Makalu

Darasin physics akan motion, force da kuma friction

 • A yau ma kamar kullum zamu kawo bayanai ne dangane da ilimin kimiyya da ya shafi physics, kuma za mu maida hankali ne akan motion, force da kuma friction.

  Kamar yadda a baya cikin bayanan mu na baya akan kinematics da dynamics, mun ce shi KINEMATICS reshe  ne na physics da yake lura da yadda motion yake aukuwa ko faruwa. A inda shi kuma DYNAMICS (shi ma reshe ne na physics) yake lura da yadda motion yake faruwa sa’annan kuma yana kokarin sanin abunda ya jawo aukuwan motion din. Abunda ake so dalibi ya sani a nan shi ne, ya iya gane kowani kalar motion sannan kuma ya san misalan su kamar yadda zamu kawo bayanai a cikin wannan makala.

  MOTION

  Ita ‘motion’ tana karkashin kinematics ne, wanda kuma tana nufin ‘tafiya’ ko kuwa mu ce canjin guri da abu ke yi ta yadda ake lura da lokacin aukuwan canjin. A harshen Turanci zamu iya cewa motion is the change in position of a body with time with respect to a reference point. Or motion is the movement of a body from one point to the other. Ita motion tana aukuwa a dukkan naukan ‘matter’ (state of matter – solid, liquid and gas), kuma motion na kasancewa a yanayi daban-daban. Misalan motion suna nan kamar haka, movement of the earth round the sun, rotation of the sun about its axis, an aeroplane flying in/on the sky and a man walking or running.

  Rabe-raben motion (types of motion)

  Ita motion an kasa ta ne kamar haka;

  1. Random motion
  2. Translational motion
  3. Rotational motion
  4. Circular motion
  5. Oscillatory or vibratory motion
  6. Relative motion

  Random motion: Wannan nau‘i na motion ba ya da “direction”, wato abun na tafiya ne a ko ta ina kawai, wani lokaci ana kiran wannan nau’in zig-zag motion. A Turance zamu iya kawo shi kamar haka random motion is the movement of a body in a zig-zag or disorderly manner with no specific direction. Misalan irin wannan motion sune; motion of dust particles in air, the motion of smoke particles da motion of butterfly da sauransu.

  Translational motion: Wannan nau’in motion kuma shi ne idan mutum ko abu ya tafi straight babu kaucewa. A Turance zumu iya cewa is the type of motion whereby a body or an object moves in a straight line. It is also called rectilinear motion. Misalan wannan nau’in motion ga su kamar haka; walking from one wall of a class to the other but in a straight line, da kuma dropping of fruit from tree to the ground.

  Rotational motion: Wannan shi ma wani nau’in motion ne dake faruwa idan tafiyan abu ya kasance yana FORMING CIRCLE ta yadda kuma abun zai kasance yana makale a guri guda. Muna iya kawo shi a Turance kamar haka; this type of motion occurs when a body moves in a circular path about its axis. Misalan sa na nan kamar haka; the rotation of the blades of fan, the rotation of a wheel about an axis, the rotation of the earth about its axis da sauransu.

  Circular motion: Shi circular motion yana aukuwa ne idan asali dama akwai CIRCLE sai kuma abu ko mutum yazo ya zagaya shi CIRCLE din. A Turance zamu ce is a type of motion in which an object or a body moves round a circle and in this kind of motion the speed is constant. Misalin irin wannan nau’in motion sune, movevement of the earth round the sun, movement of a car around a round-about da sauransu.

  Oscillatory or vibratory motion: A wannan irin motion kuma abun (wato object) yana tafiya  gaba ne sa’annan sai kuma ya dawo baya, wato to and fro ko kuma abun ya tafi sama ya dawo kasa. A harshen Turanci kuwa zamu iya kawo shi kamar haka ‘this is the motion of a body in a to and fro manner about a fixed point’. When a body moves to and fro about a fixed point we say, the body is oscillating. Misalan su sune, motion of the balanced wheel of a wristwatch, motion of a simple pendulum, motion of a loaded test-tube inside water da sauransu.

  Relative motion: Wannan irin motion yana faruwa ne idan mutum na tafiya a cikin mota sai ya ga kamar itatuwa ma suna tafiya. A Turance muna iya rubuta shi kamar haka, ‘relative motion is the motion of an object with respect to a reference point (mun yi bayani a baya akan reference point)

  EXERCISE:

  1. Write a short note on the following:

  a) vibratory motion

  b) translational or displacement motion

  c) random motion.

  2. Differentiate between rotational and circular motions.

  3. mention three types of motion you know with at least one example each.

  CAUSES AND EFFECTS OF MOTION

  Sir Isaac Newton (wani masanin physics) ya yi bincike akan motion ta yadda ya gano cewa kowani abu (object) na kasancewa ne a gurin da aka ajjiye shi (wato state of rest –inertia). Idan ka ga ya bar gurin da yake akwai abunda ya sa shi barin gurin, sannan sai ya ce wannan abun kuma shine FORCE.

  Kuna iya duba makalar mu da ta yi bayani akan yadda ake samo equation na motion da misalan yadda ake amfani da shi wajen amsa tambaya a physics.

  FORCE

  Shi kalmar force a fannin ilimin lissafi da fasaha, wato physics, na iya daukar ma’anar duk wani abu da ke iya sa wani abun ya tafi ko ya tsaya guri guda. Force, vector quantity ne domin yana da ‘MAGNITUDE AND DIRECTION’. A Turance zamu iya cewa, ‘force is the push or pull or is that which changes or tends to change the state of rest or a uniform motion of a body. Unit na force shi ne: NEWTON(N).

  TYPES OF FORCE

  Force iri biyu ne, ko ya kasance; contact force ko kuma field force. Contact force shi ne force dake existing, wato kasancewa, tsakanin bodies guda biyu da suke manne. Misalan sa sune friction, upthrust, reactional force, thrust, tension da sauransu.

  Field force shi ma force ne dake existing sakanin bodies guda biyu amma wadanda basu manne ba ko basu tare. Misalansu su ne, electric force, magnetic force, gravitational force da nuclear force.

  Friction: Force ne dake opposing relative motion kuma yana faruwa sakanin bodies ko abu guda biyu dake tare ko manne. Friction can be defined as the force that opposes the relative motion between any two bodies or surfaces in contact.

  Shi ma friction ya rabu gida biyu, akwai dynamics friction da static ko limiting friction.

  Static friction shi ne frictional force dake existing sakanin surfaces guda biyu kafun su fara tafiya ko kuma lokacin da zasu fara tafiya. Amma shi Dynamics frition, frictional force ne dake faruwa yayin da surfaces guda biyu suke cikin tafiya.

  LAWS OF SOLID FRICTION DA KUMA CALCULATION AKAN FRICTION

  Laws of friction: Friction yana da laws  guda biyar kamar yadda zamu gan su:

  Na farko: friction is always opposing motion.

  Na biyu: Friction depends on the nature of surfaces in contact. Abunda ake magana anan shi ne friction between two rough surfaces is greater than the frictional force between smooth surfaces.

  Na uku: It does not depend on relative speed between the surfaces.

  Na hudu: Friction does not depend on the area of the surfaces in contact. Sai kuma na karshe

  Na biyar: Frictional force is directly proportional to the normal reaction(R) between the two surfaces in contact . A nan zamu iya rubuta shi mathematically kamar haka:

  Ta yadda m = mass na body, g = acceleration due to gravity.

  Kafin ku yi exercise din idan kuna so kuna iya duba wannan makala da ta yi darasi akan banbancin dake tsakanin mass and weight, dimension, position, distance and displacement.

  EXERCISE

  1. Define force
  2. Mention the two types of force and give two example each.
  3. Mention three laws of friction you know.

  Tambaya ta farko: A crate slide down an inclined plane such that the frictional force opposing its motion is 40N. If the normal reaction of the plane on the crate is 50N, calculate the coefficient of dynamics friction.

  Shi coefficient of friction bai da units haka za a  bar shi.

  Zaku iya samun karin bayani kan friction a cikin makalar mu ta gaba game da circular motion.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All