Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 06

MATAKIN NASARA 06


 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  PEN WRITERS


  BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


  *Pɑge 11 & 12*

  Misalin karfe 1:45pm na rana Habib ya sake dawowa da abinci lafiyayye da nama zuƙu-zuƙu, daidai lokacin ita ma Usaina ta kawo abincin da ta dafa a gida, shinkafa da wake ne da mai da yaji da salad.

  A wannan lokacin ne Habib ya samu sukunin keɓewa guri guda dasu Hassanar, ta ce, “Na rasa wace irin kalma zan furta a bakina domin nuna godiyata gareka, mun gode mun gode.”

  “Karki damu da yin mini godiya, Allah za ki yi wa godiya. Wannan abu da muke ni da mahaifiyata kanmu muke yi wa.”

  “Godiya ta zama dole a yi maka, wanda duk ba ya gode wa mutane to ba zai taɓa gode wa Allah ba, saboda haka ina kara jaddada godiyata gare ka Allah ya saka da alkairi.”

  Sun jima suna hira su ukun, daga karshe ya ce zai tafi, ya bude mota ya dauko waya da layi sabbi kar! ya mika wa Hassana tare da cewa, “Ga wannan wayar ki rike saboda idan akwai wani abu da ake bukata sai ki kira ni, number ta na cikin layin.”

  Wani irin yanayi ta ji ta tsunduma ciki, tunda take ba ta taɓa yin koda mafarkin rike waya ba, "Allah me iko! Allah na gode maka, ni kam wane irin abu zan yi wa wannan bawan Allahn na faranta masa ransa? Na rasa ma ya ya zan yi masa godiya?"

  A zuciyarta take wannan maganar bayan da ya mika mata wayar sai bakinta ya kulle ta gaza cewa komai, ɗan lokaci me tsayi aka dauka sun yi shiru kafin daga bisani ya dakatar da shirun da cewa,

  “Ki karɓa mana tafiya zan yi, kuma idan na tafi ta hakane kawai zan san yadda ake ciki, duk abin da za a bukata ki sanar dani kawai.”

  “Don Allah ka bar shi babu abin da za a bukata ma, bayan na ga duk an gama komai Hajiya ta biya. Ni dai ka bar shi kawai don Allah, wannan ɗawainiyar ma da kake ta isa haka, Allah ya saka da mafificin alkairi mun gode sosai.”

  Fushi ya ɗan yi har ya sauya fuskarsa kadan sannan ya ce, “Akwai abu guda ɗaya da ba na so! Idan na bayar da abu ba na so a ce ba a so, duk abubuwan da nake yi ba tambaya ta kika yi ba, ni ne na yi niyya, kuma haka na ga mahaifiyata na yi. Sai dai idan alherin ne ba kya so, to sai na ƙyale ki, amma gaskiya ba na son na sake ba ki wani abin ki ce ba za ki karɓa ba.”

  “To shi kenan ka yi hakuri don Allah da ma na ga ɗawainiyar ce ta yi yawa, kana ta kashe kudi a kanmu.”

  “To mene ne amfanin kudin idan ba a kashe su ba, za a kai mutum kabari da su ne? Ko kin taɓa ganin wanda ya mutu aka kai shi kabari da dukiya? Wannan abin da muke yanzu da kudin shi ne zai bi mu kabarin namu, ya zame mana alkairi. Amma idan muka rike kudin to sharri za su zame mana a kabarin.”

  Yana gama fadar wannan maganar ya bude kofar mota ya shiga tare da cewa, “To sai na ji ki” Ya yi wa motar key ya fice.

  Hassana da Usaina tsayawa suka yi a wajen, Hassana ta ce, “Wannan bawan Allahn ban san da me za mu saka masa ba? Ya yi mana abubuwan da ba za mu taɓa mantawa da shi ba a rayuwarmu”

  Usaina ta karɓa mata zancen da cewa, “Haka ikon Allah yake, kuma kin manta ne? Ke ce kike cewa idan muka yi hakuri Allah zai yaye mana dukkan matsalolinmu. Godiya za mu ci gaba da yi wa Allah sannan mu yi masa da addu'a shi da mahaifiyarsa, banda wannan mu dai ba wani abu muke da shi ba da za mu ba shi. Allah ya saka masa da alkairi.”

  Bayan sun gama wannan tattaunawa, cikin asibitin suka koma wajen Inna, can ma ɗin zancen Habib ɗin suka ɗora bisa wannan abin arziki da ya yi musu.

  Hassana ta nuna wa Inna wayar da ya ba ta tare da cewa, “Kin ga ma har waya ya ba ni wai idan ana bukatar wani abin na kira sa na fada masa.”

  “Hakika wannan yaro da mahaifiyarsa babu abin da za mu ce da su sai godiya, Ubangiji Allah Ya ba su abin da suke nema duniya da lahira, ki duba wannan uban abinci da aka kawo me yawa haka, Allah saka masa da alkairi.” Inna ce ta yi wannan maganar.

  To nan dai suka ci gaba da 'yan hirararrakinsu yayin da Baba ke can ɗakin da za a yi masa aikin tun bayan wasu allurai da aka yi masa gabanin fara aikin. Usaina nan ta yini har dare, tana shirin dawowa gida ne, Habib ya sake komawa kai musu wani sabon abincin. Tuwon shinkafa ne haɗaɗɗe da miyar taushe, ga shi wancan abincin ma da aka kawo da rana ba a cinye shi ba.

  Yana isa ciki ya kira wayar da ya ba wa Hassana, ji ta yi waya ta fara ruri haɗe da motsi, firgita ta yi domin ba ta saba ba kuma ta manta shaf da wayar na jikinta. Fito da wayar ta yi ta ɗaga tare da cewa, “Assalama Alaikum.”

  “Amin wa'alaikums salam, Habib ne ina nan cikin asibiti wajen ajiye motoci, ki zo ki dauki abinci.”

  Ya kashe wayar, ta dubi Usaina da Inna ta ce, “Habib ne wai abinci ya sake kawowa yana wajen ajiye motoci zo mu je.”

  Suka mike suka fito daidai lokacin shi kuma ya gama parking din motar, suna isa wajen ya fito ya bude boot suka kwaso manyan kulolin cike da abinci, suka shige gaba ya bi bayansu har dakin da suke zaune. Habib ya gai da Inna, ta amsa tare da yin godiya haɗe da sa masa albarka.

  Sun jima sosai a nan, sai bayan Isha Usaina ta mike za su koma gida ita da Khalid. Habib ma mikewar ya yi ya ce akwai inda yake son zuwa ne, tare suka fito da Usaina ya ba ta naira dubu daya (₦1,000) su yi kudin mota, ba don akwai inda za shi ba da har gida zai kawo su.

  Nan suka yi sallama ya shiga mota ya tafi, Usaina ta fito bakin titi suka tari me Keke Napep suka shiga, yayin da Hassana kuma ta koma cikin asibitin wajen Inna. Su biyu za su yi zaman jinyar, kodayake ana saran ba wani jimawa za su yi a asibitin ba. Da zarar an kammala aikin kwana ɗaya ko biyu za a iya sallamar su su koma gida.

  ***

  Washegari da safe Usaina ta shirya ta je ta fada wa wan mahaifiyarsu Alhaji Idi, sai dai ya riga ya fita ba ta same shi ba sai matarsa. Bayan sun gaisa take fada mata cewa an sake mayar da babansu asibiti za ayi masa aikin. Matar ta yi matukar farin ciki da murna bisa jin wannan labari, daga karshe ta yi addu'ar Allah ya sa ayi aikin a sa'a, Allah kuma ya ba shi lafiya.

  Wannan mata tana da kirki sosai, mutuniyar kwarai ce, mijinta ne dai ba mutumin kirki ba. A baya can ta kasance tana taimaka wa su Inna da kudi da kayan abinci, tana yawan kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci, amma da mijin ya samu labari sai ya taka mata burki. Har saɓani suka samu akan haka.

  Ta yi matukar kokari wajen fahimtar da shi hakkin 'yan uwantaka. Wajibinsa ne ya kula da rayuwarsu Hassana kasancewar sa yana da halin da zai iya yi musu komai. Amma ya yi biris da lamarinsu. Babu irin magiyar da ba ta yi masa ba akan ya taimaka ya ɗauki nauyin karatun su Hassanar amma mutumin sai ya yi funfuris kamar ba shi da wata alaƙa ko dangantaka da yaran.

  Daga karshe ta tattara ta zuba masa ido, domin iyakacin abin da za ta iya ke nan. Ita ma ɗin ba wani daɗin zama take ji da shi ba, hakuri dai take zaman 'ya'ya ne, sannan kuma an riga an manyanta. Yaransu biyar da shi, duk cikinsu kuma babu wanda ya yo halinsa dukkansu masu son zumunci ne. Shi ne dai ya hana su, amma wasu daga ciki wanda suka fara girma tuni suka saka ƙafa suka yi fatali da wannan tsari nasa.

  Domin babban ɗansa ana kiran sa Mustafa yana karatu a Sokoto, yana son Hassana sosai kuma yana da kudurin idan ya gama karatu za su yi aure.

  ***
  To bayan Usaina ta bar gidan, sai matar ta kira shi a waya take sanar da shi kamar yadda Usainar ta fada mata, sannan kuma ta nemi izininsa akan za ta je asibitin ta duba su kuma ta kai musu abinci. Nan take ya ce ta bari sai ya dawo gida tukunna za a san yadda za ayi.

  Tunanin banza da wofi ya fara game da yadda aka yi suka samu kudin da za ayi aikin, “To wa ma ya biya musu wannan kudi, mtssww! Karyar banza dole dai sai sun sa mutum ya yi asarar kudi.”

  A zuciyarsa marar tausayi da imani yake wannan tunani, ya zaci kowa ma irinsa ne babu na Allah. Ya dauka kowa ma irin mugun halinsa gare shi wanda yake ganin kamar wayonsa ne ko karfinsa ne ya tara masa dukiyar da ba ta isa cefanen miyar wani gidan ba na shekara daya. Allah wadaran masu kudin da ba sa tallafawa na ƙasa da su.

  To a asibitin kuwa tunda gari ya waye misalin karfe 8:00am, tawagar ƙwararrun likitocin da za su gudanar da aiki akan babansu Hassana suka dira a kansa suka kama aikin, babu wata matsala aikin yana gudana bisa taimakon Allah.

  Misalin karfe 9:00am Habib ya baro gida zuwa asibitin da nufin kawo musu abincin karin-kumallo, karfe 9:30am kuwa yana cikin asibitin. Wayar Hassana ya kira ya shai da mata cewa ya shigo asibitin.

  Nan da nan ta fito ta nufi wajen da ya yi parking ta yi sallama haɗe da gaishe shi, ya amsa tare da bude boot suka debo abincin, Hassana ta ce, “Kai dai ba. ka gajiya haka.”

  Murmushi ya yi sannan ya ce, “Kuma ba na fatan na gaji da irin wannan aikin har abada.”

  Ita ma murmushin ta riƙa saukewa ba tare da ta sake cewa komai ba, ta debi kulolin abinci da wani babban flas din shayi da wata babbar leda cike da bread \ud83c\udf5e, suka isa ciki, Habib ya zauna tare da gai da Inna, ta amsa tare da cewa, “Ya ya hajiya?”

  “Hajiya tana lafiya, tana yi wa me jiki sannu.”


  Ku taba link din nan domin shiga group dinmu a BAKANDAMIYA

  https://bakandamiya.com/group/95/pen-writers-association  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

0 comments