Makalu

Kaico da Halina: Babi na Daya

 • MARUBUTA

  Binta Garba Saleh

  Ummu Nabil

  Miss Xerks

  SADAUKARWA

  Ga duk wani marata

  TUKWICI

  Gaskiya Writers Association

  Alhamdulillahi Ala Ni'matul Islam. Muna Farawa Da Sunan AllAH Madaukakin Sarki Mai Rahma,Wanda Jin kansa Ya Cika Ko'ina, Tsira Da Amincinsa Su Tabbata Ga Shugabanmu ANNABI MUHAMMADU (S.A.W), Ya Allah Muna Rokonka Kasa Yanda Muka Fara Lafiya Mu Gama Lafiya,Ya Allah Ka Bamu Ikon Fadakar Da Al'umma Abinda Zai Amfanemu Baki daya,Ka Kuma Tsare Mana Harsukanmu Daga Fadar Abinda Zai Cutar Damu Da Al'umma Baki daya,Ya Allah Ka Kauda Idon Makiya Mahassada Akanmu,Ya Allah Kayi Mana Sakayya Ga Duk Wanda Ya dauki Hakkinmu Ba Tare Damun Masa Komai Ba,Sannan Kuma Ya Allah Ka daukaka kungiyar Gaskiya Writers Da Mutanen Cikinta Baki daya, Ka Kau Da Fitina Ka Wanzar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Juna, Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

  Ba mu yi wannan littafin Ba Domin Cin Zarafi, Hakikanin Labarin Ya Faru Ne A Gaske, Tin Daga Farkonsa Har karshensa Ba kirkira Bane *GASKIYA* Ne, Sai Dai Mun dan Sauya Wani Abu Tare Da karin Abubuwan Da Ba'a Rasa Ba.

  SAREWAR BINTA G. DAUDAWA

  SHAFI NA 1

  TAUSAYI

  Tun daga tsakar gida inda suke magana da mahaifin nata ta baroshi a guje zuwa d'akin mahaifiyarta tana kuka tana cewa.

  "Don Allah Umma kiyiwa Abba magana nina ce bana son sa, ya barni na auri Mumin, idan har ban auresa ba zai ce naci amanarsa, kuma ni babu Wanda nake so sai...".

  Wuf mahaifiyyarta tayi ta rufe Mata baki tare da rungumeta ajikinta saboda gudun kada ta ida fad'ar abinda yake zuciyarta.

  Don muddun ta ida akan kunnen mahaifin nata har ita bazai raga mata ba.

  Ashe sadda ta rugo d'akin kusan tare dashi suka iso, tsaye kawai Yayi Yana kallonsu cikin k'unar rai.

  Rufe bakin nata Yayi dai-dai da daka masu tsawa da Yayi.

  "Miye abin rufe mata baki?, Ki barta ta fad'a Mana tunda ta Zama tattiriyyar Mara kunya, ana fad'a tana fad'a".

  "A'a Malam,kaga kabi d'iyar nan ahankali don ka samu tabi abinda kakeso".

  Gyara tsayuwarsa Yayi tare da d'aga hannunshi ya dafe k'yauran d'akin ya kallesu shek'ek'e yace,

  "Wallahi Babu fashi, babu mai canja min maganata, Kuma bazan taba yarda kuyi Mani bak'in ciki ba".

  "Innalillahi wa Inna ilaihirraju'un".

  Abinda mahaifiyarta ta fad'a kenan saboda bak'in cikin maganganun da yake fad'a.

  Dalla mata harara yayi yaci gaba da kallonta ta saman idonshi yace,

  "Mi kike nufi? ni kikeyiwa salati?, To wallahi ki kiyaye ni saboda idan bakiyi sannu ba yanzu na gasa Maki jiki".

  Yana fad'ar haka ta d'ago Kai ta kalleshi ta had'iye miyan dake cikin bakinta,Kuma ta Gaza ce mashi komai.

  Murmushin mugunta Yayi masu sannan ya daki k'yauran d'akin  duk gaba ki d'ayansu sai da suka zabura don tsoro.

  Dan ita Mu'umina har tasa duka ya kawo mata tayi ta maza ta janye k'afafuwan ta ta k'ara duk'unk'unesu jikinta Yana rawa.

  Ganin haka Ya sheke da dariya yace,

  "K'aryar banza kawai, idan kin San kina da tsoro kiyi abinda na Sanya ki mana, to ki sani Babu fashi, ko kina so ko baki so Muhannad ne mijinki Sha Sha Sha kawai wadda bata gaji arziki ba, Kuma ki shirya nace Masa anjima yazo".

  Yana kaiwa Nan Mu'umina ta Kwandara k'ara tana kara rik'e mahaifiyyar ta tana cewa,

  "Don Allah Umma ki taimaka Mani ki hanashi yi Mani auren Dole".

  Juyawa Yayi tare da Jan uban tsaki Yana cewa,

  "Ba kuka ba, ko na jini zakiyi banga shegen da zai Hana ni aiwatar da abinda nayi niyya ba, auran Muhannad ba ,ko gawarki zan kai sai kin auresa".

  Bin shi tayi da idanuwanta da suka kad'a sukayi jajir saboda halin bak'in cikin da take aciki.

  Cikin zuciyarta take fadin _Mutum kamar ba musulmi ba ace Babu imani kwata-kwata ajikin Mai rai.

  K'utawa tayi sannan ta mayar da hankalin ta akan y'ar ta dake ta faman risgar kuka baji ba gani.

  "Haba Mu'umina irin wannan kukan haka zai iya jawo maki ciwon da zai illata rayuwarki, ki share hawayenki ki mik'a lamarin ki ga Allah kinji ko, babu abinda yafi karfin adu'a".

  Da sauri Mu'umina ta d'ago kanta fuska share-share da hawaye harda majina tace, 

  "miye aibun Mumin da har Abba bai son Shi iyi Umma?".

  Mahaifiyyarta ta gyad'a Kai cikin damuwa tace,

  "baida wani aibu Mu'umina, Sai dai laifinsa d'aya rashin kudi da bai dasu, Kuma wannan ai daga Allah ne".

  Mu'umina ta tashi daga jikin mahaifiyyarta ta zauna dirshan agabanta tana share hawayen dake fuskarta tace,

  "Don Allah Umma ki kwatanta wa Abba da yardar Allah shima Mumin d'in yau da gobe zaiyi kud'in, Kuma duk abinda yakeso zanyi mashi alokacin tunda nima makaranta ta zan cigaba dayi har in Sami aikin da zan rink'a taimaka maku".

  Tausayi sosai ya kamata na y'arta saboda ba tun yanzu ba tun tana y'ar mitsitsiyarta take da wannan zuciyar tason ta taimaka masu anan gaba, Amma mahaifiinta ya gaza gane haka.

  Hannu tasa ta share mata hawayen da suka rage tace, 

  "Yi shiru y'ata kiji abinda zan fada maki, ni bana ra'ayin abinda mahaifinki yake yi, amma kuma da gani harke bamu da yanda zamuyi dashi tunda duk ak'ark'ashin inuwarsa muke".

  Mu'umina tayi ajiyar zuciya ta rik'o hannunta jikinta Yana rawa tace,

  "Umma na amma kinsan fa halin mutumin da Abba yakeso ya aura mani, mashayin giyane Kuma Mai neman Mata fasik'i, don a yanda naji babu irin laifin da bai aikatawa Wanda Allah ya hana".

  Wani d'aci mafiyyarta taji acikin zuciyarta, ace k'aramar yarinya har tasan illar irin wad'annan laifuffukan Amma Shi babba dashi idanuwansa sun rufe.

  Jawota tayi ta rungume ta tsam ajikinta tana shafa bayanta saboda yanda taga Mu'uminar tana mayar da numfashi da k'arfi alokacin da take lissafin miyagun ayyukan Muhannad d'in.

  Sun Jima a haka tana rarrashinta sannan tasa ta tashi ta nufi d'an kurkuk'un d'akinta.

  Ajiye jikkar makarantar ta tayi ta zare uniform d'in dake jikinta, Amma daka ganta kasan jikinta baida wani k'arfi.

  Ada sadda ta dawo daga makaranta wata irin yunwa takeji, Amma haduwar da tayi da mahaifinta yasa ayanzu ko yunwar ma ta daina ji.

  Wanka tayi ta gabatar da sallar azahar dake kanta.

  Y'ar simple kwalliya tayi ta saka riga da wando na parkistan pink colour.

  Kayan suna amsarta saboda duk sadda ta Sanya su Sai kayi zaton daga Indian tazo, saboda Mu'umina tana da tsananin kyau kominta a tsare yake yanda kasan ita tayi kanta.

  chocolate colour ce irin kalar indiyawan asali su ba farare ba Kuma ba bak'ak'e ba.

  Mu'umina doguwace ba can ba, Kuma tana da girkakken jiki.

  Boost d'inta cike yake da dukiyar Fulani irin girkakken tasa, sannan Kuma cikinta a d'ame yake don idan ka ganta Sai kayi tsammanin bata cin abincin kirki, duk da tana k'aramar yarinya kuturinta acike yake don tana da hips sosai.

  Kai duk wanda yaga Mu'uminah tana tafiya dole ya kalleta ya kuma sake kallonta.

  Shiyasa idan tasa uniform d'in makaranta Sai ta kawo k'atuwar abaya ta zira yanda zata rufe jikinta sosai.

  Turo k'ofar d'akinta da akayi yasa ta d'ago idanuwanta tana kallon Mai shigowa.

  Ummar ta ce  d'auke da kwanon abincinta tana cewa, "Ashe bakici abincin nan ba?".

  Mu'umina ta b'ata rai tace, "Umma na k'oshi ne".

  Girgiza kanta tayi tare da samun wuri bisa y'ar soshashshiyar katifar Mu'uminar ta zauna tana cewa,

  "Duk abinda zakiyi banda zama da yunwa, matso kici abincin".

  Haka ta zauna da Hannunta ta rink'a bata abincin, tun tana amsa badon tana Jin dadin shi ba har ta fara dagewa taci gaba da amsa.

  Abinci taci sosai har sai da ta rink'ayin kamar zatayi amai sannan ta k'yaleta.

  Kusan yau haka Mu'umina ta wuni acikin d'aki har zuwa k'arfe biyar na maraice yaro ya shigo yace,

  "Ance ana sallama da Mu'umina inji Mumin".

  Karaf akan kunnenta, aikuwa ta zabura tare da surar abayarta ta nufi d'akin mahaifiyarta.

  Durk'usawa tayi agabanta ta sunkuyar da kanta k'asa tace,

  "Umma ki taimaka Mani Mumin yana waje Yana kirana".

  Numfasawa tayi kawai ta zuba Mata idanuwanta tana kallonta.

  Jin tayi shiru yasa Mu'umina ta fara zubar da hawaye tana sa Hannu tana sharewa.

  Umma duk taji tausayinta ya kamata, don haka  shahada kawai tayi Saboda tasan Abbanta ya hanata fita tace,

  "Tashi kije amma kada ki dad'e".

  Share hawayen tayi tace, "na gode Umma na gode".

  Da sauri ta nufi k'ofar gidan gudun kada ta gamu da Abbanta ya korota.

  A inda suka Saba Zama ta sameshi bisa sock away na sabon gidan dake jikin gidansu da ake ginawa.

  Damuwar da take aciki yasa taji kamar ta mak'alk'aleshi ta rungumeshi sabodagaba d'aya Babu abinda take buk'ata Sai rarrashi.

  Haka nan ta jure ta rab'a kusa dashi ta zauna, amma idanuwanta suna zubar da hawaye.

  Cikin damuwa ya juyo gareta Yana kallonta yace, "Mu'umina masoyiyata miya faru, waye ya dakar mani ke?, ki fad'a Mani yanzu inje in rama Maki".

  Ji tayi wasu hawayen sun kutso da k'arfin sushar-shar-shar suna zubowa kamar an bud'e famfo.

  Mumin ganin haka yasa ya rud'e da sauri ya dawo gabanta ya tsugunna suka rink'a fuskantar juna, acikin zuciyarsa ji yake kamar yajata ajikinshi ya rungume saboda damuwa.

  K'asa ya k'arayi da muryarshi yace, " Mu'umina my love Miya faru?kada ki b'oye Mani ki fad'a Mani abinda yake damunki".

  "Ubanka yake damunta".

  amsar kawai dayaji an bashi kenan.

  Juyawar da 

  za suyi Sai sukaga Abba da wani matashin Alhaji tare da d'ankoronsa atsaye jikin mota suna kallonsu.

  Tun daga shi har Mu'uminar Sai gasu a tsaye cikin firgita suke kallonsu.

  Abban da kanshi ya matso kusa dasu Mu'umina Yana huci ran nan b'ace yace,

  "Kaine Mai hurewa y'ata kunne Ko, sau nawa kakeso in fad'a maka ka daina zuwa k'ofar gidan Nan?".

  Da sauri Mumin ya zube bisa gwiwoyinsa tare da duk'ar da kansa k'asa yace, 

  "Abba don Allah kayi hak'uri, inason Mu'umina da yawa, karka rabamu, Ina tunanin yanda zan iya rabuwa da ita".

  Muje Zuwa Yanzu Kafcen Ya Fara, Mu'umina,Mumin da kuma Muhannad,ga Kuma Abba a gefe,tirkashi...

  *****

  Ku biya kudi ku ci gaba da karanta labari mai kayatarwa son ranku.

  Sabon Salo, Wannan Littafin Namu Na Kudi Ne Sai Dai Akwai 5Free Pages, Dan Haka Ga Duk Mai Bukatarsa Yana Iya Tuntubarmu A Kan Wadannan Numbobi Da Zasu Zo A kasa Domin Samun Mallakarsa Akan dalilan din Kudi Naira dari Uku #300, Dan Allah Kar Cin Zarafi Ya Kawoki/ka Garemu Domin Mu Bamu Bidar Kowa Da Fitina,li'ilafi quraish.

  Zaki/ka Turo 300 Ta Wannan Account Number din 2209854592 Sa'adiyya Zakariyya (Zenith Bank), idan kin tura kiyi screensht ki tura ta cikin numbobin dake zube a kasa ta whatsapp account namu, idan babu accnt kuma kina iya transfer na recherge card na katin MTN.

  08145146915

  08164475119

  08033481518

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake gashin kifi karfasa

  Posted Jul 12

  Gasashshen kifi karfasa ko grilled fish ko kuma grilled tilapia abinci ne da mutane da yawa suke so kuma suke sha’awar koyon yadda ake sarrafawa. Saboda haka Umyuman ta koyar da yadda ake gashin kifi a cikin recipes da ta koyar a lokacin Ramadan a cikin zaurenta n...

 • Bita ta musamman akan rubutun gajerun labarai: Rana ta biyu

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta darasin ranar farko. DARASI NA 1 Abubuwan lura a rubutun gajeren labari A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin ...

 • Ko Ruwa Na Gama Ba Ki: Babi na Biyar

  Posted Jul 12

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu. Kan Jummai na ƙasa ta ce, "Habeeb ne". kusan duk ba s...

 • Physics: Darasi game da energy da kuma work 

  Posted Jul 8

  A wannan makala zamu yi bayani ne akan ENERGY da kuma WORK. Game da wannan darasi abubuwan da ake so dalibai su lura da su sune, energy, work, types of energy, sources of energy, classification of sources of energy, law of conservation of energy da mathematical problems...

 • Tekun Labarai: Idan Farauta ta Ki Ka

  Posted Jul 8

  Ku latsa nan don karanta farkon labarin. Ka sani ya kai Sarkin zamani, an yi wani bafatake mai nasibi a harkar saye da sayarwa, duk abin da ya kama sai ya yi daraja. Akwai lokacin da dirhami ɗaya ke jawo masa ribar dirhami hamsin. A kwana a tashi sai kasuwancin ya juya...

View All