Rubutu

Blogs » Abubuwan Al'ajabi » MATAKIN NASARA 1.

MATAKIN NASARA 1.

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*  *Pɑge 19 & 20*


  Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba, ya ci gaba da cewa, “Ko ba haka ba ne? Ko ya yi miki kashedi akan kada ki kira wani sai shi kadai?”

  Murmushin dai ta sake saki me dan sauti sannan ta ce, “Kai yaya Mustapha! Kai dai ka fiye kishi. To waye kuma zai hanani kiran mutane, ko ba zan kira kowa ba, ai kai banda kai.”

  “Ai ina da gaskiya ne, ku din nan ba tabbas ne da ku ba. Duk yadda mutum ya amince muku lokaci daya za ku iya sauya tunani. Ina can amma kullum ke ce a raina.”

  “Hmmm! Wallahi ni ma kana raina yaya Mustapha, so ya karatun?”

  “Karatu babu dadi amma an gama AlhamduLillah!”

  “To ya yi kyau, Allah Ya taimaka.”

  Ya dan ɓata fuska kadan alamar ɓacin rai ta bayyana a fuskarsa, sannan ya ce, “Na ji abin da Abba ya yi wa Inna, bai kyauta ba sam, kuma ban ji dadin abin ba, wannan rashin adalci ne da wulakanta zumunci. Don Allah ki yi hakuri kada kisa komai a ranki.”

  Murmushi ta yi tare da tace, “Haba yaya Mustapha wace irin magana kake haka? Wallahi babu komai, ai komai samun dama ne. Da ace yana da damar taimakawa da ya taimaka. Babu komai Allah ne bai ba shi ikon yin taimakon ba, addu'a da fatan alkairin da aka yi ma mun gode AlhamduLillah!”

  Ya ɗan yi shiru kana ya ce, “Wai ina Usaina ne tunda na zo ban gan ta ba?”

  “Usaina ba ta nan tana zuwa wani gida ne aiki, a can take zaune amma duk bayan sati biyu tana zuwa ta yini sannan ta koma.”

  Ya ɗan nuna rashin jin dadinsa a kan hakan, to amma tunda ya san halin da suke ciki sai ya ce, “Allah Ya taimaka, duk ranar da za ta zo ki sanar da ni.”

  A nan wajen ma dai sun jima sosai suna ta zance, sai misalin karfe 9:00pm na dare sannan suka yi ban kwana, ta karɓi wayarsa ta saka masa lambarta sannan ya tafi.


  *_RIJIYAR ZAKI_*

  To, shi kuwa Habib tun lokacin da suka zo da hajiyarsa dubiyar Babansu Hassana bayan sallamo su daga asibiti, bai sake dawowa ba kimanin sati biyu ke nan. Ya ɗan yi ban-iska, kodayake suna waya lokaci zuwa lokaci.

  Bayan makonni biyun ne ya yi wani sabon shirin zuwa gidan, amma wannan karon zuwan na musamman ne. Zuwa ne na ƙashin kansa, zuwa ne na yaɗa manufarsa.

  Shiri ya yi na-gani na-fada, kwalliya ya caɓa, ya ci adon manyan kaya shadda gizna me yauƙi da hular zanna irin 'yar maiduguri. Agogo da takalma iri ɗaya masu matukar kyau da tsada. Ya feso wani turare wanda za'a iya jiyo ƙamshinsa tun daga nesa kamar taku saban'in a tsakani.

  Yana gama shirin, ya dauki wayarsa ya lalubo number Hassana ya ƙwalla mata kira tare da cewa, “Ina kan hanya.”

  Nan da nan ita ma ta mike domin fara shirin tarbar sa, ganin ya ɗan kwana biyu bai zo ba, yasa ta dan shirya masa wani dan girki na musamman, duk da dai ta san abu ne me matukar wahala Habib ya ci abincin gidansu.

  Tana gama girkin ta shiga ta watso ruwa a jikinta, ta yi 'yar kwalliyarta simple makeup, amma abinka da wanda aka ce kyakkyawa ne, sai gashi ta yi ras! da ita tamkar ta je gidan yin kwalliya. Ta yi kyau sosai gwanin sha'awa.

  Karfe 12:00pm na rana Habib ya iso kofar gidan, kafin isowarsa sai da ya tsaya a Sahad Store na kan titin mandawari ya haɗo wasu kayan shopping, kana ganin kayan za ka fahimci akwai wani saƙon sirri, da shi wanda ya sayo kayan yake son aika wa zuciyar wacce za a kaiwa kayan.

  Wayarta ya kira bayan ya yi parking, tana ganin kiran ta tabbatar ya iso, ɗagawa ta yi tare da cewa, “Assalma Alaikum.”

  Ya amsa fuskarsa cike da murmushi, “Amin wa alaikumus salam, ina kofar gida.”

  “Tom ina zuwa ganin nan, ba ni minti daya.”

  Ta kashe kiran, ta sake duba mudubi sannan ta dauki hijab ta saka ta fito, yana cikin motar, tana leƙowa ya ɗan sauke glass ɗin bangare shi yana sakin murmushi me cike da ɗimbin saƙonni.

  Ta karasa kusa da motar, ganin yadda yake ta sakin murmushi yasa ita ma ta fara sakin nata lallausan murmushin tare da cewa, “Barka da isowa.”

  “Barkan ki dai ranki ya daɗe.”

  Murmushin ta ci gaba da yi har da ɗan sauti sannan ta ce “Hmm! Bisimillah ka shigo mana.”

  “Ai wannan zuwan naki ne, ina ganin ba sai na shiga ba. Amma dai mu shiga na gai da su Inna da Baba.”

  "Hmm! Zuwan nawa ne kuma?" A ranta ta yi wannan maganar bayan taji wani abu da ya kewaya a zuciyarta \ud83d\udc93.

  Ya fito daga motar suka shiga, kamshin turaren dake jikinsa ya game gidan kaf! Da kamshi tamkar an yi ɓarin turaren a wajen. Ya yi sallama sannan ya shiga dakin, Inna ce da Khalid kawai a dakin, Baban baya nan ya ɗan yi tattaki zuwa majalisa, dayake ya fara takawa sosai.

  Habib ya zauna bisa tabarmar da Hassana ta shimfida masa, ya gai da Inna cikin ladabi da girmamawa kansa a ƙasa ba tare da ya dubi fuskarta ba.

  “Ina Baba yake?” Ya tambaya,

  Inna ta ce, “Ya dan fita waje ne yanzu nan ba jimawa.”

  Ya ce, “AlhamduLillah! Lallai Baba jiki ya warware ke nan, to Allah ya kara masa lafiya.”

  “Allahumma amin! Ya ya hajiyar da fatan duk kuna lafiya.”

  “Lafiyarta lau, tana gaishe ku.”

  Bayan kamar mintuna ashirin (20 minutes) Habib ya ce, “Inna ni zan koma, a gai da min da Baban idan ya dawo.”

  Ya saka hannu a aljihu ya zaro wasu kudi ya aje gaban Innar tare da mikewa.

  “Oh kai dai baka gajiya! Allah Ya saka da alkairi Allah ya jikan magabata, ka gai da hajiya.”

  Ya fito Hassana ta yi masa rakiya wajen mota. Jingina ya yi a jikin motar, minti kamar daya babu wanda ya yi magana tsakaninsu, zuwa can ya ce, “Wai ko ina Usaina ne ban gan ta ba?”

  “Ayya Inna ta aike ta gidan kawunmu shi yasa ba ka gan ta ba.”

  “Okay, to ya labari?”

  “Hmmm! Labari sai ku masu kewaya gari.”

  Sakon dake zuciyarsa yake son bayyana mata amma ya rasa ta ya ya zai kamo kan zancen, me zai ce mata ne? "Ina sonki zance ko kuwa me?" A ransa yake ta wannan sake-saken daga karshe dai ya nisa tare da cewa,

  “Ina bukatar wani abu guda daya a wajenki, ina fatan kuma zan samu?”

  Kirjinta ta ji ya fara wani dar! dar! dar!, tare da tunanin to wane abu ne kuwa take da shi har da Habib zai yi sha'awa, har ma yana rokonta? Shi dai ba shi da siffar mutanen banza bare ya yi mata zancen banza. Sannan kuma indai batun soyayya ne ko a mafarki ba zai yi yu ba ace saurayi ɗan hamshaƙin attajiri kamar Habib ya ce yana sonta. Sam wannan haɗin ba zai yi matching ba.

  Cikin karayayyiyar zuciya ta ce, “Wane abu ne kuwa wannan da nake da shi har sai ka roƙe ni? Kai dai kawai tsokana ta kake.”

  Ya yi murmushi tare da cewa, “Ni na gan shi kuma ina son ki yi mini alkawarin za ki ba ni kafin na fada miki ko mene ne.”

  “Hmmm! To shi kenan ka fada mini ko mene ne zan ba ka indai ina da shi. Babu abin da na mallaka a duniya da za ka bukata face na ba ka shi, ina jin ka.”

  Ya ɗan yi shiru sannan ya ce,“Ina son ki ɗan ba ni wani gurbi a cikin zuciyarki da zan yi wata ajiya!”

  “Hmm! Ban fahimci me kake nufi ba, ajiya a cikin zuciya kuma, ka warware mini wannan zancen.”

  “Ina sonki ne \ud83d\udc96\ud83d\udc9e.”

  Wuta ta ji ya ɗauke mata da wannan kalamai nasa, lokaci me ɗan tsayi suka yi shiru babu wanda ya sake cewa komai kanta sunkuye ta sauke wani gajeren numfashi sannan ta ce,

  “Don Allah don Annabi ka bar wannan maganar, abin nan ba me yi yuwa babl ne. Ka tambayi wani abin daban, ni ba na daya daga cikin irin matan da suka dace da kai. Rayuwata da taka sam ba iri daya ba ce, ka nemi mace me irin matsayinka, ni dai na gode da kulawarka.”

  Kallon ta kawai yake sai da ta gama surutan sannan ya ce, “Ashe kina da saurin mantuwa ke nan? Yanzu har kin manta alkawarin da kika dauka cewa ko mene ne za ki ba ni? Shin da ma alkawari bai kasance abu me muhimmanci ba a wajenki? Ban yi zaton cewa ashe kina daya daga cikin irin mutanen nan masu wulakanta alkawari ba. To shi kenan na gode Allah ya saka da alkairi, ni zan wuce.”

  Cikin yanayin kiɗimewa ta ce, “A'a a'a ba fa haka nake nufi ba, ba ka fahimce ni ba, ka tsaya don Allah. Ni ina nufin ka auri mace wacce ta dace da kai me ilimi, me matsayi da daraja irin taka. Ni ban dace da kai ba, don Allah ka nemawa kanka macen da rayuwarka za ta ci gaba da kasancewa cikin farinciki kamar yadda ka taso.”

  “To idan zan yi amfani da shawarwarinki ke ce kika dace da ni. Tunda kin ce na zaɓa wa kaina, to na san kaina kuma na san abin da zai dace da ni, don haka ke na zaɓa. Kuma ki sani maganar matsayi da daraja, wa ya fada miki cewa na fi ki matsayi ko daraja? Indai kina son rayuwata ta ci gaba da wanzuwa kamar yadda kike fada, to ki amince da bukata ta. Hajiya ta ba irin mutanen nan ba ne da ke nuna kyamar hada zuri'a da masu karamin karfi. Abin duk da kike tunani ba zai taɓa faruwa ba, da ni da ke duk 'ya'ya ne, iyaye ne suka tsugunna suka haife mu. Kasancewar na taso cikin rayuwar jin dadi, hakan baya nufin nafi karfin auren 'yar masu karamin karfi, shi arziki da rashinsa duk na Allah ne. Ke nake so kuma ke na zab a abokiyar rayuwata.”

  Maganganun sun mata nauyi sosai, anya kuwa wannan al'amari zai yi yu? Auren 'yar talaka fitik da kuma dan mashahuran masu kudi???  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

2 comments