Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » CIKIN BAURE: Babi na Sha-uku

CIKIN BAURE: Babi na Sha-uku

 • >>Previous page

  Tsammanin Abbas dariyar jin daɗi ce Asma'u ke yi, wanda kuma haka yake fata ya ga ya yi mata abin da zai faranta mata zuciya, tambayarta ya yi "Yau ne sunan; ko yaushe?", ta ce "Gobe ne", d'an nazari ya yi kafin ya ce "Aaa! Ba gobe Thursday za ki koma awo ba?", ce mashi ta yi "Sai next week ai", saboda sati hud'u aka ba ta, jinjina kai ya yi alamar gamsuwa, daga bisani suka 'karasa breakfast d'in.

   

  Gyaran d'akin suka shiga yi, bayan sun gama kuma suka fito tsakar gida. Fiddo kwanukan wank-wanke Asma'u ta shiga yi, inda shi kuma ya ja tunga a 'kofar d'aki yana 'kare mata kallo. Fad'in matsananciyar soyayyar ta da ke tafarfasar mashi zuciya ma 'barnar baki ne, domin ba 'karamin kyau d'an matashin cikinta ya yi mata ba, uwa uba kuma fuskarta da ko a d'aure ta ke kyau take, bare kuma cike take da walwala. "Asma'u kyakkyawa ce", ya fad'a tare da bin bayanta da idanu lokacin da ta koma kitchen, lumshe idanun ya yi, a ransa ya sake fad'in "Allah ka kawar da fitinar dake shirin raba ni da ita, Amiin." 

   

  Ta 'bangarenta kuwa bata ma san yana yi ba, domin itama ta yi nisa a cikin tunanin Nas da fuskarsa ta zame mata madubi a zuciya, don haka ko 'kwayar idon Abbas zata fad'o saboda kallon ta, ba zai dame ta ba. 

   

  Gabanshi ta zo ta tsaya, kafin ta fad'i abin da ke bakinta ya ce "Kin gama fiddo kayan?", kai ta d'aga "Eh", hannunta mai taushin gaske ya ru'ko "Ok, amma wa zai wanke, wa kuma zai yi d'auraya?", ta fahimci neman magana ya ke, ita kuma ba so take ba, dan haka ta ce "Ka bari kawai zan yi duka, tunda aikin na mata ne", girgiza kai ya yi "A'a, ki wanke dai in d'auraye", bata yi mashi gardama ba ta ce "Toh", zare hannunta ta yi cikin na shi ta nufi wurin kwanukan. Kan kujera ta zauna, shi kuma a kan rijiya. Tunda suka fara yake satar kallon ta, a ranta kuwa ta ce "Wahalalle", saboda son maso wani da yake mata ya yi yawa. Ta zo saka plate a robar ruwan d'aurayar ne ya ri'ke mata hannu ya matse, had'e rai ta yi "Meye haka?", bakinshi d'auke da dariya ya ce "Hannunki ne da taushi", baki ta d'an ta'be "Uhmm", domin babu wani abu da zai iya birge ta da shi. Haka suka cigaba da wank-wanken yana tsokanar ta, wani wurin ta yi dariyar yaƙe, wani wurin kuma ta banzatar da shi. Bayan sun gama ne suka kai kwanukan kitchen tare da maida komai a mazauninsa sannan suka fito. 

   Umurtar ta ya yi da ta zauna ta huta, aikuwa ta shige d'aki ta bar shi da tsakar gidan yana gyarawa. Wayarta ta d'auka ta shiga WhatsApp, kai tsaye contact d'in Nas ta bud'a, wanda gwargwadon yadda ta zo WhataApp, gwargwadon yadda take bud'e dp d'inshi ta yi ta kallo, wani lokaci har mutane su yi ta magana, amma bata lura ba, bare ta yi masu reply, yanzun ma tana cikin tababar ta 'kara yi mashi magana tunda ya amsa mata, ko kuma ta 'kyale shi ne kiran Maman Hudah ya shigo a wayarta, d'aga kiran ta yi tare da sassauta murya ta yi sallama, bayan Maman Hudah ta amsa ta d'ora da fad'in "Sai a yi ta magana, amma ki yi shiru, kuma ga ki online", 'yar dariya Asma'u ta yi tare da juya idanu daga kwancen da take ta ce "Sorry, ina ba idanuna abinci ne", da yake wannan yaren mai sau'kin ganewa ne sai Maman Hudah ta ce "Soyayya dad'i, ki ce Abbas ya cika maki waya da pics d'insa", dogon tsaki Asma'u ta ja "Raba ni da wannan dan Allah, in kalli hotonsa in ji me, ina kallon fuskar cikon burina da nake mafarkin samu a nan gaba", daga can Maman Hudah ta d'an jinjina, daga bisani ta ce "Ta'b, toh ki ji tsoron Allahn da ya halicce ki", bata bari Asma'u ta 'kara magana ba ta tsinke kiran, "Can maki", Asma'u ta fad'a tare da jan tsaki, domin a yanzu babu wata gaskiya da wani zai fad'a mata, kuma ta gamsu da ita.

   

  Sallamar Abida ta juyo a tsakar gida, maimakon ta fito, sai ta bar ta da Abbas da ke wanke tsakar gidan, tana jin lokacin da ya ce ma Abidar ki shiga wurin Asma'un ki kar'ba, "Ko uwar me za ta kar'ba?", Asma'un ta tambayi kanta had'e da shan mur, ko da shigowar Abida 'dakin bata fasa danna wayarta ba, da yake Abidar miskilar kanta ce sai ta haɗe rai itama "Chager za ki ba ni" , daga kwance Asma'u ta nuna ma ta chager "Ga ta chan a kan kujera", wani mugun kallo Abida ta yi mata, sannan ta nufi kujera one seater ta d'auki chager da ke kanta, kamar zata bige Asma'u ta fito ɗakin, Abbas ya ce "Toh ki kular mani da chager dai", ai kuwa ta ce "Toh mijin Hajiya", ya ce "Me kika ce?", juyowa ta yi na ce "Mijin Asma'u", bata tsaya sauraron me yake cewa ba ta fice daga gidan. 

   

  Da isarta gida kuwa ta samu Ummansu a ɗaki tare da tsegunta mata, wai Abbas ke aikin gida, ita kuma Asma'u ta shige d'aki sai danna waya take, da yake Ummansu ba surukar tsanani ba ce sai ta ce "Toh me ye naki a ciki? Mijinta ne ai, duk abin da ya yi mata bai fad'i ba", Abida ta ce "Umma amma ai ba irin waccan sakarar miji zai yi ma bauta ba", Ummansu ta ce "Shin ba mace bace?", Abida ta yi shiru, ɗaurawa Ummansu ta yi da "Toh ki sani kowace mace tauraruwa ce a wurin mijinta, kema ki yi fatan Allah ya ba ki wanda zai hidimta maki." Abida ta d'ade da fahimtar Ummansu bata son laifin Asma'u, dan haka dolenta ta chanja hira. 

   

  A can gidan kuwa, bayan Abbas ya yi shirin fita ne ya zo gefen Asma'u kan kujera ya zauna, tambayar ta ya yi "Me za ki dafa mana?", ta ce "Duk abin da kake so", murmushi mai sauti ya yi "Ke ba ki da za'bi ne?", amsa ta ba shi wadda ta 'kara dulmiya shi, inda ta ce "Za'binka ai shi ne za'bina a komai" ya ce "Anya kuwa?", shiru ta yi tana 'yar dariya, cewa ya yi "Ahaf!", yana dariya shi ma, domin idan har maganarta gaskiya ne, toh ba za ta iya neman saki ba a wurinshi. Girki mai sau'ki ya ce ta yi musu, bayan ya mi'ke ne ya ke fad'a mata wurin Alhaji nan zai je yanzu, tambayarshi ta yi "Wane Alhaji kuma?" ya ce "Alhaji Nas mana 'dan unguwarku", sosai gabanta ya fad'i, har ta kai ga fuskarta ta bayyana sirrin zuciyarta, ba shiri ta mi'ke, inda Allah ya taimake ta ma ya nufi 'kofa, da sai ya fahimci halin da ta shiga daga ambatar Nas, bayanshi ta bi suka 'karasa maganar. Da zai tafi ne ya bu'kaci ta yi hugging d'inshi, idanunta a rumtse da d'an kwanto jikinshi, 'kasan ranta kuma tana jin kamar ta yi kuka, domin yana tilasta mata abin da mutum d'aya kaɗai ta yi ma tanadi.

  Shi kam ji yake kamar su dauwama a haka, cikin kunne ya rad'a mata "Ina matu'kar sonki, son da bana iya rabuwa da ke Asma'u", 'dago da kanta ta yi dan ta tabbatar da gaskiyar maganarsa, gani ta yi ya marairaice, hannayensa kuma sama kamar mai neman gafara, bata san lokacin da tsoro ya sanya ta fad'in "Za ka sa'ba al'kawari kenan?", shiru ya yi, dan shi kam ba zai iya cika al'kawarin rabuwa da ita ba, hakan ya bata damar ja da baya ta dube shi "Ni kam ina a kan bakana, ba zan fasa yi maka abin da zai faranta ranka ba har zuwa lokacin da al'kawarinmu zai cika. Batun cika naka al'kawarin kuma ya rage naka, ni dai ina tabbatar maka da ba zan iya rayuwa da kai ba, sannan ban damu da abin da duniya zata fa'da a kaina ba dan na guje ka, domin ba inda aka ga auren dole." 

   

  Tunda ta fara maganar yake kallonta, bai kuma 'kyafta ba sai da ta kai 'karshe, kai kawai ya girgizawa tare da fad'in "Allah ya kyauta toh! Lallai Asma'u kina bu'katar ayi maki ru'ƙuya", cewa ta yi "Ko bori za'a taka a kaina dai ka sani bana son ka", tana rufe baki ta juya a fusace ta nufi d'aki.

  Zuciyarshi a dagule ya raka ta da fad'in "Allah ya kyauta." Mashind'insa ya fidda waje, bai zame ko'ina ba sai a sabon gidan da Alhaji Nas ke ginawa, inda kuma ya taras da Abdul har ya riga shi zuwa. 'kar'kashin wata 'katuwar bishiyar zaitun da ke gaban katafaren gidan dake fuskantar filin Nas suka koma, kowannen su a kan mashind'insa ya zauna suna jiran Nas da ya ce masu yana hanya. Tunda Abbas ya zo wurin Abdul ya lura da ya'ke kawai yake, bayan sun gaisa tare da 'yan maganganu ne Abdul ya ce "Ya ita madam d'in, kun daidaita ko?", kamar Abbas zai yi kuka ya ce "Inaa fa, da farko kamar zamu daidaita, amma da alamun hakan ba zai yiwu ba, dan ni dai ba zan iya 'boye 'kaunar da nake mata ba, ita kuma bata son haka", Abdul ya ce "Allah ya kyauta toh", Abbas ya ce "Amiin dai." 

  Maganar Asma'u ta 'karshe ce ta dawo ma Abbas a rai, ci'ke da 'kunar zuci ya dubi Abdul da ke duba waya, "Abdul, yarinyar nan ni take fa'da ma bata so", Abdul da shi ma ranshi ke a 'bace ya ce "Toh kai waye da ba zata fad'a ma haka ba Abbas, idan za ka dawo hayyacinka ma, toh ka dawo, tun kafin yarinyar nan ta illata ka", muryar Abbas a disahe ya ce "Kamar ya in dawo hayyacina Abdul? Ka san dai yadda son da ya saki rassa a zuci yake da wahalar cirewa, kawai zan yi iya yina wurin ganin na shawo kanta da yardar Allah", cike da jin haushin shi Abdul ya ce "Toh Allah ya ba ka ikon shawo kanta, amma kafin hakan yana da kyau ka sanar da waliyyanku don su san da zaman wannan matsalar", Abbas ya ce "Ko?", dan bai taɓa kawo batun saka manya a maganar ba, sai yanzu da Abdul ya faɗa, Abdul ya ce "Ƙwarai", shiru Abbas ya yi, dan ba sosai ya gamsu ba, a ganinshi tsaf zai iya shawo kan Asma'u ba tare da wani ya ji ba, "Toh zan faɗa masu, sai idan na ga abin ya ci tura", ƙwafa kawai Abdul ya yi, dan ya fahimci Abbas ya yi nisan gaske a soyayyar Asma'u. 

  Cikin yanayi marar daɗi suka cigaba da maganar, nan Abdul ya ba shi shawarar ya sassauta soyayyar shi ga Asma'u, domin lura da irin son da yake mata ne ya sa take wahalar da shi, ba don Abbas ya gamsu ba ya yi mashi godiya. 

   

  Maida hankalinsu ga masu fidda fundation a filin Nas suka yi, cigaba da yaba girman filin suka yi tare da 'kiyasta kud'in da zasu samu contract na blocks d'in. 

  Motar Nas suka hango ta shigo a layin, Abdul ya ce "Mutumin nan na ji da kuɗi", domin motar da yake ciki ko hasidin iza hasada ya san ba ta yara ba ce, a taƙaice Abbas ya ce "Lallai kam", don shi a yanzu ba abin da ke burge shi, sai soyayyar Asma'u

  Tun kafin Nas ya faka motarshi suka sauko daga kan mashinansu. Ko da fitowarsa motar suka ƙarasa wurinshi, cike da girmama juna suka gaisa da juna. 

  Idanun Nas masu kwarjinin gaske ya sauke a kan Abbas, kawai sai sanyin jikin Abbas ya ɗarsa mashi tausayinsa, bai iya tambayar shi damuwarshi ba, amma sai ya ce "Kun ji ni shiru ko? Wallahi wani aiki ne ya ɗan riƙe ni", Abdul ya ce "Ai ba komai Alhaji". 

  Wurin filin suka ƙarasa, nan ma masu fitar da faundation suka gaishe da Nas, sannan suka cigaba da aikinsu. 

  Abbas ya dubi Nas dake tashin ƙamshi ya ce "Masha Allah, Oga wannan fili babba ne", Abdul ya ce "Wallahi kuwa", shi kuwa murmushi kawai ya yi. Ƴan maganganu Nas ya yi ma masu ginar ƙasar, sannan suka koma wurin motarsa su uku. 

  Baya mota ya buɗe ya ɗauko hoton gidan mai ɗauke ƙayataccen bene ne ya ce "Kun ga kalar gidan da nake so zan yi", Abdul da ya karɓi hoton ya ce "Masha Allah, ai babban goro sai magogin ƙarfe maigida, irin wannan katafaren gidan sai ku", Abbas ya karɓe da faɗin "Gidan ya yi ba ƙarya", a yanzu ma dariya kawai Nas ya yi, don shi ba mai irin surutun nan bane, a cikin magana goma da mutum zai yi mashi, da ƙyal ya ke iya saka baki a cikin uku ko huɗu, sai dai ya kan yi murmushi ko dariya, musamman a inda aka kuranta shi. 

  Kai tsaye maganar contract suka cigaba, nan suke faɗa mashi ƙaramin kamfaninsu ba zai iya ba shi kaɗai. Nas ya ce "Ku ƙoƙarta dai", Abbas ya ce "Allah kuwa mai gida, bama son a samu matsala ne."

  Cewa Nas ya yi "Okay, bari a baku kaso biyu cikin uku toh", Abdul ya ce "Ɗaya bisa ukun ma ya yi Oga", domin haɗamarsu bata kai inda Nas ke son kai su ba." Nacewa Nas ya yi sai dai ya basu biyu cikin ukun, saboda ya ga yadda suke blocks ɗinsu ba tare da ha'inci ba, kuma ta wani ɓangaren tausayin bayanannen raunin Abbas ya sanya mashi son ya taimake su. 

  Godiya suka yi mashi, tare da alƙawarin fara aiki daga gobe, saboda aikin ba kaɗan bane. Kuɗi masu yawa ya tura a account ɗin kamfaninsu na kafin alƙalami, wanɗa da su ne zasu fara aikin, ce masu ya yi su bi a hankali, domin ɗayan kamfanin da zai ba aikin suna da blocks ɗin da zasu bashi har aci ƙarfin aikin. Sun kuma ji daɗin basu lokaci da ya yi. 

  Tafiya Nas ya yi saboda jiranshi da ake. Su ma ɗin basu bar wurin ba sai da suka tsara yadda zasu yi aikinsu a sauƙaƙe ba tare da wahala ba. 

   

  Asma'u kuwa ta birkice, jira take Allah ya maido Abbas ta nuna mashi ba zata lamunci rainin wayon shi ba, domin ta fahimci ɗaukar yarinya yake mata, shi ya sa ya yi mata tsarin da ba zai yiwu ba. 

  Shi kam bai dawo ba sai bayan la'asar, inda ya ke ma Asma'u bata zo ba, bare ya sa ran zata kawo mashi abinci, da dai ya gaji da zama ne ya ɗaga murya "Asma'u ba ki ji na dawo ba?", daga can cikin bedroom ta ce "Na ji mana", ya ce "Toh fito ki ba ni abincina", ai kuwa ce "Ban girka ba."

   

  Tun a maganar farko ya fahimci tsuntsayen tsiyar sun tashi, amma bai ɗauka abin ya kai nan sai a maganarta ta ƙarshe. Miƙewa ya yi ya nufi bedroom, daga tsayen da yake a bakin ƙofa ya ce "Asma'u, kina son tsira a gidan aurenki kuwa.?"

   

  Daga tsayen da take itama a gaban mirror ta ba shi amsa mai nuna zallar ƙiyayyarsa a gare ta "Na rantse in dai a gidanka ne bana son tsirar, shi ya sa nake son ka rabu da ni tun kafin ni da kai mu halaka", kasa magana ya yi saboda ƙunar rai, sai dai ya juyo falon a ƙufule ya zauna. 

   

  Maganar Abdul ce ta fara zo mashi a rai na saka iyaye a cikin wannan rikici. 

   

   Shawara ya yanke da zuciyarshi cewar zai fara sanar da mahaifan Asma'u kafin na shi, domin ba ya son na shi su tsane ta. 

  Da dai ya natsu da wannan hukunci, sai ya tashi ya ɗauki mashin bai tsaya ko ina ba sai gidan Aunty, tunda  ita ce ja gaba wurin ba shi auren Asma'u..

  Next page>>

Comments

2 comments