Rubutu

Blogs » Abubuwan Al'ajabi » Kowanne mutum yana so ya samu iko irin na mahaukata

Kowanne mutum yana so ya samu iko irin na mahaukata

 • Kowanne mutum yana so ya samu iko irin na mahaukaci,amma babu wanda yake so yayi rayuwa irin ta mahaukata.

  Mahaukaci shi ne wanda hankalinsa da tunaninsa suka samu matsala,shi ne wanda bai san kima da mutuncin kansa ba,shi ne wanda ya manta da ibada,ko da kuwa ya yita to bazai iya aikata ta a yanda ya dace ba.
  Mahaukaci shi ne wanda kwakwalwarsa bata lissafa masa abin daya dace sai na shirme,shi ne wanda in ana zabga ruwan sama bai san ya samu guri ya fake ba, Mahaukaci baya wanka balle aski.

  A wannan yanayin da mahaukata su ke a hakan mutane suna so su samu iko da isa irin tasu,wanda ko shugaban kasa baya iya samun wannan abu da mahaukata suke da shi.


  Meye abin da kowa yake so din?

  *Mahaukata suna iya fadar duk abin da suke so a kowanne waje amma babu wanda zai tanka musu balle ya musanta.

  * Idan Mahaukaci yayi kisa to ya kashe banza,babu wanda zai dauki mataki akansa.

  *Duk abin da mahaukata suka aikata babu wanda zai kai su kotu don yanke hukunci saboda su din daban suke.

  Irin wannan ikon na aikata abin da aka so ba tare da an hukunta mutum ba,babu wanda baya son samun wannan mataki a duniya,amma a hakan babu wanda ya samu,duk mukaminka da karfin ikonka indai ka yi magana akan abu kace haka za ayi to sai an samu wani ya tanka ko da kuwa baya cikin wanda kake mulka,wanda zai iya wannan sai mahaukaci wanda bashi da hukunci balle a hukunta shi.

  Rayuwar mai hankali da mahaukata akwai abin dubawa ga masu cikakken hankali,lafiyar su da tamu ba daya bace,zai yi wuya ka ga Mahaukaci a kwance bashi da lafiya,zafin rana bata fiye yi musu illa ba,sanyi da dukan ruwan sama duk suna shanye shi,suna tafiya babu takalmi,suna daukar abu a bola su ci,ruwa ko na kwata ne Mahaukaci zai sha ya kwana lafiya.

  Wannan kadai ya isa mu gane Allah ya tsarawa kowanne mutum rayuwarsa,babu wanda yake iya bada lafiya sai Allah,shi ne mai kula da rayuwar mai hankali da mahaukata,kamar yanda masu karin magana suka ce KOMAI AYI A GAMA YA FI,WAI MAHAUKACI YA GAMA MAIMAI YA JUYA DA GIRBI.

  Allah yasa mu dace Amin.

  Mukhtar Musa Karami
  Kano, Nigeria.

Comments

0 comments