Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 22

MATAKIN NASARA 22

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 43 & 44*


  Usaina ta ce, “Ki je kawai ni ina nan, ai maganar hajiya gaskiya ce. Shan zaki idan ya yi yawa yana haifar da illa ga lafiyar jiki.”

  Mami ta ce, “Au ke ma kin zama mai wa'azin ce ko kuma likita ce? To ya yi kyau sai a yi wa wanda za a yiwa wa'azin. Ni kun ga tafiyata.”

  Mikewa ta yi ta deɓi ledojinta ta nufi daki. Hajiya ta dubi Usaina ta ce, “Ke ma je ki kin ji, ba hana ku sha na yi ba, amma dai a riƙa shan kaɗan.”

  Usaina ta mike ta nufi dakin, tana shiga Mami ta kalle ta a yatsine ta ce, “Me kuma ya kawo ki ke da ba kya shan zaƙi? Kuma da kin san haka za ki yi da ba ki bari na sayo kayan da yawa ba. Ni saboda ke sayo. Idan kuwa don kin ji hajiya ta faɗi wannan maganar ne, to wallahi idan za ki biye wa hajiya sai ta hana ki cin komai a duniya. Ita ba lafiya ce da ita ba, shi yasa take ganin kamar kowa ma haka yake.”

  “To ai ke ma ba lafiyar ce dake ba, gara hajiya ita larura ce daga Allah, amma ke fa? Mai lafiya ba zai taɓa aikata abin da kike aikatawa ba.”

  “Hmm! Usaina wulakanci kike mini yau, na ga neman rigima kike tun ɗazu, maganar da ranki ya miki daɗi kike faɗa mini kai tsaye.”

  “Yo ke ɗin me kika gama faɗa wa hajiya yanzu, akan tana faɗa miki gaskiya. Ko ba abin da kika gadama ba kika faɗa mata? Sai ke ce yanzu za ki ce ina faɗa miki magana, kin manta gidan radio nake faɗa miki.”

  Mami ta yi dariya sosai sannan ta ce, “Na ji komai za ki faɗa mini, ki faɗa lokacin ki ne. Yanzu dai ga kayan nan ki ɗauka ni ba na son komai ke na sayawa.”

  “Hmm! Ni ina zan kai wannan kayan zaƙin haka? Kashe ni kike so ki yi ke nan. To in dai ke ma ba za ki sha ba, ni ma ba na so.”

  “To shike nan zan sha zo mu raba.”

  Nan dai suka sha wasu chocolates suka aje sauran. Suka ci gaba da hira, Mami kokari take ta ga ta kauda wa Usaina wancan ɓacin ran da ta saka mata.

  Da Magariba ta yi Kabir ya dawo, a falo ya iske su hajiya da Usaina da Mami. 'Yar kwalliyar Nan da Usainar ta yi, ta ba shi sha'awa sosai duk da cewa ba wani tsayawa ta yi ta tsara ta ba. Saboda haka zama ya yi shi ma aka ɗora hirar tare da shi, ya riƙa kallon Usaina tare da aika mata saƙonni ta cikin murmushi. Kunya duk ta kama Usaina. Hajiya ta mike ta haye sama ta bar su su uku a nan.

  Kabir ya kalli Usaina fuskarsa dauke da annuri ya ce, “Tea nake so.”

  Mami ta yi murmushi tare da cewa, “Ka ga masoya, ni ma a dafa da ni, na ci albarkacin masoya.”

  Harara Usaina ta aika mata sannan ta ce,“Kin daɗe ba ki sha ba, idan kina so ki tashi ki shiga kitchen din, ko ba ki da hannu ne?”

  “Da hannuwana biyu ras har ma sun fi naki, amma ba zan dafa ba, wanda kika yi da hannunki nake so kuma sai na sha.”

  Murmushi Usaina ta yi ba tare da sake cewa komai ba, ta mike ta nufi kitchen. Mami ta dubi yaya Kabir cikin sigar shagwaɓa ta ce, “Kana ji ma tana faɗa mini baƙar magana sai dariya kake ko?”

  “Tare na gan ku ban san me ya haɗa ku ba, babu ruwana. Ke ma wataran za ki fada mata maganar. Kuma ni ban ga laifinta ba, idan mutum ya ji haushi to shi ma ya yi zuciya ya nemo abokin da za su riƙa shan shayin tare mana.”

  Haɗe rai ta kara yi, ta yi kicin-kicin da ita tare da mikewa ta nufi sama, jikin hajiya ta kwanta da shagwaɓa sosai tana matso hawaye, hajiya ta ce, “Mene ne kuma Mami? Hala ke da Kabir ne ko?”

  Ta gyaɗa kai alamar e.

  “Me ya yi miki kuma, ba yanzu na baro ku ba, kuna hira?”

  “Wai gori yake mini har yanzu ba ni da mai sona.”

  “Yi shiru kin ji rabu da shi, idan na ga rawar kansa ta yi yawa sai na ce ban amince ba. Idan ya so na ga ta shegantakar da har zai riƙa yi miki gori.”

  Babu jimawa Usaina ta gama haɗa tea ta ɗoro kofuna uku a kan faranti. Ta nufo falo, Kabir kawai ta gani. Bayan ta dire farantin shayin, tambayarsa tayi, “Ina Mami din kuma? Ba dai korar ta kavyi ba? To ai sai ka sha kai kaɗai, ka ga tafiya ta ni ma.”

  Ta juyo za ta tafi ke nan ya yi saurin riƙo hannunta, ta juyo tare da watsa masa wani irin kallon mai cike da mamaki, idonsa cikin nata ko kiftawa ba ya yi, kusan minti daya suna kallon-kallo, ba wanda ya yi magana shi kuma yana riƙe da hannun bai saki ba.

  Murmushi ya saki sannan ya ce, “Ki tsaya ki saurare ni, kin yi mini tambayoyi ba ki bari na baki amsa ba har kin yanke hukunci. To ni ba korar ta na yi ba, magana muke kawai ta yi fishi ta haye sama wajen hajiya. Da ma na ga kamar rigima take nema.”

  “To me ka faɗa mata har ta yi fishi? Babu wani rigima da take nema, tun safe muke ta hira babu wani damuwa a tare da ita, akwai abin da ka faɗa mata mana?”

  “Hmm! Ni dai ba wani abu na fada mata ba, cewa na yi ya kamata ta nemo wanda za su rika shan shayi tare. Shi ne ta ji haushi.”

  “Dole ne ta ji haushi sosai mana, ai wannan kamar cin fuska ne. Gaskiya ka daina haka, ni zan bar gidan nan ma in dai haka za ka rika yi.”

  “Shike nan amma ni da wasa nake mata ai.”

  “To na ji sakar mini hannu mana, ko so kake wani ya fito cikinsu ya gan mu? Ka kula fa, ka bi a hankali kada murna ta sa ka bata komai.”

  “Shike nan ki je ki lallabo ta.”

  “Wa? Ni, haram sata gidan barawo. Kai da ka bata mata rai kai za ka je ka bata hakuri ka lallabo ta.”

  Daga nan falon yana zaune ya kwalla mata kira da gabadaya muryarsa, “Maaammiii!” Har firgita Usaina ta yi saboda tsananin karar muryar.

  A can saman Mami ta mike za ta sakko, hajiya ta ce, “Ke rabu da shi, ko so kike ya sake fada miki abin da ya fi wannan zafi?”

  “Ki bar ni hajiya, zan je na yi masa wankin babban bargo ne. Idan na kyale shi ma ya samu dama ke nan kullum ma sai ya yi mini.”

  Mikewa ta yi ta sakko tana kumbure-kumbure, tana karasowa Usaina ta tare ta da cewa, “Ki yi hakuri da maganar da yaya Kabir ya fada miki. Kawai ya fade ta ne ba tare da ya san girmanta ba a kan mizanini auna zantukan da kan taba zuciya. Shi da wasa yake miki, ya ya ma zai yi miki gorin masoyi. Shi din yana da masoyiyar ne, yaushe ya je ya nemo ta ba mu sani ba. Ki manta kawai. Ga tea din tun dazu na gama, zo mu sha kayanmu. Shi din sam masa za mu yi.”

  Mami na ta zumburar baki hade da hararar yaya Kabir, Usaina ta kama ta suka zauna tare kan kujera daya two seater. Usaina ta mika mata cup din shayi daya ita ma ta dauki daya, yaya Kabir da ma tuni ya dauki nasa ya fara sha, murmushin tsokana kawai yake musu. Haka dai suka rika shan tea suna ta hirarsu, a zolayi wannan a tsokani wancan, har kowa ya manta da wani abu na damuwa. Sun jima suna taba hira, har lokacin kwanciyar barci, yaya Kabir ya yi musu sallama ya wuce dakinsa.

  Usaina ta kalli Mami ta ce, “To ke sai da safe ko, ni ma na yi nan.”

  Dakinta na asali ta nufa, wanda aka fara kai ta lokacin da ta zo gidan. Abin da Mami ta yi mata na lesbian din nan yasa ta dauri aniyyar ba za ta sake kwanciya tare da ita ba. Tana isa dakin ta shiga ta turo kofa za ta rufe, Mami na biye da ita a baya, ta danna kofar ta shiga tare da cewa, “To ki rufe yanzu.”

  “Ban gane na rufe ba.” Usaina ta fada ba tare da ta kalli fuskar Mamin ba.

  “Ai ba za ki taba ganewa ba, me yasa za ki zo nan ki kwanta? Da ma a nan kike kwanciya, kuma da ma ke kadai kike kwanciya?”

  Cikin murmushi Usaina ta ce, “Ina ganin hakan zai fi kyau mu raba wajen kwana, kowa ya kwanta daban-daban. Tunda da ma can ba tare muke kwanciya ba, ko akwai laifi ne hakan?”

  “Ban sani ba, idan an yi abu shike nan bavya wucewa a wajenki? Duk tunanin da kike ma ki daina, babu abin da zan miki, na ce ba zan sake miki ba ko, ya kamata ki yarda da ni. Amma idan kika kwana ke kadai a nan da safe hajiya za ta tambaye ki, me za ki fada mata? Kin ga idan bavki yi wasa ba ma sai ki daura wa kanki jakar tsabar da kaji za su bi ki suna tsattsaga, a ce kun hada ba ki da yaya Kabir shi yasa kika dawo nan ke kadai. Kin san halin hajiya sarai.”

  Babu shakka hajiyar za ta iya yin wannan zargi, don haka dole Usaina ta fito suka koma can dakin Mamin inda suke kwana tare.

  Kwanciya suka yi yadda suka saba cikin bargo daya, sai dai Mami ba ta yi wannan isakncin nata ba da ta saba yi na dorawa Usainah cinyoyinta ko kuma taba mata nono da sunan magagin barci. Lami lafiya babu wata matsala suka kwana. To wannan kenan.

  ***

  Kamar yadda hajiyar Habib ta yi masa alkawarin bayan tarewar su Hassana a sabon gida, za a tambayar auren Hassanar. To hakan ne ya faru, bayan ta kira Malam Ibrahim kanen mahaifin Habib, sun tattauna akan maganar, aka tsayar da jibi a matsayin ranar da za su je.

  Habib ya kira Hassana ya sanar da ita rana da kuma lokacin da wakilan nasa za su je. Don haka sai suvma suka yi shirin tarbar bakin a bisa al'ada. Baban su Hassanar ya fada wa aminansa da kuma limamin unguwar. Haka Inna ma ta fadavwa wanta, Alhaji Idi Abbansu Mustapha. Duk wanda ya dace a fadawa dai an sanar da shi kuma kowa ya hallara.


  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

2 comments