Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSAKA A WUYANKI: Babi na daya

TSAKA A WUYANKI: Babi na daya

 • A kowanne lokaci idan na kalli kaina na kan fashewa da kuka idan na tuna yadda nake rayuwa da wannan abu a wuyana, Tsaka ce wacce ban san yadda akayi ta zo wuyana ba,itace sanadin da yasa na zama abar gudu a gida da waje,yan uwana da sauran mutanen gari,na zama abar buga misali,na zama kamar kurma bayan ina ji da kunnena,na zama kamar makauniya ina gani amma nake kawar da kai,tsangwama da kyarar mutane duk saboda wannan Tsaka da take manne a wuyana.

  Abin da na kasa ganewa har yanzu shi ne,ni mutum ce ko aljana,ko a Film ko a littafi ban taba jin wani labari makamancin wannan ba

  ..Abu yayi nisa har na daina yarda mu hadu da mutane,ni kenan na killace kaina a daki, koda Makaranta da nake iya zuwa itama abin ya gagara,da zarar mun zauna da 'yan Group dinmu dan yin muraja'a zanga sun tarwatse tare da fadin TSAKA A WUYANKI,na daina shiga dakin Lecture,duk inda na wuce maza da mata sai nuna ni suke kamar watan Azumi,na zama bare a dangina duk mutuncinmu da mace 'yar uwata bata yarda mu zauna guri daya,hatta kananun yara idan na daukesu da zarar sun kalli wuyana to kuwa zasu kwanyare da kuka,na zama abin tsoro ga yara abar gudu ga manya,haka nake zama a daki idan na gaji in ta shi in fita,to yanzu ma kamar kodayaushe fitata keda wuya mukai arba da wasu kannena suna ganina suka hada baki "wayyo aunty TSAKA A WUYANKI" ya zanyi da raina? rugawa sukai da gudu,hawaye naji yana kwaranya a kumatuna ina tsaye na kasa gaba balle in koma baya,zuciyata ta dauki zafi.

  Wacce masiface wannan ta hau kaina?haka rayuwata zata koma? jiri naji ya fara daukata.


  Ko ina na kalla sai inga yana juyawa ganin hakan yasa na dafe bango a hankali na lallaba na zauna dirshan hawaye mai zafi ya ci gaba da ambaliya a kumatuna,hannuna nasa na shafa wuyana kamar kullum ba komai a wuyan nawa.
  "me kike anan? baki yarda ba ko? me yasa ke bakisan kaddara bane?"
  ko ban waigaba nasan me wannan magana mamatace
  "Mama kema haka zamuyi dake,haba mama a idonki 'yan uwana suke guduna......" ban samu damar karasawa ba kuka yaci karfina,tashi nayi na nufi dakina,da sauri naga mama ta biyoni,
  "Haba A'isha ni fa na tsuguna na haifeki ni kuwa ta ya za'ayi in gujeki,kukan da kikeyi ne bana so karki sanya kanki cikin damuwa",tambayar ta nayi
  "wai mama a yanzu haka kina ganin Tsakar a wuyana?"
  "Gata nan kuwa a wuyan naki"
  "to mama me yasa ba zaki sa hannu ki daukemin ita ba?"
  "baki da hankali 'yan nan ni zan sa hannu in taba wannan aba haba A'isha ta duk matan Duniya wa take iya zama kusa dake inba niba?in da bazata illataniba da ba abin da zai hana in dauketa amma kalleta fa!

  Zan mu ci gaba a kashi na biyu
  Mukhtar Musa Karami
  Abu Hisham

Comments

0 comments