Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSAKA A WUYANKI: Babi na biyu

TSAKA A WUYANKI: Babi na biyu


 • "To kuma mama kin yarda kowa na guduna kuma zakice in daina damuwa,mama wallahi har na manta yaushe rabona da bacci,kwana nake a zaune nayi addu'a amma..."
  "karkice haka Aisha Allah yana sane dake kuma zai miki maganin wannan abu"
  shiru tayi tare da kama hanyar fita daga dakin.

  Rayuwa kenan mu kenan duk inda mukaji wani mai magani ko a ina ne to sai munje,tun Abbanmu yana bada kudin zuwa har ya gaji ya daina,yanzu daga ni sai mamata ,koda zaman dakin bana iya samun sukuni muddin Safiyya (kanwata ce 'ya a gurin kishiyar mama) zata shigo to dole,nasha tsaki da bakar magana,in kuwa da sabo to na saba,mamata naga ta kara shigowa
  "sauri ki shirya zamu tafi wurin magani"
  mikewa nayi na dauko Hijab na sanya na bita muka rankaya,muna tafe gabana yana faduwa,
  "wayyo aunty har yanzu tana nan baki cireba zata cijeki fa... Allah aunty gatanan a wuyanki,"
  kannena ne, wai a gida kenan,bare kuma in fita idon duniya,abinma da yafi dauremin kai ta yaya ake iya ganin wuyana bayan kuma a rufe yake ruf da hijab.


  Ji nayi na kasa ci gaba da tafiya,mamatace ta kama hannuna,ganin mun nufi hanyar fita nace "mama Bus zamu hau,kin san fa shiga jama'a laifine a gurina," cewa tayi
  "meye da Bus din da bazaki shiga ba kinga wuce mu tafi"
  ban kara yin maganaba na bita muka fita,muna tafe duk inda muka bi sai an nuna mu wata tsohuwa muka gamu da ita kafin muyi kiliya naji tace "oh zamani kenan yanzu kuma da Tsaka aka koma yin ado ke 'yan nan yaki"
  "ba tsaka bace larura ce Iya" mama ce tafada mata haka
  "yarinya banyi tsufan dana dena ganiba ni gaskiya nake san fada muku hakan bakyau ku daina"
  "to iya mun daina" tafiya mukai muka barta tana ta fadace-fadacenta, "mama kinga abin danake gudu ko? mama yawo cikin jama'a ba nawa bane".

  Jin taki kulani yasa nima nayi shiru har mukaje titi, daga hannu mama ta fara yi tana tare mota,har zanyi magana amma na fasa dan gudun abin da zai biyo baya,mota tana tsayawa mama tasa kafa ta shiga, taka kafata keda wuya naji wata 'yar karamar yarinya tace "wayyo! aunty kalli wuyan wata"


  Ban fasa shiga motar ba dan bana san naji mama tayimin magana
  "yau mun shiga uku Driver tsaya"
  wata mata ke fadin haka yana tambayar me ya faru ni kuma har na samu guri na zauna wacce na zauna a kusa da ita ta waigo ta kalleni bata kula sosaiba naji tace 'Yan mata adon gar..." kafin ta karasa fada ta hango abin da nake gudu ta gani din da sauri ta mike tace
  "ke! badai a kusa daniba ki dauraTSAKA A WUYANKI kuma ki zauna kusa dani ai ni zaman motar ma bazan iya ba ku duba jama'a wata sabuwar kwalliya"

  Da karfi take maganar cikin kwakwazo,nan da nan kowa ya juyo da ganinsa gareni,da yake da yawancin wadanda suke cikin motar matane nan da nan suka cika mota da ihu,masu yara kowacce ta kama hannun yaranta duk sun fita wasu har da yin raunika,me kuwa zan gani.mutanan dake waje sunga anata fita daga mota harda faduwa,sai kuwa suka taho gurin mota dan ganewa idanuwansu abin da yake faruwa,wasu suna fadin wuta ce,wasu kuma suna fadi meke faruwa,waigawa nayi na kalli mama daga ni sai ita muka rage a motar.

  Zan ci gaba a babi na uku

  Mukhtar Musa Karami
  Abu Hisham

Comments

0 comments