Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 09: Kisan gilla

 • Wata zararriya Anty Hanifan ta koma a wurin. Kunnuwan ta bai sauraran su, kwakwalwar ta bai fahimta idanuwan ta duhu duhu ya mamaye shi. Ba abinda ke fita daga bakin ta sai ambaton yaran ta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Sai sun mata ihu ta zaune can kaman kuma wacce aka tsungula sai ta mike tsaye a zabure tana kiran "yara na yara na." Har barazanan harbin suka mata amma sai tayi ta kallon su kaman bata fahimta abinda suke fadi. Zuwa can ta kara sakin ihu yaran ta. Ummi dai birgima kawai take. Hafsa kuwa ta kanta take, wuri daya ta samu tana jin azaban da ke zagaye kowani ilahiri na jikin ta. Nishin wahala kawai take ta zuba ma kafafun ta da sukayi suntum idanu.

  Wannan karon ma Mama Rabin ce ke dafa Abinci. Madina kam ta rasa inda zata doss, ta rasa waya fi bukatan taimakon ta a cikin su. Tilas ta je ta kamo Anty Hanifa ta ajiye ta wurin da Ummi take. Ba tace musu komai ba saboda tasan ba maganan da suke bukatan ji a halin da ya riske su.

  Hafsah ne ma Mama Rabin ta tofa ma addu'a. Mazan wurin kafafun su da hannayen su a daure yake so basu da abun yi a wurin.

  Madina zafin da take jin kirjin ta na mata ya sata tsakuran Abinci. Sai ma zuciyan ta dake raya mata mutanen da take tare dasu a cikin wannan kuncin na bukatan agaji a wurin ta. Hanifa da Ummi kaman safe yanzun ma ko kallon arziki abincin bai samu ba. Hafsa kuwa hannu baka hannu kwarya take cin abincin. Ba wai don tana kin dadin shi ko kuma yunwa ba. Aa, tasan tana bukatan abincin ne. Yaran da ke cikin ta na bukatan abinda zai cigaba da tafiyar da rayuwan su kafin su iso duniya. Kuma wannan hanya daya kadai da take tsammanin zai taimake su. Su Madina basu matsa ma Ummi da Anty Hanifa suci Abincin ba saboda sun san baya daga cikin matsalan su a yanzu. Akwai lokacin da basu da zabi da ya wuce tilasta ma kansu shigan abu cikin su.

  "Ku gafara ga zaki nan." Kalaman da suka ji na fitowa daga bakin yan ta'addan kenan. Yanda su ke gyaeawa Suna wani Kara natsuwa yanda kasan ance wani Sarki ne zai fito. Hadda sunkuyar da kai a kasa.

  Can ko sai sawun tafiyan shi ya fara ratsa kunnuwan su. Tafiya yake a hakimce, yana kallon gefe da gefe. Yanayin fuskan shi kaman kasan da yake takawan ya mishi kadan. A haka ya karasa gaban su, gaban mutanen da aka tara mai. Kallon su yake daya bayan daya kaman mai kiyasin wani abu a ranshi. Tukunna ya fuskancen su da kyau. "Ban daukan iskanci da rainin hankali. Ban da hakuri ko kadan, ban zama inuwa daya da mai taurin kai. Kudi kawai nake bukata, sune kawai zasu tsaya a matsayin fansan ranku. Ku rike wannan ku kiyaye." Cikin wani irin kaushi da gadara muryan shi ke fita. "Abinda kuga ya same muku daga daren jiya zuwa gobe bakomai bane. Abinda zai faru da ku zuwa gobe ninkin balin kine. Zaku gani ganin idanun ku in aka min abinda nake so." Suna gani daga cikin idanuwan shi, ba wani shakka akan abinda yayi magana akai. A shirye yake ya kauda duniya saboda samun kudin Haram. Ya rufe fuskan shi idanuwan shi kawai ake iya gani, amma muryan shi ma mai sa kidima ne.

  Hannun shi kawai ya nuna saitin da Mama Rabi take yaran shi suka nufi inda take suka daukota. Durkusawa yayi yana kallon ta cikin idanu kasa tayi da idanun ta. Cikin harzuka yasa hannu ya dago fuskan nata jikin shi har wani rawa yake. Bai yi wata wata ba ya zuba mata Mari ako wani bari na fuskan ta. Duk kasa su kayi da kansu. Madina fadawa tayi tunanin irin bakar zuciyan wannan mutum, zuciya mara amfani da imani. Zuciyan da zata iya daga hannu ta mari matan da take kyautata zaton zata iya haifan shi. Inma bata haifan ba, tabbas zai kasance kanin ta na karshe.

   

  Bata kidima ba, sai yanda taga ya shako wuyan ta yana wani irin huci. Waya ya amsa ya danna kiran wata numban. An fara magana yayi saurin katse su. "Kwana nawa na baku, baku cika min alkawari ba?"

  Cikin rawan murya yace "Dan Allah ka mana afuwa kudin muke nema Wallahi. Wancan karon mun hada dukkan wani dukiyan mu mun kawo maka. Dan Allah ka Kara rage mana wani abu."

  "Kun fi kowa talauci ne? Na riga da na gama magana. Kana wasa dani."

  Muryan ne ya kara tashi cikin tsoro da tashin hankali "Dan Allah ka..." Bai tsaya kara Jin wani zance ba ya katse kiran.

  "Ni ba shasha bane, ban magana biyu." Yana fadin haka ya ciro bindiga daga jikin shi. Duk a take jikin su ya dau rawa. A zabure Madina ta mike tana kiran "Aa Aa ka tsaya." Mai da idanun shi yayi kanta. Ganin haka ya sata fadin "Zan biya mata ni ko nawa ne. Dama kawai nake bukata."

  "Wacece ke?" Ya fada da babban muryan. Jikin ta har wani irin tsuma yake ganin yanda ya zuba mata idanu. Wani daga cikinsu daga can gefe ne ya dan sunkuya a gaban sa "Ranka ya dade, itace wacce Oga Abbah ya Maka magana a kai." Wani irin zaro idanuwa yayi, sai ya kada su.

  "Ki kulaaa, Abbah yana da mahimmanci a wurina. Kar ki Kara katse min magana na."

  Hannu ya mikawa na gefen shi, wanda shine ke bi mishi. Ogan nasu da ke jagorantan su. Ba abinda suka kara ji sai karan bindigan da ya sauka akan cikin Mama Rabi. Nan take ta fadi kasa ba rai. Rai kenan bakon duniya, kowanne da silan tafiyan shi. Kowanne da yanayin kaddaran tafiyan shi.

  Dabas! Madina ta zauna a kasa. Tana Jin wasu notinan kanta na warwarewa, kwakwalwar na juyawa, tsakiyan kanta na bugawa, zuciya ta na toshewa, ganin ta na daukewa, tunanin ta na yankewa. Sautin wani sabon kuka ne ke tashi a wurin, kuka ne irin wanda ke hade da tsoron makoman kansu a wurin.

  "Ku amshi numbobin. Duk wanda bai baku ba kuyi ta dukan shi har sai ya fada." Yana fadin hakan ya mike. Har ya fara tafiya ya dakata ya tsaya. "Bakuwar Abbah a ware ta gefe. Kar kowa ya taba ta."

  Madina dai ko da aka dauke ta daga cikin su bata san me yake afkuwa ba. Bata san me take ji ba, gabadaya komai nata ya gushe. Gatanan ne dai a duniya amma ba ta iya fahimtan komai. Bata san lokacin da ta dauka a hakan ba. Zuwa lokacin da hankalin ta ya fara dawo gare ta, taji mutanen gefen ta na magana akan ana son siyan wasu gabobi na jikin dan'Adam. Nan take jikin ta ya hau tsuma, idanuwan ta suka kara rikidewa. Kunnuwan ta kuwa ba abinda suke sauraro mata sai sautin harbin da aka ma Mama Rabi a ciki.

  Kaman mutum mutumi tana zaune ta ga an dauko gawar nata. Kaman wata rago haka suka hau fede gawan. Dan Adam mai daraja da yake bukatan a sallace shi a suturta shi. Tsaf suka fede gawan nan suka ciro duk wani abu a jikin ta. Kallon su take amma ba zata ce ga abu daya da take tunani ba, ba za tace ga abinda take fahimta ba. Tana gani suka gama cire duk wani abu mai amfani a gare su.

  "Karnuka nan suna Jin yunwa, ku basu abinci." Daganan Kuma sai sautin haushin karnukan da taji ya mamaye kunnuwan ta. Wani kururuwa suke suna haushin. Kaman abinci haka suka wulla musu saura wuraren da basu bukata. Cikin rawan jiki karnukan suka hau cin nama da kasusuwan. Sai take jin kanta kaman ba a duniyan da ta sani take ba, kaman wannan wani sabon duniya ne da dodunan da suke ji a tatsuniya ke wulakanta mutane saboda rashin sanin darajan su. Koma dai ina ne, tana da tabbacin ba zata kara ganin wani abu mai muni da bakan tan abinda ta gani yau ba. Kuka take so tayi amma ta kasa, ciwon da take ji a jiya da safiyan yau ta ke nema  tsaf ya bace. Tsungulin kanta take tana neman jin zafi ko da a fatan jikin tane sai da bata jin komai. Kanta da zuciyan ta sun mata nauyi kaman dutse aka sa aka danne wurin.

  Tana nan zaune taga an dawo da yaran Anty Hanifa maza biyu. Dayan a hannu aka fito dashi ba zata iya gane ko a raye yake ko a mace ba. Dayan Kuwa idanuwan shi sunyi jajur, jiyoyin kanshi duk a tashe. Tafiya yake yana gwale kafa  ga wani ihun azaba da yake saki. Ta gaban ta suka wuce ta bisu da idanu. Jini ta gani kaca kaca a bayan babban da ke tafiya yana ihun. Ganin zai bata musu lokaci yasa daya daga cikin su ya daga shi. Sai a lokacin ta kara lura da jinin ke kwarara daga jikin yaran duka biyu. Nan take kwakwalwar ta ya fahimtar da ita meke faruwa. Luwadi aka yi dasu.

  Tunani hakan kadai ya sata jin abu ya tsaya mata a wuya bayan nauyin da wurin yayi. Wani karfin guiwa taji yana taso mata, kuna taji zuciyan ta ya fara mata. Lokacin kidiman da ta shiga a dalilin mutuwan Mama Rabi ya fara sakin ta. Silalewa tayi a hankali ta karasa wurin da ta barsu. Anty Hanifa dai na ido hudu da yaran ta suma ta dinga yi tana farfadowa duk ta fita daga hankalin ta. Yaran ma ihu suke. Ummi ce dai tayi jugum tana kallon su. Da alamun kukan ya gama gagaran ta. Karasawa wurin su tayi ta dauko karamin yaron da har yanzu bai san inda kanshi yake ba. Bata tsaya cewa komai ba tayi gaba dashi. Wurin Nass in da ta hango ta karasa, cikin kuna take furta maganan da daga ji zaka san da kyar take fitar dashi. "Da kuka tanadi irin azaban da zasu dinga yi baku tanaji magungunan su bane?" Dagowa yayi ya kalle ta kaman zai yi magana sai kuma ya fasa. Bai tanka mata ba ya bar wurin. Ita ms hanya inda taga ruwa ta nufa, a hannun ta debo ruwan ta dinga shafawa a fuskan yaron tana hura mai iska ta hanci. Cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya fara tari kafin ya bude idanu, bakin shi dauke da sunan maman shi. Kuka ya hau yi da alaman azaban da ya sha ke ratsa shi har yanzun. Cikin tarin karfin hali ta zare mishi wandon jikin shi. Ruwan tasa ta dinga wanke mishi wurin da yake kiran yana mishi ciwo yana kuka mai firgitarwa. Kuna zuciyan ta keyi tana kamanto abun da kanin ta Adnan. Duk da ba ta shiga hurumin su, tana jin yaran a ranta. Hakan yasa ta ke kamanta wa da Adnan in tana jin dukkan zafi na ratsa su. Tana shirin barin wurin sai ga Nass dauke da maganin pain reliever. Amsa tayi kafin cikin dakewa tace "Ina son Vaseline" juyawa ya kara yi. Ita kuma taba yaron maganin sannan ta koma suka dauko dayan tare da Ummi. Haka ta kula da yaran nan, ta basu magani ta shafa musu Vaseline a wurin don rage wani nau'i daga cikin radaddin da ke damun su. Da kanta ta jasu suka shiga dakin da aka kaisu hadda yaran. Sannan ta koma gun Hafsa da har yanzu nishin wahala take.

  Kamo hannun ta tayi duka biyu ta daura akan fuskan ta bayan ta sunkuya. "Ki daure ki lallaba mu tafi daki." Idanuwan ta dauke yake da abubuwa da dama da leben ta ya kasa furtawa. Hafsan na iya hango hakan, sai ya zamo kaman magana suke ta idanu. Yunkurin mikewan tayi amma ta gaza. Jinjina mata kai Madinan tayi alamun zata iya. Don haka ta kara yunkurawa. Wannan karon karfin halin daure zugi da azaban da take ji tayi ta kama hannuwan Madinan da kyar ta samu ta tsaya. Sai dai kafafun nata na neman gaza daukan ta tilas ta dafa bangon wurin da take. Da dafen bango, da rike hannun Madina a haka suka samu suka karasa dakin. Tana shiga ta zube kasa sai wani irin zugi da ko ina na jikin ta ya dauka. A yanzu ma ta kasa kukan girgiza Kai kawai take. Cikin takaici Madinan ta kamo hannun ta daya ta sa a nata domin ta nuna mata tana tare da ita. Ba Wai don zata iya taimaka mata ta kowani hanya ba.

   Anty Hanifa ta gaza furtawa, amma daga idanun ta Madina na hango tarin godiyan da yake cikin su. Da kai ta jinjina mata. Gabadaya maganan nasu ya koma kaman kurame. A lokacin daga Ummi har yaran Anty Hanifan duk sun samu bacci, duk da shi dinma bana dadi bane.

  Duk da shirun da suka yi, duk da gajiya da dimauta da ke ratsa kowani jijiyoyi na jikin su bai hana su Jin zafi da ciwon yanda mutuwan Mama Rabi ya kasance ba. Matar da suka sani a rana daya amma ta musu abinda ba zai ta taba gushewa a ransu ba. Ballantana Madina da taga zahirin yanda makoman gawan ya kasance. Haka ta tsinci kanta da yi mata addu'a. Sai dai da ta rufe idanun ta karnukan nan take hangowa, yanda suka afka ma sauran gawa. Nan take jikin ta ke daukan rawa, gumi na tsatsafo mata. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Abinda idanun ta ke hangowa kawai kenan. Kunnuwan ta har a lokacin na jin sautin harbin da ya katse rayuwan Mama Rabi. Tana ji kaman tayi ta kurma ihu ko zai sauwaka mata yanayin da take ciki. Ji take kaman tana neman zarewa. Ji take kaman tana da dama da za ta hana mutuwan mama Rabin amma ta gagara aiwatar wa. She feel so helpless to her bones, kaman kasusuwan jikin ta na karyewa. Zuciyan ta na wani irin bugawa. Shin zata taba dawowa daidai? Hakan ba abu bane mai yiwuwa.

  Da kukan yunwa yaran Anty Hanifa suka tashi bayan Magriba. Ita kadai ce mai sauran lafiyan da take ganin zata iya yi musu wani abu. Don haka ta lallaba ta hau buga kofan. Bayan kaman yan mintuna aka bude. Nass ta gani a wurin, sai ta tsinci kanta da sakin wani ajiyan zuciya. "Muna bukatan Abinci da ruwa na sha da na Sallah." Kaman dazu bai ce mata komai ba ya kulle kofan ya bar wurin. Bayan kaman yan mintuna ya Kara dawowa. Ajiye musu kawai yayi ya juya. Wannan karon har Ummi da Anty Hanifan sai da wahala ya sasu afkawa abincin. Sannan duk suka yi sallah, suna tuna wa'azin Mama Rabi. Sai suka hau rokon mafita wurin Allah da yi mata addu'an samun rahma da gafara a wurin Ubangiji.

  Wannan daren da wuri aka bude kofan. Nass ne. Kallon su yayi a hankali ya furta "Maigida na bukatan daya daga cikin ku ya kwanta da ita."

  Take zuciyan su ya hau dukan uku uku, cikin su ya duri ruwa, firgici ya canja musu kamannin. Ganin haka yasa Madina mikewa cikin kasala da sanyin jiki "Muje." Bai motsa ba ya girgiza kai "Banda ke"

  Kallon shi tayi tana mamakin dalilin da yasa shi furta haka. "Ke zo" ya fada yana nuna Ummi. Da sauri ta shige jikin Anty Hanifa tana sakin ihu.

  "Dan meyesa? Bata da karfin yin wani abu, mutane fiye da bakwai suka mata fyade jiya taya kake tunanin zaka ta iya tsinana wani abu a yau?"

  Tabe baki yayi, fuskan nan nashi ba ka iya karantar komai akai yace "Wata tazo"

  "Meyasa bani ba?"

  "Saboda ke ajiyan wani ne." Yana fadan haka ya nufi inda Anty Hanifa take, da karfi ya hau janta. Mutumin da ke bayan shi ya taya shi, tana turjewa tana ihu. Yaran ta da Ummi na ihu suka tafi da ita.

  Tun daga dakin da suke, suke jin sautin ihun ta hakan ya sa dukan su bankwana da natsuwa. "Anty Ummi kashe mamanmu za ayi?" Karamin ya tambaya ta girgiza mishi kai.

  "Abinda aka mana za a mata ko?" Babban ya fada nan kan kasa amsawa tayi sai rikitaccen kukan da ta saki.

  Suna cikin halin sai gashi an rako Hanifan ta dawo. Fuskan ta a bushe sai dai duk jirwaye. Yanda take kokarin gyara tafiyan tane ya tabbatar musu da ba mutum daya bane ya shige ta. Amma karfin hali take kar ta nuna musu komai ya faru da ita. Karfin hali ne take kawai saboda ta gusar da yaran ta daga damuwa.

  ...

  Likes da comments in dai shiru bayan views sai karuwa suke. Don't be lazy please, signing in kawai zaku yi fa. Ina bukatan samun karfin guiwa daga gare ku. 

Comments

0 comments