Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 23

MATAKIN NASARA 23

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 45 & 46*

  Misalin karfe 4:15pm, bayan idar da sallar La'asar keda wuya, Habib ya dauko Malam Ibrahim da kuma wani ƙanen hajiyar ana kiransa Alhaji Musa suka iso gidan su Hassanar.

  Waya Habib ya yi, ya sanar da ita cewa sun iso fa, suna kofar gida. Ita ma isar da saƙon ta yi ga Baba, dayake yana gida. Da aka idar da sallar dawowa ya yi, ya duba ko baƙin sun iso, saboda haka takalmansa ya sa ya fito. Malam Ibrahim da Alhaji Musa ne suka fito daga motar, Habib bai fito ba.

  Bayan sun gama gaisawa Baba ya ce, “To Bisimillah!”

  Ya shige gaba suna biye da shi a baya har zuwa Masallacin unguwar, inda a can ne sauran mutanen ke zaman jiran su Malam Ibrahim din. Gaisawa aka fara yi sannan liman ya jagoranci addu'a.

  Bayan an gama addu'a Baba ya dubi Alhaji Idi da liman ya ce, “Waɗannan su ne magabatan yaron da yake neman auren Hassana.”

  Liman ya ce, “To Ma Sha Allah, sannun ku da zuwa.”

  Nan dai aka yi dukkan abin da ake yi bisa al'ada aka gama. Aka ba da kudin dukiyar aure, sannan aka saka rana watan Muharram, ya kama watanni bakwai ke nan. Daga karshe Baba yake sanar da mutanen cewa, “Ai yaron Ɗa ne ga marigayi Alhaji Sa'eed Na Kowa.”

  Gabaɗayansu mamaki kama su ya yi, har da Alhaji Idi wanda tunda aka zauna bai ce uffan ba. Fuskarsa a ɗaure baya fara'a. Liman ya sake jagorantar rufe zaman da addu'a tare da fatan Allah Ya tabbatar da lamarin, Allah Ya ba da yadda za ayi. Aka yi musabaha aka watse kowa ya kama hanyarsa. Hassana ta taka matakin farko na zama amarya, saura kuma 'yan baya.


  *_BAYAN SATI DAYA_*

  Yau ranar lahadi ce, kuma ita ce daidai cikar sati biyu, wato ranar da Usaina take zuwa ganin gida. Tun sassafe ta tashi ta gama duk aikaceaikacenta, ta yi wanka ta shirya tsaf! Tana jira a ɗan ƙara jimawa sannan ta taho.

  Mami ce ta same ta ta ce, “Ashe fa yau ne ranar zuwanki gida ko, shi yasa na ga sai wani gwalli da zumuɗi kike.”

  “Ai dole na yi kowa ma yana son danginsa. Ke ɗin yanzu ba ga ki ba a gaban hajiyarki ba, kina taɓararki yadda kike so.”

  “Hmm! Usaina wallahi yanzu ban san me yasa kika rena ni ba, kai tsaye kike faɗa minu duk maganar da ranki ya yi miki daɗi.”

  “To meye kuma abin raini a nan, don na ce ga ki a gaban hajiyarki kina tsula tsiyarki, ai ba ƙarya na yi miki ba ko sharri.”

  “Hmm! Zan yi miki rashin mutunci Usaina, ni ce ma nake tsula tsiya ko? Yanzu dai mu bar wannan maganar, tare zamu tafi dake. Ni ma zan je na gai da su Inna, kuma ina son na ga Hassana.”

  “Ki yi zamanki ni dai ba na son rakiyar, na gode.”

  “Au rowar gidan naku za ki yi mini, ba kya so a je a ga gidan naku ne ko ya ya? To bari ki ji sai na je, tare zamu tafi, bari ma ki gani na shirya.”

  Murmushi Usaina ta yi ta ce, “Mutum sai naci kawai anvce ba a son rakiyar amma ya kafe sai ya je.”

  “E an yi nacin, ni ba don ke zan je ba ai, wajen su Inna da Hassana zan je.” Mami ta fada tare da mikewa ta nufi toilet tayo wanka ta komo tacyi kwalliya. Lokacin hajiya ta sakko falo tana zaune suna tattaunawa da Kabir.

  Bayan Mami ta fito daga wankan sun gama shiri, sun fito falo Mami ta ce, “Hajiya tare za mu tafi da Usaina, zan je na ga gidansu.”

  Hajiya ta jinjina kai tare da cewa, “Oh! Ikon Allah, wannan shaƙuwa taku haka, kamar ma ke ce Hassanar tata. To babu komai sai kun dawo, ku gai da mutanen gidan.”

  Kabir dake zaune shi ma ya yi farat ya ce, “Bari na zo na kai ku tunda yau weekend ce, ni ma sai na ga gidan ko? Davma ina son na tambaye ta, to kuma ga shi ma za su je, ko ya ya kika gani hajiya?”

  “Babu shakka hakan ya yi, da ma ya kamata a ce ka je ka gai da magabatanta, wannan tunani naku daidai ne Allah ya tsare, ku gai da mini da su.”

  To dayake da ma a shirye yake cikin manyan kaya, mikewa kawai ya yi suka fito suka shiga mota, murmushi kawai yake saukewa a fuskarsa. Ita kuwa Usaina ba ta yi farinciki da wannan tafiya da hajiya ta haɗa ba. Yaƙe take, ita ba yanzu ta tsara Kabir zai je gidansu ba, ta so a ce sai ta zo gidan ta fara yin bayani an yi shiri sannan idan ma zavsu zo, sai su zo din.

  Suna tafe a mota suna ta hira gwanin sha'awa, Kabir ya ɗan ratse hanya suka tsaya a wani waje da ake sayar da kayan marmari, ya sayo kaya masu yawa sannan suka biya ta Grand Square, nan ma aka haɗo kayan shopping sosai.

  Suka kamo hanya sai Tudun Wada kai tsaye, Usaina na ba shi direction din inda zai bi har suka iso kofar gidan. Ya yi parking, suka fito gabaɗayansu.

  Mamaki ne ya lulluɓe zukatan Kabir da Mami, gida ne suka gani ga shi nan mai kyau babu laifi. Yanayin gidan kawai za ka duba ka fahimci mazauna gidan ba sa cikin wahalar da 'yarsu za ta yi aikatau. To amma me yasa Usaina take aikin wanke-wanke? Sannan kuma ga ta ma ba irin munana 'yan matan ba.

  Abubuwan da Kabir da Mami suke ta saƙawa ke nan a zukatansu.

  Usainah tavce ,“To bisimillah ku shigo mana.”

  Kabir ya ce, “A'a ku fara shiga dai tukunna.”

  “Ka ga ka shigo kawai, ko kuwa cinye ka za a yi da za ka tsaya ka ce ba za ka shiga ba?”

  Murmushi ya yi, zai sake magana Mami ta ce, “Ya isa haka yaya Kabir, mu shiga, idan mun gama abin da za mu yi, sai ku ci gaba da wannan gardamar taku.”

  Usaina na gaba Mami na bin bayanta sai shi kuma Kabir din a baya, suka shiga cikin gidan tare da yin sallama. Hassana ce a tsakar gidan tana wanki, ta amsa sallamar tare da ɗagowa, maimaikon ta ga Usaina ita kaɗai, sai ta ga mutane har uku har da namiji.

  Da sakin fuska ta ce,“Sannun ku da zuwa.”

  Ta tsame hannunta daga wankin. Cikin falo suka shiga gabaɗayansu har Kabir wanda kunya ta fara ɗaure wa fuska.

  Zama suka yi a kan kujeru. “Ina Inna ne, ko barci take?” Usainah ta tambaya.

  “E ta ɗan koma barci ne, bari na taso ta.” Hassana ta ba ta amsa tare da mikewa ta nufi dakin Innar, “Inna Usaina ce ta zo har da wasu baƙi. Da alama 'yan gidan da take aikin ne.”

  Inna da Hassanah tare suka komo falo, Kabir ya yi saurin zamewa daga kan kujera ya zube a ƙasa sosai ya gaicda Inna, haka ma Mami tavyi, sannan Hassana ta gaishe su.

  Bayan an numfasa da gaishe-gaishen, wajen ya yi shiru, Usaina ta katse shirun da gabatar da su Kabir din, “Inna wannan ita ce Mami da nake baku labari, shi kuma wannan Kabir wanta ne. Hajiya ce ta ce su zo su ga gidanmu.”

  “Madalla sannun ku da zuwa ya gidan, ya ya hajiyar da fatan duk kuna nan lafiya.”

  Mami ta amsa, “Lafiya lau wallahi, hajiya ma ta ce tana gaishe ku.”

  “To madalla muna amsawa. Ke Hassana maza ki zubo musu abinci da ruwa.”

  Hassana ta mike ta nufi kitchen ta zubo musu abinci sannan ta dauko jugs guda biyu da kananun cups ta kawo ta dire wa Mami da Kabir. Inna ta mike ta koma dakinta, ita ma Hassanar ta fito kan wankinta, aka bar Usaina da bakin nata.

  Sun dan jima shiru babu wanda ya yi magana, Usaina ta dube su ta ce, “Bisimillah mana, ga abinci nan kuma ga ruwa.”

  Kabir ya yi gyaran murya hade da murmushi sannan ya ce, “Am... ni dai AlhamduLillahi na koshi.”

  “Ban gane ka koshi ba? Ko dai ka rena abincin gidan namu ne?”

  “Hmm! Kodaya kawai dai ba na jin yunwa ne.”

  Usaina ta dan bata rai kadan sannan ta ce, “Babu wani ba ka jin yunwa, kawai ka ce kyamar abincin gidanmu kake, to shike nan ba komai.”

  Dariya ya yi sannan ya ce, “Ba haka ba ne, don Allah ki fahimce mana. Ba...”

  Ta katse shi da cewa,“Ya isa haka malam babu abin da za ka fada na yarda da kai. Ke Mami dauki naki ki ci, ko ke ma din kyamar mu za ki yi?”

  “Hmm! Usaina yanzu tashen neman rigima kike sosai, babu dama mutum ya yi magana sai ki rikice. To ni ban ce ba zan ci ba, ki sa hannu mu ci tare. Ki ma kirawo Hassanar mana ba sai mu ci tare ba.”

  Ganin yadda Usaina ta bata rai yasa Kabir ya dan cin abincin ya sha ruwan sannan yavce, “Alhamdulillah! To gashi dai na ci abincin gidan naku sai ki daina fishin ko? Kuma abincin ya yi dadi sosai. Ba don na koshi ba, kin san cinyewa zan yi duka har ma na ce ki karo mini.”

  Dariya ta yi tare da cewa, “Yanzu na ji magana, amma da ka ce wai ka koshi.”

  Za su fara cin nasu abincin ke nan Kabir ya ce, “Amma yanzu za mu koma ko?”

  Wata harara mai cike da mamaki Usaina ta aika masa, ta ma rasa me za ta fada masa. Ta koma yanzu sai ka ce ana korarta!

  Mami ce ta ba shi amsa da cewa, “Ka ga ka tafi kawai mu muna nan, ai ka san yini take duk ranar da ta zo gida ko. Sai yamma za mu koma. Idan za mu taho zan kira ka sai ka zo ka dauke mu.”

  “To shikenan, kira mini Inna mu yi sallama ko?”  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

0 comments