Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 08: Rashin imani

 •  Tun kafin Asuba ya farka, ya dinga sintiri a dakin shi. Can Kuma ya kunna waya cike da fatan zai sami ko wani irin labari, ko da kuwa mara dadi ne akan Madinan. Amma tsit kake ji, da alamun har zuwa lokacin labarin batan ta bai baza gari ba. Inma batan tayi kenan, wani zuciyan ya sanar dashi. Rashin sanin hakikanin wurin da Madina take yana mishi wani irin ciwon da yake ratsa har can cikin zuciyan shi. Asuba ma a dakin shi ya lallaba yayi ta, yana idar kuwa bai bi takan komai ko kowa ba ya dau mota ya fita. Sai ma daya bar gidan sannan ya fara tunanin ina zai dosa. Tunanin halin da Madinan ta kwana yana mishi tsaye a rai yayin da jikin shi yake bashi tabbas ba a cikin hali mai kyau bane. Idanun shi sunyi rudu rudu ga wani azababben ciwon kan da ya tashi dashi. A yanzu dai ba tasu yake ba don haka tilas ya ciro wayan shi, Mukhtar ya kira. Bai wani tsaya gaisuwa ba, don baida karfin guiwan yin ta ma.

  "Akwai wani labari?"

  "Jiya da dare har wurin karfe daya babu. Mun shigar da cigiya dai a gidajen TV da radio. Sa'ada ma sun yi magana da bloggers, za a sa cigiyen ko za a samu wani labari. Kuma In Sha Allah zuwa karfe takwas zamu kai report police stations. Kai ma kayi kokarin yin hakan a Abuja, In Sha Allah ba wani matsala." Dan jim yayi, a ranshi kuwa yana tunanin tabbas komai sai da natsuwa ake yin ta. Ko daya daga ciki wadannan ba wanda ya fado mishi a rai banda zuwa station. Shima Mukhtar inne ya shawarce shi. 

  Yanzu ma hanyan station in ya nufa, yana zuwa akayi referring in shi Kubwa. Unfortunately, a can ya tadda Daddy da jami'an tsaro dayawa suna kokarin binciken CCtV footage in. Luckily, an gano Madina an Kuma tabbatar da bata shiga train in ba. Har taxi in da ya kai ta mabuchi sai da aka samo. A nan Kuma gizo ke sakan. Yan wurin sun tabbatar da basu san driver in da ya tafi da ita ba.

  Tangal tangal Abdul ya fara yi, jin zancen nasu daya kasance kaman wani shirin film. "Jiya ya fara zuwa nan, ya roke mu akan yana da uzuri. He offered me some money sai na bar mishi costumer in ya tafi da." Bayanin da suka tsaya yi kenan. Abdul silalewa yayi ya zube a wurin, duk wani saurin kuzarin da ya rage mishi ya Kau. Karkarwa jikin shi yake, zuciyan shi gabadaya ya gama yankewa. Tunanin inda aka Kai Madinan ma ya kasa, balle Kuma nufin manufan zancen nasu. Tuni police in da suke tare suka yi arresting drivern da aka ba cin hancin.

  Daddy ya bude baki zai yi magana numfashin shi ya fara kokarin sarkewa, garin ya fara mai duhu duhu. Cikin wahala ya rike gefen zuciyan shi dake dukun uku uku kafin ya fara silalewa kasa. 

  ...

   Fitan Mama Rabi ba dadewa haske ya ratso dakin da suke. Sai a lokacin Madina ta iya hango fuskan wadanda ke cikin dakin. Nan ta kara tabbatar da karantar Ummi. Yayar nata dai da girman ta. Duk jikin su a mace yake. Mata mai cikin da ke takure a lungu tana juye juye ta Kare ma kallo. Sai a lokacin ta gano dawa suke tare.

  "Kece daman?" Ta fada cike da mamakin. Gun ta, ta rarrafa tana mai kamo hannun ta. Tayi nauyi dayawa. Daga jiya zuwa wayewan garin tana da tabbacin ninkuwan kumburan kafan ta, Kai hatta jikin ta bakidaya ma ya kumburo. Bata da experience amma ta fahimci tana gab da sauka. Ko yaushe labor zai iya taso mata. Nishi kawai matan ke saki a wahalce da sauri da sauri. 

  "Madina" muryan ta dauke da rauni, da alamun itama a lokacin ta fahimci da Madinan suke tare.

  Tana so ta tambaye ta ya akayi tazo wurin sai dai tasan shine abu na karshe da Hafsan zata bukata. Duk da nata kunan zuciyan bata gaza fuskanto halin da mijin Hafsan zai shiga ba. Kaman ko ta shiga ranta sai taji tana fadin "Ina tunanin Khalid, Ina tsoron tashin hankali ya illata shi. Ina fargaban wani abu ya samu yara na, ya zamu yi? Shekara bakwai Madina, bakwai muna neman haihuwa. Sai yanzu Allah ya bamu. Amma ji inda kaddara ta kawo ni. Madina in wani abu ya samu yarana, na shiga uku." rikitaccen kuka ta saki, hawayen masu tsanin zafi, karan shi mai narkan da zuciyan duk mai saurara. Madinan ma bata da wani zabi da ya wuce taya tan, zuciyan nata ya gama narkewa. Har tana Jin bata da wani matsala in aka duba na irin mutanen da suke a tare yanzu.

  Mama Rabi ashe abincin safe ta fita tanadar musu. Kaman kullum lokacin ta ke fita. To jiki da jini sai ya zamo ta saba da hakan ma. Abincin ma wani koko ne mai shegen tsami sai wani bushashen bredi. Haka Madina ta saki baki tana kallon Mama Rabi suna ci, ita kallon abun kadai har amai amai taji ya fara taso mata. Hafsa kam mai fama da tsohon ciki, yunwa ne yasa ta cin abinci dan dole kaman saura. Hanifa da Ummi, kallo daya zaka musu kasan abinci shine karshen abinda suke bukata a lokacin. Tabbas dukkan su Suna cikin tashin hankali amma ba shakkan tashin hankalin mutane biyu ya shallake na kowa.

  "Zaki Kara fita Anjima ne?" Anty Hanifa tayi maganan kaman da kanta take. Amma Mama Rabi da ke ta gane da ita take sai ta amsa mata. "Tun da na zama ni kadai ce mace a nan kullum ni ke girki. Wanda aka kawowa da baya ma yara ne."

  "Zan iya bin ki?" Ta Kara tambaya, tana fidda wani huci mai zafi dauke da buri samun nasara a fuskan ta.

  Tun kafin Mama Rabin ta bata amsa ta sake fadin "Ina so inga yarana a wani hali suke ciki, tunanin su yana firgita ni. Ina tsoron makoman iyali na a nan wurin." Kamo hannun Ummi da har lokacin ta ke jikin ta tayi tana dan hura mata iska. Har yanzu ajiyan numfashi take. Kana ganin ta kaga wacce ke cikin masifan rayuwa.

  "Maza?"

  "Dan shekaru Sha daya da Takwas" jinjina Kai Mama Rabin tayi cike da gamsuwa.

  "Zamu je da izinin Allah" da Kai ta amsa ta, tana mai nuna godiya.

  ...

  A daidai wannan lokacin a garin doha dake Qatar. Prof Maryama Ahmadu ce zaune gaban students inta tana musu lectures. Magana take tana sarkewa, duk bayan mintuna sai ta kurbi ruwa. Sam saukan ruwan ya gaza yaye mata bushewan da take ji makokaranta yayi. Sai yamutsa fuska take, tana kokarin daidaita buguwan da zuciyan ta ke yi. Su kansu student in sai suka tsinci hakan a matsayin bakon yanayi a gare su. Sun santa, sun san kaimi da jajircewan ta. Mace ce da tayi zarra a cikin dubban maza. Sun fahimci tana bukatan hutu, tana cikin wani hali da take son guje mawa. Fuskantan bai boye hakan ba. A hakan ta cigaba da koyarwan nata, bakidaya karfin halin nata na neman gagarar ta. Suna son su ce mata ta hutu, suna son gaya mata kowani dan'adam na bukatan shi amma suna tsoron maganan su yasa tayi tunanin sun hango wani gazawa a tare da ita.

  Class rep in ne yayi kokarin daga hannu, cike da burin cikan kudurin shi. "Yes Sufyan" ta fada tana kokarin karkata hankalin shi gare ta.

  "Ki min uzuri Malama ina neman alfarma a gun ki."

  Interest in tane ya fara tafiya kanshi don haka tace "Ina sauraran ka."

  "We are having a test immediately after your class. If you can please do us the favour of leaving some of your time, so we can revise."

  Dan jim tayi, zuwa can ta daga kanta cike da fahimta. "Anything for my students" 

  A tare suka hada bakin wurin fadin "Thank you Ma" hannu ta daga musu. Su suka tattara mata kayan ta zuwa office.

  Tana fita ajin taji makaranta bakidaya kaman yana mata wani duhu. Haka kurum sai take jin rashin kiran Madina a wayewan garin yana damun ta. Kullum ta kan kira ta kafin ta aiwatar da komai na rayuwan ta. Duk da ba wani dogon magana suke ba, duk da bata taba sanar mata ko nuna mata hakan na dauke mata dayawa daga cikin matsalolin ta ba. Muryan Madina kadai na rage mata kaso mafi yawa daga cikin al'ammuran ta.

  Motan ta ta hau, kai tsaye ta nufi gidan Yayan ta inda take tsammanin ko yaya ne zata ji labarin Madinan. Ita kam tana jin wani irin nauyi tattare da kiran da zuciyan ta yake yawan sanar da ita tayi ma diyar nata. Bata kiran ta sai dai ita ta kira. Ko da kuwa missed call ya zama sai dai ita din ce zata kara kiran. 

  Lafiya kalau ta sami matan gida, Hajiya Nasreen. Sauran yaran duk basa gidan sai Yasmeen da ta gama school tana jiran offer in aiki. Hira suke amma sam bata iya sauraran su da kyau. Sai da taji Yasmeen in na ambatan Madina sannan ta tattaro hankalin ta gare su.

  "Nikam Mah wai Deena bata tsoron matsalan dake tattare da shirin nan da take. Yan Nigerian nan namu sai a hankali fa."

  "Allah dai ya kare ta." Hajiya Nasreen ta amsa. Daganan sai ya zamto kaman wani shafi suka bude na tattauna al'amarin kasar ta mu.

  "Ni tunda ta tafi ma ba muyi magana da ita ba." Yasmeen ta fada. Hajiya Nasreen ma tace "Nima kam shiru." Kaman jira take sun fadi wannan zance, nan take take ji zaman ya gundure ta ba tare da sanin halin da diyar nata ke ciki ba. Sallama ta musu ta tafi akan wani uzuri ya taso mata a cikin makaranta.

  Da kyar ta iya karasawa motan, ta lallubo numban Madinan. Tasan zai yi wuya Madinan ta kai lokacin ba ta kira ta ko wani taji halin da take ciki ba musamman da tasan tana fama da jiki. Jin amsan da aka bata yasa zuciyan ta yankewa nan take. Tilas ta hada da ambaton sunan Allah, tana Jin firgici na zagaye duk wani nau'i nata.

  Cikin rawar jiki ta ke rubuta numban da shekaru bai sa ta manta dashi ba. Numban da ke ajiye cikin kwakwalwar ta, numban da ta dauka ya gama mata amfani a rayuwan ta. 

  ...

  Gajiyan gabadaya ya gama mutan musu da jiki. Masu karfin kukan ma a yanzu sun gaza. Kai duk ya dau ciwo, jiki ko sai faman turara yake yayin da zuciyoyin su ke cikin fargaban abinda zai iya faruwa dasu. Duk sun gama jigata bakidayan su. A lokacin kuma da Allah ya so su da rahma wani irin baccin wahala ya tafi dasu. Ba za su iya sani ko lokaci da suka dauka a baccin haka kuma ba zasu iya cewa ga a yanayin yanda baccin ya dauke su ba. Suna dai cikin tane, saukar wani azababben abu a jiki yasa su wata irin kururuwa. Kururuwan da ya tada wasu daga ciki tun kafin su samu nasu rabon. Ihu dishashun muryoyi kawai ke tashi a dakin sanadiyyan tika tikan itatun da ke sauka akan su. Dukan su kawai suke baji ba magani, duka irin na son hallaka wanda ake ma shi. Duka irin wanda ake ma wanda ake tuhuma ya aikata babban laifi kaman su kisa a gidan kaso. Duka ne irin wand mutum kan rasa ta ina zafin ma yake shiga. Ihun su duk ya gama ratsa dajin. Neman taimako suke, neman kaico suke amma ba Wanda ke sauraron su.

  "Ku kyale su, Ya isa haka!" Cikin wani irin Kara ogan nasu ya fada haka. A lokaci daya duk suka tsaya suna haki kaman Wanda suka sha dambe. 

  "Kaiiiii!" Wani irin kururuwa ya saki Wanda har bango dakin sai da ya amsa. Balle Kuma wanda ke cikin dakin, tuni jikin su ya dau tsuma. Duk koke koken ya tsaya cak! Duk da bai Kai ga dakatar dasu in ba ma.

  "Ku fito dasu." Yana fadin haka yayi waje. 

  "Ku mike tsaye ku fito" Mama Rabi da Madina ne kawai suka samu daman iya mikewa.

  Ummi Kam a rude take bin jikin ta da kallo. Bayan shatin bulalen da duk ya gama bin jikin su ita kam hadda jini ne ke fita akan ciwukan da suka ji mata. Anty Hanifa kokarin jan Ummin take su mike saboda tsoron su kara musu wani lahanin. Hannuwan ta duk yayi rudu rudu.

  Bangaren Hafsa kam abun nata har yafi rarraunana. Girgiza kai kawai take tana taba cikin ta. Kaman tana tsoron wani abu ya samu cikin ne. Ganin haka yasa Madina Isa gare ta da sauri. Hannun ta take kokarin rikewa ta tada ita, sai dai da alamun kafafun ta sunyi rauni da baza ta iya tsayawa kan kafafun ta ba.

  Wani irin tsaki mai Kara daya daga cikin mutanen yaja. "Me kuke jira ne? In ba zasu tashi ba ku jawo su m..." Kafin ya ida maganan duk suka fara jawo su a kasan zuwa waje. Hadda Madinan da taje taimako. Janta ake ma, hankalin ta na kan Hafsan da ke ta fizge fizge. Sai lokacin idanunta suka fada kan kafafuwan ta da suka yi suntum, suka yi wani irin ja jawur. Nishin wahala take fitarwa, yanayin da ya tsorata duk wani mai Lura. Sai dai Kash hakan ba ya daga cikin matsalan masu jantan ko kuma wadanda suka sa a jata.

  A tsakiyan aka baza su. Duk idanuwan su sun kumbura sai numfashin wahala suke kokarin yi. A lokacin aka fiddo da mazan wurin. Su kan ma an rufe musu baki da idanu har kananun da ke cikin su. Daya bayan daya suka hau cire musu. Wani irin kallo suke ma duniya, kaman wadanda suka kasance baki a cikin ta. 

  "Mama Mama Mama" ihun kiran da ke fita kenan daga bakin kananan hara guda biyu dake wurin. Yaran Anty Hanifa, rarrafawa suka yi da niyyan isa wurin ya bayan sun hango ta tana kokarin isa inda suke. Da ke hankalin mutanen bai kansu sai ya basu daman isa ga junan su. Rungume yaran tayi tana saki wani irin fitanannen numfashi. Su kan kukan su ne ke karuwa. Cikin kidima ta fara duba jikin su ko wani abu ya same su. Shatin bulalun ta gani kaman na jikin ta, nan take yanayin ta ya kara daburcewa. She look protective, she looks ready to kill the world for her children amma ba daman haka, ba wani abu da zata iya yi. Hakan yasa duk wani karfin ta ya raunana. Yanayin da ya tausasa zuciyan duk mai kallon su, yanayin da tsoron da jama'an wurin keji bai sa sun Gaza jin ciwon yaran da uwar su na ratsa su ba.

  "Ku dauko yaran" Abinda kunnuwan ta suka jiyo mata kenan. Juyawa tayi a rikice tana shirin ganin mai ke shirin faruwa. Mutane biyu taga sun nufo su. Nan take taji bugun zuciyan ta na kara ninkuwa. Jikin ta yayi wani irin sandarewa. Ko kallon arziki basu mata ba suka fizgo yaran daga jikin ta. A lokacin kwakwalwan ta ya samu signal in abinda ke faruwa. Kokarin kwace yaran ta fara, saukan wani katon abu taji a hannun ta. Nan take ta silale kasa. Ba ta karasa ba tayi saurin mikewa tana bin su. "Ina zaku kai min yara na. Me zaku musu. Wayyo Allah rayuwa ta." Kalmomin da ke fitowa daga bakin kenan. Mota taga an shigar dasu ya tashi. Kaman mahaukaciya haka ta bi motan tana gudu tana ihu. Ummi ma bayan ta ta biyo duk azaba da kafafun ya ke mata. Gudun ma kaman dada kara mata radadin da ke kasan nata yake. A haka ta karasa ta rungume Antyn nata. A tare suka saki wani irin rikitaccen kara cike da takaicin canjawan rayuwar nasu a kwana daya tak.

  ...

  Ina nan ina jiran comments inku da likes domin samun karfin guiwan cigaba da rubutu. 

Comments

0 comments