Makalu

Sabbin Makalu

View All

GIDAN DUHU

 • BABI NA BIYAR

  °•ABIN MAMAKI AGWAGWA DA ƘIN RUWA•°

   

  Gudu nake ƙwalawa a cikin ƙwalelen jejin ina gwale ƙwala-ƙwalan idanuna da suke liƙe da ƙwalelen kaina, na juya ƙwalelen kan nawa, ina waiwayen ƙwalelen filin da na baro baya a firgice.
  Ban yi aune ba sai ji na na yi na faɗi ƙasa rikicaa! Hakan kuma ya faru ne sakamakon cinkaro da na yi da wani ɗutse mai ɗan girma. A take gaban goshina ya fashe sai ga jini shar yana zuba daga wajen.
  "Ahhh!" Na saki ƙara cikin siririyar murya tare da dafe goshin nawa, saitin wurin da nake jin raɗaɗin, ganin zan iya yin asarar jini da yawa ya saka na cire ɗankwalin da ke kaina na ɗaure wurin tamau. Hakan ya taimaka sosai wurin dakatar da zubar jinin.
  Na yunƙura da dukkan ƙarfina na miƙe kan duga-dugaina ina mai ci gaba da gudu cikin matuƙar ƙarfin hali.
  Sanin cewa tsayuwa ta a wurin daidai yake da kasa rayuwata a faifai ina tallar ta.
  Fatana bai wuce na gan ni a gefen babbar hanya ba, domin samun abin hawan da zai tsiratar da ni daga wannan haɗarin, kafin waɗancan azzaluman su ankare da rashina a wurin, domin na san ba shakka za su biyo sawuna.
  Tuni na manta da duk wani raɗaɗi da zafin ciwon da nake ciki na ci gaba da cin hanya a guje.
  Duk lokacin da na taka sawuna a kan ƙarangiyar da ke shimfiɗe a jejin ƙayoyi marasa adadi ne ke nutsewa a cikin tafin ƙafafuwana da basa sanye da takalmi, sai dai na runtse ido na ci gaba da gudu.
  Bayan wasu 'yan daƙiƙu na riga na gama galabaita jiri ya fara ɗiba ta, da ƙyar na ƙarasa inda nake muradi, ina zuwa nan kuwa na zube a kan titin a galabaice.
  Sai dai ko tsuntsu ban ga alamar yana giftawa ta wurin ba.
  Na waiga ina ƙare wa makeken jejin da na fito kallo yayin da nake hangensa dishi-dishi, na mayar da duba na kan titin har iya ƙarshensa ban ga alamar da ke nuna akwai wasu halittu da ke rayuwa a wurin ba.
  'Ɗif!' wuta ta ɗauke mini ba na iya ganin komai sai duhu. Har zuwa lokacin da kunnuwana suka karɓi baƙuncin sabon sauti mai ƙarfi. Sai da na nutsu da kyau na fahimci cewa ƙarar adaidai sahu ne na ji.

  "Baib... baiwar Allah me me yay...ya saamee ki?" Waɗannan kalaman ne suka ratsa masarrafar jina, wanda nake kyautata zaton matuƙin abin hawan ne ke furta su.
  Jikina ya hau kakkarwa tamkar ana kaɗa mini mazari, laɓɓana suka hau rawar disko sai dai na kasa furta ko da harafin A ne.

  "Tat...tashii mum mu tafi, baa zan bab barki a nan ba kina buƙatar taimakoo."
  Ya faɗa a karo na biyu.
  Daidai lokacin ne wutar da ta ɗauke a idanuna ta dawo, tamkar yadda haske ke kuranye duhu bayan maido wutar lantarki, haka duhun da ke cikin idanuna ya yaye. Na sauke dubana a kansa ina yunƙurin miƙewa sakamakon tuna haɗarin da nake ciki da na yi. Ba tare da dogon nazari ba na karɓi kyakkyawan tayin nasa, duk da cewa ban san kowaye shi ba. Sai dai an ce wanda ya nutse a cikin rijiya yana neman taimako idan zare ka zura masa kamawa zai yi. To ni ɗin ma hakan ce ta faru da ni.
  Da ƙyar da siɗin goshi na yi nasarar miƙewa ina layi tamkar wacce ta kwankwaɗi barasa, na shige cikin adaidaitar, ya fisge ta da sauri muka bar wurin.

  "I...inaa zann kaik...ki?" Ya tambaya cikin in-ina, wanda na fuskanci cewa yanayin maganarsa kenan.
  Shiru na yi don na ba wa ƙwaƙwalwata damar yin nazari a kan abin da zai fidda ni.
  'Kina da inda ya fi gidan Abbanki ne a yanzu?' na tsinto tambayar a wani sashe na zuciyata.

  Can kuma na hau girgiza kaina a hankali 'Ina! Ba zan je can ba, idan kuma ta tabbata shi ne ya kashe baba Haris fa? A yanzu ba ni da tabbacin kotu ta sallame shi ko yana a tsare, zuwa gida barazana ne ga rayuwata. Abbana ya zame mini carbin ƙwai mai wuyar ja, To ina zan nufa?'

  Waɗannan tambayoyin nake ta tusawa a injin niƙa kalaman ƙwaƙwalwata, amma duk tushin da nake yi musu sun gagara yin laushin da zan fahimci ma'anarsu ballantana na samu amsar su.
  Don haka na jingine wannan tunanin tare da karɓar sabuwar shawarar da ƙwaƙwalwata ta bijiro mini da ita ba tare da yin dogon nazari ba.
  "Nan wane gari ne?" Na tambaye shi a wahalce.

  "Mam...mambiya ne."
  Na yi farinciki da jin cewa ba a fitar da ni daga mahaifata ba.
  "Tudun Feƙa zaka kai ni."
  Tun daga nan ban sake cewa uffan ba, sai sauke tagwayen ajiyar zuciya nake yi, ina cike da farin ciki yau na zama sakakkiyar tsuntsuwa har na samu nasarar hawa hanyar da za ta sada ni da gidan da nake hangen cewa can kaɗai ne mafakar da ta rage mini, gidan mutumin da nake ji shi kaɗai ne bangon da ya rage da zan iya jingina da shi, da shi kaɗai na yarda a wannan lokaci.
  A haka na ci gaba da karatun wasiƙar jaki, ina jiran tsammani.
  Bayan shafe doguwar tafiya na ji ya sassauta da saurin da yake shararawa ya ce "Gag..gamuu a un gu...guwar."
  Na tashi zaune daga kwanciyar da na yi na ɗan dudduba kafin na ce "Gaba kaɗan."
  Ya ci gaba da tafiya a hankali, kwatsam sai gamu a ƙofar wani tanƙamemen gida na alfarma.
  Na yi busasshen murmushi a hankali na furta
  "Nan zan sauka, bari na shiga na karɓo maka kuɗinka."
  Cike da farincikin dawowata a cikin ahalina, na fito na tsayu sosai a kan ƙafafuwana, tuni na manta da cewar akwai wasu raunuka da suka mamaye ilahirin gaɓɓan jikina. Da gudu na isa ƙofar na fara ƙwanƙwasa ta tamkar wacce aka ba wa kwangilar fasa ta.
  "Waye ne wai? kada ka ɓata mana ƙofa fa."
  Mai gadin gidan ya faɗa daga ciki, cikin fusatacciyar murya.
  "A ....Amira ce." Na faɗa cikin rawar murya ina waigen baya sai kace wacce aka sakowa mahaukacin kare, sai jera ajiyar zuciya nake.
  "Wace Amiran?" Muryarsa da ke doso kofar ta sake dakar dodon kunnena.
  "Amira jikar nan gidan." Na faɗa murya a dusashe.
  Ya leƙo kai daga jikin ƙofar kaɗan, yana ɗora idanunsa a kaina ya yi saurin buɗe ƙofar tare da ba ni hanya yana faɗar "Ikon Allah! Ke ce da kanki ƙaramar Hajiya?"
  Na gyaɗa masa kai ya ɗaga hannu sama yana faɗar
  "Allah ma ji roƙon bawa, Allah mun gode maKa da Ka dawo da wannan natsattsiyar halittar a cikin danginta."
  Ya sauke kansa yana bina da kallo kwatankwacin kallon da zaka yi wa baƙuwar halittar da ta bayyana a gabanka. Na san hakan bai rasa nasaba da ƙarjamewar da na yi na fita a kamannina gaba-ɗaya. Ba iya kamanni ba, daidai da fatar jikina ta canza launi daga fara zuwa ɓaka.
  Duk wannan kyan dirin da nake da shi a da yanzu babu, cikar fuskar duk babu ta zurmuƙe, sai fa idanun da girmansu ya ƙara fitowa sakamakon ramar da na yi, dogon hancin nawa ya ƙara sirancewa. Sai shatin duka da ƙananun raunuka da suka baibaye ilahirin sassan jikin nawa.
  Duk na lura da wannan ne a lokacin da nake zaune a bayan adaidaitar na duba fuskata ta cikin gilashinta.
  Gano hakan ya sa na sakar masa ɗan murmurshi da kumburarrun idanuna ina faɗar "Dattijo yana ciki ne?"
  "I, haka nake tsammani." Ya amsa a gajarce.
  Ai da hanzarin na nufi ƙofar da za ta sada ni da babban falon gidan ina ƙwala masa kira da iya ƙarfin da ya rage mini "Dattijo! Dattijo!!"
  Sai dai muryar ba ta fita sosai kasantuwar ta riga ta gama dusashewa, dole ƙanwar naƙi ta sanya na kame bakina na gimtse ko don ƙafewar da yawun bakina suka yi sakamakon ƙishin da ya addabe ni.
  Ko da na isa falon ba kowa, sai na nufi ma'ajiyar kayan sanyi a sukwane na buɗe tare da ɗaukar zandamemiyar robar ruwa, na ɗaga ban ajiye ba sai da na shanye ta tas.
  Sa'annan na samu wuri na zauna a kan kujera ina mayar da ajiyar zuciya, tuni na manta da rayuwar wani mai adaidaita da na bari a waje.
  'A'ah! Malam Sale ya ce Dattijo yana gida to yana ina kenan?' Na tambayi kaina a cikin zuciyata.
  'Mai yiwuwa ya shiga ɗakinsa ne, ki ɗan ƙara masa lokaci, gaggawa aikin shaiɗan ne.' zuciyata ta shawarce ni.
  Na ɗago kaina na sauke shi a kan kulolin abincin da ke ajiye a gefe da farantai, da alama dai bai jima da kammala cin abinci ba.
  A hanzarce na miƙe na je na buɗe kulolin cikin sa'a na samu ya rage abincin da alama bai wani ci da yawa ba.
  Na yi murmushi ni kaɗai cikin raina na ce 'Sa'a wacce tafi manyan kaya, idan Allah Ya so ka sai ya baka kyautar shantalin ruwa yayin da kake a tsakiyar sahara.'
  Don haka ban yi wata-wata ba na buɗe kulolin na hau auna wa cikina abincin ba jira, tamkar dai mayunwacin zakin da ya shafe wuni biyu bai yi kalaci ba.
  Da ma can tashin hankalin da nake ciki ne ya sanya na gagara tuna wa da wata aba wai ita yunwa. Da yake zuwa lokacin zogin da nake ji a goshina ya ragu sosai.
  Ina tsaka da cin abincin ne wani tunani ya ziyarci zuciyata 'Me ya sanya Dattijo ya jima haka bai fito ba?'
  Haka kurum na ji hankalina ya kasa kwanciya ina tsananin buƙatar na magantu da shi, kafin maharana su yi nasarar gano ni, domin a yi wa tufkar hanci.
  Dalili kenan da ya sanya ni miƙe wa a kan duga-dugaina na nufi ɗakinsa, sai gani a tsakiyar ɗakin nasa amma abin mamakin shi ne ba kowa a ɗakin, ƙofar banɗakin kuma a buɗe take alamar dai ba kowa a ciki.
  Don haka a sanyaye na fito ina taka wa a hankali tare da jefa wa kaina tambayar
  'Ina Dattijo ya shiga haka, lokacin da nake cikin ƙishirwar ganinsa?' Ko dai ya fice ne ba da sanin mai tsaron ƙofar ba?'
  Zuciyata ke ta bijiro mini da waɗannan tambayoyin yayin da fargaba ke kawo mini ziyara a karo na barkatai.
  "Bari na je sashen ma'aikatan gidan kawai, zan fi samun nutsuwa da kula wa a can." Na faɗa murya ƙasa-ƙasa.
  Na bi ta ƙofar baya na fice daga falon tare da bin hanyar da za ta sada ni da can.
  Na zo zan wuce ta gaban ɗakin da muke yi wa laƙabi da °•masaukin aljanu•° sanadiyar tun tasowarmu ba mu taɓa ganin kowa ya shiga ɗakin ba haka kuma a kulle yake.

  Ɗakin ya zama tamkar ƙwai ta fuskar kasa samun nasarar shiga cikinsa, sai dai banbancinsu da ƙwai shi ne, shi wannan ɗakin yana da ƙofa saɓanin ƙwai da ba shi da ita. A wata fuskar kuwa suna kamanceceniya ta yadda ya kasance idan har aka samarwa ƙwai ƙofa to akwai barazanar rasa ilahirin albarkatun da ke ciki, haka wannan ɗakin ya kasance.
  Koda muka tambayi kakanmu dalilin kasancewar ɗakin a haka shi ne ya faɗa mana cewa aljanu ne suka sauka a ciki, kuma ba yadda ba a yi ba sun ƙi barin wajen sun ce gadar wajen suka yi daga kakanninsu, dalili kenan da ya sanya ya rufe ɗakin ba ya bari kowa ya raɓi kusa da wurin ma. Tun a lokacin ya sanya mana tsananin tsoron ɗakin.
  Sai dai wani abin al'ajabi sai na dinga jiyo alamar motsi daga cikin wannan ɗakin.
  Mummunar faɗuwar gaba ta ziyarce ni
  'Baƙin gidan sun sauka yau kenan?' na faɗa a raina ina kusantar ɗakin cikin sanɗa.
  Duk da cewa a firgice nake tamkar ɓeran da mage ta rutsa, amma a haka zuciyata ta ci gaba da ingiza ni ina kusantar ɗakin.
  'Yau dai ko sarkin aljanu ne zai sauka a cikin ɗakin nan zan so na gan shi.' zuciyata ta raya mini.
  A haka na ci gaba da sanɗa har na zo jikin bangon ɗakin, idanuna suka sauka a kan wundon ɗakin da take a buɗe.
  Ba jira na bi bango tamkar ɓarauniyar da ke son sulalawa cikin wani gida, na je saitin wundon.
  "Salamatu! Salamatu!! Salamatu!!!" Wannan sautin ne ke fitowa daga cikin ɗakin cikin wata iriyar murya mai kaushi.
  Na zazzaro ido waje 'A aljanun ma akwai masu irin sunayenmu?' na yi tambayar a raina.
  'Tun wuri ki bar nan kafin su ankare da wanzuwarki a wurin, don gudun afkawa kogin nadama.' wani sashe na zuciyata ya shawarce ni.
  Har na juya da nufin barin wajen zuciyata ta azalzale ni da son sanin meke faruwa a cikin ɗakin. Kafin na gama samo sahihiyar matsayar da zan tsayu a kanta na ji wata iriyar ƙara tana tashi daga cikin ɗakin.
  "Meke faruwa a ciki ne?"
  Na faɗa murya ƙasa-ƙasa tare da yin hanzarin juyowa na kalli wundon. Ta yi mini tsayi ta yadda ba zan samu damar leƙawa ba, dalili kenan da ya sanya na kinkimo wani bulo cikin tarin wasu bulalluka da aka yi wani ɗan gyara da su a wasu kwanakin baya da suka wuce. Da ƙyar ina sauke ajiyar zuciya na iya cicciɓar bulon na ajiye daidai wurin na taka tare da zura kaina a hankali don ganin me yake faruwa.

  Na zazzaro ido tamkar an take kwaɗo a cikin ruwa, tsabar razana har sai da na kusa kifowa ƙasa. Har na buɗi baki zan fasa ihu, na yi saurin toshe bakina da tafin hannuwana duka biyu.
  Ba komai ba ne ya razana ni face ganin kakata (Margayiya Salamatu, matar Dattijo) tsaye ta zama mutum-mutumi ga kuɗaɗe marasa adadi a ƙasanta.

  A take gumi ya shiga karyo mini tamkar wacce ta haɗiyi kunama, babu shiri na sauka daga kan bulon na nufi ƙofar fita don guduwa. A raina ina ta tunanin a yadda ya kamata na fahimci al'amarin. Shin kakarmu Salamatu ba ta mutu ba kenan? Ko ita ma dai aljanu ne suka sace ta suka ɓoye ta yadda ni ma wasu suka yi mini a inda na gudo? To amma ita ai kamar gata suke yi mata, don na ga tarin kuɗaɗen da suka ba ta a ƙasanta.

  "Kuɗin jini ne." Wata zuciyar ta kawo mini tsegumi, wanda ban yi wani dogon tunani ba na ji na gamsu da hakan. Sai a lokacin ma na tuno da wata gudar dubu da ba ta gama fitowa daga bakinta ba. 'To kenan wa yake yin kuɗin jinin da ita? Aljanun ne ko waye?' Na tambayi kaina.
  Har na je gaf da ƙofa zan fita wani tunani ya faɗo mini, sakamakon tunawa da wayata da na yi, wacce na samu nasarar gudowa da ita. Hannu na karkarwa na lalabo ta daga aljihun rigata tare da kunna ta, cikin sa'a wayar tana da chaji. Sai kawai wani tunani ya sake bijiro mini, cewa na koma wundon na sake leƙawa na ɗauki hotunanta ko don a fi yarda da ni idan na je ba da labari.
  Da wannan tunanin na juya, na sake hawa kan bulon na leƙa ɗakin. Bayan na shi ga kyamara na fara ɗaukar bidiyo. Duk da cewa ba wadataccen haske a cikin ɗakin, amma ba laifi ina iya hango komi da ke faruwa a ciki...

  "Ɗan dakata Barista! Kina nufin a aljanu ma akwai matsafa kenan? Wannan fa shi ne abin mamaki wai agwagwa da ƙin ruwa." Hanifa maƙociyata ta dakatar da ni cikin hanzari a karo na farko, domin tunda na fara karanta musu labarin ba wacce ta yi yunƙurin dakatar da ni, sai dai lokaci zuwa lokaci su share hawaye su ci gaba da baza kunnuwa. Hakan ya saka ni jan fasali na ɗago idanuna da suke kan littafin ina murmushi.
  Kafin na ba ta amsa Husna ta share hawayen da suke ta tsere a kan tagwayen kumatunta ta ce
  "Gaskiya Amira ta ga rayuwa, yanzu kuma ko wanne tafkin hatsari za ta kuma afkawa a ciki?" Ta sauke zancen tana ajiyar zuciya.
  "Me kuke ci na baka na zuba? Ko kuna so ku riga Liman shiga massallaci ne?" Na watsa musu tambayoyin, tare da kafe su da kadarar mujiyata.
  Airah da tun ɗazu ta kafe ni da manyan idanuwanta, ta ɗauke gutunwar ƙwallar da ta samu mazauni a gurbin idonta ta ce
  "A gaskiya na jima ban ji ƙayataccen labari mai cike da ruɗani da abin tausayi irin wannan ba. Kowaye makashin nan ya iya takunsa sosai, tunda har ya iya shafe sawunsa daga kan doron da za a iya gano shi."
  Husna ta yi caraf ta ce "Ni fa har yanzu tsinannen Abban nan na Amira nake zargi."
  Na yi saurin juyawa na kalle ta da shanyayyun idanuna da suka fara ƙanƙancewa sakamakon dafin da ke cikin zuciyata, na jefe ta da wani irin kallo.
  Kafin na buɗi baki na ce wani abu, daddaɗar muryar mijina ta kawowa kunnuwanmu ziyara.
  "Assalamu alaikum!"
  Na wadata fuskata da murmushi tare da miƙewa tsaye ina nufar inda yake "Wa'alaikumus Salam Habibi sannu da dawowa!"
  Makwaftan nawa suka miƙe dukkanninsu bayan sun gaisa da mijina Usman, ya shige ciki.