Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 05

MATAKIN NASARA 05


 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  PEN WRITERS


  BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


  Pɑge 9 & 10

  Inna ta fashe da kuka, cikin kukan take jero wa Habib wasu kalaman godiya da addu'ar tsari daga dukkannin sharri na sarari da na boye.

  Habib ya ce, “To ni zan koma, Baba Allah Ya sawwake, Allah Ya kara lafiya, sai Allah Ya kai mu goben.”

  Kafin ya mike ya zaro wasu kudade 'yan dubu-dubu masu dan yawa ya aje gaban Inna sannan ya mike ya fito. Hassana da Usaina suka yo masa rakiya har waje.

  Da suka fito wajen ne yake tambayar su wane asibiti ne aka kai mahaifin nasu? Hassana ta ce, “Asibitin Malam Aminu Kano ne, kuma naira dubu dari takwas da hamsin suke nema.”

  “Babu matsala wannan, ku shirya da wuri goben zan dawo sai a kai shi.”

  Su duka biyun suka hada baki suna fadin, “Ba mu san wane kalmomi za mu furta maka ba na godiya, mun gode mun gode, Allah Ya saka da alkairi. Ka ceci lafiyar mahaifinmu a daidai lokacin da kowa ya juya mana baya.”

  Habib ya katse su da cewa, “Wannan ai ba komai ba ne, duk yi wa kai ne wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi, Allah dai Ya ba shi lafiya. Ni zan wuce sai goben.” Suka yi sallama ya dauki hanya a kasa, su kuma suka juya gida.

  Habib babu wanda ya sani a wannan unguwa, kai hasalima bai taba shigowa cikin layin nasu ba sai wannan lokaci. Ta gefen titi kawai yakan wuce jifa-jifa. Duk zuwan nan da ya yi har sau biyu, da motarsa yake zuwa amma su Hassana ba su sani ba. Zuwa na farko da ya yi har suka hadu a kantin Dahiru, katin waya yake nema sai ya yi parking din motar a can baya gefen titi ya tako da kafa zuwa kantin. Wannan zuwan ma hakan ya yi, aje motar ya yi a baya ya karaso da kafa.

  To bayan Habib ya bar gidan su Hassana, yana tafe a mota yana ta tunanin halin da ya ga mahaifinsu, ya yi matukar tausaya masa, a hannu guda kuma yana duban inda suke rayuwa ta wahala da kunci da rashi, ya yi kukan zuci sosai. \ud83d\ude13

  Bayan haka a wannan zuwan ne ya samu sukunin ganin fuskarsu sosai. Duk da kasancewar su a cikin rayuwar ƙangi da wahala, amma sun ba shi matukar sha'awa da burgewa.

  Kyawawan yara ne masu siffa da diri me ban sha'awa, babu shakka da a ce sun samu kulawa, tun farko ba a cikin wahala suka taso ba, da wani ma idan ya gan su sai ya yi zaton ko larabawa ne, domin farare ne sosai irin farin nan me kyau, ga su da gashi baki wuluk me tsananin tsayi.

  Yanayin jikinsu duk da ba sa samun wani abinci me gina jiki, ba ramammu ba ne, tsayinsu madaidaici, su ba gajeru ba su kuma ba dogaye can ba. Suna da kyakkyawar surar da ake bukata a tare da mace.

  Don haka Habib ya yi kwadayin auren Hassana, kuma ya aje wannan buri a ransa, In Sha Allahu sai hakan ta tabbata. Wannan tunani yake ta yi har ya isa gida.


  *_SHIN WAYE HABIB?_*

  Cikakken sunansa shi ne Habib Sa'id Nakowa, haifaffen unguwar Rijiyar Zaki ne, ya yi dukkan karatunsa daga Primary har jami'a a nan gida Nigeria.

  Mahaifinsa, marigayi Alhaji Sa'id Nakowa dan asalin unguwar Baƙin Ruwa ne ta cikin birnin Kano. Shahararren dan kasuwa ne a fannoni daban-daban kuma dan kwangila ne. Kasancewar bunƙasar harkokin kasuwancinsa ya sa yake da manajoji da yawa, akalla dai mutane sama da dubu sha biyar (15,000) suna aiki karkashinsa.

  Habib shi kadai aka haifa a gidansu, bayan shi ba a sake samun wani ɗan ba. Mahaifinsa ya rasu shekaru biyar da suka wuce.

  Mahaifiyar Habib sunanta Hajiya Aisha, ita kuma haifaffiyar unguwar Dogon Nama ce. Mace ce me matukar tausayin masu kananan karfi, ta gaji hakan ne a gidansu. Domin mahaifinta ya kasance yana ciyar da gajiyayyu da mabukata abinci da ake dafawa ba dare ba rana.

  Wannan ya sa tun bayan rasuwar mahaifin Habib ta kafa wata gagarumar gidauniya wacce ta haɗa da ciyarwar, tallafa wa marayu da zawarawa, biya wa dalibai kudaden jarrabawa, tallafa wa marasa lafiya da kudaden magani da dai dimbin ayyukan jinkai.

  A takaice dai Habib ɗan Kano ne usul gaba da baya, wanda ya fito daga tsatson naira tsaftatacciya. Ɗan gata ne na ajin karshe kuma Ɗa ɗaya tilo a wajen iyayensa, babu shakka ba sai an tsaya bayyana yadda soyayyarsa take a zukatan iyayen ba.

  Habib zai yi shekara kamar ashirin da takwas zuwa da tara (28-29). Tun gabanin mutuwar mahaifin, ya tara dukkannin manajojinsa da lauyoyinsa, ya ce ya naɗa Habib a matsayin babban Darakta, shi ne zai ci gaba da kula duk wata harkar kasuwanci da ta kamfani.

  Sannu a hankali Alhajin ya rika nuna wa Habib abubuwa da yadda ake mu'amala da mutane, cikin kankanen lokaci Habib ya kware sosai, kuma mutane suka san shi suka saba da shi, wannan ɗan tarihin Habib ke nan a takaice. *_Mu koma kan labarin_*

  Isar Habib gida bayan sallar Isha suna hira da hajiyarsa, ya dauko mata labarin baban su Hassana.

  “Hajiya yau na ga abin tausayin da ban taɓa gani ba, abin ya tsaye mini a rai, abin tausayi \ud83d\ude13.”

  “Wane abin tausayi ka gani Abbana, a ina ne?”

  Habib ya gyara zama sannan ya kwashe labarinsu Hassana tun daga farko har karshe ya fada mata daga karshe ya ce,

  “Don Allah ina so ki ba ni dama na taimaka musu, gobe na ce musu zan koma domin a kai shi asibiti a yi masa aikin.”

  “Haba Abbana! Wannan ai ba wani abu ba ne da sai ka yi magiya. A ina suke da zama?”

  “Wata unguwa ce can wajen Brigade ana ce mata Tudun Wada.”

  “To babu matsala, Allah Ya kai mu goben tare za mu je, irin wadannan bayin Allahn muke nema. Duk wanda ka gani yana bukatar taimako, to ka taimaka masa ta kowacce fuska, kai koda kalma me dadi ce ka fada masa, kai ma Allah Zai taimake ka.”

  Habib ya yi farinciki sosai yadda hajiyar tasa ta karbi bukatarsa, da ma dai ba shi da wani shakku a kanta domin taimakon irin wadannan mutanen shi ne aikinta. Babban abin da yavfi faranta masa rai shi ne da ta ce, za tay i tattaki ta je da kanta ta gano yadda abin yake.

  ***

  Washegari tun sassafe su Inna da su Hassana suka tashi suka shirya tsaf, misalin karfe 9:00am Habib da hajiyarsa suka iso a wata babbar motar kirar Honda Odyssey \ud83d\ude90 irin family car din nan, ya yi parking daidai kofar gidansu Hassana, suka yi sa'a kuwa Khalid na kofar gidan.

  Habib ya kira shi, a guje Khalid ya nufo wajensa yana cewa, “Sannu da zuwa yaya.”

  “Je ka yi mini sallama da Anty Hassana.”

  Da gudu Khalid ya sake kwasa ya yi cikin gidan nasu ya fada daki yana fadin, “Anty Hassana ga yaya Habib shi da wata mata sun zo da mota suna kofar gida.”

  Dayake sun riga sun gama shiri jikinta a kintse yake, hijabi kawai ta saka ta leko, ido suka hada da Habib ta sunkuyar da kai ta karasa fitowa wajensu. Ba ta san kowace ce suke tare ba amma ga dukkan alamu mahaifiyarsa ce saboda kama da kuma girmanta. Durkusawa ta yi sosai ta gai da hajiya sannan ta mike tare da cewa, “Bisimillah ku shigo.”

  Ta shige gaba hajiya na tsakiya Habib kuma na baya, tiryan-tiryan suka shiga gidan, hajiya ta yi sallama suka gaisa da wasu daga cikin mutanen gidan dake tsakar gida suna aikace-aikace.

  Suka shiga dakin, tuni Usaina ta shimfida tabarma, suka zauna, bayan an yi gaishe-gaishe, hajiya ta dubi babansu Hassana ta ce, “Sannu bawan Allah, ya ya jikin?” Ya amsa, "Da sauki."

  Habib ya karɓe zancen da cewa, “Inna wannan ita ce mahaifiyata na yi mata bayani shi ne ta ce ita ma za ta zo ta duba shi.”

  Inna ta fashe da kuka tana fadin, “Wannan yaro Allah Ya yi maka albarka Allah Ya raba ka da manya lafiya, yadda ka saka farin ciki a ranmu, Allah ya saka farin ciki a zuciyarka da magabatanka ranar gobe kiyama.”

  Shi ma marar lafiyar kukan kawai yake tare da yi wa hajiyar godiya, daga karshe hajiyar ta ce, “Sai mu tashi mu tafi asibitin don a samu yin aikin da wuri”

  Nan suka mike, Habib ya goyo baban ya fito da shi ya shigar da shi mota, Hassana da Inna suka zauna kusa das hi, aka bar Usaina da Khalid a gida.

  Ba jimawa suka isa asibitin Malam, dayake an san ita hajiyar, nan da nan aka zo aka dauki marar lafiyar a irin gadon daukar mararsa lafiya aka shiga da shi cikin asibitin. To dayake da ma an taɓa kawo shi asibitin a baya, ba wata matsala ba ce sabuwa, 'yan gwaje-gwaje aka sake yi masa aka tsayar da cewa za ayi masa aikin bayan awanni ashirin da hudu (24 hours).

  Dukkan abubuwan da ake bukata kama daga kan aikin har magungunan da za a bukata aka yi wa hajiya total ta rubuta check ta biya.

  Inna ta zube a kasa tana kuka haɗe da yi wa hajiya gidiya, babu irin kalmomin godiya da addu'ar fatan alkairin da ba ta ambato ba, hajiya ta ce,

  “Babu komai ki mike, wanann ai shi ne abin da ya dace mu yi. Duk mutumin da Allah ya bawa ikon taimakawa to wajibi ne ya taimaka. Allah dai Ya sa ayi aikin a sa'a Ya kuma ba shi lafiya.”

  Bayan an gama duk abubuwan da za ayi a wannan lokacin ne, hajiya da Habib suka fito za su tafi, Inna da Hassana suka rako su wajen mota.

  ***

  A gida kuwa da rana ta yi Usaina ta dafa abinci, ta tafi asibitin ta kai musu domin ta san dole za su nemi abincin. To su Habib ma dawowarsu gida keda wuya, hajiya ta sa 'yan aikinta suka hada abinci na musamman.  Ku taba link din nan domin shiga group dinmu a BAKANDAMIYA

  https://bakandamiya.com/group/95/pen-writers-association  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*


Comments

2 comments