Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 10: Rashin madafa

 •  

  Gari gabadaya ya dauka, ko wani shafin Sadarwa ka shiga abinda ke trending kenan, batan Madina.

  #Madinaismissing

  #weneedmadinaback

  #bringbackmadina

  #northisbleeding

  Popular hashtags in da ke ta yawa a kafafun Sadarwan. Sai posts masu dauke da hotunan Madinan, a kasa ana bada labarin abinda ya faru.

  Ta bar Abuja by road zuwa Kaduna biki and she is no where to be found. Bloggers duk sun daddaura da different captions insu. Arewa we are not safe. Is it because they want to silence her? Miye laifin ta? Fadin gaskiya?

  Dagabaya ne makusantan wanda aka kama a ranar suma suka fara sharing hotunan su. Musamman Hafsa da take dauke da tsohon ciki.

  Tana da ciki wata tara, haihuwa yau ko gobe. An dauke ta a hanyan ta na tafiya Kaduna, inda zata haihu wurin mahaifiyar ta.

  Haka aka dinga daura pictures in wadanda ba a gani ba daga bin hayan Abuja. Hakan ya tabbatar ma al'umma kidnapping in nasu aka yi. A lokacin ba a riga da an kira kowa ba. Kowani shafi ka shiga zancen ake, masu post nayi, masu sharing nayi, masu reposting haka, wasu a story suke sharing, masu gani su wuce suna Allah ya kyauta ma duk suna nan. Masu video suna magana duk gasu musamman influencers da celebrities in da in suka ki maganan ma har dragging in su ake. Kaman ana huce wani haushin akan su. Sai dai shin wani mafita hakan zai haifar? Trending hashtags da dragging Celebrities zai fiddo su Madina daga inda suke? Ko Kuma zai sa gwamnati tashi tsaye ta gano inda bakin zaren yake ne? Hankula sun tashi, zuciyoyi suna ta tsuma musamman ga masoya da makusantan Madinan.  Allah ya kubutar dasu. Allah ya kawo musu madafa. Duk ba irin comment in da ba a gani ba. Har da masu karyatawa ba kidnapping in bane. Taya za a dauki yar mai kudi? A dai binciko in da take kawai.

  Bangaren Abba kuwa sai da aka danganta da Asibiti aka bashi taimakon gaggawa. Abdulhamid ke kanshi kafin ya samu daman kiran Mami. Ya kasa tsaye ya kasa zaune, jikin shi sai tsuma yake. Yana jin abubuwa sun taru sun cunkushe mai. Mamin na iso wa ya bar asibitin zuwa headquater in police station in. Kai tsaye aka mai iso sanin matsayin shi.

  "What's the way out? Ta ina za a fara bullowa matsalan nan?"

  "Dole mu jira zuwa lokacin da zasu kira ko?" Nan take idanuwan shi suka kada, bai san lokacin da ya mike a zabure yana buga table in da ke gaban shi ba. Sai da yayi wani irin kara da har wanda ke gaban nashi sai da yaja baya.

  "Kana nufin in barta har sai lokacin da suka ga dama suka kira? Ba tare da munsan halin da take ciki ba? In kashe ta suke da niyyan yi fa?" Jigum CP in yayi cikin rashin sanin mai zai gaya ma Abdulhamid in kuma. He don't have the right to execute anything. Banda investigation in da yake na wannan driver in a yanzu. Zuwa yanzu sun tabbatar iya gaskiyan shi yake  fada musu.

  ...

  Washegari duk aka sasu a gaba ana kiran numbobin da suka bada. Sai asa su suyi magana cikin rudani da tashin hankali suna kiran yan'uwan nasu su taimaka su ceto su. Madina na jin duk abinda ke wakana, irin tashin hankalin da yan'uwan ke shiga duka sanda aka kira su. Da irin yanda wadanda kenan in suke kukan neman agazawa da taimako. Banda girki ba abinda aka sata a ranar. Ba Wanda ya mata magana, ba Wanda yabi ta kanta. Basu tambaye ta numban kowa nata ba itanma bata basu ba. Haka ta zauna tana kokarin girkin da itace ma da wuya ta hada shi, don kwatakwata bata san yanda zata fara ba amma dake jiyan a gaban ta Mama Rabi tayi sai ta hau yin abinda ta gani har wutan ya hadu. Sai ta hau girkin da bata tuna ta taba yin irin shi ba a rayuwan ta. Abu daya ta lura dashi, mahimmancin mutumin da ya kawota wurin yasa suka gaza taba ta. Sai tsoron ta ke kara ninkuwa sosai. A dan tafiyan da suka yi dashi kawai tasan rashin jmanin shi mai girgiza mutum ne. Tasan ba zai taba mata da sauki ba. Kilan ma ita ma kashe ta zai yi, karnuka su cinye sauran ta bayan sun saida abinda zai musu amfani.

  Da aka zo kan Hafsa, cikin kidima take magana tana fada ma mijin ta. "Muna bukatan ka nida yarana Khalid. Zan iya haihuwa a kowani lokaci daga yanzu. Ina bukatan fita daga bakin halin nan ka ceto ranmu Khalid" cikin rauni take fizgo maganganun.

  Khalid in cikin kuka da tsoro yake kiran "Hafsa yanzun nan zan aiko musu ko nawa suke bukata ko da abinda na mallaka ne gabadaya. In Sha Allah zaku iso gare ni lafiya." Daga haka suka dauke wayan a kunnen ta suna mishi magana. A take ya amince zai aiko musu da kudin sabanin dayawa da suka nemi a musu ragi. Kuma tana ji aka hau ciniki, Wai dan'Adam ake ciniki sai kace wani dabba ko kaya.

  Million Hamsin suka bukata, Jin zai kawo musu ya sa Suna kashe wayan suka kalli junan su. "Oga wannan shege ne ya kamata a kara wani abu."

  "Barshi ya fara kawo wadannan in."

  Hafsa dai hankalin ta bai kai kansu ba, balle har ta iya wani sauraran su da kyau. Cikin ikon Allah kafin yamma Khalid ya kira su ya hada kudin. Wasu daga cikin su suka dau wata hanya mai nisa dan amsan kudin, hanyan da kwatakwata bai hada hanya da inda suke ajiye mutanen da suke kamawa ba ballantana ayi tunanin kama su.

  A daren ranar duk sunyi jigum dauke da tunanin halin rayuwa a zuciyoyin su. Dauke da tunanin abinda za iya faru cikin daren, wayewan gari ko kuma zuwa lokacin da zasu dauka a wurin. Zuciya ta gama yankewa, idanuwa sun bushe karara, kwakwalwa kuwa fahimtan ta na neman zautuwa. A cikin wannan fadi tashen su ke zaune. Fadi tashen da a wajen duniya ya kare a trending hashtags kawai. Yayin da ba wani kwakwaran mataki na tsaro da aka yi yunkurin turawa binciko lamarin banda wadanda aka sa akan hanyan kawai.

  Wurin karfe sha biyun dare suka bude kofan. Budewan da suka san ba zai taba zame musu alkhairi ba. Nass ne tare da wani a bayan su. Duk idanu suka zuba mishi yayi da idanuwan su ke Kara duran ruwa. "Dake, dake da ke ana bukatan ku." Anty Hanifa, Ummi da Hafsa ya nuna.

  "Me za a musu? Baka san matan aure bane? Wannan ai dabbanci ne?" Ji tayi shiru ne karshen abinda za ta iya a yanzun. Abun ba iya zuciya yake kona mata ba, hatta gashin jikin ta ji take wutan yana shafa.

  "Sannan ba kaga tayi nauyi bane? Baka ga halin da take a ciki bane? Ya Allah wannan wani irin rayuwa ne."

  "Madina" taji ya kira sunan ta. Bai taba tanka mata ba sai yau amma mamaki shine karshen abinda zai fado mata a yanayin da take ciki. "Ki kiyaye bakin ki a nan wurin. Kisan abinda zaki dinga furtawa. In kika gaya ma wani bani ba zai yi wuya ki Sha." Yana gama fadin haka yayi hanyan waje. Ba wanda ya iya Kara kwakwaron motsi a cikin su.

  Ko zuwa yayi ya ma wasu magana can zai gasu sun shigo cikin ihu da hargaga. "Dauko mana su" wani daga ciki yayi magana. "Wannan Oga ke bukatan ta, da alamun gobe ta iya barin nan shine yake son huce kishin shi." Dariya suka kwashe da. Wani yace "ni takaici na wannan da aka hana mu tabawa da ba karamin romo za mu kwasa ba." Madina yake kallo, suna hada idanu ta sakan mishi wani kallon tsana da Allah wadai kafin ta maida kanta kasa. A zuciye yayi kanta, wani irin kwallo yayi da ita sai da kanta ya hade da bango, azaban na ratsa ko ina na jikin ta. Sai sakin zazzafan numfashi take, ta gefen kanta har jini ne ya fara zuba.

  Kafin suka ja su duka ukun, suna ihu da fizge fizge amma ko sauraron su ba su tsayi yi ba. Azaban da Madina keji tuni ya gushe mata. Ba wai don ba zafin ba. Aa, tunanin Hafsan da suka dauka ne ya mamaye ta, tana tunanin bala'i irin wannan. Sai dai yanzu ba abinda bata gani a wannan rayuwan ba. Musamman mutuwan Mama Rabi da yake ko ina na jikin ta. Tana Jin sabon zafin abun na ratsa ta. Hafsa take ji, ita ce ta mata tsaye a rai yanzu. Tana bukatun taimako maimakon hakan sai bala'in da aka nemi Kara mata. Da wanne zata ji? Ciwon jikin ta? Abinda ke cikin ta? Ko kuwa abinda za su mata. Tana cikin wannan tunanin ne taji ihu da hargowa. Na Hafsan ne da ya hade da na Ummi. Rasa inda zata sa kanta tayi, tana jin tashin hankalin na dada shigan ta. Tana tausaya musu da ita kanta da bata san nata makoman ba.  Tasan share ta da suke yi ba a son ransu bane, ba yanda suka iya ne. In zasu samu daman duk sai sun huce haushin su a kanta.

  Sai wurin karfe biyu aka dawo dasu. Kowa a birkice, ba inda kanshi yake. Ummi  fuskan ta har ya kumbura, shatin mari ne ta ko Ina. Kuka take kaman wacce za a zare ma rai. Madina na son agaza mata amma a yanzu ba halin yin hakan saboda akwai wacce tafi bukatar ta. Hafsa ce da tunda suka dawo da alamun bata san inda kanta yake ba. Rayuwan juya mata take. Magana take ba tare da tasan abinda take fadi ba. Kyarma take tana fidda huci ta ma rasa ina ke mata ciwo. Har ji take kaman ba a jikin yake ba ma. Dole suka yi kanta harda Anty Hanifa. Ta dade a hakan sun rasa mai yakamata su yi specifically.

  Zuwa can Anty Hanifa ta fuskancen ta da kyau. "Ina ga fa nakuda take Madina." Zaro idanu Madinan tayi tana kallon ikon  Allah." Tabbas ta tuna Hafsan ta gaya mata tana tsoron nakuda ya riske ta a nan saboda likitoci sun tabbatar mata ba zata iya haihuwa ba da kanta. CS za a ayi a ciro yaran. Nan take Madina ta gaya ma Anty Hanifan.

  "Sai Kiga Allah ya saukaka lamarin Madina, ba zai hada mana zafi biyu ba In Sha Allah."

  Madina ba irin addu'an da bata yi ta tofa mata ba. Duk wanda ta iya a rayuwar ta sai da tayi shi har da wanda bai danaganci abun ba. Ta Hausa, turanci da larabcin ba Wanda harshen ta bai furta shi ba. Gabadaya daga su har ita sun gama jigata. Sai wurin Asuba nakudan ya tashi gadan gadan, tilas Anty Hanifa ta tsaya amsan haihuwan. Abun mamaki, abun Ikon Allah sai gashi matan da aka ce ba zata iya haihuwa da kanta ba kan yaro na kokarin ratsawa. Kukan farin ciki Anty Hanifan ta saki, kafin ta yi kokarin cigaba da taimaka mata tana nishi ba. Cikin ikon Allah sai gashi yaron ya fito da sauri ta riko shi. Jijjiga shi tayi, yasa kuka. Sannan ta dauke shi ta mika ma Ummi da har ta gaji da kukan tayi tsit. "Sa shi a dankwalin can ki rufe shi " abinda tace kenan sannan ta cigaba da taimaka ma Hafsan ita da Madina. Kaman ma wani sabon nakudan ta fara, don har tafi na farkon shan wahala. Haka suka yi ta fama kafin su samu yaron shi ma ya fito tare da taimakon Ubangiji. Yana fita, cikin azaba da gajiyan da ya gama shigan ta, ta saki wani uban ajiyan zuciya daganan idanun ta suka kulle. "suma tayi." Anty Hanifan ta fada. Tilas Madina ta tashi ta kwankwasa kofan. Kaman kullum Nass ne a wurin tana ganin shi tace "Ruwa Ruwa Dan Allah" cikin kidima da tsoro tayi maganan. Nan take kuwa ya wadata da ruwan. Suka sa ma Hafsan aka samu ta farfado. Kana ganin ta kasan ta gaji, tana bukatan hutu tana bukatan bincike da kulawan likitoci abubuwa dayawa da ake ma mai jego amma ba hali. Matar da ba irin tanadin da ba ayi ma haihuwan ta ba. Hatta kudin asibitin da za ayi aikin da komai na bukata ba abinda ba ayi ba dai dai na yan gata amma sai gashi a inda ta haihu. Ubangiji kenan mai yin yanda yaso. Asuba nayi Madina ta fita, Nass tasa ya sanar ma ogan su sannan ta fara kokarin daura ruwan zafi. Da yake wurin a tsare yake, kowa da bindiga a hannun shi hakan yasa ba wanda yace mata kala don sun san ba za tayi kokarin yi wani abu ba.  Anty Hanifa tayi ma yaran wanka. Bayin da suke shiga a bukkan yake don haka a nan aka wanke Hafsan. Gatan da ta samu kawai kenan, cikin ikon Allah ta samu wani irin bacci daga ita har yaran nata.

  Da ta farka haka ta dinga kallon yaran tana jin kaunar su na ratsa ta. Tana jin ina ma Khalid dinta na nan da bata san irin farin cikin da zai shiga ba. For the first time taji farin ciki na shigan ta tunda tazo wurin gani take kaman ba ta da wani bakin ciki kuma. Ko a haka Ubangiji ta ya barta ya gama mata komai. Sannu suka dinga mata, tana musu godiya da idanun ta. Ruwan dumi, Madina ta samu ta ba yaran. Ita ma Uwar ta samu ta ci Abinci, sannan aka samu ruwan nonon ta ba yaran ta. Ba kuka sai kallon su take tana jin abun kaman a mafarki. Abinda ta dade tana marmari yau gasu a gaban ta. Kash! Khalid baya tare da ita balle ta nuna mishi riban hakurin su.

  Suna cikin wannan halin, kowa zuciya ya dan lafa sai ga ogan nasu ya shigo yana hargowa. "Mu mutumin nan zai hada da Yan sanda? Ni zai ma iskanci da taurine kai? Na gargade shi bai ji ba saboda haka zai gane kuren shi ku kwaso min yaran."

  Duka yaran na kan cinyan Hafsa, ita kadai ce a dakin, ta kasa gajiya da kallon su. Sai fadada murmushin ta take tana gode ma Allah da irin ni'iman da ya saukan mata. A dai dai lokacin taji  sawun mutane na shigowa dakin. Su biyu ne duk dauke da bundigogi a hannun su. Ba tare da sun ma kowa magana ba daya daga ciki yasa hannu ya zare yaron farko. Kaman ya sani ya wani irin cinna kara. Kallon shi Hafsa take wani irin tsoro na darsuwan mata a rai. Cikin kidima tayi saurin mikewa tsaye. "Ka bani yaro na" cikin wani irin babban muryan da ita kanta bata dan tana dashi ba tayi maganan.

  Bai mata magana ba, sai fizgo na hannun ta da yayi. "Mu tafi" yace ma sauran. Wani irin super tayi ta kamo bayan rigan shi, tana kokarin kwace yaron hannun sa. Kan bindigan yasa ya buga mata a goshi. Sai dai ko gizau ba tayi ba, ta kara kokarin jan shi take tana wani irin ihu mai rikita duk mai sauraro.

  "Ku zo ku kamata" ya fada cikin babban murya. Nan take maza hudu suka yi kanta suka nufi waje. Duka nauyin rikon da suka mata bai hana ta kokarin turjewa ba. Bai hana ta fizge fizge tana kururuwan kiran yaran ta ba. Ihu take mai firgitarwa, ihun da yasa su Madina da Anty Hanifa fitowa suna kokarin ganin meke shirin afkuwa. Ganin yaran a hannu su yasa Madina zubewa a kasa, idanun ta kan Hafsan da duk ta gama fita a hayyacin ta. Yaran ma sai tsalla ihu suke.

Comments

0 comments