Rubutu

Blogs » Noma da Kiwo » Shinkafa da Manomanta a Arewacin Najeriya

Shinkafa da Manomanta a Arewacin Najeriya

 • A kullum daraja da Alfanun shinkafa yar Hausa karuwa yake yi,musamman da ya kasance a yanzu tana dab da zuwa,yayin da kamfanonin shinkafa suka bazama har gonakin da ake noma shinkafar suna saye tun kafin a kai ga girbeta.

  A rubutun daya gabata na Shinkafa mun yi bayanin yanda kamfanin sarrafa shinkafar ya wadata a Arewacin Najeriya, yadda har ta kai ta kawo yanzu idan ka duba yankin karamar hukumar Kura ta jihar Kano inda nan ne cibiyar noman Shinkafa a Arewa,zaka iske turawa da Wakilansu,haka Indiyawa da yan China suma duk da Wakilansu dama masu kudinmu nan da suka bude kamfanin sarrafa shinkafa, sun je sayen shinkafa wacce ko girbinta ba a yi ba.

  Ta wata fuskar wannan abin ci gaba ne a gurinmu,musamman da Allah ya wadata Arewacin Najeriya da kasar noma wacce ko me aka shuka zai fito kuma a ci.

  Tun bayan da Shugaban kasa Muhammad Buhari ya halarci bikin bude wani babban kamfanin sarrafa shinkafa a Gunduwawa da ke karamar hukumar Gezawa jihar Kano,wannan ya kara baiwa masu ja da baya wajen bude kamfani damar yin na su kamfanin musamman na sarrafa shinkafa,inda a yanzu haka an samu kamfanunuwa sama da hamsin a rukunin,kuma kowanne yana sarrafa shinkafa mai tarin yawa.

  Manoman Shinkafa suna ta karbar kudaden nomansu tun kafin su girbeta,hakan yana basu damar kara shirin noman wata ta hanyar tanadi na taki da sauran su,tabbas ta wannan ɓangare mun samu ci gaba sosai,idan muka duba yanda kasuwar shinkafa ta Gezawa ta cika da shinkafa samfera abin dai sai sambarka.

  INA MATSAKAR TAKE?
  Duk da nasara da ake samu ta yawaitar shinkafa me yasa har kullum shinkafar take yin tsada? A dan wani bincike da na yi game da hakan yana da nasaba da yawan cin ta mu ta gida da hankalin kowa ya dawo kai,a baya iya talaka ne yake cin irin shinkafar mu ta gida,to yanzu kuma kasancewar tana samun gyara wanda idan kasa hannu ka debi wacce aka sarrafa za ka yi mamakin yanda ashe mu ma ta mun da muke nomawa mai kyau ce rashin kayan aiki ne yasa muke yi mata kallon rashin kyau.

  Hakan yasa bayan an samu ci gaban kamfanin sarrafata sai masu kudi da sauran wacce ake fita da ita waje yasa ta yiwa talaka nisa,to amma kuma har yanzu masu sarrafawa da hannu,masu dafa samfera a tukunya suna nan suna ci gaba da yi daga gefen kasuwar Gezawa idan ka tafi hanyar zuwa Gumel,haka ma a yankin Kura sunan nan ana ta yi.


  Idan muka lura da kyau za mu fahimci wani abu game da wannan noman da wasu ke ganin ci baya ne,yayin kuma da wasu suke ganin daraja ce muka samu ta musamman.

  1. Na farko mun samu ci gaba maimakon mu jira a kawo mana daga wasu ƙasashen yanzu mu ne muke bayarwa.

  2. Mun samu yawaitar manoma ta yanda wasu da yawa sun samu arziki ta hanyar noman shinkafar.

  3. Ta dalilin yawaitar kamfanonin shinkafa mutane da yawa sun samu aikin yi zaman banza ya ragu sosai.

  4. Muna samu mu ci shinkafarmu ta gida cikin aminci,ga gardi da santsi duk ta dalilin sarrafawa da take samu mai kyau.

  5. A hankali kuma mutanenmu suna koyon bude kamfani da kansu musamman na sarrafa ita shinkafar maimakon turawa ko kwarori da yan China da a baya su kadai muke ganin suna bude kamfani.


  Tabbas mun samu babban ci gaba da ya kasance mutanen kasarmu sun fara fahimtar zuba kudaden su wajen noma yayin da wasu suka zuba kudaden su wajen bude kamfanin sarrafa shinkafa.  Mukhtar Musa Karami, Kano Nigeria

Comments

0 comments