Rubutu

Blogs » Tarihi da Al'adu » Yadda al’adun aure ke gudana a kasar Nijar 2

Yadda al’adun aure ke gudana a kasar Nijar 2

 • Wannan cigaban maƙalar farko ne mai ƙunshe da gamsassun bayanai a kan al’adun aure a jamhuriyar Nijar wanda ni Real A’icha Hamisou Maraɗi ta gabatar a zauren Marubuta da ke nan taskar Bakandamiya. A wannan lokaci maƙalar ta yi bayani ne mai faɗi a kan al’adar ƙunshi da sanya amarya da ango a lalle har zuwa ga yadda ake wanke ma’auratan da sauran shagulgulan da ake aiwatarwa a wannan tsakani.

  Assalamu alaikum jama'a Barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a cikin wannan shirin namu. Fatan na same ku lafiya? Ya gida ya haƙuri? Allah Ya ƙara mana shi.  Fatan alkairi a gare ku gaba daya ahalin Bakandamiya na gaishe ku kyauta Admin da members na gidan MARUBUTA.

  In ba ku manta ba a shirin da ya gabata mun tsaya a daidai inda na ce maku ana yi taro tsakanin ƴan'matan amarya da abokan ango, suna yi meeting wa junansu. Yadda meeting ɗin yake shi ne kafin zuwan ranar ango zai kira amarya ya faɗa mata rana kaza akwai meeting, ita kuma sai ta fara kiran kawayenta tana faɗa masu rana kaza akwai meeting tare da abokan  (yawanci bayan sallar la'asar ake yi). In ranar ta zo sai ƴan'matan amarya su taru gidan su amarya zuwa la'asar , in sun iso sai su yi shawara wa junansu abubuwan da za su rubuta wanda angaye za su ba su in sun je wajen su. Bayan sun gama tsarawa sai guda cikinsu ta rubuta saman takarda. Sai a kira angaye a ce masu su zo su ɗauki ƴan'matan amarya, in kuma sun zo to sai su kwashi ƴan'matan amarya cikin mota su kai su inda za a gudanar da taron. Bayan an je an gaisa sai ɗaya daga cikin ƴan'matan amarya ta karanta takardar da suka yi rubutu a kai angaye suna saurare bayan ta gama su ma sai su ce ga abubuwan da su bayar sai ayi tattaunawa kowa yana magana wa junansu.

  • Ga abubuwan da ƴan'matan amarya suke cewa a ba su kamar haka:
  • Kuɗin kunshi
  • Kuɗin kari (breakfast)
  • Kudin kujeru da runfa
  • Kuɗin abincin ƴan'matan amarya ranar aure
  • Kuɗin damu
  • Katon Chewing-gum
  • Juice
  • Da sauran su

  In angayen ba su da mako nan da nan ake gamawa in Kuma masu mako ne sai ayi ta fafatawa.

  Bayan an gama sai su faɗi ranar da za su kai masu kuɗin da suka yi masu alkawari, wasu kuma tun ranar suke bayarwa kun san kowa da kalar halinsa. Daga nan sai su ba ƴan'matan amarya lemon su zo tafi da shi, wasu kuma tun can suke raba shi. Da suka gani yawanci wasu ba su sha a can suna jin nauyi sai suke bada shi ana tahowa da shi gidan amarya sai sun je can su raba. Sai su mayar da ƴan'matan amaryar gidansu amarya wasu kuma a kai su har gida in suna buƙatar hakan.

  Yanzu bari in ɗauki kowane ɗaya daga cikin abubuwan da na lissafa a sama in yi bayaninsu.

  Ƙunshi: wata al'ada ce ake yi a ranar a sanya amarya lalle da washegarin ranar. Yadda ake yi shi ne, amarya za ta wuni gidan wata ƴar'uwarta ko kuma kawarta. Za a yi masu girki mai daɗi su da angaye. Amma na angaye ya fi daɗi gaskiya za su zo su ɗauki abinci su bayar da kuɗi. Tun da safe ƴan'mata amarya da amarya suke zuwa  amma angaye bayan suke zuwa ɗaukar abinci.

  Kari (breakfast): akwai ƴan'mata amarya masu kwana a gidan amarya in ta shiga lalle, su ne angaye suke ba su kuɗin breakfast.

  Kudin kujeru da runfa: ana ɗauko kujeru da runfa wanda ake zaman biki da su, sai angaye suke bayar da kuɗi.

  Kuɗin abincin ƴan'matan amarya ranar aure: abincin ƴan'matan amarya ranar biki, angaye suke ba su kuɗi sai su yi girkinsu ba tare da sun sha iyaye kai ba, in kuma ba su iya girkin suna ƙarawa iyayen sai su zuba masu abincin. Wasu kuma ko da an ba su kuɗin ba su girkin sai dai iyaye su zuba masu. Ya dangata.

  Damu: Al'adar damu ita washegari da amarya ta kwana gidanta, sai a dama fura daga gidan amarya a zo da ita gidan amarya a rarraba wa mutane( yanzu kuma ba kowa yake yin fura ba,wasu yagourt wasu kunun hamsa, ya dangata dai). Sannan kuma sai a yi wani abu da ake kira "HE". Shi wannan "HE" ɗin iyayen amarya ne za su ba ango kuɗi da kayan abinci,sannan a ba mahaifiyarsa bugun shinkafa da jarkar mai,da turmin atanfa da sauran abubuwa,shi kuma uban angon sai a ba shi sallaya da kuɗi. Yayannun ango , ƙanensa, cousin ɗinsa, kakanninsa, kishiyar mamarsa,matar yayannunsa,matan ƙannensa. Duka ake ba su wani abu ko da ba shi da su. Sai dai ba wasu kuɗi ba ne masu yawa. Duk ango ne ake ba kuɗi mai yawa. Wannan al'adar tana da karfi sosai a wajen hausawa duk wacce iyayenta ba su ba angi wani abu ba kun san halin mata da tsegumi sai an yi da su.

  Bayan an gama "HE" sai a ba ƴan mata furar da ake yi su kai wa angaye, ko su zo su ɗauke su ko kuma su shiga adedeta sahu su iske su. In an je can sai a dinga zuba masu cikin cup suna sha in sun gama su ba mu kuɗi. Sai mu damu gidan amarya ko kuma mu wuce gidanjenmu sai a raba kuɗi.

  Katon Chewing-gum: ita angaye suna kawo ta ne saboda zaman lalle da ake yi a da(duk da yanzu wasu sun bar yin sa.shi zaman lalle yadda ake yin sa in amarya ta shiga lalle ne sai angaye da ƴan'matan amarya su zo kofar gidansu a jera kujeru ana hira, ana yi ana cin chewing-gum). To duk da kaso mafi yawa yanzi ba su yin shi amma sai sun kawo ta. In sun kawo sai a ba uwar amarua kwali uki ko huɗu sai a aje sauran har bayan biki sai a raba.

  Ranar da amarya za ta shiga lalle, tun da asuba wata mata za ta shafa wa amarya lalle. In safiya ta yi kuma sai iyaye su yi jikon ruwan lalle da amarya take wanka da su tun farkon shigarta lalle har zuwa ranar ɗaurin aure. Gaskiya ban san sunayen abubuwan ba saboda in an je siye sai dai a ce wa masu siyarwa su haɗo kayan da ake jikon lalle amma bari in faɗa maku wanda na sani.

  • Lalle sansami (wanda ba a daka ba)
  • Hano
  • Ɗoɗowa
  • Kaɗa
  • Jema
  • Sassaken waru
  • Farar albassa

  Da sauran su waɗanda ban sani ba. In an haɗe su sun jiƙa sai a sanya kaɗa. Zuwa ƙarfe goma amarya da kawayenta za su tafi wajen kunshi, wacce ba ta samu damar zuwa ba tare da amarya sau dai ta iske su a can.

  Na ɗan yi mantuwa kaɗan. Kafin angaye su tafi in sun zo ɗaukar abinci suna ba ƴan'matan Chewing-gum wacce suka yi masu alkawari. Bayan sun tafi da abinci sai su samu wani waje su ci gabaɗaya, wani lokaci kuma tare da 'Camera man' suke tafiya yana ɗaukar su hoto da bidiyo. In sun gama cin abinci sai wasu su dawo da motoci su kai ƴan'matan amarya gidan wanka. Wasu kuma ba su kai ƴan'mata gidan wanka sai dai in sun zo kunshi su ba su kuɗin adaidaita sahu su hau. Sannan su tafi gidan uwar amarya wacce ita ma can ta tara mutane waɗanda za su zo wanka amarya waɗanda tun ana gobe sanya amarya lalle take aika masu da Chewing-gum wacce ita ce abun gayyatar tasu. Sai an ɗauko mata a mota a taho da su gidan da za a yi wankan amarya.

  Su kuma ƴan'matan amarya daga gidan za su wuce gidan wankan amarya wato uwar wanka.  Uwar wanka ta kasance cikin dangin mahaifiyar amarya ko kuma ƙawar mahaifiyar amarya ta kusa ɗin nan.

  Ita uwar wanka ita ce wacce za ta yi wa amarya kayan damu( kayan damu kaya ne sosai wanda uwar wanka za ta jajirce ta siye su. Wata mata ma tun yarinya kafin ta samu miji take siyen kayan tana ajiyewa saboda kar abun ya zo mata a bazata. Wato kayan damu kaya ne wanda amarya za ta yi amfani da su a gidan mijinta wato kwanonin cin abinci, tukunya, murhu, bokiti manya, da sauran kayan amfani. Kayan suna da matuƙar yawa gaskiya kuma ana kashe kuɗi gaskiya ba laifi).

  Yanzu a wannan zamaninmu har shagali ake yi gidan wanka saboda nan ma uwar wanka tana dafa mana kayan daɗi in an zo mu ci abinci in akwai hali akwai zuciyar yi kuma wanda in ƴan wankan amarya sun zo ake zuba masu su ci. In kuma babu halin haka sai dai a sha ruwan gumba.

  Yadda ake yin wankan amarya shi ne

  Ruwan lallen da aka jiƙa su ne ake tararewa (tacewa kuke cewa ko) sai a zuba a cikin bokiti sannan sai a zuba wasu ruwa sannan a rakka amarya banɗaki tare da mata biyu ta wajen uwa ta wajen uba. Wasu iyayen su suke yi mata wanka da kansu wasu kuma bari suke yi ta yi da kanta. Wannan ruwan lallen su ne ruwan wanka amarya har zuwa lokacin da aka ɗaura aurenta. (Ban san yadda ake yin wanka ba ni dai ina gani suna shiga banɗaki kuma ban taɓa tambaya ba).

  Bayan an gama wanka sai a dawo gida, sai kowa ya tafi gidansu. Washegari ma ana tafiya wajen kunshi kamar yadda aka yi jiya amma in an gama gida za su dawowa.

  A ranar ake yi wanka ango. Shi kuma da dare ake yinsa bayan isha'i. Shi ma kamar wankan amarya saboda tare da abokansa za a tafiya kuma da iyayensa. Sai dai shi ango da kansa yake yin wankansa. Bayan an gama wanka uban wanka sai ya dinka wa ango dogayen kaya na shadda. Bayan an gama wanka sai a ba shi kayansa ya taho da su gida.

  Zan dakata a nan sai wani mako idan Mai kowa mai kowa Ya kai mu.  Fatan alkairi ga masu bibiyar wannan shirin.na gaishz ku kyauta na kuma gaishe ku. Jinjina gare ku waɗanda suke ba ni kwarin gwiwa.

  Nana A'isha ta Maraɗi ce take yi maku fatan alkairi.

  BISSALAM

Comments

0 comments