Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Abubuwa uku da za ka amfani zamanka da mutane da su

Abubuwa uku da za ka amfani zamanka da mutane da su

 • 1)
  Kowanne guri zai iya yi maka kaikayi kasa hannu ko wani abu ka sosa.
  Amma ka taba tunanin yanda zaka sosa kaikayin zuciyarka? mafi yawan masu sanya maka kaikayin zuciya bazaka gane su ba,saboda kullum suna zuwa gare ka ne da hasken fuska,karka zargi kowa,amma karka saki jiki da kowa,karka janyo mutum ya matsi jikinka,sannan karka yasar da abokan zamanka,dole akwai mai son farin cikinka.
  Aboki ko kawa tamkar fitila suke gareka,baza ka taba iya tafiya cikin duhu babu haske ba dole sai ka haska zaka gani

  2)
  Ba cin amana ne abin haushi ba,ka yarda da mutum ya ci maka amana shi ne damuwar.

  Idan baka shirya cirewa mutum damuwa ba,to karka cusa kanka domin sanya masa wata damuwar.
  Idan har baka shirya baiwa mutum farin ciki ba,to karka rusa masa nasa farin cikin.
  Kowanne mutum yana rayuwa ne iya tasa wanda duk ya takura kansa da bibiyar rayuwar wani to kuwa karshe rayuwarsa zata samu matsala\ud83d\udc4c\ud83c\udffd


  3)
  Ka koyi darasi daga gurin Alkalai zaka samu rayuwa mai kyau,Alkalai suna daukar kowacce irin magana,amma kuma basa amincewa da kowacce magana sai da hujja.

  Karka yarda ka zama malamin kanka,idan ka kasance kullum a matsayin dalibi to kullum zaka kasance mai samun karatu a sadaka,matakin kowacce irin nasara shi ne hakuri da juriya.


  Mukhtar Musa Karami
  Kano, Nigeria.

Comments

0 comments