Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 07: Matsanancin hali

 •  Duk da sanarwan da matan layin MTN take ta mishi na layin da ya ke kira a kashe ne bai hana shi cigaba da danna numban ba. A duk dakika daya, buguwan zuciyan shi ke karuwa sau dari. Tafiya kawai yake a cikin mota yana tunanin abinda ke shirin bullowa a rayuwan shi. Ganin har Isha'i na shirin yi bai gabatar da ko da sallan Magriba yasa shi tattaro natsuwan dole, sai dai ko na minti Kadan bai zauna mishi ba. Tilas ya kama kiran sunan Allah a ranshi sannan ya iya tsayawa a masallaci ya gabatar da sallolin yana mai rokon Ubangijin shi ya kawo mishi dauki. 

  Yana fitowa ya kara danna numban Mukhtar, tun dazu daman suke waya.

  "Ban san meke faruwa ba Abdul, amma tun dazu muke train station in. Gashi har jirgin da ya taso shidda ma ya iso amma ba alamun ta."

  Silalewa yaji yana yi a wurin, yayin da kanshi ke juyawa, yawun bakin shi ya kafe. Kokarin dago harshe yake domin ya fidda abinda ke ranshi amma ya gagara haka. Sai ma wani nauyi da yake jin na yayime harshen da idanuwan shi.

  "Mun tambayi mutanen wurin, mun nuna musu hotunan ta amma ba wanda ya ganta. Sa'ada ta tabbatar min sun yi magana tana kan hanyan tun karfe biyun."

  "Na shiga uku Mukhtar ina Madina ta shiga?" Da wani irin karfi ya fisgo maganan. Tambayan da shi kanshi bai da amsa ballantana Mukhtar in.

  "Ka natsu Abdul, mu bi abinnan yanda ya kamata. Kamata yayi mu fara bincikowa ko ta shiga train in ko kuma by road ta biyo."

  "Hakane bara naje station in." Ya amsa cikin wani irin sanyi.

   Abinda ya kara daburtar dashi a lokacin, kiran da yaga yana shigowa cikin wayan shine. Nan take ya fara jin wani gumi na tsatsafo mishi, idanuwan shi suka kara kadawa, duhu na mamaye ganin shi. Tilas, yayi parking akan hanya yana jin yanda sautin bugun zuciyan shi ke ninkuwa ba adadi a duk lokacin da wayan shi ke kara ruri. Wani zuciyan ne ya fara mishi wasiwasin kilan kyakyawan labari zai ji akan Madinan, kila ba abinda ya same ta. Da sauri ya daga wayan, bai ma iya tsayawa sallama ba sanadin tambayan da yaji Daddyn nayi mishi. Tambaya ce da ya guji jin ta tun lokacin da kiran ya fara shigo mishi.

  "Abdul kun isa ne?" Nan take yaji zuciyan shi ta yanke. Wani irin sanyi ke kara shigan shi. 

  "Daddy ina Abuja." Cikin rashin sanin abin cewa ya furta zancen. Bai san ta Ina zai fara ba, ta ina zai sanar ma wannan mahaifin batan yar shi. Yar da kowa ya san bai hada ta da kowa. 

  "Ban gane ba Abdul, to ina ita Madinan? Meyesa numban ta bai shiga?" Cikin daga murya da kidima yayi maganan duka a take.

  "Daddy bansan zata tafi ba, nima neman ta nake." Bakin shi kawai ke furta abinda yazo kanshi ba tare da ya tantance su ba. Abu daya ne a rubuce, Daddy ba zai taba fahimtan shi ba, yanzu ko da anjima duk abu daya ne, ba zai saurare shi ba.

  "Baka da hankali ko?" Shine abinda ya furta na karshen sannan ya kashe wayan.

  Tukin kawai ya cigaba dayi yana kokarin ganin ya isa train station in. Tsabagen rudewa sam ya manta gidan su Madina yafi kusa da station in kubwa akan Idu. Tara saura, jirgin da zai iso daga Kaduna tuni ya sauka hakan ya sa ba wadatuwan mutane dayawa a wurin. Wani irin tafiya yake mai hade da tuntube yana jin kaman iskan wurin na kokarin tafiya dashi. A haka ya samu ya karasa wurin mutanen da ya hango. A daddafe ya musu bayani suka hada shi da ogan su. Ma'aikatan wurin ba wanda ya ganta saboda haka ogan ya bukaci ya basu zuwa gobe zasu yi bincike hadda Maitama station in, ko me ake ciki zasu neme shi. Ba dan yaso ba ya bar wurin sai dan ya tabbatar da su dinma basu da wani abun yin. Ga yawancin ma'aikatan duk sun riga sun tafi, dole dai sai goben

  Bangaren Daddy kuwa yana kashe wayan cikin gidan ya nufa. Mami, Ammar, Amal da Zainab duk suna zaune. Tun daga bayyanan shi Mamin tasan ba lafiya "Lafiya kuwa?" Ta ambata duk da ta riga da ta gama sanin sam babu lafiyan

  "Madina ta muku sallama?

  "Eh, tace min zata tafi Kaduna kun riga da kunyi magana.

  "Wani dreba ya kai ta." Dan jim tayi sannan tace "Ban tunanin da driver ta tafi gaskiya, wani abu ya faru ne?

  "Me?" Ya fada a tsawace. "Taya zata fita ita kadai kuma baki damu kiga ya ta bar gidan ba? Kinsan me kike fadi kuwa?"

  Shirun tayi ba wai don tana son hakan ba sai dan bata da wani zabi da ya wuce shirun duk da tarin maganganu da yake cike a wuyan ta. To me zata ce? In dai akan Madina ne ba abinda bata ji ba ko gani ba. Tun abun na mata zafi har ta iya jure duk wani nau'in ciwo akan haka.

  "Useless human being!" Ya fada iyakacin karfin sa, kafin ya fita daga sashen nata bakidaya. Kallon yaran ta tayi sabanin da da yanayi irin wannan ke tsorata yaran su dinga kuka. Yanzu kam wani abu ta gani a idanun Adnan, abinda ta dade tana tsoron ganin daga yaran kenan. Kallo ne na zallan takaici da bakin ciki. Kallo ne da bata burin ya shiga tsakanin Uba da dan shi.

  "Mami meyesa Daddy ke fada? Meya samu sister?" Amal ce tayi maganan cikin sanyin jiki.

  "Bakomai Amal kuje ku kwanta, akwai school gobe ko." Ta karasa maganan tana jin wani tululun bakin ciki ya mata tsaye a zuci.

   Daddy kam yana fita gun securities in gidan da drivers ya nufa. Suma haka ya rufe idanu ya balbale su. "Alhaji Ina ga fa bolt ta kira" daya daga cikin securities in ya fada cike da tsoro.

  "Kuna gani yata zata fita ta hau bolt?" Ya fada kaman suna da wani ikon da zasu iya hana Madinan abu, kaman za ta iya tankwaruwan musu. Tsakanin su da ita gaisuwa ne, amma ba wanda ta ke shiga harkan shi cikin su. Ba wanda zai ce ga wani magana na minti daya ya shiga tsakanin su to ta ya suke da ikon sa kai a cikin hurumin rayuwan ta. Ganin dai fadan nashi ba zai samar da wani mafita ba yasa shi daukan driver suka fita.

  Abdulhamid kuwa ba zai ce ga wuri kaza da yake a cikin garin Abuja ba, tafiya kawai yake ba tare da sanin ina yake jefa motan nashi ba. Yana cikin wannan yanayin ne kira ya shigo wayan shi. Ba tare da ya duba waye ba ya daga, abu daya kawai yake burin ji, inda Madina take, ko ina ji yake in aka fada mishi a shirye yake da yaje. Bai iya sallama ba, bai iya amsa sallama da aka mai ba.

  "Kana ina ne Abdul?" Sanyayan muryan mahaifin shi ya sauka kan kunnuwan shi. Duk da natsuwa da yake ji a cikin murya yana iya jiyo karfin hali da ta tafi tare da natsuwan.

  "Kan hanya Abbah"

  "Ka same ni a gida yanzu" yana fadin haka ya katse kiran. 

  Rashin sanin takamaimen inda yake ne yasa sai da ya alakanta da goggle map sannan ya iya jan kanshi gida. Ya riga yasan dole neman nashi ya na da alaka da bacewan Madina, shiyasa bai yi ko dar ba lokacin da yaga Daddy zaune a falon Abban su. Ya kuma san sanin waye mahaifin shi ya kawo Daddy har cikin gidan su. Yau da wani ne ya haife shi wanda bai kai Abba ba, yana da tabbacin kwanan gidan kaso zai yi, ko sauraran shi Daddyn ba zai tsaya yi ba.

  "Abdul Ina Madina?" Abbah ya bukata. Kaman karamin yaro na maida zance, tiryan tiryan ya fada musu duk wani abu da ya afku.

  "Kai kace tare zaku tafi Abdul, sanin kanka ne ba zan taba barin Madina tayi tafiya a cikin halin da muke ciki ita kadai ba. Kasancewar ta yar jarida kadai ya isa ya sata a matsala, meyesa zaka min haka bayan tabbacin da ka bani?" 

  Wani irin sarawa kan shi yake kara yi, kaman guduma haka yake jin saukan maganan Daddyn akan shi. Me zai ce mishi? Hakan ya sa yayi tsit da bakin shi. Ganin shirun duk ba zai basu mafita ba yasa ya Abbah ya fara tausasa Daddyn da har ya fara rikicewa, muryan shi rawa take. Ya kasa hango Madinan shi a hannun mugayen mutane. Ko da ya bar gidan ma bai iya wucewa gida ba sai da ya fara kiran manyan masu tsaro yana sanar musu abinda ya afko rayuwan shi. Zancen dai daya ne, a san inda Madina tayi sannan a san ta inda za a fara. Gabadaya ya gama karaya, kaman wani yaro karami haka ya dinga kuka, wiwi.

  Lafuza masu dadi mahaifin nashi ya bashi "Je ka kwanta Abdul, gobe ma san madafa amma wannan damuwan duk baza ta fiddo ta ba. Ji yayi dakin yayi mishi wani irin fadi, rayuwan shi na wani irin juyi yana kokarin hango inda Madinan shi take. Sam! ya kasa alakanta ta da wani mugun abu. Zuciyan shi gabadaya ta gama cunkunshe wa. Sauki yake nema ko ta Yaya ne, ko ta kowani irin fanni ne. A hankali kwakwalwar shi ta fara sanar dashi abinda ya kasance mafitan shi a koyaushe, abinda ya shigan mishi jiki da kullum dare in bai yin ba bai iya samun bacci da sauki. Ya riga ya mishi mugun shiga ba tare da ya ankara ba. Duk da halin da yake ciki bai hana shi jawo wayan shi ba, ya fada duniyan da yake ganin shine zai kawo mishi saukin da yake bukata a wannan lokaci a nan take. Duniya ce da inda yana cikin ta ya kanji zuciyan shi ta bushe, ba wani abinda ya ke fahimta inba abun da yake kallo ba. Duniya ce da yana katse ta yake jin nadama da kyaman kanshi yana shigan shi. Haka Kuma duniya ce da duk yanda yaso barin ta, kwakwalwar shi kan tuna mi shi guntun zaki da zuman da ke cikin ta.

  ...

   Basu san har lokacin Asuba yayi ba sai da suka ga wannan babban matan ta mike da haramar sallah.

  "In da me sallah a cikin ku, lokaci yayi." Cikin sanyayyen murya tayi maganan wanda ya kara sanyaya musu jikin su. Ba sai sun tambaye ta ya aka yi ta san lokacin sallan yayi ba, yanayin ta kadai ya nuna musu jikin tane ya bata. Wani irin kunya ya lullube su, tun jiya ba wanda ya tuna da batun sallah, ko dan saboda rudanin da suka shiga. Sai dai Kash, ita Sallah ba abu bace wanda rudanin ya isa sawa ka manta da ita. Kaman yanda suka ga tayi taimaman haka suma suka yi sannan duk suka gabatar da sallolin su da wadanda basu yi ba.

   

  Haka matan nan ta tasa su a gaba tana sanar dasu mahimmancin sallah domin ba sai an gaya mata akwai sakacin sallan a rayuwar su ba. Anan take sanar dasu sunan ta Rabi da yanda ta tsinci kanta a wurin. In aka cire yanayin zuwan Madina, bai da wani bambanci da nasu. "Ba zan gaya muku abinda ya faru dani a nan ba saboda ban fatan ya faru da kowacce daga cikin ku. Ina bukatan ku da ku dinga addu'a a koyaushe domin Ina da yakinin Allah zai saurari kukanmu."

  "Amman Mama Rabi" Madina ta fada fahimtan da tayi matar zata haife ta. "Kin ce mana Satin ki uku a nan. Kenan muma zamu iya kai wadannan ranakun a wurin nan?"

  Girgiza kai matan tayi "Ban isa sanar daku iya kwanakin da zaku yi a nan ba saboda ni dinma ban sani ba. Kila in aka turo kudin da suke nema su sake ku." Ko a yanda tayi maganan kadai ya kara sa su a firgici.

  "Nikam ni na hana su numban kowa nawa saboda nasan basu da arzikin da zasu iya biyan miliyoyin da ake bukata. Zan takura musu ne kawai, in sasu a rudanin. Sai dai Kash, cigiyata da suka sa yasa suka samo numban yarana a shafin sada zumunta. Ansa ne akan duk wanda ya ganni ya kira numban. Nan suka kira su, suka musu duk wani barazanar su. Bansan me suka yi suka turo musu kudin da suka turo musu ba domin basu da halin shi. Sunce bai cika ba, ragowan suke jira. Da zan yi magana dasu zance kar su basu su.

  Hanifa Yayar Ummi ce tace "Amma Mama Rabi to ba kya tsoron su kashe ki?"

  Murmushi mai ciwo ta saki "kwana na ya kare kenan in haka ta afku. Ban yarda a ba mutane hakkin da ba nasu ba, su sa kansu a bashi. Ina tausayin yarana, dukkansu fama suke da rayuwa. Ban wadata su da jin dadi ba, bana sasu a matsala in azurta wasu kudin da ba zai musu ko albarka ba." Ta karasa maganan tana girgiza kai. Duk turus suka yi suna kallon ta. Tabbas sun sha jin irin kalmomin nan a bakin wasu, wanda suke kwance a gida hankali kwance suke bada shawaran a daina biyan kudin garkuwa. Ko sune aka kama zasu sadaukar da kansu saboda gaba a samu cigaba. Amma wannan zance ne da ke fitowa daga matan da ta fada hannun masu garkuwan, ta zauna a cikin su, ta dandani azaban su. Amma take irin wannan furucin. Hakika Imani baiwa ne, sai wanda Allah ya ba ma.

  "Ku saurara kuji shin in mutanen nan suka cigaba da tara kudin da suke samu gun mutane shin kuna ganin dadin hakan da wadatar kudin ba zai sa su bunkasa wannan muguwan sana'an ba? Ba shawaran kuyi haka nake baku ba, ku yara ne yanzu kuke tasowa. Sai dai ni goben ku nake dubawa." Duk zancen nata ya gama ratsa su. Madina kuwa tunani take ko ita da take ikirarin taimakawa Al'umma, ko ita da take shirye shiryen mafita akan matsala kasan mu. Ba fa za ta iya wannan sadaukarwan ba. 

  "Amma Mama Rabi, rayuwan ki na da mahimmanci musamman gun yaran ki da sauran al'umma. Samun irin ki yayi karanci a yanzu. Ina jin cewa duniya na da bukatan ki."

  Hanifa ce tayi bayanin. Kallon ta Mama Rabin tayi "Yarana duk sun girma. wannan ma al'umma nake ma."

  "Zan biya in sun bani dama. Ina da abinda zan basu, kina iya fada musu hakan." Madina ce tayi magana tana kallon maman da duk wani burin rayuwa ya kau a idanun ta.

  "Azurta sune ban so. Kar ki furta ma kowa hakan. Wannan gargadi ne a gareki." Daga cikin idanun ta suke iya ganin tana nufin abinda ta fada in da dukkan Gaskiya ta. Daga haka ta mike daga wurin tayi hanyar kofan. Abun mamaki, lokacin suka ga an bude kofan. Bayan mutumin da ya bude kofan tabi suka fita waje.

  ...

  Views na karuwa amma har yanzu likes da comments shiru. Signing in kawai zaku yi kuyi liking da comments fa. Abinda nake bukata kawai kenan.

   

Comments

0 comments