Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 08

MATAKIN NASARA 08

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 15 & 16*


  Sannu a hankali 'yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa suka rika tururuwar zuwa dubiya da fatan alkairi ga Baba.

  Alhaji Idi wan Inna bai je asibiti ya duba shi ba, haka ma yanzu da suka komo gida bai zo ba, sai dai matarsa da ragowar 'ya'yansa da suka rika zuwa akai-akai, su ɗin ma ba da san ransa ya bari ba.

  Shi ba komai ba ne ya sa ba ya son zumuncin ba, saboda kada ya kashe kudinsa, ƙarda ne, Alhaji ƙankamo ke nan. Hannun jarirai ne dashi. A bahagon tunaninsa yadda suke cikin ƙunci, matukar ya rika hulɗa da su har ya bari 'ya'yansa suna mu'amala da su Hassana to dole ne su rika kawo masa bukatunsu.

  Hatta da 'ya'yansa ɗin ma ba wata sakewa suke samu ba, ko babban ɗansa wato Mustapha dake karatu a Sakkwato ba da son ransa yake kashe masa kudin makarantar ba. Sai da wani abokin kasuwancinsa ya shawarce sa cewa, idan bai bari yaransa sun yi karatun zamani ba, to babu shakka yana ji yana gani za a rika damfararsa, wannan ne dalilin da ya sa ya kai 'ya'yan nasa makarantar Boko.

  Idan ka ga an ɓanɓari wanann mutumin wani abu, to mace ce, macen ma kuma ta banza, ita kam ko nawa take so zai iya ba ta cikin ɓari da rawar jiki. Abin takaici ma ba manyan mata masu zaman kansu yake kulawa ba kaɗai, har da 'yammata ƙanana, a takaice dai wannan mutum ɗan tasha ne tattacce.

  To sai dai albasa ba ta yi halin ruwa ba, Allah ya kuɓutar da dukkannin 'ya'yansa daga gadon wannan miyagun halayen nasa.

  ***

  BAYAN SATI DAYA

  Bayan sati ɗaya da sallamar su Inna daga asibiti, Anty Laure ta sake dawowa duba marar lafiyar, sannan kuma su tattauna dangane da fara zuwa aikin Usaina. Bayan sun gaisa, ta yi wa Babansu Usainar sannu. A lokacin ne ma ya ji labarin samo wa Usaina aikin, fatan alkairi haɗe da godiya ya yi wa Anty Lauren.

  Nan Anty Lauren ta ce da Inna, “Yanayin aikin shi ne a can gidan za ta zauna, bayan sati biyu za ta rika zuwa ganin gida.”

  Daga Innar har Usaina ba su ji daɗin tsarin aikin ba, ita Inna fargabar yau take, ɗan yau ba shi da tabbas, ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba. Koda ace ita Usainar ta tsare mutuncinta, to idan kuma ya kasance akwai samari a gidan fa?

  Ita kuwa Usaina abin da ya dame ta shi ne barin su Innar da ta yi, sam ba ta so, a tunaninta tun farko ta zaci irin aikin nan ne da mutum zai je da safe, idan dare ya yi kuma ta dawo gidansu. To amma babu yadda suka iya haka suka amince. Wanda ruwa ya ciyo shi ko takobi aka mika masa kamawa zai yi.

  Don haka a nan take Anty Laure ta ce da Usaina ta shirya su tafi, babu musu ko gardama Usaina ta mike ranta babu daɗi, ta haɗa 'yan tsummokaranta suka yi sallama da Baba da Inna, Hassana da Khalid suka rako su har titi, suka tari Keke Napep sai unguwar Bompai.

  Wani katafaren gida Usaina ta ga sun tunkara, gida ne kamar flat house daga wajensa amma idan ka shiga sai ka ga ashe bene ne. Fuskar gidan daga waje tamkar wata ma'aikata, fulawowi ne jajaye da koraye sun baibaye katangar gidan daga sama. Yayin da wasu dogayen bishiyoyi masu tsananin tsayi ke kaɗa ganyansu sakamakon iskar dake kaɗawa fil-fil-fil gwanin sha'awa.

  Ƙarasawa suka yi kusa da wani ɗan ƙaramin ɗaki dake jikin katangar gidan wanda tagarsa take waje kusa da wata ƙaramar kofa. Sallama Anty Laure ta yi daidai tagar ɗakin, wani mutum matsakaici ya leƙo. Gaisawa suka yi da Anty Laure sannan ya fito ya buɗe musu 'yar ƙaramar kofar nan suka shiga.

  Usaina ta ji sassanyar iskar nan dake kaɗawa ta ƙaru sosai yayin da suka shigo harabar gidan. Tafiya Anty Laure take Usaina na bin ta a baya tana kalle-kallen abubuwan da ba ta taɓa gani ba. Kafin su kai ainahin inda za su shiga asalin gidan sun yi tafiyar kamar mintuna biyu.

  Fulawowi da bishiyoyi ne na adon gida iri-iri, kukan tsuntsaye ne kawai ke tashi, daga can gefe guda kuma tafkin linƙaya ne wato swimming pool \ud83c\udfca, daura da shi kuma wani ɗan lambu ne da bishiyoyin umbrella suka yi wa wajen ƙawanya. Rana ba ta sauka a kan ƙasar wajen, koda yake ba ƙasa ba ce wasu korayen ciyayi ne masu ban sha'awa wajen kallo.

  Suna isa wajen da gundarin gidan yake, wata 'yar matattakala suka hau me taku kamar biyar zuwa shida wacce ta sada su da ƙofar shiga, Anty Laure ta danna wani madanni kusa da ƙofar, 'yan daƙiƙu kamar 15-20 aka buɗe ƙofar.

  Wata tsaleliyar budurwa ce jajir da ita tamkar a taɓa ta jini ya fito, ta risina tare da cewa, “Sannu da zuwa Anty Laure.”

  Anty Laure ta amsa cikin sakin fuska, “Yauwa Mami sannunki.”

  Suka ƙarasa cikin falon, nan Usaina ta ga ashe abin da ta gani a waje na ƙawa ba komai ba ne, yanzu ne za ta bawa idanuwanta abinci, yanzu ne zavta ga inda aka maida naira tamkar yayi.

  Falo ne tangameme wanda faɗinsa da tsayinsa ya fi ƙarfin kwatance, abin sai wanda ya gani. Jefa ƙafar da Usaina za ta yi bisa carpet ɗin ta ji lumus, ƙafarta na lumewa kamar za ta shige ƙasa, ga wani sanyi da ya ratso ƙafar har ta fara jinsa a ƙwaurinta.

  Wasu maka-makan kujeru ne irin leather seats ɗin nan wanda ake musu polish bayan an yi mopping ɗin su da kumfa, sun kewaye falon, sai wata damɓareriyar talabijin ɗin plasma da aka damɓara a bango me kallon yamma. Daga saman falon kuma wata tankasheshiyar fitila ce me tsananin haske, tana da wasu sarƙoƙi masu launin ruwan zinare.

  Baya ga na'urar sanyaya daki wato (AC) kuma akwai wasu narka-narkan fankokin tsaye guda biyu da suka saka falon a tsakiya, wato ɗaya daga gabas tana kallo yamma sannan kuma ga ɗaya daga yamma tana duban gabas. Kai tsayawa bayyana yadda wannan falo ya haɗu ya zama ƙauyanci, ga waɗanda ba su san meye duniya ba kuwa, sai su nemi su karya ta mutum.

  Zama Usaina ta yi bisa carpet ɗin nan, yayin da Anty Laure ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun me zaman mutum biyu wato two seater. Ita kuwa wannan budurwa wato Mami, sama ta nufa domin sanar da hajiya. 'Yan mintuna kamar biyar su Usaina na zaune, sai ga Mami sun dawo ita da hajiyar.

  Babbar mace ce ta ɗan fara manyanta, aƙalla zata kai kamar shekara 55-60, ita ma fara ce sosai, kamar su ɗaya da Mami, kallon ɗaya za ka musu ka gane cewa 'ya da uwa ne.

  Tana ƙarasowa ta,ce, “'Yammata ya ya za ki zauna a ƙasa, tashi maza ki zauna bisa kujera ai ba a zama a ƙasa.”

  Usaina ta mike ta zauna kusa da Anty Laure, ita ma hajiyar da 'yarta zama suka yi a kan kujera, yayin da Anty Laure ta gai da hajiyar cikin risinawa, haka ita ma Usainar ta yi koyi da Anty Lauren.

  Bayan sun gama gaisawa, Anty Laure ta ce, “Hajiya wannan ita ce yarinyar da aka samo za ta yi aikin.”

  Cikin fara'a da sakin fuska, hajiya ta ce, “Ma Sha Allah! Ya ya sunanta?”

  Anty Laure ta ce, “Sunanta Usaina.”

  “Kai Ma Sha Allah! Ashe tagwaye ne, ina Hassanar ta take? Da fatan dai kin yi mata bayanin abin da za ta rika yi ko?”

  “E na yi mata wanke-wanke ne da shara, na yi mata bayanin komai tun tuni.”

  Hajiya ta ce, “To madalla da fatan dai ba me wasa ba ce?”

  Murmushi Anty Laure ta yi sannan ta ce, “Hajiya ai Usaina in dai wajen aiki ne ba na jin ta, ita da 'yar uwarta jajirtattu ne. Ba zan taɓa kawo miki yarinya me wasa ba.”

  “To shi kenan, Mami kai ta ɗakin nan ta aje kayanta ta huta.”

  Mami ta mike Usaina na biye da ita a baya suka shiga wani ɗan ɗaki madaidaici dake can kusan ƙuryar falon. Cikin ɗakin gado ne da katifa da sif, da lokoki.

  Suna shiga Mami ta ce, “Nan ne ɗakinki da za ki rika kwana, ga sif nan ki zuba kayanki a ciki, nan kuma shi ne toilet.” Ta faɗa tare da nuna mata wata 'yar ƙofa daga cikin dakin.

  Usainah ta ce, “To na gode.”

  Nan Mami ta baro Usaina a dakin ta dawo falo tare da cewa, “Hajiya na kai ta.”

  Anty Laure ta nisa tare da cewa, “To hajiya ni zan koma, ina son zan shiga kasuwa ne akwai wani turare da zan nemo.”

  Hajiya ta yi wa Anty Laure ihsani me ɗan tsoka, ta yi mata godiya sannan ta mike ta fito.

  Usaina da aka bari a ɗaki ita kaɗai, duniyar tunani ta tsunduma, tunani take me zurfi game da yadda rayuwa take sauyawa, daga wannan mataki zuwa wancan. Kodayake a yanzu wannan da ɗan dama-dama idan aka kwatanta shi da wanda suke kai a baya. Aiki duka aiki ne, amma wannan aikin ya fi na kamfanin barkono da suka baro sau dubu.

  Tana zaune tana wannan tunani Mami ta dawo wajenta. Ita kam Mami yanayin Usaina ne ya fara burge ta sosai, sha'awa take ba ta, a hannu guda kuma tana ba ta tausayi. "Ga ta kyakkyawar yarinya amma kuma an kawo ta aikatau, gaskiya wannan ba ta dace da me aiki ba."

  Mami a ranta take wanann zance kafin daga bisani ta ce da Usainar, “Taso muje falo hajiya na kiran ki.”

  Mikewa Usaina ta yi suka dawo falo, gaban hajiyar ta je ta durƙusa kanta sunkuye ta ce, “Hajiya gani.”

  “Ki kwantar da hankalinki Usaina kin ji, ba rabaki a ka yi da danginki ba, kamar yadda na faɗa wa Laure duk bayan mako biyu za ki je ki gai da magabatanki sai ki dawo.”

  Kanta sunkuye ba tare da ta ɗago ba, ta ce, “Babu komai hajiya, na gode.”

  Hajiya ta dubi Mami tare da cewa, “Mami kin nuna mata ɗakinta ko?”

  “E hajiya na nuna mata har ma ta aje kayanta a can.”

  “To ki kai ta kitchen ki nuna mata guraren da za ta yi aikin, yanzu dai babu wani abin sai dai gobe ta fara.”


  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

0 comments