Rubutu

Blogs » Abubuwan Al'ajabi » Hausa a cikin Hausa: Kashi na farko

Hausa a cikin Hausa: Kashi na farko

 • Hausa a cikin Hausa,wani salone da Hausawa kan yi amfani da shi wajen isar da sakon magana a dunkule,wanda hakan yana faruwa ne cikin salon ba'a ko jefar da habaici,ko kuma wani abu da ake kira zaurance.


  Kai tsaye zamu fara da daukar wadannan kalmomi masu harshen damo mu yi amfani da su don fahimtar da mutane me ake nufi da Hausa a cikin Hausa.

  Ma'anar kalma mai harshen damo:
  Kalma mai harshen damo tana nufin mutum ya fadi wata magana wacce kai tsaye da wani yake,amma dai maganar ta na ma'ana biyu,ta kowacce ma'ana zaka samu ta bada fa'ida,an fi yin hakan ne a lokacin da ake gargadi ko hannunka mai sanda.

  Harshen damo;
  Abin da yasa ake misalta abin da harshen shi ne,harshen Damo yana da baki biyu,da zarar ya fito da harshen zaka ganshi a rabe gida biyu,wani yayi gabas wani yayi yamma ko kuma Kudu da Arewa,a duk dai yadda ka kalleshi zaka ganshi gida biyu ya kasu.

  Yanzu za mu dauki wadannan kalmomi mu yi amfani da su tare da yin bayanin me suke nufi tare da ma'anarsu.
  1. ZARAR BUNU
  *BUNU
  *DANBOTO
  *FALLO
  *YANTA

  2.JIRAN GAWON SHANU
  *GAWO


  ZARAR BUNU
  Kalmar zarar bunu ana furta tane lokacin da wani yaci amanar wani nasa ta boyayyiyar hanya,abin nufi yana yi ne a boye a hankali har ya kai ga cimma burinsa na cin amanar wanda ya nufa din,abin da ake nufi da Bunu shi ne,wani abu ne da ake samunsa a daji,ciyawace amma mai tsayi sosai,akasarin inda aka fi samunta shi ne tsohuwar makabarta ko kuma iyakar gona,ana dasata a gurin ta girma sosai sai a yanke a gyarata daga nan ake yin wani abu da ita sai ta koma Bunu inda ake yin abubuwa da ita kamar rumfar FALLO (abu ne da ake yinsa mai fadi tare da tsayi daga tsakiyarsa,yana Kasancewa kamar rufin kwano doron zabuwa da Shuci ake yinsa) ko DANBOTO (shi ma dai salon rufi ne na Shuci wanda ake yiwa rumfa ko Rumbu) duk bayan an yi mata YANTA take zama haka.

  YANTA
  Yanta shi ne a shirya wannan ciyawar da ake kira Shuci a daure da igiyar rama ana saka ta ne kamar yanda ake sakar Tabarmar kaba,amma ita da igiya ake yinta kuma bata yin hadi kamar na Tabarmar.

  Ana gama yin yanta to wannan ciyawar ta tashi daga Shuci ta zama Bunu,wanda shi wannan bunu a kauyuka shi ne katangar su,wasu da shi su ke rufin daki,wasu ma daki kai tsaye suke haÉ—awa da shi.

  To idan Bahaushe yace Zarar Bunu to shi wannan abin da nayi bayanin yanda ake hadashi,idan kazo zaka iya zarar wani abu a jiki ba tare da an sani ba,saboda ciyawa ce mai tsayi kamar tsintsiyar laushi,ana Zara mutum bazai Ankara ba sai ta kusa karewa sannan sai a gane.

  Shi yasa ake ambata boyayyiyar cin amana da kalmar zarar bunu.

  JIRAN GAWON SHANU
  Idan Bahaushe yace yana jiran Gawon shanu to yana nufin jira ne yake yinsa na rashin tabbas,kamar dai mutum ya tsaya jiran fitowar gwamna daga gidansa bayan kuma basu yi magana cewa zai fito din ba,ka ga mutum bashi da tabbacin fitowar gwamna din sai dai yayi ta zaman jira idan ya fito ya ganshi in kuma bai fito ba dama ya sa a ransa zai jira.


  Meye Gawo?
  Gawo dai wata bishiya ce ta qaya wacce take fitowa ta girma sosai harma ta yi 'ya'ya,to sai ya kasance 'ya'yan nata suna yiwa shanu da awakai dadin ci sosai,hakan yasa idan shanu suka zo wucewa ta jikin bishiyar da zarar sun ji iska ta kada 'ya'yan sun bada wani sauti sai su tsaya cak suna jiran fadowarsa kasa don su dauka su ci.


  Shanu suna iya kwana a wannan gurin muddin ba korasu aka yi ba,kuma shi wannan dan itaciya yana daukar sama da awanni bai fado ba,amma a hakan basa gajiyawa da jiransa.

  Wannan yasa Bahaushe yake danganta mai jiran da bashi da tabbas da sunan jiran Gawon shanu.

  Za mu ci gaba da yin bayanin irin wannan Dunkulalliyar Hausar a Makala ta gaba insha Allahu.

  Mukhtar Musa Karami, Kano, Nigeria.

Comments

0 comments