Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSAKA A WUYANKI: babi na hudu

TSAKA A WUYANKI: babi na hudu


 • Ji nake kamar kaina zai tarwatse dan tsananin azabar ciwon da yakemin muna ta tafiya a kafa har muka kai dai-dai Legal,hannuna nasa dan shafa wuyana abin mamaki sai naji Hijab dina yana jikina,wannan abu yana dauremin kai to ta ya ake suke ganin wannan muguwar aba haka a wuyana.

  Tsayawa mama tayi tare da waigowa ta kalleni,tashin hankali na gani gaba daya idonta ya kumbura tare da yin jajur kamar gauta,
  "mama ki daina kuka komai yayi farko zai yi karshe,a yanzu haka wasu suna gadon Asibiti a kwance tashi zaune kawai suke son yi amma baza su iyaba,to mama ni kuma gani da kafata nake tafiya,dan haka mu godewa Allah akan duk halin da muka tsinci kanmu"

  Bata yi magana ba,kallon wuyana kawai takeyi cewa nayi
  "wai mama yanzu haka kina ganin Tsakar a wuyana?" tare da mamakin tambayar da nayi tace
  "gata nan kuwa"
  "to mama wai bakya ganin Hijab din dake wuyana ko akan Hijab take?"
  "ko daya Aisha gata radau a wuyanki ni kam bana ganin komai a wuyanki in ba itaba" "mama zaki iya dora hannuna akanta yanzu?"

  "Ke kuwa 'yannan ta ya zanyi in dauki hannunki in dora akan abin da zai cutar dake kin ga ki zo mu hau Adaidaita sai ya kaimu har can in anje wajan maganin a san yanda za ayi"
  "mama kina ganin abin daya faru damu a mota nidai mama da mun hakura mun koma gida,mu roki Abba ya bamu mota sai akaimu gobe"
  "Aisha baki san halin da muke cikiba amma ki bar wannan magana iya nan kinji"
  bana son yawaita damunta da tambaya dan haka na kame bakina amma zuciyata cike da mamakin wannan abu,hannuna nasa akan Hijab din, nace
  "mama kalli kiga na dora hannun akanta?"
  "Aisha bana son ki takurawa kanki akan abin da ya zama kaddara"
  ta rufe bakinta sai ga mai Adaidata sahu,hannu mama ta daga masa ya tsaya kafin ayi maganar ina zai kaimu mama ta shiga,nima kuwa na shiga "muje malam"
  "ina kenan Hajiya?"
  "Fanshekara zaka kaimu"
  da alama bai lura da abin dake wuyanaba hakan sai yasa naji sanyi a raina,muna tafe har mukaje wajan bada hannu inda zamuyi kwana muna tsaye wata tazo zata shiga,
  "wayyo Allah yau na shiga uku..


  Zan ci gaba a babi na biyar

  Mukhtar Musa Karami
  Abu Hisham

Comments

0 comments