Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » DAMA SUN FAƊA MINI 01

DAMA SUN FAƊA MINI 01


 • MABUƊI


  Kalmar sila wata kalma ce da Bahaushe yake amfani da ita don nuna sanadi ko dalilin samuwar wani abu. A wasu ararrun kalmomin na shi, yana iya cewa maƙasudi ko musabbabi, wanda duk suna nufin abu ɗaya ne da sila. Sila takan zamo ta fuska-fuska, kamar yadda silar samuwar labarin 'Dama sun faɗa min' ta zamana dalilin zaman majalisa irin na al'ada ta matasa, wanda kuma taurarin cikinsa ba wasu  ba ne face ƙungiyar asirin da suke yi wa amaryar wata takwas Zainab barazanar hallaka duk abin da zata haifa, Zainab wacce take zargin mijinta Aliyu da zama ɗan ƙungiyar asirin da ya bayar da abin da zata haifa ga ƙungiyar tasu, Aliyu wanda shi kuma ya fitittike cewa shi ba ɗan ƙungiyar asiri ba ne, sai iyayen Zainab da suka maka Aliyu a kotu cewa 'yarsu ba zata zauna da ɗan shan jini ba, da kuma Alƙali da muƙarrabansa da mu kanmu 'yan kallo wanda da mu aka kawo ƙarshen tirka-tirkar.
  Sai dai kafin mu kai ga wancan labarin na ƙungiyar asiri, ku fara ɗora mutum na farko da ya fara taka rawa a cikin namu labarin a kan majigin tunaninku. Wani abokinmu ne Gali, wanda mutum ne mai yawan barkwanci. Irin mutanan nan ne da komai nasu ma abin dariya ne, ga shi da shegen baccin tsiya kamar manjan sanyi. Babu dama ya zauna yanzu sai ka ga ya kama bacci.
  Hausawa suka ce 'A san mutum a kan cinikinsa,' to shi ma Gali da cinikin nasa ya saƙa nasa zaren a cikin labarin, baccin na shi dai ya fara daga zamansa a majalisar kamar dai yadda ya saba. A cikin baccin ne kuma bayan 'yan daƙiƙu aka tsinkaye shi yana tona wasu sirrika na shi da matarsa, don haka babu shiri don gudun kada ya gama feɗewa kan shi rigar mutunci guda cikin abokan namu da ake kira da 'Bashir ɗan kimiyya' scientist's ya doke shi a cinya.
  "Tashi malam 'Dendroaspis polylepis' kar ka yi mana shaɓaɓa a nan." Cewar Bashir daidai lokacin da aka sheƙe da dariya gaba ɗaya. Shi kuwa gogan bayan ya yi firgigit ya farka yana ƙoƙarin goge yawun baccin da ya fara gangaro masa ya   amsa.
  "Wani sunan kuma yau aka canza min da yaren nasara aka bar kasa sarkin bacci?" Jin haka cike da mamaki Bashir ya amsa masa.
  "Au ashe ka ji abin da na ce kenan? To ba suna na sauya maka ba, sunan macijin kasa kenan a kimiyyance. Don haka malam kasa sarkin bacci ka dena faɗar sirrin gidanka a kwararo kana bacci."
  Cike da takaici yake kallonmu ya ce "Surutu nake ta yi muku ko?" Bai jira amsa ba ya ɗora.
  "Allah Ya yaye min wannan matsalar dai kawai! Amma a ce babu dama mutum ya kwanta bacci sai ya yi ta yin surutai marasa kan gado." Da ajiye zancen nasa da kuma ajiyar zuciyar da na yi duk sun faru ne kusan lokaci ɗaya. Rana ta farko kenan da na ji ya ba ni tausayi, don kuwa wannan ba ƙaramar matsala ba ce ga wanda Allah Ya jarabta.
  Daga can gefe na ji Musa yana bada labarin irin matsalolin da hakan yake haifarwa, sanadin da ya sa Bashir ɗan kimiyya ya sake yin farat.
  "Aikuwa kamar a haska duhu da lantarki haka ka hasko min wani rikici da ake tsaka da yin shi a kotu 'mai sunan ayaba '." Bashir ya yi maganar yana kallon Musa wanda shi yake cewa 'mai sunan ayaba' kasancewar farkon sunan ayaba kenan a kimiyyance wato 'Musa sp '.
  "Na je kallon rikicin tun wancan satin ina jira na koma wani satin naga yadda zata kaya kamar yadda Alƙalin ya ce zai ci gaba da sauraron ƙarar. Sai da ka yi magana ka ankarar da ni ashe fa kusan matsala ɗaya ce ta haifar da shi, ga shi aure yana shirin mutuwa a sanadinsa. Bama mutuwar auren ba kaɗai tana iya yuwuwa a yankewa wanda ya yi shaɓaɓar hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai." Gaba ɗayanmu muka watsa masa kadarar mujiyarmu, zuciyata cike da mamakin yadda za a yankewa mutum hukuncin kisa kawai don ya yi magana a mafarki. Aikuwa kamar kunnen da ya buƙaci susa haka na ji zuciyata tana muradin labarin, don haka da hanzarina na sake buƙatar ƙarin haske.
  "Aikuwa ya kamata mu ji yadda aka yi aka haihu a ragaya! Ta yaya za a ce an yanke wa mutum hukuncin kisa kawai don ya yi zance a mafarki?" Na ƙare maganar ina kallon shi kamar yadda na ga duk sauran yan majalisar suma suna kallon shi. Kamar dama jira yake yi na rufe baki ya ɗora maganar.
  "Aikuwa ka dena mamaki, don kuwa shi wanda ake zargin abokinmu ne, ajinmu ɗaya da shi a makaranta..."
  "To muna jinka, bamu labari." Na yi saurin tarar numfashinsa. Yayin da shima ya fara magana da cewa:-  BABI NA FARKO
  °°Dama sun faɗa min°°

  Kamar yadda Zainab matar wanda ya yi shaɓaɓar take bayar da labari, cewa ta yi 'yan ƙungiyar asiri ne suke ta yi mata gizo da barazanar cewa sai sun shanye jinin duk abin da zata haifa, wanda kuma kai tsaye mijin nata ya nuna mata yana da masaniya a kan su.
  Rana ta farko da suka fara yi mata barazanar wai a cikin asibiti ne bayan ta fito daga ganin likita zata koma gida, tana tafe sai take jin kamar tafiya a bayanta. Tana waigawa kuwa suka yi ido huɗu da wani mutum mai mummunar halitta da yasa 'yar autar hantar cikinta ta kaɗa. Babu shiri ta kautar da kanta gami da ƙara sauri tana yi tana waige.
  Me zai faru? Ai tana ɗaga kai ta kalli gabanta bayan ta ji motsin tahowar wani ta gaban nata ta hangi wani irin mummunan mutumin da ke bayanta, don haka babu shiri ta sauya akalar tafiyarta zuwa ɓarin hagunta. Sai dai bata ci wani dogon zango ba taga kamar an jefo mata wani a gabanta, wannan karon ma bakinsa har dalalar da jini yake yi.
  Cikin tsananin firgici da matsanancin bugun zuci ta ja da baya turus bayan ta rusa kururuwa da nufin ta jawo hankalin jama'a kanta ko za a samu wanda zai kawo mata ɗauki. Sai dai kuma abin da ya sake firgita ta shi ne gani da ta yi gaba ɗaya jama'ar cikin asibitin sun rikiɗe mata sun koma dodonni. Kowa ta gani yana sanye da wata jar riga mai kama da alkyabba sai dai ba alkyabba ba ce, daga bayan rigar tana sharar ƙasa da kwatan-kwacin yadi uku, yayin da gabanta iya cibiyarsu take. Idan har bata manta ba ta taɓa jin wata ƙawarta na cewa irin rigar shaiɗan kenan. Launin rigar ja ne irin ja na jini, sannan akwai hoton baƙin ƙadangare an yi wani ɗan rubutu mai kama da watsal-tsalan yara a ƙasan ƙadangaren daga bayan rigar.
  Suna tahowa inda take suna kiran sunanta da wata irin murya mai ban tsoro. Kamar yadda ƙudaje ke bin mushen da ke fitar da turirin wari haka suke bin hangamammen bakinsu mai haƙora cako-cako da zasu yi saurin tuno maka da bakin manjagara ko tarko. Wani irin baƙin jini yana dalala daga bakin nasu babu kyan gani, duk ya ɓata musu ilahirin jikinsu tun daga kan wuya har ƙirjinsu irin yadda yaro mai timbiɗi ko yoyon baki kan yi da gaban rigarsa.
  "Zainaaaaaab.! Zainaaaaaaab.!! Zainaaaaaaab.!!!... Sai kin ba mu ɗan da ke cikinkiiii..." Maganar su ta fizgi hankalinta gami da sake dugutsuma tunaninta, sai a lokacin taga ashe gaf suke da ƙarasowa inda take suna masu ɗaga hannayensu masu ɗauke da farata cakar-cakar kamar takobi.
  "Ki gudu kada su hallakaki." Wani shashi na zuciyarta ya bata shawarar da ba ta yi wani dogon tunani ba ta karɓeta ta hanyar fakar numfashinsu ta runtuma a guje ta ɓarin damanta da taga 'yar faraga, tuni ta manta da batun tsohon cikin da ke jikinta haihuwar yau ko gobe.
  Sai dai hakan da ta yi shi ya ƙara ta'azzara mata lamarin, don kuwa zama ya yi kamar a tsokani kare a gudu, yadda karen zai bi mutum haka suma suka rufa mata baya kamar ƙurar mota a cikin babbar farfajiyar asibitin da taga ya rikiɗe ya koma fili fetal kamar dokar daji, suna tafe suna wani irin ƙara mai kama da ƙaran faifan injin markaɗe.
  Firgicinta ya daɗu ne lokacin da ta tabbatar da tazararsu da ita baifi tazarar da ke tsakanin liman da mamu ba, bugu da ƙari a lokacin ta gama gajiya babu abin da ta ke yi sai haki kamar wacce ranta zai fita, a ɓangare guda kuma hannunta na tallafe da tsohon cikinta da ta ji yana barazanar faɗowa don ciwo. Hakan ne ya tilasta mata rage gudun, tana yi tana waigensu gaf da ita sanadin da ya sa ba zato ba tsammani ta yi turuuusss...! Ta faɗi a cikin fasassun kwalaben magani da allurai tana tsala ihun kiran Muradinta ko zai taimaka mata. Duk da haka cikin tsananin ƙarfin hali ta sakeyin yunƙuri da niyyar ta tashi amma ina cikinta ya ce bai san zancen ba, lokaci guda kuma ta ji mararta tana wani irin ɗaurewa kamar zata fashe.
  Su kuwa dodonnin mutanen sai suka ɗauka da shewa cikin wani irin sauti mara daɗin ji, suna wani irin tanɗar baki irin na raƙumin da yaga ruwan jiƙaƙƙiyar kanwa, kana suna tunkararta kamar masu shirin daka mata wawa. Ganin haka yasa ta tattaro duka ƙwarin gwiwarta ta ci gaba da jan jiki da baya da baya don ganin ta guje musu, sai dai bata yi wani dogon zango ba bayanta ya ci karo da wani abu da ta fi kyautata zaton bishiya ce. Saɓanin tunaninta tana waigawa ta ga ashe ƙafar wani dodon ne wanda duk ya fi sauran dodonnin mutanen girma da muni.
  Ta sake tsandara ihu ta yi tsalle irin na sufurin ta dira a tsakiyarsu tana waige-waige da yi musu magiyar kada su cutar da ita. Aikuwa kamar busar sarewa haka magiyar ta zama, gani ta yi ma kamar ƙara zuga su take yi. Don haka kawai sai ta saduda ta rufe ido tare da dunƙulewa tana shirin jin saukan takubban faratansu.
  A dai dai wannan lokacin shassheƙar kukanta ya tsananta ta yadda har ya farkar da mijinta da suke kwance ya fara taɓa ta zai tashe ta yana tambayar ta ko lafiya take kuka. Ai kuwa tana farkawa ta tsandara ihu gami da ƙanƙame ɗan matashin mijin nata.
  "Mene ne? Me ya faru?" Ya shiga tambayarta a kiɗime kamar yadda itama take ba shi amsar a kiɗime tana waige-waige.
  "Bi..bi...biyo ni suka yi za su kashe ni." Jin haka ya ƙara jawo firgitacciyar matar tashi jikinsa bayan ya fahimci mafarki ta yi. Don haka sai ya fara yi mata addu'o'i yana tofa mata yayin da ita kuma take maƙale da shi kamar zata shige jikinsa, fuskarta ta haɗa gumi sharkaf kamar sabuwar kuturwa. Bai daina addu'ar yana shafa bayanta ba har sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ta dawo cikin hayyacinta ta nutsu sosai sannan ya tambayeta abin da ya faru.  Nan take ta kwashe labarin mafarkin nata gaba ɗaya na ganin dodonnin mutanen da ta yi da kuma ce mata da suka yi wai sai ta ba su ɗan cikinta sun sha jinin shi.
  Jin haka ya yi shiru alamun damuwa suka bayyana ƙarara a kan majigin fuskar shi, tuni ma ya saki matar tashi ya miƙe tsaye ya fara safa da marwa a cikin yalwataccen ɗakin nasu mai dishi-dishin hasken lantarki na bacci.
  "Murad.! Me ya faru?" Zainab ta tambaye shi tana mai ƙara yin nazarin shi ganin yadda a cikin ƙanƙanin lokaci yanayin shi ya sauya. "Dama sun faɗa min" ya ambata hakan dai dai lokacin da ya goya hannayen shi a baya da alamar ƙololuwar damuwa a tare da shi.
  "Dama sun fada maka?" Zainab ta maimaita furucin na shi ƙasa-ƙasa.
  "Su waye suka faɗa maka? Kuma me suka faɗa maka?" Ta yi mishi tambayar da ta dawo da shi hayyacinsa ya yi firgigit kamar ya tashi daga bacci, sai a sannan ya fahimci ya yi suɓutar baki zancen zuci ya fito fili, kamar yadda ita ma Zainab ɗin sai a lokacin ta gane cewa bai san lokacin da ya ce 'Dama sun faɗa min' ɗin ba.

  \u00a9Jibrin Adamu Jibrin Rano.

  A saurari cigaban labarin, ga mai buƙatar ducument na labarin za a ba shi a N300 kacal.
  Domin ƙarin bayani 08132505026

Comments

3 comments