Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 04: Sauri ya haifi nawa

 • Train station in Maitama aka sauke ta. Gabadaya, batun ticket ma bai fado mata ba sai da ta karasa wurin. Ta ga mutane na mika wayan su ana scanning sannan su wuce. Shin ta Ina zata fara ne? Wayan da ta kashe ta kunna. Sunan App in ma a Instagram ta tuna ta ganshi, ba wai zata iya tunawa exact sunan bane. Dole sai da ta shiga google tayi browsing sannan ta samu tayi downloading.

  Tana signing Email a ranta tana jinjina lallai ba laifi kasar na samun cigaba iya gwargwado. Shiyasa a wasu lokuttan ma tana ganin rashin godiyan jama'an kasar da a kullum basu da aiki sai zagi da aibata shuwagabbanin. Ba wai tana ganin basu da laifi bane. Aa tana ganin kaman talakawan kasan sun fi bada babban gudumowa lalata al'amura dayawa fiye ma dasu masu mulkin. Duk inda taron marasa karfi yake a kasar, to tana fa da tabbacin kashi casa'in da tara a cikin su zuciyoyin a mace take da mugunta da rashin tausayi.

  Hankali kwance ta samu wuri ta gama komai, tana ganin yanda hankalin mutane kalilan ke zuwa gare ta. Bakin shade da face mask ta maka a fuskan ta. Ba wai mutane ne bata so ba, yanayin da take ciki ne bata bukatar alaka da kowa. Wurin booking seat in ranar ta shiga da lokacin, kaman wasa ta fara ganin reserved akan seat numbers in ko wani coach in da ta shiga sai ba tayi wani mamakin ba ganin dimbin mutanen da ke shiga cikin station in. Kanta bai gama daurewa ba sai da ta gama shiga duka taga ba wanda ya rage available.

  "Subhannallah!" Ta fada da dan karfi hade da mikewa tsaye. Idanunwan ta Kai gun inda tasan ana saida ticket in, ta ganshi a rufe. Nan take ta fara jin wani irin zufa na tsatsafo mata. Ina zata fara? Me zata yi? Ina mafita? Tambayoyin da take ta faman yiwa zuciyan ta kenan kafin ta fara Kai kawo a wurin.

  "Assalamu Alaikum Hajiya kina bukatan wani abu ne?"

  Bata iya juyawa kallon wanda ya mata sallama ba sai da zuciyan ta ya raya ma ta ba mamaki zai iya taimakon ta.

  "Kina bukatan wani abu ne? Akwai wurin sai da drinks da snacks a can wurin" ya fada yana mata nuni da wani cafe a can gefe. "Akwai toilets in kika shiga ciki" ya kara fada yana jiran sauraron amsan ta.

  "Ticket!" Ta fada da dan karfi. Bai fahimci mai take nufi ba, a fuskan shi ta karanci haka don haka ta kara fadin "Ticket in jirgin da zai tashi nake so na duba a app ina duka anyi reserving."

  "Hajiya ai da tunda kika zo kika yi magana. Baza ki samu a app in ba ai, tun jiya aka yi reserving" Kafin ta samu daman magana ya kara fadin "Amma Ina zuwa" wayan shi ya ciro yayi dialling wani numba.

  "Yah za a samu ticket a wurinka kuwa?" Taji ya fada, can ya sake fadin "Na yanzu fa, za a iya samu?"

  Ba tare da ya kashe wayan ba yace "To wai akwai wanda ya ajiye ma economy class har yanzu basu zo ba in zaki iya siya dubu shidda. Dagowa tayi tana kallon shi, yayin da zuciyan ta ke kara aminta da tabbas rashin Imanin Talaka ya wuce misali. Last da tasan kudin jirgin economy in N1.3k ne. Bayan corona aka ce ya koma 3k. Shine suke saidawa har a 6k. Tukunna ma abinda aka bude app, wanda take ganin cigaba ne aka samu mutum ya siya abin shi yana gida, shine wasu ke siya suna ninka kudi suna saida ma mutane. Kallon mutumin dake gaban ta tayi, sanye da uniform in ma'aikatan wurin, hakan ya kara tabbatar mata da koma menene dai, ha'incin daga wurin su ya ke fitowa.

  "Hajiya gwara kawai in da kudin ki siya ki wuce, jirgi ya riga ya bar Idu yana hanyan isowa nan. Kuma ko jira zaki yi ma, ticket in karfe shiddan ma sai dai ki siya a nan ba za ki same shi ta waya ba duk an siye." Burin ta daya, ta isa Kaduna. Ita ba reporter bace a yanzu shiyasa bata tsaya recording maganan nashi ba. Burin ta, ta isa kafin karfe biyar in Yamma. A hakan ma tana da yakinin kafin ta kai an fara events in tunda na Yamma ne. Duk da tasan zai yi wuya in ba ayi African time ba.

  Handbag inta ta bude, ta zaro dubu shiddan ta mika mishi. A take yayi waya aka turo mishi ticket in ya tura mata. Sai wani washe baki yake yana mata godiya. Kala bata ce mishi ba, sai Allah wadai da take ta yi a zuciyan ta taja akwatin ta ta wuce. Tun kafin ta shiga wurin ma, jirgin ya riga ya iso. Mutanen ciki kuwa already suna waje. Ganin dandazon mutane a wurin ne, kowa na kokarin neman hanyan inda zai tafi seat in shi. Jin maran ta a cike sannan kuma ba ta son cinkoson da take fuskan ta yasa ta nufi bayi da nufin rage marar nata. Har ajiyan zuciya tayi ganin toilets in basu baci ba kaman yanda take tsammanin. Duk da haka sai da ta kwara ruwa kafin ta shiga, tana mai cike da taka tsantsan saboda cutan sanyin da ya zama ruwan dare a jikin mata a wannan zamanin. Ko Ina zata, dauke da Dettol take yawo, cuta ne da ake saurin dauka ta kowani irin karamin hanya. Lokacin da ta fito daga bayin, jirgin na faman horn alamun a lokacin zai tashi.

  "Madam ya baki fita ba? Ai jirgin zai tafi ya barki." Wata ma'aikaciyar wurin ta fada da zafi. Nan take kuwa ta fisgi akwatin tana kokarin sauri. Tana Jin matan na fadin "Ai gudu zaki yi." Sai dai me? Tana fita taga jirgin ya fara tafiya a hankali. Tana ganin yanda mutanen da suka rage a waje ke gudun shiga. Kawai sai ta tsaya cak! Kaman wanda wani abu ya shiga jikin ta, ta zuba musu idanu. Ta san ta riga da ta rasa jirgin tun a lokacin da ya fara tafiya. Wannan gudun da taga ana yi kam ba ta hango tana yin shi ba. Ba wai don tana jin tafi karfi ko nauyin yin shi ba. Kawai dai saboda ita mutum ce wacce kowani wahala tana iya daukan shi in har tasan shi kadai ya rage mata zabi wurin cimma ma burin ta. Wannan kuwa bata ganin shi kadai ne zabin nata, musamman sanin gudun ka iya haifar mata da wani matsala da bata shirya fuskanta ba.

  Tana Jin yanda ma'aikatan wurin ke fadin "Hajiya sai dai Kuma ki jira na karfe shidda" wasu na tsegumin "kaga yar hutu bata iya gudu" masu dan hankalin na bata zabin ta nemi mota ya kai ta station in gaba ta hau a can. Ba wanda ta tanka a wurin, kanta ta fara jin yana juya ma ta. Saukin ta daya, Kaduna tasa wa ran zuwa a ranar ba hawa jirgin ba. Saboda haka zuwa Kadunan zata fuskan ta. Wayan ta, ta fiddo ta maida flight mode. Bata kalli kowa ba, ba ta tankawa kowa ba har ta fita daga wurin arrival in. Mutumin da ta siya ticket in a wurin shine yayi saurin karasawa wurin ta yana fadin "Ya dai naga jirgi ya wuce kina nan?"

  Kallon shi ta dan yi sai ta kauda kanta. "Gashi Kuma ba zai yiwu in maida miki kudin jirgin ba tunda an riga anyi scanning. Amma za iya miki replacing da na karfe shidda."

  "Ka barshi kawai."

  Wurin masu taxi in da ta hango a tsa tsaye ta nufa. Suna ganin ta suka fara kokarin kiran ta zuwa wurin su. Da zata iya da ta tambaye su shin meya sa basa layi, in wannan ya dauka wani ya bi bayan shi. Sai take ganin kaman zai fi. Amma wannan survival of the fittest ne. "Tashan da zan samu motan kaduna." Ta fada tare da sakin akwatin nata, duk wanda ya dauko ko tsakanin su shi zata bi. Matsalan su ne ba nata ba, abinda ke gaban ta wannan baya da gurbi.

  Mabuchi mai taxi in ya sauke ta. Nan in ma dai tana sauka aka fara Kiran "Madam na KD you dey go?"
  "Hajiya Kaduna ne?"

  Sai dai abun da ya burge ta a wurin sabanin can, lodi ake yi sai mota daya ya cika sannan wani ya matso layi. "Kaduna zani" ta ambata tana kallon motocin, duk kananan motoci ne. Wanda ke gaban ta mutum ukku ne a baya sai daya a gaba. A tunanin ta motan ya cika "Ina motan da zan shigan?" Ta bukata tana kara kallon motocin.

  "Hajiya ai mutum hudu ake sawa a baya" taji an amsa. Kara mai da idanuwan ta bayan motan tayi. A yanda taga passengers in wurin sun zauna, bata ga gurbin da za ta iya dosanawa ba ma balle kuma batun tafiya har Kaduna a ciki. "Ko da mun dau mutum ukku kudin mutum hudun suke biya." Mutumin ya Kara fada. Ganin alamun tsarin bai ma ta bane yasa wani inyamuri yace "Or you wait for the next car to load.

  "Sai ma su biya kudin mutum huddun in wanda suka zo in sun yarda." Wani bahaushe ya kara sa mata.

  "Am in hurry" ta fada tana kara kallon time in da wayan ta ke nunawa. Kusan uku saura kenan, ita da za tayi attending event in karfe huddu.

  "Hajiya just pick drop" taji wani ya fada a bayan ta. Ji tayi kaman ta mari kanta, meyesa tun dazu idea in hakan bai fado mata ba? "Za a kaini har inda zan sauka?"

  "You just have to add some money ma"

  "No problem" ta amsa. Ai nan da nan driver in ya dauko motan ya saka ma ta akwatin. Sai da suka fara tafiya tukunna ta lura ba da drivern da suka yi magana suka tafi ba. Wannan kam bahaushe ne sabanin inyamurin da ta gani. Sai ta tsinci kanta da yin hamdallah a zuci. Ance wai naka naka ne, Kuma ba wanda zai kai shi jin zafin ka. Ta kuma san koma menene zai faru akan hanyan, zai tsaya mata kuma zai taimaka.

  MacBook in da ke hannun ta tayi connecting da WiFi. Ba komai bane a ranta illa son ganin me ake ciki da bikin. Instagram account in da aka bude musamman don bikin ta shiga. Hotuna da videos lallen kawayen amaryan ta fara cin karo dasu. Suna ambaton "Wahala for who no dey KD by now." Sai taji kaman da ita suke. Kallo ta bi kowaccen su da shi, in akwai wanda bata sani sosai a cikin su ba to yan uwan Amaryan ne wanda ba wani kawancen kirki ke tsakanin su ba. A lokacin kuma ta gasgata zancen Sa'adan da kyau da tace mata tana bukatan ta a kusa. Duk cikin tarkacen da ta gani a wurin ba wanda ta ga alamun zai iya maida hankali yayi ma Amaryan wani abun arziki.

  Tunanin hakan ne yasa tayi saurin kiran Sa'adan ta WhatsApp call. Daga muryan ta Kawai da taji yanda ta amsa mata sallaman ta gane bacin ran da ke tattare da ita. "Madina ba a kawo snacks in ba har yanzu, har an gama decorations."

  "Bara na kira su, can gidan sister Fatin za a kai ba?"

  "Eh nan ne, Kun kusa ko?"

  "Karki ki damu, na riga da na taso. Zan iso ko da anfara event inne. Makeup artist infa ta iso."

  "Tun dazu tace tana hanya, itan ma shiru."

  "Bara na kira ta itama, akwai wani abu kuma?"

  Shiru Sa'adan ta danyi can tace "Gabadaya na rikice, abubuwa sun min yawa. I don't think I will get married again bayan wannan."

  Dariya Madinan tayi "Allah ma ya rufa mana asiri kawata. First and last." Daga haka suka yi sallama. Amma a kasan zuciyan Madinan tana jin guilt na shigan ta. Tun da aka sa ranar Sa'adan ke ce mata dan Allah tazo sati daya kafin bikin. Duk da, da ita aka yi shirin komai amma sai take jin sam ba ta kyauta ba da bata tare da ita a yanzu ba.

  Tunda ta shiga motan yake lura da dukkan motsin ta. Yanda ta mikar da kafan ta kan seat in tana danne danne da waya da system in da ya hango a hannun ta. Yana sauraron duk wani tattaunawa da suka yi da wacce ta kira. A hankali ya kara satan kallon ta, sai yake ganin kaman akwai inda ya san fuskar. A yanzun ba wannan bane matsalan shi sai yayi tunanin bara ya dan jata da surutu ko zai kara fahimtan wani abu a tattare da ita.

  "Hajiya ai zama mu isa Kadunan kafin lokacin da kika bukata, tunda hanyan ba laifi kuma bama wasu mutane dayawa. Yawanci yanzu jirgin kasa ake bi saboda tsoron garkuwa da mutanen da ake."

  "Wai da gaske a hanyan nan ake tafiya da mutanen?" Cikin firgita tayi maganan. Sam! Ita ta shafa'a, tunanin ta bai kawo nan ba lokacin da zuciyan ta ta bukaci hawa motan.

  "Hala kin dade baki bi ta hanyan ba?"

  Ba tare da wani tunani ba tace "Nafi 10 years ma. Ta flight nake zuwa mostly" wani irin siririn murmushi ne ya bayyana a fuskan shi. Nan ya fara zayyana mata labaran abubuwan da ke faruwa akan hanyan. A matsayin ta na yar jarida, tasan labarai kala kala akan garkuwa da mutanen da ake. Daga bakin da take jin shi a yau ya kasance daban. Sai ta maida dukkan hankalin ta wajen sauraron shi. Domin labarin na fita ne daga bakin wanda abun ya taba faruwa dashi, yasan abun, yasan yanda komai ke wakana. Tiryan tiryan ya dinga bata labarin.

  "To wai su mutanen nan basu da imani ne?" Bai bata amsa sakamakon typing da taga ya dan yi awayan shi. Can ya dago yace mata "Hajiya imani fa kika ce? Kinga a rayuwar nan ka guji duk wanda bai tsoron rasa ranshi."

  "Bangane ba, meyasa basa tsoron hakan? Me suka gani a rayuwan su da har suka dauki mutuwa ba a bakin komai ba."

  Murmushi yayi yace "Wahalar rayuwa da masifun ta. Ai duk Wanda ya taso Talaka a kasarnan to fa ba shakka ya shiga uku." Girgiza kanta tayi tace "Ya danganta ga yanda mutum ya dauki kanshi. Yanzu kai ba gaka ba, ba aikin dreba kake ka samu naka ba. Nawa ke aiki kala kala duk dan su samu daman rufa ma kansu asiri? Shin su din tawwakali suka fi masu garkuwa da mutanen da baza su rungume kaddara ba?"

  "Hajiya rashin zabi ne yake sa dayawa daga cikin su fadawa harkan. Kaine yau sai ka sha wahala kake samun abun sawa a bakin salati, aka ce maka ga hanya mai sauki. Kowa kinga da irin lissafin shi"

  Girgiza kai kawai tayi, tana jin lamarin na kona mota zuciya. Tana jin wani bakin ciki da Allah wadai da mugayen talakawa. "Amma kai yanzu baka tsoro?"

  Wani irin dariya ya kwashe dashi. "Haba Hajiya ni Kuma menene ban gani ba a hanyar nan? Ai neman halas da wuya."

  labarin irin wahalan rayuwan da ya taso a ciki ya fara bata "Mai arziki ba zai taba fahimta ba Hajiya. Kin ganni nan Almajiri ne, tun bansan komai ba aka kawo ni garin Kaduna da sunan karatun da na bige a bara."

  ...

  Likes and comments in dai, su kawai bake bukata. Mara account sai yayi joining, Mai account Kuma zai yi signing in ne kawai sannan a samu daman likes da comment in.

Comments

0 comments