Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 05: Mugun Mutum

 • Labarin da suke bai hana gaban ta dukkan uku uku ba. Wasu labaran nashi kaman wani almara haka take jin su. Duk da haka hankalin ta yafi karkata ga isa garin Kadunan lafiya. Duk bayan yan mintuna sai ta duba lokaci, yanzu haka bai fi mintuna talatin ya rage a fara event in ba. Ita har yanzu gata a hanya, balle a fara batun shiryawa.

  Tana cikin wannan tunanin ne taji motan ya fara wani kara, can sai ya dau jacking kafin ya zo ya tsaya baki daya. Kaman da wasa dreban sai kokarin ta da motan yake abu sam ya faskara. Tilas ya fita daga motan ya na duba meke faruwa. Hakuri ya dinga bata, ita kam takaici, tsoro da bakin ciki duk sun tarun mata. Ko maganan ma kasa yi tayi. "Nasan uzurin ki Hajiya, yanzu za ki bar nan Kar ki damu." Ya fada yana kokarin kiran waya.

  Ga wurin daji ne ba ka ganin wullawan ko da tsuntsu. "To daman kasan motan naka ba lafiya kaje dauko passenger?" Sai a lokacin ta iya magana jin ya kira wani yana sanar dashi inda suke. Wanda take zaton bakaniken ne.

  "Kiyi hakuri Hajiya, kinsan karfen nasara ba tabbas" Siririn tsaki taja. Daganan Kuma tilas ta zuba ma sarautar Allah Ido. Idanuwan ta duk sun fifito, ga wani zufa na keto mata. A rude take, sai fatan Allah ya basu daman barin wurin nan lafiya.

  "Ki kara hakuri, kokarin tada motan nake. Wanda nake jiran ma ya kusa isowa" ganin yanda ranta ya baci yasa shi fadin hakan "Hajiya shi rayuwa ai dan uzuri ne, nima bazan so muyi ta tsayuwa a nan ba da yamma nan." Abu daya ya hana ta gasa mishi magana, saboda tasan tana bude baki kuka zata saki, wani kululun bakin ciki ne ya mata tsaye a nan. Tilas ta fiddo wayan ta, tasa a flight mode, ta fara buga game. Sai dai, shi kanshi ji tayi bata da natsuwa da kwanciyar hankalin yin shi, hakanan ta dinga shige shige a wayan, abunda ya tsaya mata rai sai kara taso mata yake. Hakanan ta kashe wayan don kaman ma kara mata zafi yake. Abu kaman almara, yamma ya rufe garin.

  Dai dai lokacin taga wani haske ya keto su, sai da ta kura idanu sosai ta gane ashe mota ne ke kara so wa inda suke. "Yauwa gashi nan ma ya iso" dreban yayi maganan yana karasawa wurin motan. Tana dan hango su, magana ya mishi sai gashi sun dawo a tare. Tana ganin suna ta dube duben su, can mutumin yace "Wannan motan fa sai taga makanike, matsalan da dan girma"

  Ba ta sanda ta saki salati ba tana mai sa hannu a kai. Sai lokacin hankali wanda ya ke taimaka musun yayi kanta. "Lafiya?" Ya ambata yana kallon ta.

  Drivern ne ya mishi bayanin abinda ke auku wa. "Nace Dan Allah tunda kadunan zaka ka wuce da ita, ni in koma nan kauyen da na baro in nemo makanike?"

  "Ba matsala" yace yana nufan motan shi.

  Tana jin drivern na mata bayani tayi banza dashi, fita kawai tayi a mota yayin da ya biyo ta da akwatin ta zuwa dayan motan. "Kiyi hakuri kinji?" Kallon arziki bai samu ba.

  Baya ta bude ta shiga, mutumin bai ce mata kala ba yaja motan suka wuce. Sanyin Ac in da ya fara ratsa tane ya sa ta fara tunanin ba motan haya bane wannan in. Sun dan taba tafiya ta duba time, har hudu ta gota. Ganin lokacin event in har yayi ya sa ta ce mishi "Dan Allah ko zaka dan kara gudu, ina da uzurin da zan yi" ba tare da ya juyo ya kalle ta ba yace mata "nawa kika biya ni?"

  Da sauri ta dago tana kallon shi, idanuwan ta a bude. "Ai na biya abokin ka"

  "Kinga ya bani kudi?" Ba ta amsa ba sai tsakin da ta kara ja, wanda ya zame mata jiki. "Zan iya biyan ka, ka fadi nawa kake so ka kaini inda zani straight kawai in mun shiga gari" Ita tsakanin ta da Allah tayi maganan ba tare da wani shayi ko dar ba.

  "Anya kina da kudin da zaki iya biyana kuwa?"

  "Ko nawa kake so zan baka Malam. In dai zaka kaini inda nake bukata akan lokaci. Ba ka da matsala."

  "Toh shikenan" kaman da wasa kawai taga ya danna lock in motan baki daya, sai gani tayi kawai ya ja motan da gudu sosai. Wani irin relief taji ya ziyarce ta, dama ya iya irin gudun nan tun dazu ya tsaya yana bata mata lokaci? Basu fi mintuna goma suna tafiya akan titi ba, kawai taga ya gangara daji. A firgice, ta dago idanuwan ta, tana fadin "Malam lafiya? Ina ne nan?"

  Dan shiru yayi for some seconds, can yace "Ina kedai kaduna zaki? Kar ki samu matsala, nan hanyan shortcut zamu bi"

  Duk da gaban ta bai daina bugawa, sai ta danji sanyi. Wato yaji kudi shine yake son burge ta ko? Tunani ta fara yi a ranta anya shi din ba driver bane? Koma dai menene neman na kai yafi zaman banza. Ta cigaba da ayyanawa a ranta.

  Sai dai me? Lulukawa kawai suke suna ta faman shiga ramuka. Gashi jan motan yake tsakanin shi da Allah. In suka shiga wani ramin har buguwa take a kanta, ko kuma ta bugu jikin kofan.

  Cikin firgita ta zaro idanun ta "Malam lafiya kuwa? Rai ai a sannu ake bin shi"

  "Ina kaduna zaki biya ni in kaiki? To baki da damuwa" za tayi magana taji sun shiga wani rami, kanta ya bugu sosai. Wani irin karan azaba ta saki "wai kabi a hankali mana"

  wannan karon kam bai tanka ta ba, tun tana magana a hankali har ta fara ihu. Bakidaya cikin ta ya duri ruwa Kuma jikin ta ya gama bata cewa ba lafiya ba. Ko dai da mai tabin hankali take tafiya ko kuwa mugu. "Wai kashe ni kake son yi ne?" Ihu take sosai, amma ci kanki yaki yace mata. Sai ma kara speed kawai da yake ta faman yi. Hakan ya sata birkicewa a lokaci daya, masifan da bata san ta iya shi ba taji yana rike mata wuya.

  "Wai wannan wani irin stupidity ne? Idiot kawai!" Ta fada da wani irin kara da sai da yasa shi juyowa. Ta cigaba da fadin "Daman ku talakawan nan ba tarbiyya kuke dashi ba. Zuciya fal mugunta da hassada" Wani irin kallon ya sakan mata da ya sa ta yin shiru. Ba alaman wasa ko sauki a idanun shi. Kaman a mafarki, kawai sai gani tayi ya zaro wani irin bindiga a aljihun shi. Gum! Ta zama nan take, ko motsi ya gagare ta. Cigaba da tafiya yayi, kawai sai ji yayi ta saki wani irin kuka, tana magana dai daya "Dan Allah kayi hakuri ka maida ni in da ka dauko ni, wlh ko nawa kake bukata zan baka. Dan Allah kar ka cutar dani"

  A zuciye ya juyo ya saita bindigan kan ta, idanuwan shi har wani ja suke yana huci da sauri tayi kasa. Sai jin dum! Na kara bindinga tayi saman kanta. Gabadaya ta gama sadakarwa ita ya harba taji ya mata wani tsawa "Dago kanki!" Har sai da motan ta amsa. Da sauri tayi yanda yace. Sai lokacin taga bayan ta, glass in motan yayi watsa watsa. "Kinga yanda nayi da glass in nan, kika kara min magana haka zan yi da kanki"

  Ai da sauri tasa ma bakin ta sakata, jikin ta duk ya dau rawa. Kukan ma kasa shi tayi, duk ta gama firgita har wani zawo take jin na shirin zubo mata. Shikenan! Ta faru ta Kare! Ita kuma nata ya kare. Daman ashe abinda ya dawo da ita Nigeria kenan ba shirin ta ko bikin Sa'ada ba. Allah sarki, mah ya zata yi in ta rasa ta. Ita kadai ta haifa. Abubuwan da suka dinga mata yawo kenan. Sai lokacin taji data sani, da ta bi maganan AD. Amma daman ance in kwana ya kare ba makawa sai an tafi, ita kuwa hanyan ajalin ta kenan.

  Ba ta kara sanin ina kanta yake ba, ba wai don ya mata wani abu ba sai dan duniyan tsoro da ta shiga. Ba ta san iya adadin tafiyan da suka yi ba, taji motan ya tsaya. Da sauri ya fita daga motan yana fadin "Fito!" Cikin karkarwa ta fara kokarin bude motan sai dai tsoro ya hana ta maida hankalin da har zata iya budewan. Ganin bata bude ba, a zuciye ya balle murfin motan, ya wani jawo ta har sai da tayi kasa. Bin ta kasa yayi, ya dago kanta sai ji tayi kawai an kifa mata wani irin muguwar mari. Zabagen gigicewan marin, ji tayi komai na ta ya wani irin daukewa na dan lokaci kafin ta zube kwance a kasa. Kaman wanda ya katse ma hanji, a razane sai kuma ta saki wani irin gigiceciyar kara tana fadin "Wayyo Allah na" ji take kaman ya cire mata fuska, saboda wani irin saukan abun da taji kaman guduma. Ga duhun da ya mamaye a idanuwan ta, anya bai nakasa mata idanuwa ba. Wani irin karkarwa jikin ya dauka, ta ma rasa me zata yi, ta kwanta ne kota mike. Duk ta haukace, ta ma rasa ta ina zafin yake. Hannun ta, ta kai kan daya bangaren fuskan, nan inma yanda kasan an mare shi. Sai wani irin azababben kuka take, mai cike da tsantsan azaba da rauni.

  Sautin kukan tane ya fiddo da mutanen da ke wurin daga bukkokin da su ke. Maza ne kusan biyar kowa daga inda ya fito. Tsayawa su kayi suna kallan shi, sai can daya daga ciki yace " Oga daga ina haka? Ka fasa tafiyan ne?"

  Girgiza kai kawai yayi, bai amsa shi ba. Sai wani kuma yace "ba kaga ya samo kaya bane." Kasa kasa yayi maganan yana kallon gefe.

  Zuwa lokacin da kanta tayi shiru, sai wani ajiyan zuciya take saki kaman mai neman shidewa.

  "Nass" wanda ya kawo ta ya kira daya daga cikin wadanda suke wurin. Da saurin ya amsa da fadin "Oga Abbah"

  "A min iso wurin Zaki." Da kakkausar murya yayi magana. Hannuwan shi a nade, fuskan nan ba ko alamun dariya ya zuba mata idanu. Alamun kirae yake tayi wani abu ya dau hukunci.

  "Angama ranka shi dade." Nass in ya amsa. Daya daga cikin ginin kasan gun ya shiga. Bai Jima ya fito yana kallon wanda ya kira da ogan nasa.

  "Yace kana iya shiga." Har da sunkuyar da kai yayi yayin maganan.

  Bai wani jima a ciki ba ya fito. Ranshi a hade, ko kallon Inda Madinan take bai yi ba ya yafito Nass da hannu. Gajeran magana ya mishi.

  Motan ya bude ba tare da ya bi ta kanta ba ya jawo wayan ta, da tarkacen ta. Da ido ya ma wanda ke kusa da Nass magana yazo ya amsa, tare da akwatin ta. "Ku adana min su, ban so a samu matsala"
  Cike da ladabi suka amsa mai. A lokacin ya dauko wani motan ya bar dajin a sittin.

  Tsawa da aka mata a kai ya sa ta tashi cikin firgici tana neman wurin buya. Su biyu suka sata a gaba zuwa inda wanda taji an kira da Abban ya bada umurnin a kai ta. Tana shiga, suka sa kwado suka kulle tana ji, dan ba wai bukkan kara bane. Ba haske ko kadan a daki, ba ta yanda za ta iya gane akwai window ko babu. Yayi wani irin duhu, ta yanda ta ke jin da ta bude idanu ta kulle su duk abu daya ne. Kukan ma dai yanzu kam kin zuwa yayi, da lalube ta samu inda ta zauna. kasa ne kawai a wurin, can jikin bango ta samu ta shige. Tana jin wani irin zafi na taso wa daga cikin jikin ta. Duk ta gama hada zufa, wurin ko kadan ba iska. Anya za ta iya kai gobe a wurin nan kuwa da ranta? Ba abinda ba ta saka ma ranta ba, zuciya fal tsoro. Abun ma sai take ganin shi kaman wani irin mummuna mafarki, sai mintsilan kanta take ta tashi, amma shiru kake ji. Ko da wasa bata taba hango rayuwa zai kawo ta irin wannan wuri ba, wurin da take tsakankanin mutuwa da rayuwa. Shin yan yankan kaine? Ko kuwa masu garkuwa da mutane? Amsan bashi bane abu mai mahimmanci a wurin ta a yanzu. Ga wasu addababbun saura da suka taso ta gaba, idanuwan ta ma tsabagen suna cikin bala'i ko alaman baccin ba ji suke ba. Tana nan zaune ta takure kanta tana karkarwar da ta rasa na menene, gabadaya jikin ta ya mutu daman ga uban gajiyan ramukan da suka dinga afkawa. Wani irin nishin wahala take, kafin kace kwabo wani irin mugun zazzabin da bata tuna ta taba yin shi ba yayi awon gaba da ita.

  Tana cikin wannan halin ne taji ana taba kofan. Maimakon hakan ya bata wani hope sai ma tsoro da ya birkita ta. Hasken farin wata da ya ratso bayan an bude kofan ne ya bata daman ganin mutanen dazu da suka kawo ta wurin da wasu mata uku a tare dasu. Cikin karkarwa suka shiga cikin dakin sannan suka ka kara rufe kofan.

  Ana buga kofan, daya daga cikin su ta fashe da kuka.

  "Kul!" Suka ji tashin muryan wata daga can wani lungu a dakin. Ita kanta Madinan bata lura da ita ba sai hakan ya tsorata ta.

  "Kiyi shiru ki rufa mana asiri, mutanen nan ba abinda ba zasu iya ba. Ku yita addu'a dukkanku Kun ji?"

  "Baiwar Allah kema kamo ki sukayi?" Madina ce tayi maganan cikin rawar murya da kaduwa. Jin ciwon dake fitowa a kowani kalma na matan.

  "Sati na Uku kenan a nan wurin." Ta amsa

  "Dan Allah me da me suka miki?" Wata daban ce tayi maganan, cikin toshashen murya mai cike da rauni.

  "Ba abinda basu min ba." Ta basu amsa. Daga nan taja bakin ta tayi gum. Sun inma ba wanda ya iya kara wani magana. Sai sautin ajiyan numfashi da bugun zuciya kawai.

  Daren ranar dai a haka ya wuce musu, ba wanda ya iya bacci saboda tsoro ga Kuma wani irin sanyi dake shigan su duk sai karkada jiki kawai suke.
  ...

  Ina nan dai Ina tsumayan likes da comments inku, in kunyi signing in.

Comments

0 comments