Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Dabarun rubutun labari 6: Muhimmancin bincike wajen gina labari

Dabarun rubutun labari 6: Muhimmancin bincike wajen gina labari

 • Assalamu alaikum warahmatuLLAHI ta'ala wa barakatuhu. A maƙalar da ta gabata mun tsaya ne a kan yadda ake samar da ganɗoki a labari, inda muka yi bayani sosai muka kawo misalan irin yadda ake samar da ganɗoki (wato zaƙuwa da son jin cigaban labari). A wannan maƙala insha Allahu za mu tattauna ne a kan baɗoki, sannan daga bisani mu kawo muku bayani akan muhimmancin bincike wajen gina labari.

  Kamar yadda na faɗa tun a waccan maƙalar, baɗoki kishiyar ganɗoki ne. A ganɗoki murna da zaƙuwa makaranci yake yi ya ji abin da zai faru a gaba, amma a baɗoki fargabar da tsoron abin da zai iya faruwar ne suke fusgar manazarcin labarin. Za mu fi fahimtar darasin idan aka bayar da misali, don haka zan sake buɗewa da wani misalin a cikin labarina Kukan Jini.

  Kukan Jini

  A cikin jerin irin ni'imtattun ranakun nan ne kyawawa da ke ƙayace da ni'imar daddaɗar iska mai kaɗawa haɗe da wani irin ƙamshin ƙasa mai daɗi, da yake ba a daɗe da fara yayyafi ba aka ɗauke. Sai dai duk da haka garin akwai alamar hadarin da ke nuni da za'a iya yin ruwa a kowanne lokaci.

  Yamma ta fara yi wajen misalin ƙarfe huɗu da rabi zuwa biyar, har na fara harhaɗa kayana da niyyar na rufe shagon nawa na tafi gida, don kuwa na san tunda har hadarin nan ya taso ba zai bar mutane su sake da garin ba. Ba lallai ba ne ma a ƙara yin ciniki, duba da yadda jama'a sai ficewa suke yi daga cikin kasuwar cikin sauri-sauri, kowa ƙoƙari yake yi ya isa gida kada ruwan nan ya tare shi a waje.

  A daidai lokacin ne kuma ta shigo mini cikin rumfar shago da gudu-gudu cikin alamar ruɗu da firgici kamar wata wacce ta ga mutuwa, haka kuma cikin ƙarfin  hali ba tare da jiran komai ko neman izinina ba ta shige can cikin shagon tana magana mai gauraye da haki.

  "Malam don Allah ka rufa mini asiri ka taimaka mini." Tuni kuma ta samu bayan wata ƙatuwar akwati cikin tarin akwatunan sayarwar da ke shagon ta ɓuya ba tare da jiran abin da zan ce ba.

  Gabaɗaya sai ta ba ni mamaki ta kuma ɗaure mini kai, lokaci guda kuma zuciyata ta fara ɗarsa mini lallai ba ta da gaskiya, don haka ne na buɗi baki zan yi mata magana amma ganin taron wasu ƙartin da suka ci burki a ƙofar shagon nawa suna wani haki da waige-waige ya hana  ni, don kuwa zuciyata tana raya mini ita suka biyo, kuma ga dukkan alamu idan har suka kama ta ba za ta ji da daɗi ba. To amma kuma me zai sa su biyo ta? Don kuwa kwata-kwata ba ta yi mini kama da mara gaskiya ba.

  Daga inda nake a tsaye ina iya jin muryar ɗaya cikin su yana tambayar mutum biyun da suka riga shi zuwa wurin.

  "Ina ta yi? Kun gan ta kuwa?" Wanda aka tambaya ɗin ya ba shi amsa.

  "Wallahi ba mu gan ta ba, amma na tabbata wani shagon ta shiga a nan. Don haka yana da kyau mu duba sosai." Ƙarƙare kalaman nasa sai ya sa na ji gabana yana faɗuwa sai ka ce wanda shi za'a kama, ni da ko laifin da ta yi musu ma ban sani ba. Na yi saurin mayar da fitilun idanuwana cikin shagon, watak'ila kuma hakan yana da nasaba da son ƙara gani ko ta samu kyakkyawar maɓoya inda ba za a gan ta ba kada ta jaza mini masifa.

  Aikuwa ina juyawa muka yi ido biyu da ragowar gefen gyalenta da bai gama ɓuya ba, na san duk wanda ya nufo shagon tun daga nesa zai iya hango ta. Don haka ne na sake juyawa wajen ƙartin don ganin ko sun wuce, sanadin da ya sa na ji gabana ya sake faɗuwa sakamakon gani da na yi biyu cikin su sun nufo shagon nawa gabaɗaya.

  Irin yadda ɓarawon da ya bi hanyar da ba ta ɓullewa yake yin mutuwar tsaye, haka ni ma na sanƙare cikin rarraba ido kamar ɗan dokar da aka ba wa cin hanci a cikin mutane. Wanda ya fara yi mini magana wani garjeje ne baƙi firgita maza, cikin wata irin murya ta shi mara daɗi kamar an daki hujajjiyar ganka.

  "Malam ba ka ga wata 'yar iskar yarinya ba da wani farin gyale a jikinta, mun biyo ta kuma muna kyautata zaton wani shagon ta shigo a nan ta ɓuyar mana." Ya ƙare zancen yana mai gwararo mini jajayen idanuwan shi masu kama da na soja a filin daga..."

  A lokacin da mai karatu ya zo ƙarshen wannan shafi, cike da fargaba ko tunanin "Anya kuwa ƙartin ba za su ga yarinyar ba tunda dai ta bar gefen gyalenta a waje? Ko kuwa ba za su gan ta ba? Idan sun gan ta to me za su yi mata kenan da suka biyo ta da gudu haka? Shin me ma ta yi musu?" Zai buɗe shafin gaba ne zuciyarsa cike da tarin irin waɗannan tambayoyi na fargaba, waɗanda suke gauraye da sanya zumuɗin jin amsarsu a gaba, to ire-iren wannan salon shi ake kira Baɗoki.

  A daidai wannan gaɓar kuma muka kawo ƙarshen Dabarun gina farkon labari, sai dai kuma kafin mu tafi zuwa gaɓa ta gaba wato Dabarun gina doron labari (tsakiya), akwai wasu muhimman gaɓoɓi da muka tsallake waɗanda suke da buƙatar mu yi musu komayya.

  Bayan mallakar jigo a rubutu, abubuwa muhimmai na gaba da marubuci zai yi shi ne:

  • Bincike don gina labari
  • Irin salon da za'a gina labarin

  Bincike don gina labari

  Kamar yadda muka sani bincike wata hanya ce da ake bi wajen neman sanin abin da ba a sani ba, ko kuma ƙara wa kai sani akan abin da ba a yi masa sani na haƙiƙa ba.

  Bincike don gina labari ya ƙunshi duk wasu bayanai da marubuci zai tattaro ya tsara su ya yi amfani da su wajen gina labarin. Dolen kowanne marubuci ne ya riƙa yawaita bincike a kan dukkan abin da yake rubutawa, idan kuwa ba haka ba to tabbas zai yi danbarwa. Marubuci ya riƙa sakawa a ransa cewa rubutun da zai yi rubutu ne da kowa zai iya karantawa tun daga kan mai'ilimi da jahili, babba da kuma yaro, malamai da ɗalibai, idan kuwa haka ne dolen shi ne duk abin da zai rubuta ya tabbatar daidai ya rubuta.

  Mutunci, ƙima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a ƙasa wanwar a duk lokacin da ya tafka wani gingimemen kuskure yake kuma da'awar daidai ya yi a cikin labarinsa. Kowa ya san marubuci ba likita ba ne amma kuma idan wani marubucin ya yi maka rubutu a kan aikin likita sai ka ɗauka wani shugaban likitocin duniya ne saboda tsabar binciken da ya yi wajen rubutun nasa, don haka ko likita ne ya karanta labarin ba zai taɓa ganin makusa ba a rubutun balle har ya kushe masa.

  Na taɓa faɗa a wata tattaunawa da aka yi da ni cewa akwai wata marubuciya da ta taɓa yin rubutu a kan shari'a, rubutun nata ya samu karɓuwa sosai musamman a wurin mata, sai dai kuma ga duk wanda ya san ilimin shari'a ba zai taɓa ɗaukar littafin da daraja ba, don kuwa rashin bincike ya sa ta yi wa doka karantsaye, shi kansa tauraron littafin ta saka shi ya aikata laifin da hukuncinsa shi ne kisa kai tsaye a musulunce da kuma tsarin doka irin ta kundin ƙasa.

  Amma saboda rashin bincike ta wanke tauraron da molanka ba tare da ta kashe shi ba, wanda hakan kuskure ne, don kuwa tana nuna wa masu karatu su ma su je su aikata irin wannan laifin ba za'a kashe su ba, za'a yi musa hukunci irin na tauraron labarinta.

  Kuna iya karanta wannan maƙala da ta yi sharhi akan gudanar da bincike yayin rubuta labari.

  Kamar yadda na faɗa marubuci zai iya zama likita da zai faɗa wa jama'arsa cuta da kuma maganin ta, marubuci zai iya zama malami da zai faɗa wa jama'arsa abin da Allah Yake so da wanda ba Ya so, marubuci zai iya zama Alƙali da zai sanar da jama'a doka da laifuffuka ya kuma sanar da su hukuncin kowanne laifi ta yadda zai zamana darasi ga wanda yake tunanin aikatawa ya fasa kada shi ma a yi masa irin hukuncin da aka yi wa tauraron labarin marubucin. Sai dai fa duk hakan zata faru ne idan marubucin ya yi bincike.

  Ta hanyar bincike ne marubuci zai zama shakundum, ya zama komai da ruwanka ta yadda zai iya yin rubutu a kowanne fanni kuma rubutun ya ƙayatar da duk wanda ya karanta.

  Hanyoyin yin bincike suna da yawa, kuma kowacce marubuci ya bi ta yi, to amma akwai manya-manyan hanyoyi guda uku da suke gaba da sauran waɗanda ya kamata mu tattauna a kan su yanzu.

  Tuntuɓar masana

  Hanya ta farko ita ce ta hanyar tuntuɓar wani masani a kan maudu'in da za ka yi rubu a kai, wannan hanyar ta fi kowacce hanya kai waye don kuwa a cikinta ba a fiya samun matsala ba tunda tattaunawa ce ta baki da baki, fuska da fuska, ka kuma tambayi duk abin da ya shige maka duhu. Idan kana so ka yi rubutu ne a kan shari'a to yana da kyau ka samu wani lauyan ko alk'ali ko kuma wani mai ilimi a kan shari'a ya yi maka bayani musamman ma akan wani hukunci da kake son yi a cikin labarin. Idan an yi tattaunawar ta waya ma hakan babu laifi.

  Idan a kan wani kasuwanci za ka yi rubutu a matsayinka na marubuci, yana da kyau ka samu irin wannan ɗan kasuwar ka samu ilimin hanyar kasuwancin a wurinsa, don gudun kada ka yi rubutun da duk wanda ya san irin wannan kasuwancin zai yi maka dariya da zarar ya karanta rubutun saboda kuskuren da ka tafka.

  Idan a asibiti ne ka nemi likita, idan a makaranta ne ka nemi malami ko lakcara, idan a kan tsaro ne ka nemi ɗan sanda da sauran jami'an tsaro, idan a kan tarihi ne ka nemi masanin tarihi ko tsoho da dai duk sauran wanda ka san rubutun naka ya shafe su.

  Nazarin littattafai

  Hanya ta biyu ita ce ta hanya bincikar wasu littattafai da suka shafi abin da za ka yi rubutunka a kai, ka duba duk wani muhimmin batu da kake so ka sani.

  Nema a yanargizo

  Hanya ta uku ita ce ta yin bincike a yanar gizo (Internet) ka nemi duk abin da kake nema, yawanci kuma wannan hanyar an fi yin amfani da ita idan ana son a yi bincike na gaggawa, ko kuma binciken wani wuri da ya yi maka nisa (kamar ƙasar waje), ko kuma binciken abubuwan da ba ka da sukunin mallakarsu.

  Yanayin sauyawar zamani ya sa wannan hanyar ta fi kowacce hanya sauƙi a duk hanyoyin yin bincike, domin kuwa ko nan Bakandamiya ta ishe mu abar misali. Dukkan waɗannan muƙalun tun daga jigon labari da duk sauran muhimman abubuwa da suka shafi Adabi idan marubuci ya bincika zai samu, ga shi kuma kullum ƙara ɗora sababbin abubuwa ake yi ta yadda za a ce kusan komai za a samu. Muhawara mai ma'ana wacce sai mutum ya share kwanaki yana tsarata ne idan shi zai rubuta, kawai zai sameta cikin sauƙi a shashin muhawara na Bakandamiya, banda sauran fannoni na ilimi sosai iri-iri.

  Shi ya sa a wurina ba zai zama uziri ba ga marubuci ya riƙa yin rubutu karazube babu bincike, domin kuwa duk wani ilimi da yake nema idan ya bincika zai samu.

  Zan rufe maƙalar tamu ta yau da maganar Nelson Mandela da ya ce "Ilimi shi ne makami mafi ƙarfi ko tasirin da za a yi amfani da shi a canza duniya." A ra'ayina marubuci shi ya fi kowa kusanci da wannan maganar, domin kuwa marubuci ne yake amfani da baiwa da iliminsa wajen canza wa duniya tunani ta hanyar rubuce-rubucensa, shi kuwa ilimi yana samuwa ne ta hanyar bincike, don haka yana da kyau mu riƙa yin bincike.

  Gyara, sharhi, ƙarin bayani ko tambaya ƙofa a buɗe take. 

  Sanna kuna iya karanta makala ta gaba da ta yi bincike akan salon bayar da labari.

  Jibrin Adamu Rano

  08132505026

Comments

0 comments