Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Rubutun Ajami da inda ya samo asali

Rubutun Ajami da inda ya samo asali

 • Tun kafin zuwan turawa yankin Hausa/Fulani da ma can muna da abin rubutawa da karantawa,sun sami Hausawa da karatunsu na allo sannan suna rubutu da Ajami don karantawa domin isar da sako ko tura wasika daga wani gari zuwa wani.

  Haka sarakunan Hausa Fulani suna aika wasika da Ajami,wannan rubutun Ajami ya samo asali ne daga haruffan larabci,ta inda aka juya komai nasa cikin hikima ake koyar da mutane yanda za su yi karatu cikin sauki,misalin yanda ake koyarwar yana da alaka da yanda halittar wani abu take,misali ana duba harafin larabci da me yafi kama a Hausa sai a bashi suna da abin.

  Misalin yanda abin yake shi ne, a larabci akwai BA'UN mai zuwa a karshen harafin KATABA Bahaushe yana kiranta BAAGUJE, anyi wannan hikimar ganin asalin BAA'UN kala biyu ce akwai ta farkon harafin BISMILLAH wacce kai tsaye Bahaushe BAA yake kiranta,ganin waccen ta zo a gefe sai yake kiran BAA'GUJE abin nufi anan shi ne BAA wacce ta guje ta koma gefe,haka abin yake a irin su harafin da ake kiransa da ALLI'KAFA saboda yayi kama da likafar doki,akwai wanda ake kira da ƊAMISA HANNU saboda in ka kare masa kallo zaka iske kamar an launkwasa hannu an mikar da dan yatsa daya,akwai wanda ake kira,TAKURI,ko kuma HAKURI,suna da yawa irinsu wanda in muka samu lokaci za mu dauke su daya bayan daya aji yanda ake kiransu da Hausa da kuma yanda sunan ya samo asali.

  Wannan duk cikin bayanin yanda Hausawa suka samar da rubutun ajami ne wanda har zuwa yanzu wasu suna amfani da shi wajen karatu da isar da sako,da wannan tsari da zubin karatu Turawa suka samu yankin Arewa,hakan tasa sai da suka sha fama kafin mu karbi abin da suka zo da shi din,wanda har a wannan zamanin wasu basu yarda da su yi karatun boko ba,za ku yi mamaki in kuka shiga ƙauyuka sosai za ku tarar da babu wanda yake zuwa wani waje yin karatu sai dai ku iske ana karatun allo kuma duk suna karanta ajami.


  Wannan yasa da muka kalli yanda Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya yunkuro domin dawo mana da martabar rubutunmu na ajami,ta hanyar samar da jarida ta ajami wacce kowa zai iya karantawa musamman manyan mutane da wasu basu iya karanta rubutun boko ba,kuma ko babu komai mutum ya girmama tsarinsa wanda kowa da shi yake alfahari, tabbas abin farin cikine sosai samar da Jarida ta Ajami,anyi duk wani tsari da hikima wajen tsara bayanan ciki wanda ga su nan kai tsare da sunan Jaridar mai suna TABARAU muna yiwa wannan jarida fatan alkhairi mai yawa.

  Kamar yanda muka yi bayani a sama cewa zamu dan dauko bayanan haruffan Hausa na Ajami ayi bayaninsu da yanda ake furta da kuma yanda aka dangantasu da wani abu na Hausa domin a yiwa Hausawa hikimar da za su karanta.

  Haka ma a harshen Fulani an yi wannan duk da a Hausa Fulani tafiyar daya ce shi yasa komai na su yake zuwa daya musamman da muka samu babban jigo wanda yayi Jihadi tare da kokarin baza ilimi a wannan yanki, Sheikh Usmanu Danfodiyo tare da Sheikh Abdullahi Bin Fodiyo, tabbas sai dai mu bisu da addu'a,amma duk wani kokari na ganin sun samar da ilimi a wannan yankin sun gama da shi, Allah yayi musu rahama Amin.


  Mukhtar Musa Karami, Kano, Nigeria.

Comments

0 comments