Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSAKA A WUYANKI: Babi na uku

TSAKA A WUYANKI: Babi na uku


 • Hawaye ne ya kama zuba a kumatuna,ita kanta mama hawayen takeyi,muna kallon juna ni da ita mukaji yaron mota ya leko tare da fadin
  "Dalla malama ki fito mana daga mota kawai dan tsabar hauka ki daura Tsaka a wuyanki gashi kin korar mana fasinja amma dai ba anan garin kikeba ko?,kai amma anyi asara tunda nake ban taba ganin mace mai kyau kamarkiba amma ki rasa me zaki daura a wuyanki sai Tsaka kai anya kuwa ba aljana ce ba dama naji ance aljanu akwaisu da kyawu kamar jaraba"

  A zuciyata nace kai wannan mutum da surutun tsiya yake
  " Haba hajiya ku muke jira ku fita"
  jama'a kuwa sai lekowa sukeyi kowa na fadin abin daya gadama,na mike zan fita mama tace "tsaya mai mota nawa zamu baka ka kaimu Fanshekara?"
  "kai ba hauka nakeba Ina gani na dauki Aljana a motata wato ku kaini Bangon Duniya dan Allah ku taimaka ku fita"
  "tashi mu fita Aisha"
  "au kaji Bangis A aljanuma harda Aisha"

  Ban yarda na fara fitaba nabar mama ta fara fita,nima na bita tashin hankali jama'a na gani jingim hotona ake ta dauka a waya.


  Abu kamar masifa kowa ya dauko waya sai daukar hotona ake,nidai ba wanda na kalla,wani dattijon mutum daga can nesa naji yana fadin "Haba jama'a yanzu ku haka ake kamar ba musulmai ba dan wata larura ta samu yarinya kun baibayeta kun hanata tafiya"
  ko kulashi basu ba, mamata ta kama hannuna muka kama hanya muka mike gefen titin,yaron mota naji yana fadin
  "nifa yau na samu labarin fada a majalisa Bangis wai kuwa tunda kake ka taba ganin mace mai kyau kamar waccan?"
  "yo banda abinka in akace aljani ai zancen kyau ya kare sufa a yanzu sai su sauya kala sau dubu a lokaci daya bari kaga kafin can sun bace"
  ina ta jiyo sautin maganarsu har mun fara nisa dasu amma ina jiyo wani da yake daga murya yana fadin

  "Su fa aljanu komai abu sai an ganesu kunga dai yanda iya haduwa ta hadu amma ta dauki Tsaka ta daura a wuya" ni kuwa zuciyata sai ta farfasa takeyi,duk wani tashin hankali da ake fuskanta a rayuwa ina kansa yanzu, to waya fada musu yanda aljanu suke da har suke kamantani dasu,kaina ya dauki zafi

  Zan ci gaba a babi na hudu


  Mukhtar Musa Karami
  Abu Hisham

Comments

4 comments