Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Zuciya da gwanin ta

Zuciya da gwanin ta

 • Yaran makaranta ne zaune a katafarun kujerun da aka ware musamman saboda su,  Sanye da Graduation gown a jikin su. Kallo daya za ka ma fuskokin su ka tabbatar cewa kowannen su na cikin da tsantsar farin ciki, gabadaya hankalin su ya karkata ne wurin bayanin da principal in na su ke faman yi yayin da wasun su ke ta faman ware ido su ga ta ina iyayen su za su shigo cikin hall in.

  "This is your final day in this school, i hope you will maintain the good morals, character and learning you get from this school, am very proud of your succesful SSCE results and i will tell you today you are one of the best students we feel pleasure to have in this school. With this i want to wish everyone of you a succesful life ahead, i will miss you all my children"

  Da karfi dukkan su suka hada baki wurin fadin "we will miss you too sir" Emotional ones daga cikin su kam har sun fara zubda hawaye, ranar ta kasance ma dayawa daga cikin su tamkar mafarki ne, after six years wai sune zaune a hall in makarantan a matsayin graduating students, the thing is just Unbelievable.

  Sannu a hankali juniors in su daga JSS1 zuwa SS2 ke fitowa performing akan stage. wanda duk saboda su ake yi. Abun na matukar kayatar dasu, yayin da jikin wasu ya riga da yayi sanyi barin ma da aka zo wurin da Yan SS2 ke performing spoken poetry, duk dai kalaman sallama ne da suke musu kunshe a cikin shi. Aka ce wai sabo turken wawa, sai dai a ranar yau da yawa daga cikin su sun aminci zuciyoyin su ya kasance wawan zuciyan saboda yanayin da su ka tsinci kansu a ciki, kaman ba sune su ke cikin tsantsar farin cikin zuwa ranar graduation in nasu ba.

  Daga nan su aka kira su ka fito, inda su ka fara performing cool music in da su kayi choosing musamman saboda wannan lokacin, dukkan su rike da mic, yayin da su ke ta faman rairo wakan cikin zazzakan muryoyi. Juyin da su ke ba wani sosai bane. Fuskokin su kuma ga dai shi kana ganin kasan suna cikin murna ne amma kuma duk da haka bai boye jimamin rabuwan da ke kwance kan fuskokin su ba duk a lokaci daya.  Dai dai lokacin da aka saki fire works su ka buga tsale wurin cilla graduation caps in su sama. This is a very nice view musamman ma wurin photographers in da aka kira specifically saboda wannan ranar, sun yi kokarin ganin sun yi capturing duk wani feelings da ke fuskokin daliban, wanda ya bayyana farin ciki, shakuwa da kuma tsantsar kewa da zasu yi ma juna, it the best moment ever.

  Gift presentation aka fara yi daga nan, makarantan bai da wani yawan dalibai hakan ya sa kalilan daga cikin su ne kawai ba su wani karba kyauta na musamman ba. Headboy in aka kira ya fito ya musu his well written farewell speech cikin gwanacce wan turancin da ke bakin shi, nan ma sai da aka samu dayawa daga cikin su da su ka zubda kwalla, barin ma irin girma na daban da su ke bawa headboy in, yaron ne wanda ya matukar sanin mai yake yi ga ilimi wadatacce Allah ya bashi, dadin dadawa shi in mai adalci ne sosai.

  Next headgirl ince ta fito, ita ma cikin shigan ta na kamala, da dukkan natsuwa ta ke tafiyan ta har zuwa lokacin da ta fara karanto nata speech in. "I love and hold each every one of you so close to my heart, i can't believe we are parting today, i hope too see you soon not here but somewhere better in life" daga hakan ta kare maganan ta, ita kanta jikin ta yayi la'asar idanuwan ta taf da kwalla a cikin su ta ke kallon mate in nata yayin da su ke ta faman tafa mata.

  MC in da ke wurin ne ya amshi mike in, wani joke ya danyi saboda ganin yanda duk jikin daliban yayi. "Now i will call on a very special student for a parting speech/poem to the whole school and then we will conclude today's program with closing prayers" shiru yayi yana kallon fuskokin student insu, su kan sun kosa su ji wa za a kira saboda dai basu da wani idea akan wannan performance in gabadaya. "In person of Nabeela Mainasara" Duka kallon mamaki su ka juya suna bin Nabeelan dashi. Murmushi kawai ta musu sannan ta mike ta karasa kan stage in ta amshi mic in hannun MC.

  Sai da ta gyara tsayuwan ta, ta tattaro duk natsuwan ta wuri daya sannan ta fara magana cikin karfin guiwa "i want to perform a poetry, actually it has no title, here it goes" with a very audible voice ta fara karanta poem in da ke cikin kanta.

  The long path of life,
  we began the journey the day we stepped our legs into this school.  That very day, we left our home, family, and our whole to a strange environment.
  With no acquatained nor anyone to hold on.
  That very day, life was on hold.
  Everything felt so numb, until it takes a turn.
  The need to survive thrash those sorrows
  Gradually, that strange environment becomes the new us, the home that provide an acquired serenity.
  A place we grow to love, endure, scarifice and survive.
  We become the place, for we describe it best.
  And today, what a day to be alive?
  The thorns, the flaws and hurdles we become to love is about ending.
  Here's to the memories
  To the togetherness we shared

  Cikin gwanace wa ta ke karanto poem in ta yanda sautin muryan ta ke sauka cikin zuciyoyin duk wani mai sauraron ta. Dai dai sanda ta zo inda ta ke cewa

  Here's to the lovely teachers
  The guiders
  Who devoted their time to us
  And stuck with us through it all
  They taught us and give us a helping hand

  Juyawa tayi tana kallon su, ba ko dar ta cigaba da karanta poem, jin yanda ta ke kwararo musu kalaman yabo yasa farin ciku mara misaltuwa bayyana a fuskan ta, barin ma da ta idanu da cooper Abubakar. Wanda shi ya bata duk wani karfin guiwan abinda ta ke yi a yanzu, jinjina mata kai yayi alamun yana matukar alfahari da ita. Sai da ta dan lumshe idanun ta sannan ta juya bangaren iyayen da su ka hallara cikin hall in, idanuwan ta cikin na Mamin ta take fadin

  "Here's to my parents
  The guardians, mothers and fathers
  Ever so supportive and ever so loving
  How can i repay them I'm yet to decipher
  School is such a chore
  School is such a bore
  We'd always said.
  Without hesitation parents say "School's great"

  Cracking muryan ta keyi ganin yanda su ke binta da wani kallon kin samu alfahari da ba ta juya a lokacin ba abunda zai hana ta zubewa a wurin.

  "Here's to my juniors" side in da juniors inta ke ta juya yanzu, su kam ba karamin burge su tayi ba barin ma ganin yanda sautin muryan ta ke cigaba da fitowa ba wani gargada.

  Who shall pick up the mantle
  Remember never to give up
  And strive to do what's right
  The journey is full of hurdles
  But the destination is worth the trouble.
  Here's to home away from home
  And family away from family

  Here's to my friends and accomplices.
  Such mischief we managed
  Such joy we did shared.
  History will live to remember.
  We suffered many thorns on the path,
  fulls of obstacles,
  we became aggresive to each other at the end,
  we created barriers among ourselves,
  we fought to survive,
  we cried cause we lost our loved one dear to us,
  we changed the old ones,
  eyes shed tears,
  nose keep running,
  the ears listen to words said.
  the mind becomes depressed, everybody emotionally exhausted.

  Nan kam duk yanda ta so boye hawayen da ke idanuwan ta kasawa tayi, fitowa su ke sharara ba kaukauta wa, sai dai ba wai ita kadai ke kukan ba, dayawan su sun kasa iya daurewa

  But what?

  Some were lucky they survived, they made big mistakes
  and corrected them,
  they apologized,
  they struggled together,
  they acheived sucess,
  they created memories.
  Some were lucky some were not. And now the journey is over,
  we all survived it.
  Some were injured and some were not.
  No matter what, it was all the lesson of life and we all learn from it.
  Here's to an end.
  Or maybe to a new beginning.
  Here's to new experiences.

  Daga haka ta fashe da wani irin matsananciyar kuka kan ta a kife kan podium in da ke gaban ta, a hankali mutum daya ya fara tafa wa, wani ya dauka, cikin sakwannin duka wurin ya dauka da tafi, hakan ya kara raising sautin kukan ta. Yin shi ta ke tsakanin ta da Allah ba tare da la'akari da dimbin mutanen da ke wurin ba, cikin sauri Headgirl in ta tashi da sauri ta nufe ta, rungumo ta tayi suna kukan tare, nan friends inta mata su ka fara cika wurin kowa yazo ita ya ke hugging yana fashewa da wani irin matsananci kuka. Sai da mc in ya bari suka sarara, da kan su su kaja Nabeela zuwa wurin zaman su, daganan kuma sai sheshekan kukan wadanda ke ta faman tashi a hall in.

  Ba a dade ba aka rufe taron. Daga nan kuma daliban ne su ka hau raba graduation souvenirs insu. Kowa dai ka kalli fuskan shi dai yake kawai yake, duk sunyi la'asar da har ba sa iya maganan rabuwan nasu ma, shekara shidda kam ai yafi karfin wasa barin ma shakuwa irin nasu na boarding school, tun ba ayi wayau har aka zo aka san inda duniya ta wasa. Sun riga da sunyi amanna da wuya su kara samun wasu kawayen a gaba da za su iya zama su na hakika. Zama ne wanda aka yi shi cikin dadi ko akasin ta, yau fada gobe dariya duk da haka dai an kasance tare duk na tsawon shekarun nan, tabbas secondary school are eternal one, yanayin dabban ne ta yanda ya banbata da duk wani da za samu a gama.

  Daga haka aka fara dan watsewa a hankali a hankali kowa na karasa wurin yan uwan shi da su ka zo mishi graduation in. Nabeela kam kasa kallon fuskokin dayawa daga cikin kawayen ta tayi, barin ma Aminiyar ta Zainab da sanin haduwar su ba zai ma junan su kyau ba. Bin sawun wadanda su kaje fiddo akwatunan su daga hostel tayi, kowa dai kallon juna kawai ya ke, magana ma sai ya kama ake yi shi inma da kaji muryan mutum za kaji alamun kuka kunshe a ciki. Trolley inta da side bag kawai ta dauka cikin sauri dan dai gujewa haduwa da Zainab. Zuciyoyin su duk cunkushe da tunanin kala kala, rayuwa fa kenan yanzu shikenan su kuma sun rabu, rabuwa irin ta abadan, ko da ko za su hadu to fa baza su kara irin wannan zaman da su kayi na makaranta ba. A haka kuma kowa zai cigaba da rayuwan shi cikin hanyan da ya daura kanshi, wasu aure za suyi yayin da dayawa za su tafi makaranta. Wani makarantan cikin sauki zai samu wani ko sai ya sha gwagwarmaya, kowa dai da irin yadda tashi kaddaran zata zo mai. Wanda sun tabbatar da wuya ya kasance iri daya, barin ma irin nasu makaranta daya kasance makarantan kwana, kowa da garin daya fito daga.

  Tafiya take tana kokarin karasawa inda ta hango yan gidan nasu zaune suna jiran ta, ganin da kaya a hannun ta yasa wasu su ka dan taso dan amsan nata. Amina da Sadiq kannen ta da ke school in suma, sune su ka amsan mata kayan. Sai elder cousin sister inta da ta tayi matukar mamakin gani, da sauri tayi side huggin in tayi tana fadin "wow! Anty Salma what a surprise? Yaushe kuka zo country in? Ina Uncle Yusuf da baby Areef?"

  Dariya sosai salman tayi tana fadin "relax Nabeela, duka wannan tmbyn ni kadai? Kema kinsan i won't miss your gradaution. Anyway, am very proud of you today"

  "Thank you my anty" ta fada tana kara rungume ta. Daga kan da za tayi ta hango Copper ..., four eyes su kayi ya sakan mata murmushi, tsaye yake da wasu coopers yan uwan shi sai dalibai maza da su ke magana dasu. Dauke kan ta kawai tayi saboda saurin da take taje gun mamin ta, it have been a while.

  Tayi matukar farin ciki ganin kowa da kowa,  nan mamin ta ke fada mata yanzu zainab ta wuce. "Ni ban ma son ganin ta" da mamaki Abbah yace "Zee in naki kuma?" Dan tura bakin tayi a shagwabe tace "Abbah ai kuka za ta sani" dariya su ka dan mata, Anty Salma na ce mata "sauran da baki yi ba kenan ko?" Family pictures su ka ta dauka da graduation gown in a jikin ta.

  Sai ga kawar ta Khadija tazo kiran ta suyi pictures dan yan gidan su. Tare da Amina da Anty Salma su kaje, sai da aka gama jeruwa za ayi hoto ta juya ta kalli khadija, ita ma khadijan ta kalle ta su ka hada idanu, rungume junan su sukayi sosai su ka fashe da kuka, wannan hoton da ba ayi ba kenan da kyar aka lallashe su. Musamman ta amso ipad in Abbah, da sunan za tayi hotuna da kawayen ta, sai dai sai an jeru za ayi hoton, tana kallon fuskokin friends in nata zata saki kuka suma duk haka, hakanan dai aka yi ta hotunan ba su wani iya tsayawa da kyau ba, wanin ma barin shi akayi ba ayi shi ba.

  Jan Khadija tayi su ka tafi amsan transcript a office in G and C. Sai da yayi commenting akan performance inta sosai kafin ya sallame ta suka fito. A wurin ta hadu da Friend inta Mubarak, mutunci sosai su kayi da mubarak tun suna SSS1 har SS3 insu. Dan wani matsalolin shi da yawa da ita ya ke sharing, ba  ta taba daukan shi a wani abu da ya wuce friendship in ba. Sai jiya, washegarin graduation in kwatsam ya kira ta yana sanar da ita shi kam har ga Allah yana son ta. Yanzu ma kasa kallon shi tayi sosai sai shine ya ce mata "Beela when are you leaving?" Da ke yawanci mate in nasu Beela su kece mata.

  "Soon" kawai tace mishi, ya jinjina kai ya kasa ce mata wani abu kuma. Shi inma idanuwan shi sunyi jajur kaman nata, jin sunyi shiru bai ce mata komai ya sa tace "Bara inje Mubaraka Saduwan alkhairi" da rawan murya tayi maganan. Dan runtse idanun shi yayi yace "okay, i will call you later" daga haka taja hannun Khadija su ka wuce, khadijan na fada mata "shi dai MB da gaske fa son ki yake" Khadijan kadai ta iya fada ma abin daya afku tsakanin ta da mubarak in. Dan bata ma san ta yanda za ta iya sanar da Zainab wannan batu ba.

  "Khadija ina son ganin coper Ibra" kallon ta khadijan tayi, kaman mai son karanto wani abu, basarwa dai tayi tace "dazu ko na ganshi tare da su MB suna hotuna"

  "Let search for him" Nabeela tace, sai dai duk wani lungu da sako na makarantan ba su ga coper Abubakar ba. Dole su ka hada da tmbyn friends in shi wanda su ke dan sakan musu fuska. Abokin shi na kut da kut  Coper Mansur ne ya sanar musu ai Ya tafi apartment insu da ke cikin school, bai dan jin dadi.

  "Sir please zan iya zuwa in ganshi?" Daga kai yayi yana fadin "ba matsala muje in raka ku" da sauri ta ke jan hannun khadija saboda kar ma wani ya gansu ya hana su, dan dai ita she need to see coper ibrahim, duk ko abinda zai faru. Sai dai suna dab da barin Graduation ground sai ga kanin Khadija da gudun shi yana fadin "Anty khadija kizo mu wuce yanzun nan inji Baba"

  Dan bata rai khadija tayi tace "Yanzu zamu wuce ne" gyade kai yaron yayi yace "ai tun dazu mu ke neman ki, Aliy ma ya bi can neman ki kuma baba yace kiyi sauri" apologetic look ta ma Nabeela, telling she have to go. Cikin sadakarwa Nabeelan ta gyade mata kai. Rungume juna su kayi for some seconds kowanne zazzafan kwala na fita daga idanuwan shi.

  "Sai munyi magana" Khadija tace, da kai Nabeelan ta amsa mata tana kallon khadija har ta bace. Rayuwa fa kenan, ita yanzu ko yaushe zata kara ganin Khadijan ta? Wacce ta ke ganin ko Zainab da su ke Aminai ba ta understanding inta kaman yanda khadija tayi. She always give her listening ears, in tana fada mata damuwan ta but zainab will try scolding her, tana sanar mata kaza bai dace ba kaza bai yi ba. Yanzu dai komai yazo karshe, Khadija na Living a Katsina, Another close friend Hauwa na garin Gombe, Zainab da mubarak a Abuja. Har gwara gwara Rukayya da ke bauchi ta san in taje wurin Umman ta za ta iya neman ta to amma kafin taje fa? Sai su Maryam da Hafsa dake nan cikin kano, ba su da wani yan uwa na jiki a kano banda karatun da ya kawo ta garin. only few of her close friend kaman Halima da Asiya ke cikin kaduna, suma unguwa ba daya ba, ga kaduna ba karamin gari ba balle su hadu so easily. She is going to crazily miss every one of them, secondary school life is just the best.

  Mu je ko, coper mansur in yace mata, bin shi ta cigaba dayi yayi da ya ke mata wasu yan tambayoyi akai akai. "Nabeela wani unguwa kuke a kaduna?"

  "Unguwan rimi" ta bashi amsa, ita dai attention inta gabadaya na wurin taga coper ib.

  "Nasan Unguwan rimi sosai, ta ina kuke ne?"

  "Ja abdulkadir" ta kara bashi amsa, yace "lallai nasan layi, layin Hampos da Su Universal ko?" Jinjina mishi kai kawai tayi tana Allah su karasa ko zata ga abinda idanun ta ke muradin gani.

  A/N: Salam, How is Eid? Allah ya maimaita mana. So i figure out today is the best to start the journey of a new book. This is your goron Sallah, hope you will all appreciate it?

  Have you attend boarding school or day? I guess it doesn't much matter. But Wlh as am writing this chapter I can still feel everything. Har yanzu raina na sosuwa in na tuna, our graduation day was so so emotional, kowa ka gani idanun shi yayi ja. It wasn't easy leaving that place after spending many years there. Amma hakanan muka tarkato kayanmu muka taho. Rayuwan daban ce, Kuma an barta kenan. Hence the reason ban iya hada secondary school friends Ina da kowa. Like, they know you at your worst, yet they still cherish you. Even the ones that weren't so close, I still value each of them. We share many things together, the memories are just so sweet. So if you're one of my mate and you're seeing this, just know that i will always rate you no matter what. This is a dedication to you guys, love you.

  I just hope my readers will understand my feelings Sha.

  Sabon littafi, Sabon farin ciki In Sha Allahu.

Comments

0 comments