Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSAKA A WUYANKI: Babi na shida

TSAKA A WUYANKI: Babi na shida

 • Ji nayi saura kadan zuciyata ta buga kaina kuwa wani radadi yake min,yanayin maganar da suke gaba daya ta saba da shari'a,ban yarda na kara kula su ba,juyawa nayi na kalli mama,hawaye naga tana yi hakan tasa na cewa mama, mu tafi gida

  "Karya kike yarinya mu ba'a zuwa gurinmu a koma haka keda kike da bakar masifa Tsaka bata fara aiki ba nan gaba zata fara,a sannu a hankali zata hau kan duk wanda kuka zauna dashi,kuma duk wanda ta hau kansa sai ta zuba masa dafi mai bala'i a tare dashi,mu da kike ji da gani mu muka san sirrin tsaka da ita ce tasa kika afka tsaka mai wuya,......."
  ban bari yakai karshen maganarsa ba na katseshi da cewa
  "Ni da in saɓawa mahaliccina gara tsaka ta zama ajalina,dan haka ko kadan bana jimami ko fargabar abin da tsaka zataimin nan gaba,"
  tun kafin in rufe bakina naji Motsi a wuyana, alama nakeji ta nuni da akwai wani kwaro a wuyan nawa,ja da baya na farayi,motsin karuwa yakeyi tare da sahun farata,yarrr... Naji tsigar jikina ta tashi karkarwa na tsinci kaina inayi hakika yanzu na yarda akwai TSAKA WUYANA yawo take ta ko ina tsakanin wuyana da kirjina harma zuwa cikin rigata,naji bazan iya jure hakanba,hannu na nasa wai in taba ko zan jita,wayyo Allah na lagwai-lagwai naji da sauri na janye hannuna,dan jin kamar zan fadi matacciya in naci gaba da taba wannan aba.

  Mamakin da nake mama kallona kawai take kuma taga halin dana shiga amma ko kulani batayi ba,sukur-sukur din da akeyi a cikin Hijabina ya isheni,dan haka na runtse idanuna nasa hannu a karo na biyu na damki Tsakar na matseta tare da janyota da karfin gaske,da sauri na saketa ina kururuwa,dan ji nayi kamar fatar jikina nake janyowa.

  Na rasa yazanyi da raina inda mama take tsaye nan na nufa ina fadin "mama ki taimakamin karshena yazo Tsaka mama yanzu ina jinta a jikina ki taimaka min mama....."
  ji nayi sun kece da dariya tare dacewa
  "indai Tsaka ce yanzu kika fara ganin bala'inta ki sani mu ba'a yi mana wa'azi balle har a hanamu abin da mukeyi,ke dai a haka zaki dauwama har zuwa karshen duniya ba wanda ya isa ya cire miki Tsaka in ba muba,gashi mudin kuma bazamu cire dinba.

  Ras! Naji gabana ya fadi ina matsawa kusa da mama naga itama ta fara ja da baya,tashin hankali, "mama kema guduna zakiyi?"
  daina binta nayi na tsaya cak! Tare da yin dogon tunani wai fa uwar data tsuguna ta haifeni kenan gata da kanta tana guduna,tabbas duk abin daya sa uwa ta guji danta to ba karami bane,to ina ga sauran mutane? Haka zan rayu kenan,na zama abin tsoro ga kowa,ji nayi jinin jikina yana kara gudu tare da juyawar da naga duniya tana yi,kafata kuwa tuni ta nunamin ta gaza da daukar gangar jikina hakan tasa na zauna dirshan..

  Ai zama na keda wuya naji wani abu yayi surr.. A jikina wayyo na shiga uku!

  Zan ci gaba a babi na bakwai.

  Mukhtar Musa Karami
  Abu Hisham

Comments

0 comments