Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe

 • New book alert \ud83d\udd14

  Title: Mafitan gobe

  GOBE

  Dogon tafiya ce da bata da tabbas. Gobe da nisa amma za ta karato.
  Goben da muke tsammanin haske a cikin sa. Goben da ba lallai mu ganta ba ma.

  Goben da muke mafarki Goben da muke buri
  Goben da muke hange, ta ya zamu same ta?
  Gobe ta kan zo da duhu, watarana ka ganta fara.

  Yaushe ne? Yaushe zata iso? Isowan ta bashi ne ba
  Aa, me zaka tarar?
  Miye shirinka a yau da zai wanke maka Goben?
  Me kake kallo shine mafita a gaba?

  Gobe muke duba, mu gyara zukatanmu.
  Gobe muke duba, mu kaunaci junan mu.
  Gobe muke duba, mu samu yancin mu.
  Gobe muke kallo, mu jure yau.
  Gobe muke kallo, mafarin yancin mu.
  Gobe muke fatan, samun cigaban mu.
  Gobe muke tsoron ya dawo mana jiya.
  Domin kuwa:
  Hangemu a yau shine MAFITAN GOBE

  Our decision today will determine our tomorrow.

  Ta Yaya? Ta Ina? Zamu gyara Yau inmu domin samun mafita a goben?

  Mafitan gobe, labari ne Kan rayuwa Dan Adam, hangen da tunanin sa. Zabi da abinda gobe ya ke haifarwa.

  Blurb will soon be available

  Preview chapters will be available on Wattpad. Cigaba a Manhajar Bakandamiya.

  On the 7th of March, 2022. In Sha Allah.

Comments

0 comments