Makalu

Sabbin Makalu

View All

Mafitan Gobe 11: Kisan gilla 2

 • Cikin takun kasaita da isa sautin takun shi ke fitowa. Bayyana shi ne ya dan tsagaita hargagin da ke wurin. In aka cire kururuwa Hafsa da kukan yaran.

   

  "Meke faruwa?" Shine abinda ya fito daga bakin Zakin nasu, yana kokarin kare ma kowa kallo.

   

  Ogan nasu ne cikin dukar da kai ya amsa shi "Yallabai mijin ta da yasa mu tura mutanenmu amso dukiyan ne ya shigar mana da kwalawa sabgar."

   

  Bude baki yayi hade da zaro idanuwa "Duk gargadin da nayi? Ba wanda aka kama ko?"

   

  "Babu Yallabai." Ya amsa yana kara kasa da kwantar da kai.

   

  "Shikenan ai, ku musu hukuncin da ya dace saboda gaba." Yana fadin haka ya juya zuwa inda ya fito.

   

  Ogan ne ya kalli daya daga cikin yaran shi. Wani wanda ake kira da Salihu ya kalla, daga idanun shi kasan a shirye yake ya aiwatar da duk wani abu da aka sa shi. "Fiddo da karnukan nan."

   

  Tuni cikin su ya duri ruwa, ballantana Madina da abinda ya faru da gawan Mama Rabi yake idanun ta a koda yaushe. Daburcewa tayi, tai kan wanda yaron ke hannun shi. Dai dai lokacin Hafsa tayi nasara fita daga hannun wadanda suka rike ta cikin wani irin karfi da ba tasan tana da irin shi ba.

   

  Ganin haka yasa ogan ciro bindigan shi, bai yi wata wata ba ya harbaata a kafa. Kasa tayi dan dole ga uban jinin da ke malala, duk da azaban da take ciki bai hana ta rarrafawa tana rike kafafun mutanen ba. Madina kuwa sawa yayi a daure ta a bango, da ita da duk sauran wadanda ke wurin. Sannan yayi musu barazana akan duk wanda yayi motsi harbe shi zai yi.

   

  Karnukan sai haushi suke suna hargowa, haushin da yake kada hanta duk wani Dan Adam. A tare suka cilla yaran gaban karnukan, da jikin su har rawa yake suka yi kansu. Hafsa a zabure tayi gun, mutanen suka chilli da ita kaman kwallo wannan ya wula ma wancan. Sai dai ko ta kansu ba tayi, wurin yaran ta tayi gadan gadan. Sai dai Ina, ba hali hakan. Wani irin ihu Mai dishi irin na muryan jarirai ke tashi, tun Suna kuka har kukan ya Kau. Ba abinda ya rage sai zallan jinin da ke kwarara a wurin.

   

  Hafsah fa? A hankali take jin komai na jikin ta na zarewa, dabas a kasa bata ganin gaba balle bayan ta. Duhu ya mamaye komai na rayuwan ta, ko kwakwaran motsi ta kasa. Zuwa can ta saki wani firgitaccen dariya, sai ta fara motsi da kanta gefe da gefe tana sakin wani sauti da ya fi kama da na tababbiya.

   

  Yan wurin duk rufe idanu su kayi suna jin wani masifaffan zafi na ratsa zukatan su. Suna ji kaman suyi hauka, suna jin komai na rayuwan na gushe musu. Madinan kam wani irin bugawa zuciyan ta keyi hade wani zafi da ba jin shi take ba. Ta karfi take buga saitin zuciyan kafin ta silale kasa take ba wani alaman numfashi a tare da ita.

   

  ...

   

  Khalid suna gama waya dashi ya tattara duk wani kudadden shi da yake da, duk abinda ya tara a rayuwan shi. Kasancewar shi Dan kasuwa. Super market gare shi sai motocin da ya ke saidawa wanda duk mahaifin shi ya daura shi akan su.

   

  Yana da niyyan fita ne yayi shawaran gayawa ma mahaifin sa abinda ake ciki, shi ya turasasa sai da aka sanar ma yan sandan. Bai so hakan ba, yana tsoron abinda zai haifar amma ba yanda ya iya da mahaifin shi, tilas ya bi umurnin shi bayan yaki sauraron duk wani kuka da ihu nashi. Haka suka hada plan, yaje ya ajiye musu kudin. Bayan ya ajiye daya daga cikin su yazo daukan kudin, police su kayi kanshi. Tun kafin su iso ya hango su don haka yayi ta rayuwar shi. Da kyar da sudin goshi ya sha, bayan uban ciwukan da ya sha. Abinda ya harzuka maigidan nasu kenan har ya hallaka yaran da basu ji ba basu gani. Yaran da ko awa uku masu kyau basu yi ba a duniya. Taya ya iya kallon uwar da ta dauki cikin wata tara, rashin bacci da ciwuka da basu kirguwa, ya iya kallon wahalan nakudan da aka tabbatar da rabin kafa na lahira lokacin da ake yin su. Duk ya share wadannan ya aikata wannan mummunar bala'i kan yaran da ta zubda jini da komai na rayuwan ta wurin kawo su duniya. A gaban idon ta, tana kallo, mutanen duniya na kallo. Ba ko dar, ba tashin hankali kuma ace karshen shi zai yi kyau? Kuma ace zai cigaba da rayuwa a duniya yaci ya sha. Ta ya zai iya bacci? Taya zai samu natsuwa? Taya komai zai gushe a ransu? Bayan wadanda aka yi a gaban su ba zasu taba samun daman hakan ba duk da dai ance lokacin ka iya canja komai.

   

  Khalid da bai san me ake ciki ba yana can ya rasa natsuwan shi, yana can ya rasa ina zai sa kanshi. Yayi zugum yana jiran ikon Ubangijin sa. A lokacin sai ga wayan su, jiki na rawa ya dauka. "Ka shirya ganin gawan matan ka?"

   

  "Aa Dan Allah Kar ku kashe ta" ko ina na jikin shi rawa yake, sai gumi da ya hada nan take, yana jin kanshi na wani irin juyawa.

   

  "Ka aiko mana da kudin da muka bukata a bayan gidan man Amana da ya kone a dajin Bwari. In ka kara taho mana da police, za shafe babin matar ka a doron kasa sannan kai kanka baza mu kyale ka ba."

   

  Cikin kidima ya fara basu hakuri. Wani irin dariya aka kwashe mai da "Muna jiran ka nan da awa biyu dai dai." Kit, aka kashe wayan.

   

  Jiki na rawa ya dau key in motan. Kudaden ya dauka sannan ya tada motan shi cikin masifaffan tsananin gudu ya nufi wurin da suka gaya mai. Kafin ma awa biyun ya cika ya isa wurin, ya fiddo kudaden ya ajiye. Yana mai cike da tsoron abinda zai afku gaba.

   

  Zuwa can suka kira shi suka gaya mai yana iya tafiya. "Ka dawo karfe takwas na dare ka dauki matan ka a gun." Suna fadin haka suka kashe wayan. Ya shiga mota ya tafi. Kasa komawa cikin Abuja yayi, ya samu wuri a cikin Bwari yayi parking yana ambaton sunan Allah a ranshi. Idanun shi duk sun kumbura, bugun gaban shi na dada faduwa. Yana tsoron a wani hali Hafsa take ciki a yanzu. Yana tsoron nakuda yazo mata basu isa asibiti ba, yana gudun mai zai faru inda hakan ya taso. Tuno dacewa zai samu rabo ya sa shi sakin wani irin murmushi duk zafin da yake ji na zagaye rayuwar shi. Bai san ashe mai afkuwa ya riga da da ya faru ba. Kaddara ta riga fata. Rayuwa na shirin juya mishi ta yanda bai zata ba.

   

  ...

   

  An samu sa'an daidaituwan numfashin Daddy don haka aka basu sallama wanda shi da kanshi ya matsa. "Ya labarin Madina? Meke faruwa? An ganta? Wani abu ya same ta? Ba zan ragawa duk wanda yayi sanadiyyan wani abu ya taba rayuwar ta ba." Maganganun dake bakin shi kenan tunda ya fito daga asibitin.

   

  Kan Abdulhamid a kasa ya sanar mishi da yanda su kayi da police in da ya samu. Ya kuma Kai maganan duk Inda ya dace. Girgiza kai yayi yana jin kanshi na wani irin juyawa. "Ba zan iya zama ba Abdul, ina bukatan ganin Madina. Ba zan iya hango yanayin da take ciki ba. I need to save her." Shiru ne ya ratsa falon nashi.

   

  Dai dai lokacin Kuma sallaman Professor Maryama Ahmadu ya karade falon tare da dan'uwan ta Engr Yusuf Ahmadu. Idanuwan ta duk sun kumburo, yanayin kayan da ke jikin ta ma zaka san ba lafiya ba. Sai zare idanu take, da suka cika fal da tsoro. Tsoron makoman da yarta ke ciki.

   

  Ba ta iya gaishe su ba bayan sallaman da karfin hali ya sata furtawa. "Ina Madina take? Ina yata?" Ta fadi maganan cikin halin na daburta. Ko zama ta kasa yi, idanu a zare kawai take bin Alhaji Sa'adu Ali, Mami da Abdul da kallo.

   

  "Maryama zaune muyi magana" Yayan nata da suka shigo tare ya furta. Bata iya tabi umurnin shi ba. Kallon su kawai take tana son karanto abinda ke fuskan su, duk da tsoron abinda zata karanto in da ya mamaye dukannin ta.

   

  Tilas, shi Engr in ya zauna suka gaisa da Alhaji Sa'adu. Wanda kana gani kasan yana jin jiki ga kuma rudani da ya mamaye shi. "Tun shekaranjiya da aka tabbatar min da Madina hanyan Abuja tabi a titi bansan inda kaina yake ba Engr, nayi takaicin kasancewa na a haka har kwana biyu ba tare da sanin ya rayuwan Madina yake ba a yanzu."

   

  "Titi? Titin Abuja to Kaduna fa kace. Taya za a bar min yarinya tabi wannan hanyan? Hanyan da a kullum kwanan duniya aka daina fadin wani abun alkhairi akan shi. Hanyan da a kullum ake salwantar da rayukan al'umma ba tare da wani ko wata yayi wani abu kan hakan ba." Fuskan ta Shabe shabe da hawaye.  Tana jin yanda saitin zuciyan ta ke bugawa. Iskan da take shaka ne take ji ya mata kadan. ji take kaman iskan ya gauraye da na mutanen falon kuma s“una yunkurin tafiya da nata. Zata tuna lokacin da ta fara jin haka, lokaci ne da matan da ke zaune a falon ta yiwa rayuwan su katsalanda. Don haka tayi saurin barin falon ko zata samu wani iska na daban da zai taimaka mata wurin binciko yarta. Engr Yusuf ya daga murya yana kiran ta amma ko waiwaye ba tayi ba.

   

  Cikin kuna Daddy ya kalli Mami da ke gefe "Ba kimin adalci ba Khadija, ba ki kyauta min ba tun farko da kika bar Madina ta bar gidan nan ba tare da kinsan yanda zata tafi ba. Dan ba yarki bace?"

   

  Wani irin zafi taji ya hade Mata da maganganun ga karin ganin Professor a wurin tana cin karenta babu babbaka. Yanda ya kasa tanka ma duk maganganun ta.

   

  "Ya isa Ya isa hakanan. Ya zaka dinga daura min laifin da ban san shi ba. Ya zaka dinga danganta ni da abinda banda hadi dashi. Ni na isa hana Madina abu ne ta hanu? Na isa in dakatar da ita? Ko angaya maka ta dauke ni da darajan Nan ne? Ba cin kashin da ban gani ba akan Madina, ba irin wulakancin da ban gani ba. Wlh na gaji ba zan iya dauka ba kuma. Yarinya sai kace gwal, ni na kamata? Ko ni na dauke ta?" Wani irin sanyi mai iska taji yana shigan ta bayan ta dasa aya a maganan ta. Magana ne da ta jima tana son fitar dashi. Sai dai Kash, ba ta san hakan mafarin matsalan ta bane. Bata san haka zai zamo silan budewan wani shafi mai wuya a rayuwan ta ba. Sai da ta juyo kunnuwan ta suna sauraro mata muryan Alhaji Sa'adu "Ni kike fadawa haka? Diyata kike danganta da rashin tarbiyya? Ba zaki iya ba ko? To ba matsala kije na sauwake miki sauran igiyan da ya rage miki. na sake ki khadija."

   

  A zabure Abdulhamid ya dago idanuwan shi ya sauke su jan Daddy. Daidai lokacin Kuma Engr Yusuf ya shigo rike da hannun Professor, zancen ya ratsa kunnuwan su. Duk da hawayen da ke idanun Professor Maryama bai hana ta jin saukan zancen kaman aradu ba.

   

  "Subhannallahi Alhaji lafiya da hankalin ka?" Engr Yusuf ya fada yana kallon yanayin shi. Gabadaya jikin shi rawa yake, idanun nan sunyi jawur sai wani irin numfashi da yake fitarwa da zafi da zafi. Ganin haka yasa Abdulhamid yayi saurin kamo shi ya zaunar dashi.

   

  Mami kuwa wani irin shock ne ya fara ziyartan ta. Kafin ilahirin abinda ya faru ya gama zagaye kanta. Kwakwaran motsi ta kasa, hatta Yanan yatsun ta rawa yake yi. Rayuwan ta a gidan da Madina ya fara kuma dashi ya zo karshe. Zafi zuciyan ta ke mata, sai da ta samu sakin wani irin wahaltaccen numfashi tukunna hawaye suka fara zirara daga idanuwan ta. Ba abinda bata ji ba, ba abinda bata gani ba ganin idon ta wurin Alhaji Sa'adu kan tilon diyar shi da ya daura ma soyayyan duniya. Ta koyi taya shi son Madinan, sai dai hakan ma bai tseratar da ita ba. Nata yaran kaman ba ya' ya' ba. Iya gwargwado yana nuna iyawan shi amma sam bai iya boye hakan. Haka ta haifi Amal, ya sa ma maman Madinan mai Suna. Ita kam tayi dana sani mara amfani, tayi dana sanin kutso rayuwan su a rayuwan ta bakidaya.

   

  "Ki shiga cikin gida. Zamu yi magana." Engr Yusuf ne ya fadi haka don son bata baki. Ita dai Prof ko kallon ta ba tayi ba. In an bar ta ma tashin hankalin da take ciki ya ninka na Khadijan. Ganin yanayin ta yasa Abdulhamid saurin shiga gidan ya kira Adnan yazo ya rike hannun mahaifiyar shi. Wani irin duba na takaici ya aika ma Daddy kafin ya ja ta suka tafi ba tare da ya tanka kowa ba.

   

  Engr ne ya dage suka tattauna yanda za a bullo ma abun bayan ya fahimtar da su maganganu da sa'insa ba zasu fidda Madina ba. "Ya kamata a samo information wurin family in sauran da aka ce an kamasu ranar a hanyan Kadunan, hopefully sai mu samu wani news. Maybe ko su sun kira su or something else."

   

  Duk a take suka yi na'am da shawaran shi. Wayan Abdulhamid ne yayi kara, yana ganin numban da ke neman shi yaji kirjin shi na wani irin dokawa. Haka yaja gefe domin amsa wayan. Commissioner of police ne kai tsaye yace mishi "Bansan ko labarin da zan baka zai taimaka ba. An kira Khalid Kurfi, Shima matar shi na cikin wanda aka kama a ranar. Sun bukaci kudi, yaje kai musu muka bisu sai dai sunyi escaping." Rasa abun cewa yayi bayan ya gama sauraro. A abinda ya gaya mishi, ba inda ya sanar mishi an tabbatar Madina na wurin ko bata Nan. Rudani ma ya Kara sasu, in har Madina na tare da wacce ake fadi. Shin meyesa aka kira Yan uwan ta ita Madinan ba a nemi nata ba? Godiya ya mishi kawai ya kashe wayan. Ko da ya koma ba Wanda ya iya fada ma abinda ake ciki sanin ba zai wani amfane su da komai ba. Yayi bakin cikin sanin cewa aikin su bai basu daman zuwa neman Yan ta'ada inda suke ba. Shi aikin su bincike ne, Kuma bincike ma ta zagon kasa so ba ta yanda za suyi katsalandan abinda bai shafe su ba. Dole dai sai anbi ta hanyan Yan sandan.

   

  Basu wani dadewan kirki ba suka bar falon. Kai tsaye wannan karon wurin Inspection general of police gabadaya suka nufa. Sanin irin kusancin da me tsakanin shi da Abban su yasa Abdulhamid Kiran Abban ya shaida mishi. Abban ya tabbatar mishi zai nufi can in a yanzu.

Comments

2 comments