya sakar mata hannu, yadda ya so haka suka ci naman kuma suka sha furar. Wurin bacci ma na yau ya banbanta da na kullum, domin kamar zai maida ta a cikinsa, duk wayon ta wurin son zamewa a jikinshi amma ta kasa. Cike da d'acin rai ta bashi ha'k'kinshi da ke kanta, duk da haka ya samu nutsuwa a ransa. Gefe ya matsa, dan ya san hakan ta fi buƙata, da yake iya ma mutum sai Allah, sai zuciya ta ce mata "Dama ƙishirwar buƙatarsa kawai yake son kashewa da ke, kuma tunda bu'katarshi ta biya ga shi ya banzatar da ke", sosai wannan magana ta zuciyarta ta hasala ta, sauka daga kan gadon ta yi saboda ba ta jin daɗin kwanciyar ba tare da ta raɓi jikinshi ba, dakatar da ita ya yi don ya ga alamun fita zata yi, "Ina zaki je?", ba tare da ta juyo ba ta ce "Fita zan yi saboda bana jin bacci", bata yi zato ba sai ta ga ya sauko daga kan gadon, rungumota ya yi ta baya tare da sassauta murya "Mu je mu yi hira toh." Iya ma ɗan Adam sai Allah, a ranta kuma sai ta ce "Jarababben banza", don ba kuma so take ya liƙe mata ba. Falon suka zauna, aikuwa ba su je ko'ina ba bacci ya fara fizgar ta. Tsagwayam ya ɗauko ta suka dawo bedroom, kamar jaririya ya maida ta, sai ga shi bacci mai daɗin gaske ya ɗauke ta.  

   Haka suka kasance tsawon kwana biyu, a na ukun ne suna breakfast Asma'u ta marairaice fuska ta tambaye shi zata je suna kamar yadda ta tsara, saboda mafarkin had'uwarta da Nas ya 'karu, a sabili da amsa sallamarta da ya yi, idan ba gaugawar zubar da cikin ta yi ba, toh da wahala mafarkin ya zama gaskiya.

  Cike da 'kaunarta ya ce "Toh ranki ya dad'e, da wuri zaki fita, ko sai yamma ta yi?", ranta fari sal ta ce "Da wuri dai", ya ce "Ba damuwa." Farincikin samun damar cikar burinta ne ya mamaye ta, "Na gode", ta fad'a tana shu'umar dariya....

   Next Page>>>

   

Comments

1 comment