Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Al'adar Mafarauta da makadansu a bikin sallah

Al'adar Mafarauta da makadansu a bikin sallah

 • A irin wannan lokaci na hidimar sallah,wani abin birgewa ga Mafarauta ko ince Kauraye,suna yin kyautuka amma ga iya masu yi musu kida wanda suke zuwa har gida.


  Kaura,ko Goje shi ne wanda yake fita farauta daji inda suke daukar kwanaki a can don kamo namun dawa,to a irin wannan lokacin akwai wata al'ada da suke yi ta sadaka ga makadansu,su makadan tauri suna amfani da Ganguna biyu ne wajen yin kida,tare da kaho wanda suke busawa in ana kirari,wannan yake baiwa su Mafarauta damar zuwa su kuranta kansu tare da ambaton wani ƙoƙari da sukayi,ko wajen rigima ko kuma wajen kamo Nama a cikin dawa,daga nan kuma wasu suna kirarin suna daukar wuka suna yankawa a jikinsu bata kamawa saboda sun ci magani.

  Kamar yadda suke yin hakan ga Mafarauta to da zarar sallah ta zo sukan dauki karamar Gangarsu su rinƙa bi gidajen Kaurayen suna buga gangar yanda kuma su Mafarautan suke debo hatsi ko shinkafa mai yawa su baiwa masu kidan.


  Suna yin wannan abu ne irin ranar jajibire kuma kwana suke suna yawo gidajen Mafarautan,da zarar sun je kowanne mutum da irin kirarinsa wanda in aka doka gangar komai baccin da yake zai farka ya fito,wasu kuma ana doka gangar sai an fara yi musu kirarinsu Misali akwai wanda ake yiwa kirari da GAGARA KUREN RAKUMI KURA TA BARKA BARE KARE,kowa yaji wannan kirarin ya san na Auwalu Mai kare kadan Bagaza ne,to kowanne kaura ko Goje akwai takensa.


  Da haka wannan masu kidan suke zagaye gidan manyan Mafarauta,kuma suna samun abubuwa da yawa don suma su samu su yi hidimar sallah.


  Kuma ita wannan al'ada ta su suna yi ne a kowanne bikin sallah ba sai sallar da ake yin tashe ba.


  Mukhtar Musa Karami.
  Kano, Nigeria.

Comments

0 comments