Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » BAN-TAFIN MAKAUNIYA: BABI NA DAYA

BAN-TAFIN MAKAUNIYA: BABI NA DAYA

  • Tafe nake akan tsohon Babur d'ina kamar kullum ta gefen ma'kabartar da ke kusa da layinmu na biyo,amma yau ba kamar ko yaushe ba domin dare ya riskeni a hanyar komawata gida. Ina gab da wuce ma'kabartar naji wani sauti kamar na jariri,da farko nayi tunanin 'karar Babur d'ina ce daga baya kuma da na kashe shi har yanzu dai sautin yana nan,nayi matukar mamakin wannan lamari saboda nasan duk wanda aka kawo wannan gurin to mataccene kuma matacce binneshi akeyi,'karfin kukan ya katsemin tunanina a dole na kafe Babur d'ina na fara tafiya cikin duhu dan inga abin da yake wannan kuka irin na jarirai,tafiya nake ina ya6a 'kafata cikin ciyayi bana ko tunanin abin zai faru da 'kafar tawa. Naje kusa da inda sautin yake fita sai na tuna da fitilar wayata inda na d'aukota na haska,abin mamaki na gani,Jariri sabuwar haihuwa a yashe kusa da wani 'kabari na juya zan runtuma da gudu sai wani tunani ya fadomin (anya kuwa ba wata ce tayi cikin shege ta jefarba)nan take na ci birki na juya kai tsaye na mi'ka hannu zan d'auki jariri abin mamaki sai naga yana kokarin tashi zaune, "ikon Allah yanzu haka ake haifar yara da wayo yanzu dan wannan jaririn har kana iya yun'kurin tashi" Murmushi nayi tare da kara mi'ka hannu a karo na biyu,kafin hannuna ya kai ga d'aukarsa tuni har ya tashi zaune ya matsa gefe daga inda yake a kwance,sai a lokacin na lura da gurin kwanciyar tasa,ganyayyaki ne aka shimfid'asu luf dasu kamar katifa. Zuciyata ta fara sa'kar sabon tunani anya kuwa wannan mutum ne? To amma ai aljani yafi girman haka domin ance girman aljani d'aya yafi girman d'aki guda,kuma ance faratansa kafta-kafta ne da wannan tunanin na haska 'kafar jaririn naga komai nasa irin na mutane na d'aga fitilata zuwa fuskarsa sai naga yana kokarin kare fuskar da hannunsa,na tsorata sosai da ganin hakan amma kuma da yake zuciyata ta bani tabbacin ba aljani bane kawai na dake,na 'kara matsawa kusa dashi da niyyar d'aukarsa naga dai yayi min irin ta farko,ban tsaya jiran komai ba na daukeshi tare da fad'in "shegen yaro da ba'kar gardama dan uwarka idan na barka a nan kiyashi ne zai janyeka ya kai gidansu su cinyeka" Na yun'kura zan fara tafiya gurin da na kafe Babur d'ina sai naji kamar an ri'kemin 'kafata, "aikin banza mu har wata barazana za'ayi mana da tarko" a zatona tarko aka kafa na fizgi 'kafata kawai nayi tafiyata. Nazo inda babur yake ina rungume da jaririn na kama mashin da hannu daya zan burgashi,nayi sa'a bugu d'aya ya tashi na zauna kenan naji kamar tayoyinsa a sace suke,hakan kuwa akayi ina haskawa na gansu a sacen,ban tsaya tunanin komaiba na bar Babur din a gurin na kamo hanyar gida da jariri a hannuna mai nauyin tsiya kamar dutse,ina tafe yana zillewa a hannuna shidai a dole baya so in daukeshi. Wani abu naji zarere yana bina a baya na waiga tare da haska fitilar ta baya sai naga abin a hade yake da jikin jaririn mamaki ya kamani lokacin da na lura a hade yake da cibiyar yaron,sakinsa nayi ya fadi 'kasa domin abin ya firgitani, 'karar kukansa ce ta 'karamin tausayinsa,na tsuguna domin daukarsa to a nan ne na lura ashe cibiyarsa ce ba'a yankeba "kenan gidan uwar wa cibiyar ta ke da har za tayi tsayi kamar haka..." "gidan uwarka...." Kamar daga sama naji wannan maganar,batun labarta yanda naji tsoro kam abune da zai zama kamar zolaya domin bazan iya kwatanta fasalin tsoron da naji ba nidai nasan faduwa nayi a kasa ban san iya lokacin dana dauka a hakaba. A hankali na mike na fara bin doguwar cibiyar yaron da na baro a baya yaron kuma gashi kwance yana ta tsala kuka,da ace nasan me zai faru dani a tafiyata wajan ganin 'karshen tsayin cibiyar to da kuwa na zauna ban bi diddigiba. Zan ci gaba.

Comments

5 comments