Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 03: Biyu babu

 • "Madinatul Munawwara" Kaman sautin waƙa ya ƙira ta. Ta gane magana mai mahimmanci ya ke son mata. Abinda take gudun shi, saboda rashin sanin yanda zata iya fuskan tan matsalan da yake shirin faɗo mata.

  "Ina son kasancewa da ke Madina, a ko da yaushe Ina jin kina min nisa, Ina tsaron hakan. Hankali na ya gaza kwanciya." Natsuwa, shine abu na farko da taji tana bukata a lokacin. Maganganun da yake yi kuwa gabadaya ba su ta'ammali da kalman ma. A hankali take daddana yatsun hannun ta, kaman mai neman wani nau'i na samun natsuwan ta hakan.

  "Baba da kanshi yace min yana son ganin Daddy. Amma na rasa amsan da zan bashi Ina jin kaman ban miki adalci ba in na bari suka hadu ban sanar miki ba. Shiru ne ya ratsa tsakanin su. Ta san amsan ta yake jira. Amma ba ta san ta ya ake sanar ma mutum dalilin da babu shi ba. Duk da a wurin ta dalili ne mai karfi.

  "Madina, ƙaddarar wani makusancin ka fa bashi ke yanke na ka ƙaddaran ba. Ita kanta Mah in, zata so ta ga ƙaddaran rayuwan auren ki bai zama iri daya da nata ba. Ki duba lamarin nan, ba dan ni ba dan kanki ma." Gabadaya kalaman shi suna bayyana mata yasan tsoro da damuwan ta.

  "Tsoro na dayawa ne. Ka sanni ka san sirri na da ba wanda ya sani. Shin ba za kayi dana sanin zabin ka ba a gaba?" Wani irin numfashi taja bayan ta gama maganan.

  "Ni kinsan nawa boyayyen sirrin?" Cikin dan daga murya yayi maganan. Juyawa tayi tana kallon shi, cike da tabbatar da gaskiyan abinda yake faɗin. Nan take kuwa taji koma menene wannan sirrin, shine abu na karshe da zata so ji a rayuwar ta.

  Basu ƙara wani magana ba har yayi parking a cikin gidan su. Juyawa yayi ya dan kalle ta. "Madina ki bar tafiyan nan gobe. Abu ya taso min a Office, nayi duk iya ƙoƙarina abun ya gagara sannan ke kanki a gajiye kike. Nasan kwata kwata baki runtsa ba ko a jirgi. Citsan labban ta tayi. Karo na farko a rayuwar ta taji haushin nauyin shi da take ji. Da ba zata yi shakkan sanar mishi sai ta tafi ba.

  "Nasan ki Madina please." Kaman mai neman wani babban alfarma yayi maganan.

  "Sa'ada na jira na fa, nice zan tsaya mata Kai ma kasan da hakan."

  Taran numfashin ta yayi da fadan "Zata fahimce ki Madina, zan ƙira ta da kaina." Girgiza kai tayi, alaman bata bukatan hakan. "Ban son in faɗi abu banyi shi ba, tun dazu nake gudun maganan nan da Kai."

  "Komai kamawa yake, bara naje office in in ƙara trying ko zan samu tafiyan. Zan ƙira ki." Ya faɗin hakan ne duk da yana da tabbacin da mugun wuya in tafiyan zai yiwu mishi a yau. Yana so ya cika mata burin ta, ko ta halin yaya ne. Tausayin shi taji ya kamata. Tana jin ina ma zata iya, da ta hakura kaman yanda ya buƙatan. Sai dai tasan kanta, tasan ba zata taɓa iya canja maganan ta ba. Saboda haka ne sai ta zabi faɗa mishi abinda tasan yafi wannan alfarman da yake nema mahimmanci a wurin shi. Ba wai don ya kauda maganan ba kaɗai, ita kanta ta fuskanci bata da wani zaɓi da ya wuce wannan in.

  "Ehmm nace ba..." Hankalin shi bakiɗaya ya mai da akan ta.

  "Kace wa Baba ya zo yaga Daddyn" ita kanta ji tayi kalaman nata sun zo mata a bazata. Bare shi Kuma da ya citsa yatsa yana kallon ta. Ji yake kaman ba gaske ba. "Nagode" ya faɗa, cike da mamakin da ke tattare da farin cikin da ya kasa ɓoyuwa.

  Har ta ƙarasa cikin dakin ta, tunanin kalan so da kulawan da Abdulhamid ya ke mata take. Zata so koyaya ne itan ma ta dinga faranta mishi. "Ina sonki Madina, Ina sonki sosai har zuciya ta na min zafi in na tuna da hakan." Kalaman ƙarshe da ya mata kenan kafin ya tafi.

  "Kar kayi shakka akan tawa soyayyan, nima Ina son ka ban shakkar haka." Ta amsa mai da dukkan gaskiyan ta.

  Kai tsaye side in mahaifin ta, ta nufa. sanin zai yi wuya in ya fita. Tana tura kofan kuwa ya buɗe. Yana ganin ta ya faɗaɗa fara'an shi. "Maraba da mutan Doha"

  Cikin sakalci tayi saurin karasawa inda yake. Side hugging in shi tayi sannan tasa hannun ta a nashi "Daddy na nayi kewan ka."

  "Nima nayi kewan ki Deena. Ya kika baro su? Ya Maryam in da jiki?"

  "Tace wai ta warke har ma ta koma aiki." Yanda tayi maganan kaman bata yadda da warkewan ba.

  Murmushi mai dan sauti yayi "Ina ruwan Maryama Agogo Sarkin aiki." Cike da shauƙi mai hade da ciwo yayi maganan. Yanayin da ko yaushe mahaifin nata ke shiga muddin zai yi maganan Mahaifiyan nata. Yanayin da ako yaushe take jin bakin cikin da ta danne yana taso Mata.

  "Daddy na damu da halin da take ciki. Ba fa ta hutawa ko kadan. Ina tsoron hakan ya zamto mata wani matsalan, ga shekaru na jaaa."

  Girgiza kai yayi "Ba gashi kema ta shafa miki ba."

  "Daddy ni kuma me nayi?" Flask in gaban shi ta jawo tana kokarin ƙara mishi tea in da ya ƙare. Al'adan shi ne shan tea har sai yaji ya gaji a kullum.

  "Zanje dubo ta weekend in nan da izinin Allah. Kema ki dinga kula da kanki, hutun yana da amfani sosai kinji ko?" Da Kai ta amsa tana kallon himilin files da system in dake gaban shi tunda ta shigo yake ta faman danne danne. Yakan ce mata ta gado son aiki gun maman ta amma itan tasan abun biyu ya haɗe mata. Ace a shekarun nan har yanzu mahaifin ta na fama da ayyuka bayan tarin mutanen da ke ƙarƙashin shi.

  Kallon da take mishi kawai ya sa shi gane abinda ke ranta. "Reviewing ayyukan nasu nake. Wani abu da sabo ballantana mu ƴan kasuwa, muna bukatar tabbatar da komai na tafiya yanda ya kamata." Jinjina kai tayi tana faɗin "Daddy munyi magana da AD ne yace wai Babansu na son ganin ka."

  Abu ne da ya dade yana buri. Sosai fuskan shi ya bayyana murnar da ya shiga.

  "To Allah ya nuna mana" Ɗan jim yayi sannan ya ce "Kin tabbatar da zaɓin ki Madina?"

  "Daddy ban shakkan AD, muna da fahimta sosai tsakanin mu." Har ranta take jin gaskiyan kalaman nata. Shi ma mahaifin nata ya karanci hakan a idanun ta.

  "Na barka lafiya Daddy. Zuwa ƙarfe daya zamu tafi Kadunan." Shi ɗin ma miƙewan yayi yana ambaton "Nima kam ina da meeting sha biyu da kwata. Allah ya kiyaye hanya, munyi magana da Abdulhamid in ai. Sai mun shigo daurin auren."

  Time ta duba, ta ga ƙarfe sha biyu saura. Ɗaurin auren jibi ne, amma a ranar za a fara events in bikin. Ta riga ta gama magana da Amaryar akan komin dare ranar da ita za ayi wannan event in.

  Sa'ada ƙawa daya tak a duniya da bata hada ta da kowa ba. Tuni tayi watsi da duk wasu ƙawaye saboda illar da suka wa rayuwar ta. Amma Sa'adan tare suka hau suka sauƙo. Basu da kaman junan su, shiyasa ma take ganin duniya ba wani abu da zai hana ta halattar komai na bikin ya kuma haɗe da halin ta na rashin son canja magana, komin runtsi. Wanka ta shiga da sauri, ta fito ta canja kaya zuwa wani simple jilbab. Gabadaya asheobin bikin, Amaryar ta riga tasa an ɗinkaa mata. Hakan ya sa ba ta dauki wani kaya ba.

  Setting cameras inta tayi ta ƙara hasken falon ta. Cikin kankanin lokaci tayi video in da zata ɗaura a Talks with Madeens. Page mostly tana tattauna abubuwa ne da ya shafi mata bakiɗaya. A yau mata chanza zani ba, matan ta taɓo ta ɓangaren da take tunanin ya shafi rayuwan su sosai. Sauraron video in ta tsaya yi, sannan ta tura ma social media manager inta domin sauran gyararakin da kuma ɗaurawa kaman koyaushe. Email inta ne dai ita kadai ta ke having access to domin kilacewa kowa sirrin shi.

  Sha biyu da ƴan mintuna ta gama duk wani shirye shiryen da zata yi. Bugawan da take jin zuciyan ta nayi bai hana ta jin karfin guiwan tafiyan ba. A haraban gidan ta haɗu da step siblings inta su biyu, mace da namiji.

  "Sister Madeena!" ƙaramar Amal tace tana kallon ta cike da mamaki. "Amalulu an mata." Ta faɗa cike da kunyan ganin da ƙannen nata suka mata.

  "Tafiya za ki ƙara yi?"

  "Eh Amal, Adnan azumin magana ka fara ne?" Ta fada tana kallon ƙanin nata da ya taɓe baki ya juyo yana kallon ta.

  "Haba Sister, mamin mu fa na cikin gidan nan. Amma ace har kizo ki fita ba zaki ki gaishe ta ba? Ni kuma me zan ce miki?" Rolling eyes inta tayi cike da kunya, kalaman nashi na tabbatar mata lallai kannen nata sun yi wayau. Ko dan darajan su lokaci yayi da zata danne wani abun.

  "Silly boy kaga na fita ne?" Ta amsa taɓe bakin ya kara yi kawai ya kada kai yayi cikin gidan. Ji tayi ba ta kyauta ba, ba ta ga laifin shi ba. Uwa uwace. Ajiye jakan tayi taja Amal suka yi side in Mamin nasu. Tana parlor a hakimce, kana ganin ta kaga matar gida. Sai ordering masu aiki take.

  "Ina wuni mami, mun same ku lafiya?" ta faɗa a dake. Dan ɗago kai tayi ta kalle ta "Alhmdlh, ya hanya? Ya mah?" A daƙile ta amsa. Ita ma Madinan ba tare da ta damu ba ta dauki ƙaramin ƙanin nasu Usman, tana mishi wasa. Kaman ko yaushe ji take tana buƙatan yi nisa da duk wani abu da ya danganci Mamin. Baza tace bata sonta ba, ko ta tsane ta. Inuwa daya ne a ko yaushe taƙi jinin su haɗa da matan.

  Daidai lokacin Kuma taji alamun takun mutum. Nan take ta ji ranta na ƙara ɓaci. Ɗaƙo idanuwan ta kuwa ya ƙara dagula lissafin ran nata. Ciwo ne da a kowani lokacin na rayuwan ta tana jin shi amma duk lokacin da idanun ta suka ga sanadin ciwon, sai taji komai na neman ƙara daburce mata. Kaman a lokacin abun ke faruwa. Tsawon lokaci, da canji da dama na rayuwan ɗan'adam a yau da kullum bai gusar mata da wannan taɓon ba sai dai ya koya mata yanda zata rayu tare dashi.

  "Madina kece" Daga idanu tayi ta sauke su kan me mata maganan. Wacce ada take jin in aka cire iyaye ba ta da kamanta. A yanzu kam kaf mutanen duniya zata zabe su akan ta. Murmushin yaƙe kawai ta mata. Sam ba ta iya pretending ba hakan yasa daga murmushin zalla ta gane har yanzu Madinan bata murna da ganin ta. Lokaci bai gusar da hakan ba, bata jin zai gusar dashi har abada.

  "Ya Mah? Kin zo lafiya?" Ta tambaya ba wai don zata iya kore abinda ke tsakanin su ba. Sai dai tana tunanin komin rashin samun wurin maganar nata yafi shirun. Domin shirun bai kawo musu mafita ba. In aka barta ma shirun ne ya kawo musu yanayin da har yanzu suke a ciki.

  "Lafiya" kawai Madinan ta amsa. Daga yanayin zaman ta kadai ya nuna kaman a takure take. Hakan bai hana ta kallon Zainab in ba, sannan ta ɗan kalli Mamin su Amal. Abu ɗaya ta gani a fuskan su. Tarin damuwa zalla da rashin natsuwa. A kullum haka take ganin su tun ranar da suka zaɓi hanyan da suke ganin shine mafita a gare su.

  "Anty Zainab ga Uncle Zaid nan yazo da Nanah." Fadan hakan da Amal tayi kaman ta haɗa da wani nau'in na zuciyan ta. Jin yanda zuciyan ta ke bugawa ne ya sata mikewa ba shiri. Bata shirya ba, ba kuma zata taɓa shiryawa fuskantan shi ba.

  "To Mami ni zan wuce Kaduna biki" ta faɗa a sanyaye.

  "Daddyn naku ya sani ko, ni ban son magana"
  Taɓe baki Madina tayi "mun yi magana" tana faɗan haka tayi waje. Wani irin sauri take jin yanda zuciyan nata ke ƙara dokawa.

  Inaaa, ta riga da tayi latti. Kicibis su kayi a bakin ƙofan. Ji tayi ta kasa wani motsin kirki, ji tayi kanta na wani irin juyawa. Duk yanda ta ke hango yanayin haɗuwan nasu ba hakan ya kasance ba. Jinjina tayi da jikin bango tana jin yanda yake binta da idanu.

  "Madina kece? Kina nan Madina?" Ba ta iya amsa mishi ba. Ita kam da da hali ma zata so ya bata wuri ta wuce Jin yanda zuciyan ta ke wani lugudi. Ta dauka ta gama da wannan fannin, ta dauka ta toshe shi a rayuwar ta kaman yanda take ma duk wani abu da ta bari. Ashe abun yafi karfin tunanin ta. Ashe abun ba irin yanda take hange bane.

  "Madinnaa" ya ƙara ƙira.

  "Kana lafiya?" Tayi ƙarfin halin fizgo zancen. Bai amsa mata ba, ya zaɓi zuba mata idanuwa.

  "Ban san me zance miki bama nikam, abubuwa dayawa a raina."

  Kallon shi tayi tana jin duk yanda zuciyan ta keyi ba za ta barshi ya kaita inda ta sawa ranta ta wuce shi ba. "Nana ko?" Ta faɗa tana kallon babyn hannun shi. A hankali ta sauke idanun ta kan shi. Shi din ma yanayin su Zainab in ta hango kwance a fuskan sa.

  Miƙa mata yarinyar yayi ta amsa. "She's cute." Ita kam kammanin ta duk na Zaid in ne.

  "She is the third ko? Ina sauran?"

  Jinjina mata kai yayi matsayin amsa "Suna school bamu zo dasu ba."

  "To Allah ya raya su." ƙofa ta kalla wanda ya nuna alaman tana buƙatan ta wuce.

  "Ameen nagode." Ya amsa cike da wani ƙulin bakin ciki da ya bayyana a maganan nashi. Bai da wani abun yi da ya wuce ya bata hanya ta wuce. Deenan shi, yarinyar da yake da yaƙinin ba zai ƙara son wata kaman ta ba. Yana ganin ta, ta wuce shi ba ko waiwaye. Cikin sanyi jiki ya ƙarasa cikin gidan.

  Rashin damuwa da hidiman matan gidan yasa ko kallon drivers in da ke ajiye a cikin gidan ba tayi ba. Ta riga ta nemi bolt ko da ta fita ta samu har ya iso. A ranta addu'a take Allah yasa kar Abdulhamid ya ƙira ta. Tasan ba zata iya mai ƙarya ba, ba Kuma zata iya ƙin daga wayan shi ba. Haka ƙuma tafiya Kadunan shine abu na farko da ta riga tasan ba zata iya hakura da ba.

  A wani sashe na zuciyan ta, ba abinda ya tsaya mata sai yanayin da ta fuskan ta a wurin mutanen da ta baro. Kowa ba natsuwa da kwanciyar hankali kaman yanda take gani a fuskan Mah har ma Daddy. Hangen su a tun farko bai hango musu wannan ƙalubalen ba. Rayuwa cikin ƙunci da rashin natsuwa. Kowa bai samu abinda yake so ba, wandada suke tunanin sun samun ma ba kwanciyar hankali a tattare dasu. A ƙarshe dai ba Wanda yaci riba, anyi biyu babu kenan.

  "Madinatul Munawwara" Kaman sautin waƙa ya ƙira ta. Ta gane magana mai mahimmanci ya ke son mata. Abinda take gudun shi, saboda rashin sanin yanda zata iya fuskan tan matsalan da yake shirin faɗo mata.

  Likes da comments inku kawai nace Ina bukata. In baka da account sai kayi register. Mai account Kuma sai yayi signing in za a bashi daman yin likes da comment.

Comments

0 comments