Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 07

MATAKIN NASARA 07

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 13 & 14*

  Bai jima ba ya mike ya ce zai koma, Hassana ta rako shi, suna tafe kafin su zo wajen motar ya ce, “Ban ga Usaina da Khalid ba, suna ina ne?”

  “Ba su karaso ba, watakila suna hanya.”

  “Yau za a yi wa Baba aikin kamar yadda suka fada ko?”

  “E watakila ma sun fara domin dazu sun karbi dukkan takardun dake hannunmu.”

  “To Allah Ya sa a yi a sa'a, Allah kuma Ya sa kaffara ce.”

  “Amin summa amin, Allah Ya saka da alkairi, ka gai da hajiya.”

  “Au, kora ta ma kike na tafi kenan?”

  Cikin murmushi Hassana ta ce,“A'a ba korar ka nake ba, na ga kamar kana da wani uzurin ne shi yasa, kada na ɓata maka lokaci.”

  “Duk ma inda zan je ai bai zai fi nan ba, domin nan aikin lada ne kamar yadda aka fada mana cewa, ziyartar marar lafiya aikin lada ne babba. Amma ban sani ba ko ladan ne ba kya so na samu kike kora ta?”

  “Hmm! Lada kam ai kana samu kuma koda ka tafi ma za ka ci gaba da samun ladan.”

  “To shi kenan zan tafi din amma anjima da rana zan dawo.”

  “To mun gode sosai Allah ya kara arziki, sai anjima din ka gai da gida.”

  ***

  Ganin yadda Habib yake ta jigilar kawo abinci asibitin babu ƙaƙƙautawa kuma me yawan gaske, ya sa Usaina ba ta shirya komai ba domin kawo wa su Inna. Ba ma ta zo ba sai da rana ta yi.

  Kafin ta taho, Anty Laure aminiyar Inna ta zo gidan da safe, shigarta dakin ta ga Usaina da Khalid kawai, “Ina suke ina marar lafiyar yake kuma?”

  Ta tambayi Usaina, gaishe ta ta fara yi sannan ta ce, “Ai suna asibiti za a yi wa Baba aikin, kwanansu daya a can jiya suka tafi.”

  “Ikon Allah! Ashe dai Allah Ya nufa bawan Allahn nan zai mike, to Allah Ubangiji Ya sa a yi a sa'a. Asibitin Malam din aka sake mayar da shi?”

  “E a can ne.”

  “Kai amma na yi farin ciki sosai, Allah Ya ba shi lafiya, aiko zan je dubo shi yau din nan insha Allahu. Ina Hassana ko suna tare a can?”

  “E suna can, ni ma anjima nake son zuwa asibitin.”

  “To shi kenan ma ki biyo mini mu tafi tare. Da ma maganar nan ta aikin da na ce zan tambaya miki, ki rika yi ne, to hajiyar ta ce a kai ki, ki fara aikin. Kuma ga shi yanzu gidan babu kowa, ba a san kuma lokacin da za a sallamo su ba, amma dai ko me ke ciki akwai bari mu je asibitin mu yi maganar da Inna.”

  “To shi kenan sai anjima din zan biyo miki mu tafi.”

  Anty Laure ta mike ta fito. To dayake ta san halin 'yan gidansu Innar da munafurci ko tsayawa saurarensu ba ta yi ba, ta kama gabanta ta nufi tallar turarurrukanta.

  A asibitin kuwa misalin karfe goma sha daya na safiya 11:00am, ƙwararrun likitocin nan suka kammala aikin dashen lakar, to amma ba za a sallame su ba har sai ya kara awanni saba'in da biyu (72 hours) a karkashin kulawar likitocin.

  Nan take Hassana ta kira wayar Habib take fada masa, ya nuna matukar farincikinsa sosai. Da yake yana gida a lokacin, shi ma sai ya sanar wa da hajiyar tasa, addu'a ta kara yi Allah ya kara masa lafiya.

  Habib Allah-Allah yake karfe 12:00pm na rana ta yi, 'yan aikin gidansu su kammala dafa abinci rana ya kawo asibitin ya duba marar lafiyar. Kamar misalin karfe 12:30pm kuwa an gama dafa abincin sun zuba a manyan kulolin guda uku. Tunda aka kwantar da su a asibitin, majinyata da dama ke amfana da wannan lafiyayyen abincin da ake kawowa ba dare ba rana, domin ya yi wa su Hassanar yawa.

  Habib bai jira 'yan aikin sun saka masa abincin a mota ba, da kansa ya dauka ya saka, domin da ma shi ba mutum ba ne me girman kai, lokuta da dama sai ka same shi tare da 'yan aikin gidan suna hira wasa da dariya. Yakan shiga cikinsu sosai ba tare da nuna ƙyama ko bambanci ba.

  A guje ya fita da mota ya ɗauki hanyar asibitin Malam Aminu, a daidai kofar Kabuga ya tsaya ya sayi lemo da ayaba da duk kayan dubiya dai, sannan ya wuce ya karasa asibitin. Tun kafin ya iso ya kira Hassana ya ce mata gashi nan.

  Mikewa ta yi ta fito wajen ajiye motoci daidai lokacin shi kuma ya gama shigowa asibitin, kafin ya yi parking ma har ta isa wajen. Ya fito fuskarsa cike da fara'a.

  Cikin muryarta me daɗin saurare haɗe da murmushi ta ce, “Barka da zuwa.”

  “Yauwa barkan ki dai, an yi aiki lafiya, to barka Allah ya kara masa lafiya.”

  Nan ya bude but din motar suka kwashi kayan suka shiga cikin asibitin. Yana shiga ya fara gai da Inna tare da cewa,

  “Barka Inna an yi aiki lafiya, Allah kara masa lafiya Allah Ya sa kaffara ce.”

  “Amin ɗan nan, ka yi mana abin da ba za mu taɓa mantawa da shi ba a rayuwarmu. Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya jikan magabatanka, abin da kake nema duniya da lahira Ubangiji Allah Ya ba ka, Allah ya tsare ka sharrin dukkan abin ƙi, Allah ya kara arziki.”

  “Amin.” kawai Habib yake cewa.

  Dayake ba a jima da kammala aikin ba, babu damar a shiga a gan shi har sai ya samu wasu awanni yana barci tukunna, saboda haka Habib bai samu ganin shi ba. Nan suka yi ta hira shi da Hassana har lokacin sallar Azahar ya yi, a nan Masallacin asibitin ya yi sallah.

  Misalin karfe 2:00pm na rana sai ga su Usaina tare da Anty Laure kamar yadda suka tsara za su zo tare. Bayan sun gaisa, Anty Laure ta yi wa Inna barka bisa wannan aikin ceton rayuwar bawan Allahn nan da suka fitar da rai da samun lafiyarsa.

  A nan Inna take sanar da Lauren yadda abin ya faru ta silar su Hassana.

  Dayake Habib din yana cikin asibitin bai kai ga fita ba, Inna ta nuna wa Laure shi, ita ma Lauren godiya ta yi masa sosai tare da addu'ar fatan alkairi.

  Bayan nan kuma Laure ta dauko maganar aikin da ta samo wa Usaina, take faɗa Innar cewa, “Gidan da Usaina za ta yi aiki, hajiyar ta amince har ma ta ce na kai ta kawai ta fara.”

  Inna ta yi farinciki sosai, sai ta ba ta uzuri da cewa, “To kin ga yanzu kuma ga mu a asibiti, kuma ba don Khalid ba ma da sai na ce ta tafi kawai. Sannan ita kanta Usainar ba za ta saki jiki ba har sai ta ga yadda jikin mahaifin nasu zai warawre. Ko za ki dan roƙa mana hajiyar ta kara mata sati daya kafin a sallame mu idan yaso sai ta fara zuwa.”

  “Babu matsala, wannan ba wani abu ba ne, hajiyar na da fahimta, zan yi mata bayanin komai.”

  Nan dai suka ci gaba da tattauna abubuwa na rayuwa da matsaloli iri-iri, yayin da Hassana da Usaina suke a wajen Habib su ma suna ta hirar duniya. A nan ne ma Habib ya fara tambayar su game da karatu.

  Basu yi karya ba, gaskiya suka fito suka fada masa cewa, iyakacin karatunsu aji uku na sakandire, yanayin rayuwa ya sa suka bar karatun sai dai Islamiyya da suka ci gaba da zuwa. Habib bai nuna wata ƙyama ba ko rashin jin dadi ba game da hakan.

  Domin a irin rayuwar da suka taso a cikinta babu shakka karatun boko zai yi musu matukar wahala, koda a ce ma kyauta za su samu komai, to lokacin zama yin karatun fa?

  Irin wannan rayuwa da dubban al'umma ke ciki ta ƙunci da talauci, wasu hatta karatun Islamiyyar ma ba sa samu. Za ka samu 'yammata dake tallar abinci, koma dai wane irin abin sayarwa ne da rana, sannan haka ma idan dare ya yi wata sana'ar ce za su yi, don haka ba su da wani lokacin kansu da za su samu ilimi.

  Irin haka ne sai kaga an yi wa yarinya aure ko tsarki ba ta iya ba, to ita ma fa haka za ta samar da 'ya'ya irinta matukar ba a samu miji jajirtacce ba, wanda zai canja ta ya canja mata rayuwarta. To Allah ya kyauta.

  ***

  Sai misalin karfe 3:00pm na rana Habib ya bar asibitin, jim kaɗan bayan tafiyarsa, Anty Laure ma ta shirya suka dawo tare da Usaina.

  To haka dai Habib ya rika sintiri a kan hanyar asibitin ba dare ba rana yana ta kai kawo har lokacin da aka sallame su, bayan kwanaki uku da yin aikin ke nan. A lokacin da za a sallame su Habib ya je da family car ya sake dauko su zuwa gida.

  Abin mamakin da ya kulle wa mutanen gidan su Inna da ma 'yan unguwar kai shi ne, marar lafiyar da yake zaune a waje daya baya iya komai sai an yi masa, baya motsawa sai an motsa shi, kusan shekara daya ke nan, wanda har wasu ma sun fara mantawa da shi, shi ne ya mike yake takawa da kafarsa cikin 'yan kwanakin da ba su sati daya ba? Shin wai wannan waye wanda ya dauki nauyin biyan kudin aikin?

  Ire-iren tambayoyin haɗe da tunanin da wasu ke yi a ransu ke nan, wasu kuma tsegumi ne ya cika musu ciki.

  Da ƙafarsa ya taka ya shiga gidan yayin da Habib ya ɗan riƙe shi kaɗan sakamakon jikin bai gama ƙwari ba, su Inna da Hassana suka rufa musu baya, Usaina har hawaye ta zubar saboda farinciki. Bayan ya zauna ya huta, su duka suka sake jaddada godiya da fatan alkairi ga Habib, ya yi sallama ya tafi abinsa.

  To yanzu dai Allah Ya yaye wa wannan bawa nasa larurar da tuni wasu suka fara jingina masa mutuwa, to Allah ke nan, wannan kuma kadan ke nan daga ikonSa. Ita cuta ba mutuwa ba ce, duk cutar da Allah ya jarrabi bawa da ita to akwai magani a tare da ita sannan kuma tana da lokacin warkewa. Duk irin maganin da za ayi amfani da shi ko wasu dabaru da za a bi, ba za su taba yin tasiri ba har sai lokacin da Allah Ya ƙaddara waraka za ta samu sannan cutar ta yaye.

  Babu abin da bawa ya kamata ya yi face ya lazimci hakuri da yin addu'a, hakuri shi ne *_MATAKIN NASARA_* a kan komai, da akuri ne ake cim ma rabo da burin rayuwa.

  A nan nake roƙawa dukkan mararsa lafiya na gida dana asibiti Ubangiji Allah Ya ba su lafiya Ya sa kuma cutar ta zama kanakarar zunubi ce amin.  Ku taba link din nan domin shiga group dinmu a BAKANDAMIYA

  https://bakandamiya.com/group/95/pen-writers-association  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

0 comments