Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » MATAKIN NASARA 24

MATAKIN NASARA 24

 • MATAKIN NASARA

  For indeed, with hardship there will be ease. Qur'an 94:5.

  Sɑdik Abubukɑr

  Wɑttpɑd @sɑdikgg

  LAFAZI WRITERS


  *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*


  *Pɑge 47 & 48*

  Usaina ta mike ta kira Inna, Kabir ya ɗan risina tare da cewa, “To Inna ni zan tafi sai anjima da yamma zan dawo na dauke su.”

  Ya sa hannu cikin aljihu ya dauko wasu kuɗaɗe ya a je gabanta tare da cewa, “Ga wannan a sayi ruwa.”

  “Aah! Har da wata ɗawainiyar kuma daban, to Allah Ya saka da alkairi, ka gai da hajiya, a sauka lafiya.”

  “Amin.” Ya fada tare da mikewa, Usaina da Mami har ma da Hassana suka rako shi waje, ya shiga mota ya yi tafiyarsa. Su kuma suka koma ciki, Hassana ta kama wankinta tana sauri ta ƙarasa a sha hira ita da su Usaina.

  Mami da Usaina kuwa falo suka koma, Usaina ta dubi Mami ta ce, “Wai ke ma ba za ki ci abincin ba ne ko ya ya?”

  “Ke jarababbiya ni ban ce haka ba, ki kira Hassana mana sai mu ci tare ko?”

  “Ke kin ga idan za ki ci ki ci, koda ba ta ci abinci ba, yadda take wankin nan ba zavta tsaya ba sai ta gama, ita haka take. Don haka ki sa hannu mu ci kawai.”

  Nan dai suka ci abincin su biyu, suna yi suna ta faɗan cacar bakin da suka saba. Mami ta saki jiki sosai babu wani nuna baƙunta, abinci ta ci sosai, suka cika cikinsu taf!

  Bayan sun gama suka buɗe shafin sabuwar hira, abubuwa da yawa Mami take son yin tambaya a kai amma tana jin tsoron tsiwar Usaina. Duk da haka sai da ta ce,

  “Da ma kamar ku daya da Hassana? Ai ko da za mu haɗu da ita a wani wajen zuwa zan yi na rungume ta na ce ke ce.”

  “Hmm! Allah ko, da ta yi miki ihu ta ce zaki ɗauke ta.”

  “Haba dai sai ka ce ke, ai da ganin ta ta fiki hakuri da kirki.”

  “E ɗin na ji ta fi ni, ta je ta yi ta fi na ɗin sai me kuma?”

  “Allah ya ba ki hakuri baiwar Allah, ni ba da fada nake nufi ba. Ita ɗin dai mutuniyar kirki ce, shi yasa nake yabon ta, na san da ita yaya Kabir ya fara gani da ko kallo baki ishe shi ba.” Cikin sigar zolaya Mami take faɗin wannan maganar.

  Usaina ta ce, “Ni ɗin mutuniyar banza ce ko, wallahi za ki sani Mami bari mu koma gida sai na rama duk wulaƙancin da kika mini.”

  “Allah koh? Ashe za ki rame ke nan.”

  Suna ta wannan hirar zolaye-zolayen har Hassana ta gama wankinta tsaf, ta shiga wanka ta yi ta fito.

  Falo ta shigo, kallon ta kawai Mami take, komai da komai kamar su daya, sak Usaina. Babu wani abu da za ka iya banbancewa tsakaninsu, hatta da sautin muryarsu iri daya ne.

  Kwalliya Hassana ta ɗan yi sama-sama kasancewar ana ɗan yin rana a garin, akwai zafi. Nan suka sake gaisawa da Mami.

  “Ai Usaina ta daɗe tana ba ni labarinki yau dai na ce sai na zo na gan ki mun gaisa an yi zumunci.” Mami ta faɗa tana murmushi fuskarta cike da fara'a.

  “Allah Sarki, ai ko gara da kika zo aka gaisa din, ya gidan ya hajiya, ya hakuri da rigimar Usaina kuma?”

  Mami ta yi dariya sannan ta ce, “Hajiya lafiya lau, Usaina kam akwai rigima yanzu ma muka gama bugawa da ita.”

  “Hmm! Ni ce ma mai rigimar ko? Kuma ɗin ai rigimammu ne, duk zan iya da ku.”

  Hira suka yi sosai a tsakaninsu gwanin sha'awa, Mami ta zama tamkar 'yar gidan wacce suka ta so tare. Yini suka yi tare har wasu 'yan aikace-aikacen tare da Mami suka yi. Da yammaci Kabir ya bugowa Mami waya yace, su shirya ga shi nan tafe nan da mintuna talatin (30 mins).

  Shiryawar suka yi tsaf! Karfe 6:00pm daidai ya iso kofar gidan ya yi parking sannan ya kira wayar Mami tana ganin kiran tavce da Usaina, “Kin ga yaya Kabir har ya iso.”

  Ta ɗaga kiran da cewa, “Ga mu nan fitowa.”

  To dayake ita Mami tunda rana sun gaisa da Baban su Usainar, Kabir ɗin ne ba su gaisa ba don haka sai Usaina ta ce, “Ki ce ya shigo su gaisa da Babanmu.”

  Kabir ya shiga ya gai da Baba cikin girmamawa, sannan suka fito Hassana ta yi musu rakiya har wajen mota. Mami ta dubi Hassana ta ce, “Ba ni lambarki.”

  Bata gama rufe bakinta ba Kabir ya saka hannu kan dashboard ɗin motar ya dauko kwalin waya sabuwa ya mikawa Usaina tare da cewa, “Ke ma ga taki nan sai ki ba wa anty Hassana lambarki ko?”

  Cike da murna da fara'a ta karɓa ta bude ta fito da waya, ya riga ya gama haɗa mata komai ya saka layi ya yi mata caji. Hassana ta karɓi wayar ta saka lambarta a ciki ta kira, ta ga lambar Usainar ta yi saving. Suka yi sallama, Hassana ta juya gida, su kuma suka dauki hanya.

  Tafe suke a nutse, ba wani gudu yake ba. Usaina ta fara yi masa godiya da wayar da ya saya mata, Mami kuwa tsokanar ta take da cewa, “Ba sabun ba su o'o an yi kunne.”

  “E na ji dai, ke ma ƙila ba ki wayar aka yi, daga hakan kika fara.”

  Kabir ya cafe zancen da cewa, “Kamar kin sani kuwa, ita roƙa ma ta yi don Allah na taimaka na saya mata.”

  “Yaya Kabir meye haka don Allah? Meye kuma na tona mini asiri a gabanta, ka san yanzu sai ta rena ni ko?”

  “To shike nan na yi shiru, ai da ma kun fi kusa, kwa shawota tare na gan ku.”

  Dariya kawai Usaina take wa Mamin haɗe da gwalo, tana dariyar tana cewa, “Aikin gama ya riga ya gama, na ji komai hajjaju makkatutu sarkin roƙo, da ma na ce miki zan rama duk wulaƙancin da kika mini, to na fara yanzu.”

  Hira suke gwanin sha'awa har suka isa gida lami lafiya.

  Hassana da Inna kuwa su ma hirar suka kafa bayan tafiyar su Usainar, Inna ta dubi Hassana ta ce, “Ikon Allah! Allah mai yadda Ya so. Dare ɗaya Allah Kan yi Bature in ji masu iya magana. Dubi rayuwarmu a jiya ki kuma dube ta a yau? Lallai Allah Shi ne abin dogaro, Allah mun gode maka bisa wannan ni'ima da kake saukarwa a kanmu.”

  Hassana tace, “Amin, ai Inna gaskiya Alhamdulillah. Ita ma Usaina da gani ta yi waje, yanayinsa zai yi tausayi da kulawa. Kuma da alama shi ma ya gaji arziki, yanzun nan da ya dawo daukar su ya zo mata da sabuwar waya, har ma na dauki lambarta sai gobe da safe na kira ta ku gaisa.”

  “Kai Masha Allah! Allah Ubangiji Ya hada zukatanku, Allah yadda Ka fitowa da yaran nan mazaje Allah Ka hore mana yadda za a yi. Allah Ya yi muku albarka.”

  Hassana ta amsa, “Allahumma amin.”

  ***


  *_GWAMMAJA_*

  Alhaji Idi wan Inna, ya zo wajen karɓar kudin auren Hassana ya koma gida cikin matukar mamakin yadda ya ga rayuwar su Inna ta sauya. Domin ya jima sosai bai ziyarci inda suke ba. Ya watsar da zumunci duk saboda kada ya kashe kudinsa. Koda lokacin da aka yi wa Baba aiki ma bai zo ya duba shi ba, sai ya fake da cewa uzurirrika ne suka yi masa yawa.

  Duk abubuwan da Umma take faɗa masa game da yadda Allah ya fara inganta rayuwar su Innar bai yarda ba, jin abin yake kamar tatsuniya. Sai yanzu da aka gayyato shi ya zo karɓar kudin auren Hassanar. Yanzun ma bai yi niyyar zuwa ba, Umma ce ta tilasta masa. Shi a tunaninsa baya so ya raɓe su domin kada bukatar kudi ta ta so, a nemi gudummawarsa ko kuma taimako.

  To sai dai ya zo ya ga abin da bai taɓa tsammani ba, gidan da hajiya ta saya wa su Inna da kuma Habib da zai auri Hassana su ne abubuwan da suka fi tsaye masa a rai. Babu shakka wadannan bayin Allahn sun taka tudun mun tsira.

  "Amma na tafka babban kuskure. Na yi ba daidai ba, musamman yadda na raba Mustapha da yarinyar nan. Amma bari na san me zan yi, bari na kira shi na sanar da shi an kawo kudin auren Hassana, yanzu ya nemi Usaina kawai."

  Da zuciyarsa yake wannan zantuka da ba su da maraba da karatun wasikar jaki, ba za su taɓa yin amfani ba lokaci ya kure. A kwance yake yana ta wannan tunani, zuwa can ya nisa tare da ƙwallawa Umma kira, “Ke Suwaiba, Suwaiba!”

  “Na'am ga ni nan zuwa.” Ta yi sauri ta aje aikin da take yi, ta nufi saman domin ta san jarabarsa yanzu sai ya fara fada, bare ma ta ga 'yan kwanakin nan yanayinsa babu walwala cikin damuwa yake.

  Tana isa ta ce, “Alhaji ga ni lafiya dai?”

  Ya ɗan yi shiru lokaci kaɗan sannan ya ce, “Am... Da ma maganar yaron nan ne Mustapha, kin ga wannan yarinya ba matarsa ba ce. Me zai hana ya nemi 'yar uwarta Usaina? Ina ga duk ɗaya ne ai.”

  Murmushi ta yi ta dube shi cike da mamakin maganar da take fitowa daga bakinsa, anya kuwa ba mafarki yake ba? "Yau kuma kai ne da kanka kake sha'awar haɗa aure tsakanin 'ya'yanka da su Usaina?"

  Tunanin da Umma ta yi ke nan a zuciyarta kafin daga bisani ta ce,

  “Hmm! Alhaji ke nan, wannan ai wani abu ne na daban, duk yaran ɗaya ne tabbas, to amma karka manta zukatansu kuma ba ɗaya ba ne, da bambanci. Ba ni da tabbas amma ita ma Usaina tana da tsayayye, gidan da take aiki akwai yaron gidan da yake son ta, maganar ma ta fara karfi.”

  Numfashi ya ja ya sauke sannan ya ce, “To yanzu meye abin yi ke nan?”
  *αввαи αιѕнα*

  *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

Comments

0 comments