Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 09

MATAKIN NASARA 09

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 17 & 18*


  Nan suka sake mikewa tare, Mami ta zagaya da Usaina guraren daban-daban inda aikin nata zai kasance, daga karshe ta kai ta kitchen din gidan. Kasaitaccen kitchen ne da ya hada komai na bukatar rayuwa, sannan a tsaftace yake tamkar ma ba a amfani da shi.

  Shi dai wannan bujimin gida da Usaina za ta rika aiki a ciki, gida ne mallakin wani hamshakin jami'in gwamnati a fanni tsaro. Amma ya rasu babu jimawa, ya bar matsarsa ɗaya, ita ce hajiya Kaltume, 'yar asalin Yobe ce, sai 'ya'yansu guda biyu kacal mace da namiji, Mami wacce aka bayyana a baya ita ce macen, namijin kuma ana kiransa Kabir, shi ne babba.

  Mami za ta kai kimanin shekara 19-20, ta girmi Usaina da shekaru kamar biyu zuwa uku. Ta gama makarantar Secondary Boarding School, yanzu haka dai tana zaune a gida ba ta civgaba ba.

  Kabir ya yi karatun health har matakin Masters Degree yanzu haka yana jagorantar wani asibitin kudi da Abban nasu ya gina gabanin ya mutu. Wannan kenan.

  Bayan barin Anty Laure daga gidan tallarta ta shiga gari, sai da dare ya yi sannan ta je take wa Inna bayanin yadda aka yi, bayan sun gaisa take cewa,

  “Hajiyar ta ce duk bayan sati biyu za a rika biyan Usaina naira dubu goma ( ₦10,000) ladan aikinta, sannan kuma duk bayan sati biyun ne zata rika zuwa ganinsu.”

  Inna ta yi murna sosai tare da yi wa Lauren godiya.

  ***

  To a bangaren Habib kuwa, lokacin da Baban su Hassana ya cika kwanaki bakwai a gida, shi da hajiyarsa suka sake zuwa kara duba shi, kodayake shi da ma Habib yana zuwa kuma yana kiran Hassana a waya, kusan kullum yana tambayar jikin baban.

  Suna isowa kofar gidan, ya lalubi layin Hassana ya kira ta ya ce, “Ina kofar gida tare da hajiya muke.”

  Nan da nan Hassana ta fito ta yi musu iso zuwa ciki, Baba na ganin hajiya ya mike zaune daga kwanciyar da yake tare da cewa,

  “Sannu da zuwa sannu hajiya, Allah Ubangiji ya saka miki da mafificin alkairi Allah ya jikan magabata, Allah ya shiryi zuri'a na gode na gode kwarai.”

  Hajiya ta ce, “Sannu sannu bawan Allah, ba sai ka tashi ba ma, koma ka kwanta Allah ya kara sauki.”

  “Hajiya, ai jiki ya samu AlhamduLillah, har waje ma ina ɗan leƙawa ni kadai.” Yana fada ya yunkura ya mike ya dan kewaya a cikin dakin sannan ya koma ya zauna a hankali.

  Hajiya har dariya ta dan yi kana ta ce, “Babu shakka jiki ya samu, Ma Sha Allah! Ubangiji Allah Ya kara lafiya.”

  Inna ta gai da hajiya, Habib ya gai da Inna sannan ya juya ga Baba shi ma ya gaishe shi tare da yi masa sannu.

  Baba ya fashe da kuka cikin kukan yake cewa, “Wannan yaro Allah ya yi maka albarka, Allah ya jikan mahaifanka, Allah ya ba ka abin da kake nema duniya da lahira. Dalilinka na samu lafiya, bayan na yanke kauna da sake mikewa, babu abin da zan iya cewa da kai sai Allah ya yi maka albarka.”

  Hajiya ta amsa da cewa, “Amin, ai duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Kuma duk me rai ai ba ya yanke kauna da samun ko mene ne, cuta da waraka duk na Allah ne.” Tana fadar maganar ta bude jakarta ta debo wasu 'yan dubu-dubu damƙi madaidaici ta mika wa Baba.

  “Haba hajiya ai wannan ɗawainiyar ma da kika yi ta isa, Allah ya ba da lada, ki mayar da kudinki, na. gode sosai Allah Ya sa ki ɗauka gaban Annabi.”

  “Tambaya ta ka yi ne? Niyyar kaina ce.” Ta fada tare da ajiye kudin kusa da shi, ta mike sannan ta ci gaba da cewa, “Allah ya kara sauki ya kiyaye gaba, ni zan koma, Abbana tashi mu tafi ko?”

  Su duka suka mike har da Baban suka rako su kofar gida wajen mota, Habib ya bude wa hajiya ta shiga shi ma ya shiga ya yi wa motar key suka tafi.

  Inna da Hassana da Baba da Khalid suka koma cikin gidan fuskokinsu cike da fara'a da annuri. Har yanzu dai mutanen gidansu babu wanda ya san yadda su Inna suka hadu da wannan attajirar hajiyar da ta fara sauya rayuwarsu cikin ɗan ƙanƙanen lokaci. Haka nan kuma babu wanda ya isa ya tunkari Innar da tambayar ya ya a ka yi suka hadu ko kuma dai wata tambayar makamanciyar wannan. Sakamakon wani irin bahagon zama da suke.

  Duk da kasancewar su masu karamin karfi, amma mafi akasarin su fitinannu ne. Hassada da bakin ciki ta mamaye zukatan mafi yawa daga cikinsu, sai ƙalilan da suke zama na kadaran kadahan, babu cutarwa babu kuma taimako. Irin zaman nan na kowa tasa ta fisshe shi, wato kowa ya iya allonsa ya wanke. To Allah ya ganar da al'umma masu irin wannan mugun zaman, amin.


  *_GWAMMAJA_*

  Gwammaja nan ne unguwar da Alhaji Idi wan Inna, yake da zaune. Mustapha babban ɗansa, ya kammala karatunsa har ma ya dawo gida. Kamar yadda kuka ji a baya, kafin tafiyarsa makaranta ya kasance yana soyayya da Hassana, suna son junansu. Ya kasance yana matukar tausaya musu kuma yana taimaka musu sosai da kudi, wani lokacin ya sayi kayan abinci ya kai musu. To sai dai Abbansa ya ƙi ba shi fuska, shi bai ma amince ba ya rika kula Hassana.

  Baya nan ma Babansu Hassanar ya gamu da wancan iftila'i, amma Ummansa ta fada masa ta waya, to kasancewar yana final year ne a lokacin, abubuwa sun masa yawa, shirye-shiryen exams da project, bai samu damar zuwa ba, sai yanzu da ya kammala komai baki daya. A lokacin da abin ya faru ya yi jimami da nuna alhini sosai tare da addu'ar Allah ya ba shi lafiya.

  Abubuwa dai sun faru sosai baya nan, domin bai san cewa Inna ta zo neman taimako wajen Abban nasu ba, ya hanata, sannan bai san yadda a ka yi aka samu kudin da aka yi wa Babansu Hassanar magani ba.

  A ranar da ya diro gari, Baban su Hassanar ya fara tambaya da jikin nasa, to a nan ne Umman tasa ta zayyane masa duk yadda abubuwan suka faru, da irin yadda Abbansu ya ci gaba da nuna halin ko in kula ga rayuwar su Hassana. Daga karshe take sanar da shi wanda suka dauki nauyin biyan kudin aikin da aka yi wa Babansu Hassanar.

  Yamma na yi misalin karfe 5:00pm, Mustapha ya shirya ya yo wa gidan su Hassanar tsinke.


  *_TUDUN WADA_*

  Misalin karfe 5:30pm ya karaso, bai tsaya neman iso ba kai tsaye ya sa kai cikin gidan tare da yin sallama. Da yake gidan ya kasance gida ne kamar na kowa da kowa, samarin gidan ma wasu sun fi shi girma haka suke shigi da ficinsu.

  Bayan sun gaisa da mutanen da ke tsakar gidan ya karasa dakin su Hassana tare da sake yin sallama a daidai kofar ɗakin. Nan take Hassanar ta dauki muryasa, ta amsa masa sallamar, ya bude labulen ya shiga.

  “Ah ah ah! Wa zan gani? Yau muna da manyan baki a gidan namu ke nan, maraba da 'yan makaranta sannu da zuwa, yaushe a gari?”

  Inna ce take wannan maganar yayin da Hassana ta shimfida masa tabarma ya zauna. Baban ya fara gaidawa tare da yi masa ya jiki, sannan ya juyo ga Inna ya gaida ita tare da yi mata jaje.

  Sake juyawa ya yi ga Baban ya ce, “Sannu Baba, ashe abin da ya faru ke nan, Umma ta yi mini waya lokacin, to da yake muna rubutun project ne shi yasa ban samu damar zuwa ba. Allah ya kara lafiya, Allah Ya sa kaffara ce.”

  “Ai babu komai Mustapha, abin da waje ba kusa ba, bai kamata ba ma ace ka zo, gara da ka tsaya ka yi komai a tsanake. Addu'o'in da kuka mini ga shi Allah ya karɓa ya ba ni lafiya. Ni da na yanke ƙauna da sake yin tafiya ko mikewa tsaye, amma ga shi hukuncin Allah Ya yaye mini tamkar ba ni ba, sai mu yi wa Allah godiya kawai.”

  “Haka ne Baba, to Allah Ya kara lafiya, Allah Ya kiyaye gaba.”

  Baba ya amsa “Amin.”

  “Ya ya karatun, an kammala ko? To Allah Ya sa me amfani a ka yi. Yaushe ka dawo ne?” Inna ce ta yi wannan tambayar, yayin da Mustapha ya ba ta amsa da cewa, “Yau din nan na dawo da safe.”

  “Shi ne ko hutawa ba ka yi ba ka taho?”

  Murmushi Mustapha ya yi tare da cewa, “Inna ai ba zan iya zama ba matukar ina cikin garin nan ban zo na duba jikin Baba ba.”

  “Aiko ka kyauta sosai, Allah Ya saka da alkairi.”

  Ya amsa da cewa “Amin Inna.”

  To sun jima sosai suna hira, a nan ya yi sallar magariba da Isha. Bayan Isha kadan ya ce zai koma, ya yi sallama da su Inna, Hassana ta rako shi waje. Nan suka kafa wata sabuwar hirar.

  Ya lura da sauyi game da Hassana, ta dan kara girma kadan sannan kuma ya ga waya a hannunta. Ganin ta da wayar ne abin da ya dan taɓa masa zuciya wanda ya saka masa tunanin, to a ina ta samu waya kuma sabuwa ma? Tunda dai ya san halin da suke ciki. Koda ma a halin wadata suke, abu ne me matukar wahala kaga budurwa ta sayi waya da kanta.

  Dan haka babu shakka wani ne cikin samarinta ya ba ta, wannan shi ne tunanin da yafi nutsuwa da shi.

  Fitowarsu kofar gidan keda wuya ta sake gaishe shi, bayan sun gaisa ya ce, “Saboda rashin kirki shi ne ma kina da waya amma baki kira ni kin fada mini abin da ya faru ba?”  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*


Comments

0 comments