Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 02: Shafin sadarwa

 • Tunda ta sauƙo daga cikin jirgin take ta faman sauri. Daga ita sai ɗan bag pack in da ta rataya a hannu daya, wanda ya matuƙar sawwaƙa mata wurin saurin da take ta faman zubawa. Nan da nan ta iso inda mutane ke jiran isowan nasu. Kallo ɗaya ta musu, ta fahimci bai zo ba. Ba wai dan ta ƙare musu kallo ba, yanayin da take ji a duk lokacin da take kusa da shine bai ziyarce ta ba.

  "Me ya riƙe shi?" A ranta tayi maganan tare da fidda dan siririn tsaki. Agogon hannunta ta ɗan kalla. Saurin girgiza kai tayi ganin lokaci ya kusan ƙure mata. Da azama ta ƙarasa wurin jerin taxes in da ke wurin. Cikin rawar jiki, drivers in suka nufo ta, tun kafin ta ƙarasa. "Madam where are you going?"
  "Madam let me take you to your destination"
  "My car will be more comfortable for you Hajiya"

  Ɗagowa tayi duk ta zuba musu idanu, ganin yanda kowanne su ke kokarin ganin shi ya samu customer in. Hakan kuwa ji tayi ya ƙara tabbatar mata da tunanin ta. Son kai da zari ya ma al'umman mu katutu, ba Wanda ya damu da ɗan'uwan sa. Niyyan buɗe baki ta amsa take, taji a hankali an jawo bag park in da ke bayan ta.

  Juyowa tayi, su kayi idanuwa hudu. Murmushi ke kwance kan fuskan shi. Ta riga tasan shine, ba yau ya fara mata haka ba. Cike da kauna da farin ciki yake bin ta da kallo. Sati uku kawai tayi bata garin amma ji yake kaman shekaru uku tayi. Wani irin nisa ya ke jin ta mishi bayan kullum a rana sai sun yi magana sau biyu. Ya ɗaɗe yana jin hakan akan ta. Tsoro ya kan sa shi jin kaman nisan zata mishi ko da a gaban shi take. Hakan ya ke ji sosai yanzu, sai ya ke jin na yanzun ma kaman yafi na baya. Da abu ne mai yiwuwa, da tabbas mai da ta cikin jikin shi zai yi ta yanda ba ta da wani daman yi mishi barazanar yin nisa dashi ko da kuwa na sakwan daya ne ko kasa da haka.

  "Welcome home Yar jaridanmu" Kara faɗaɗa fara'an shi yayi. Cike da barkwanci suka yi magana.

  "Mu tafi kar kiyi latti ko Munawwara" Turus taja ta tsaya, wani irin harara ta aika mai. "Allah banso" Da sauri ya hade hannuwan shi "Afuwan ranki shi daɗe" Kwafa tayi, yana mata dariya suka wuce mota.

  Gudu yake shararawa sosai gudun kar tayi lattin daukan shirin da zata yi. Tun da ya fuskanci calls in da ke ta faman shigowa da ga wurin aikin ta ne, ya ƙara gudun motan. "Yau kuma wani ɓangaren daga cikin Mafitan zaku yi duba a kai?"

  "Talauci ko arziki" ta bashi amsa cikin kasala. Saboda wani irin yanayi da tun da suka yanke shawaran bangaren da za suyi duba akan ta ke jin ya ziyarce ta.

  "Ban fahimce ki ba" Ya faɗa yana duba hanyan kwanan da zai yi, in da zai sada su da babban gidan labaran da shirye shiryen da take aiki.

  "Zamu tattauna akan tsakanin Talaka da Mai kuɗi wanene yafi hannu sosai a matsalolin da Arewancin Nigeria ta ke ciki. Sannan a tattauna wani irin mafita yafi kamata a dauka a duka ɓangarori biyun." Dan citsan leɓe tayi, tana jin yanda alamun gajiya daga dogon tafiyan da tayi ke shirin lulluɓe ta. Sai dai, burin ta da kuma manufar ta ya girmi duk wani abu da take ji a cikin jikin ta.

  "To ke wanne kike ganin sun fi hannu akan matsalolin?" Ya buƙata, yana ɗan kallonta ta gefen idanu.

  "AD ko ka manta dani ƴar jarida ce? Ra'ayi na bashi ne ba, ra'ayoyin mutane muke buƙatan ji." Dan dariya yayi har sautin ya fito waje. "Ni ba da ƴar jarida nake magana ba ai, da mata ta nake magana" Dai dai lokacin yayi parking a haraban ma'aikatan nasu. Idanuwa ya zuba mata, yana jin kaman kar ya barta ta shiga, kaman ya hana ta ko da buɗe murfin motan nashi ne. Ita kam ganin lokaci na shirin ƙure mata ne ya sata saurin kai hannu kofan.

  "Madeenaa" Tsayawa tayi tana kallon shi, jin yanda ya ƙira ta. Sai take jin sunan yayi wani daban. Ba wai don bakin shi bai saba furta haruffan ba, yanayin ne dai kawai ya bambanta. Dakewa tayi, tana share waccan yanayin da take ji tuntuni. "Kiyi addu'a kafin ki fara shirin kinji?" Gyade kai tayi, ganin alamun kaman yana jin abinda take jin. "Ki Kula Ɗan Allah, Allah ya kare min mata na" wani irin kallo ta mishi hade da sada kai ƙasa. "Zaki sani ne, je ki gama ma yau dole ki tsaya mu san ina muka sa gaba."

  Bude kofan tayi ganin ƙiran da ya sake shigowa wayan ta. "Zan dawo in dauke ki" taji ya fada. "Okay" ta amsa sannan ta nufi ciki. Idanuwa ya bita dashi ganin yanda take tafiya cikin sauri da ƙwarin guiwa, sai yake jin zuciyan shi na mishi wani irin shiru. Kaman ba ta dauke da komai a cikin ta. Kaman tafiyan Madinan ta tafin mishi da bugun da ke cikin zuciyan nashi. Ji yake kaman ya tashi ya taro ta, ko zuciyan nashi zai samu daidaituwa.

  A bangaren ta, ita ma din ƙarfin hali hade da mahimmanci da ta ba ma aikin nata fiye da komai ne ya sata daga ƙafa cikin sauri. Tana jin hakan kaman mafarin wani abu daban wanda da bata san shi ba. Kaman wani irin canji da bata shirya ma ba na shirin fuskanto rayuwan ta. Ba yau ta fara aikin jarida ba, shekaran ta na biyar kenan a cikin sa. Kuma wannan ma, ta maida shi kaman sauran dukkan shirye shiryen da tayi a baya. Madina Sa'adu Ali kenan, matashiyar budurwar da tayi ficce akan duk wani shafin sada zumun ta. Maccen da a kullum burin ta taga cigaba ya fuskanto ta, hakan yasa duk wani hanya bin shi take, burin ta kuwa ta kai inda take buƙatan kaiwan.

  Baƙin da suka gayyata har sun iso. Yau mutum biyu ne, mace da namiji. Ganin haka ta hanzarta shiryawa aka duƙufa daukan shirin. Bai wani dauke su dogon lokaci ba aka kammala. Suka yi sallama da baƙin su. A lokacin taji duk wani kasala da gajiyan da take guje ma wa ya ziyarce ta. Sai dai har yanzun ji take bata shirya tarban shi ba. Domin son karasa dayan dalilin da ya maido ta gida Nigeria a yau in nan. Tunanin da suka mata cunkus a Kai da zuci ne ya fahimtar da ita gajiyan ba daga jikin ta kawai bane. Aa har da ƙwaƙwalwar ta. Da damuwan da take jin sun mata tsaye a rai. Ballantana ma irin sensitive manganun da suka gama tattauna a shirin da suka kammala yanzun. Cikin gajiya da yaken da take ta faman yi ma abokanan aikin nata ta ciro wayan tayi dialling numban mutum ɗaya kaf a duniya da take tunanin in suka yi magana komin yaya ne zata samu sauƙin abinda take ji yanzun.

  Da kakkausar murya ta mata sallaman da taji saukan sa har cikin kasusuwan jikin ta. Sai da ta lumshe idanu, ba dan komai ba sai dan yanda sautin muryan ke ratsa ta yana ƙara tunatar da ita kewan muryan da mai muryan da tayi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. "Mah na sauƙa lafiya. Har na gabatar da shirin ma yanzu muka fito."

  "Alhamdulilah" shine furucin da Mahifiyar nata ta mata. Uwa daya, tamkar da dubu kenan a rayuwar ta. "Nayi kokarin samun ki tun ɗazu Dinatu, bai shiga ba kuma Ina da lectures nima sai yanzu na fito" ta faɗa mata uzurin da ta tabbata ko bata gaya ma tilon yar nata ba, ba zata taɓa bukata ba.

  "Mah ya jikin naki? Ba abinda kika ƙara ji ko?" Cike da kulawa tayi maganan, tana jin kaman ta koma inda ta fito in, ta tsaya kula da Mahifiyar nata, ya zame Mata manufa har karshen rayuwa. Amma ina, gadon jajircewan nata tayi a wurin ta. Sam, ba ta nuna gazawa akan duk abinda ta sa gaba. Mutum ce kaifi daya. Shiyasa duk waɗanda suka santa, ba sa mamakin jajircewa da dagiya irin na Madina.

  "Ai nace miki na warke Dinah, kema kije gida ki huta kafin ki kama hanyan Kadunan. Za muyi magana anjima." Cikin umurni tayi maganan, ba kuma ta jira amsan ƴar nata ba ta katse wayan. Cikin sanyin jiki, da son bin umurnin mahaifiyar nata Madina ta mike. Tana Jin zuciyan ta kwatakwata ba dadi. Tabbas lokacin da take jin sauƙan muryar mah in yana ratsa jikin ta, ji tayi kaman duk damuwan ta na duniya ya kau. Kaman ba wani abu mai mahimmanci a duniya kaman muryan da take sauraro a lokacin. Amma suna gama maganan, taji kaman an ɗauko dutse a lafta ma zuciyan nata. Ko sau ɗaya ne, ko da na mintuna ne zata so ace hiran su da mahaifiyar nata ya bambanta da na kullum. Shin sai yaushe burin ta zai cika?

  Wurin Abokanan aikin nata ta nufa don su samu daman gaisawa da kyau. Da Zuhra ta fara cin karo a hallway. "Ah Madina kina nan har yanzu? na dauka har kin wuce ai."

  "Na tsaya ne mu gaisa." Fuskan ta ba yabo ba fallasa ta amsa.

  "Toh fa ba dai Qatar in zaki Kara komawa ba a yau."

  "Ina su Mubarak?" Ta bukata ba tare da ta bata amsa ba.

  "Suna office." A tare suka nufi office in da Zuhra ke cigaba da jefo Mata tambayoyi. Wani ta amsa wani ta basar dashi. Tana sane da yanda zuhran ke son mu'ammala da ita. Amma Kash! ta sha ta warke. ƙawaye basa daga cikin hurumin rayuwan ta a yanzu. In an barta zata ce baya suke maida mutum. Barta dai ku tattauna abubuwan da suka shafi aiki, nan tafi karfi.

  "Agogo Sarkin aiki" cikin raha Mubarak yayi maganan bayan sun shigo office in. Sama sama suka gaisa.

  "Kaga ko Aslam ashe bata tafi ba. Ɗaya daga cikin masoyan ki ne Madina, yana ta son haduwa dake." Gabatar mata da baƙon da ke gaban shi yayi. Sai ta fadada fara'an ta suka gaisa.

  "To ni zan wuce, Kaduna na nufa a yau."

  Mubarak ne yayi caraf yace "Kaji ta ba Aslam dama na gaya maka Madina bata hutu"

  Dariya Wanda aka kira da Aslam yayi "Kai ko mutum na son cimma ma buri ai dole ya ajiye hutu"

  "Faɗa mishi dai" ta amsa tana jin Zuhra na fadin "Kuma a yau zaki yi video a Talks with Madeens?"

  Jinjina Mata Kai tayi. "Allah ya samu a danshin ki Madina."

  Da fuska ta amsa su, jin magana ya ishe ta.
  ...

  Kaman yanda yace zai dawo ya ɗauke ta, tana kokarin kiran bolt sai ga call in shi ya shigo. Nauyi nan dai da take ji a duk lokacin da wani abun nashi ya zo mata sai da taji saukan shi. Cike da sabawa da share abubuwan da ke damun zuciyan ta ta dauki ƙiran nashi.

  "Ina haraban ma'aikatan ku" ya faɗa a takaice.

  Tun daga lokacin da ta bayyana, idanuwan shi suke tsaye tar a kanta. Har a jikin ta, sai da taji kallon da yake mata. Amma hakan ba sabon abu bane a wurin ta, shiyasa ta cigaba da tafiya cike da share nauyin da ke ƙara saukan mata a sandiyyan kusanto shi da take.

  Ajiyan zuciya ta saki a hankali bayan ta zauna kan kujeran da ke kusa dashi. Zare bag in da ke hannun ta yayi, ya wulla bayan seat. Idanuwan shi har yanzu akan ta suke. "Kallo fa haramun ne ko a addinin Musulinci."

  Murmushi mai dan ƙara yayi, yana ƙoƙarin tada motan. "To ya zan yi? Tunda kin ƙi kauda duk wata mayafi dake tsakanin mu dake?" Da sauri ta riƙe kanta, lokaci ɗaya taji ya sara mata. Ta alaɗan ta hakan da ma'anar kalaman da Abdulhamid in yayi yanzu."

  "Ya dai gajiya ko?" ɗaga kanta tayi.

  "Ya kamata ki huta sosai gaskiya, ki samu kaman awanni da dama kafin ki daura ma kanki wani gajiyan" Magana ya mata cikin magana, kuma ta fahimta. Bata da ƙarfin da zata iya mishi wani jayayya a yanzu. Bayan iyayen ta, tana ganin shine mutum na ɗaya da yafi sanin ta fiye da kowa. Shiyasa ma ta mishi shirun, domin ba zata taɓa canja abinda tayi niyya ba.

  Hamman da tayi ne ya sata shafa cikin ta. "Yunwa ko?" Kai ta gyade mishi. "Baki ko tsoron yunwa, ina zamu je?"

  Wayan ta tayi saurin fiddo wa ta shiga Instagram "AD Ina labarin da na baka na wata da ta tambayeni shawara a Talk with Madeens zata bude restaurant a cikin Abuja."

  "Wacce kika sa sai da local foods a tsakiyan Abuja ko? And you think it will sell?"

  "Muje kaga wurin. Na gaya Maka ƴan Nigeria ko wani mataki muka kai abincinmu na gargajiya yafi mana. Ita kanta bata yadda ba da farko, amma sai nayi convincing inta ta gwada. Godiya tazo tana min."

  Jinjina kai yayi yana faɗin "Na dai jiki amma nasan duk yanda zata yi ba zai yi dadin wanda muka sani a baya ba."

  Location in da ta tayi locating ta google map ta nuna mai ya ɗauki hanyan wurin. Tana cigaba da bashi labarin encounters inta a Talks with Madeens. Daga yanayin ta kaɗai yana bayyana mishi yanda abun ke ƙayatar da ita. Tana jin daɗin duk wani abu da tasa a gaban ta. Duk da hakan da take yi yana mishi kaman ta neman inda zata buya daga abubuwan dake faruwa a rayuwan tane. An escape it simply its. Tana zama wata mai mahimmanci a rayuwan al'umma ba tare da ita kanta ta ankara ba.

  Tun daga waje wurin ya tafi da Madinan har ma dashi Abdulhamid in. Komai nashi tsari da tafiyan irin na gargajiya ne. Kama daga benci, kwalliya kai hatta plates in da ake serving abincin. Going through the menu, tana ganin dambun tsaki da zogale taji yawun ta ya tsinke. Shi tace a kawo mata da kunun aya. Shi Kuma ya amsa waina da damammen fura da nono. Suna ci suna lura da irin abincin da ake kawo wa mutane. Har kunnu ba wanda basu dashi, kana order za a dama maka a kawo. Hakan yasa manyan Alhazawa ne suka fi cika wurin dam, sai ko samarin da ba a rasa ba.

  Sai da suka gama santin su sannan Madina ta kira mai wurin. "Oyoyo Madeens" Dan runguman Madinan tayi tana zama kusa da ita. Baki kaman gonar auduga tace "Maimakon ku shigo ciki" bayan sun gaisa da Abdulhamid in.

  "So nake naji ya abincin tukunna. Har ya wuce tsammani na"

  "All credit goes to you madina." ƙara fadada murmushin ta tayi. Sallaman da suka ji akan su yasa su maida hankalin su wurin.

  "Sannu da kokari Hajiya Maimuna, ai ni kin taimaki rayuwata Allah. Tun randa na gano wurin nan. Kin ganta can sai kwadayin ake. Da yanzu ina can ina kwaɓa fulawa" Matan da ke gefen su ya nuna. A tare suka saki dariya, ita dai matan hankalin ta kwance cin kalallaɓan ta take da yaji ga kuma zoɓo mai sanyi a gefen ta. Tayi nauyi sosai don har fuskan ta a cike yake.

  "Madina Sa'adu Ali?" Mai cikin ne tayi magana tana kallon su. "Kuyi hakuri fa dazu santin Kalallaɓa nane ya tafi dani banji ban gani." Mijin tane ya fadada murmushin shi "Acici ba, wato baki ma san su waye a gaban ki ba. Har na fara mamakin Madinan da kike ban labarin tana burge ki kin ganta ko a jikin ki."

  "Daɗin abun ma a gidan ka na koyi cin Kuma yaran ka suka sa min." Ta faɗa da barkwanci. "Madina Ina son shirin ki Allah kina daga cikin ƙalilan da suke bada gudumowa ba tare da gurɓata tunanin mutane a shafin sada zumunta ba. Musamman ma ɓangaren ku bloggers."

  Godiya Madinan ta mata. In da sabo ta saba da haduwa da mutane kala kala a duk inda ta shiga. Da masu tunkarar ta da masu daƙa mata hannu.

  "Maman biyu tashi mu tafi ko? In ba za a fasa tafiya Kadunan a yau ba."
  Wuff! Ta mike tana faɗin "Ban Isa ba, mama ba zata barni ba ai." Ganin yanda ta tashi yasa mijin saurin riƙota "Bi a hankali ko." Sallama suka musu riƙe da ita yana binta a hankali suka fita.

  "Ban taɓa ganin mutum mai son matar shi ba kaman wannan mutumin. Kullum sai ya sa na mishi abu specifically nata ko da bamu dashi a menu."

  "Haihuwar fari ne hala?" Madina ta fada.

  "Shekaran su bakwai kenan da aure sai yanzu Allah ya kawo rabon."

  "From his eyes, kasan yanda yake jinta a ranshi." Madinan ta amsa. Ɗan ɗarawa suka yi sannan suma suka mata sallaman.

  .....

  Likes inku da comments suna da matukar amfani a gare ni. Su kawai nake bukata. Sai anyi register za iya yi. Ga musu account kuma signing in kawai zaku yi.

Comments

1 comment