Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » Dabarun rubutun labari 11: Yadda ake zakulo sunan labari 1

Dabarun rubutun labari 11: Yadda ake zakulo sunan labari 1

 • Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuh! A maƙalar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan darsau na labari. Mun bayyana ma'anar ɗarsau da ire-irensa har ma da misalai, mun kuma faɗi muhimmanci ko amfanin sanya ɗarsau a labari. Yau insha Allahu za mu tattauna ne a kan alaƙar sunan labari da kuma shi labarin. Yana da kyau mu sani cewa sunan labari yana da matuƙar muhimmanci, don akwai labaran da dayawansu sunansu kaɗai yana iya sayar da su, don haka shi kansa suna a labari naƙaltarsa ake yi kamar yadda za mu yi yau insha Allah.

  Abin tambaya shi ne, shin mene ne alaƙar labari da kuma sunansa? Abu ɗaya ne ya haɗa alaƙar tasu, wato shi asalin jigon labarin. Abin da nake so na ce shi ne; marubuci yana samar da sunan labarinsa ne bisa la'akari da jigon cikin labarin. Amma kuma ana magana ne a kan babban jigon cikin labarin.

  Idan babban jigon na soyayya ne, to ana so shi ma sunan ya yi yanayi ko ya dace da soyayya, idan na ta'addanci ne ana so sunan ya yi yanayi da na ta'addanci, idan ma bincike ne ko tsaro, duk ana son wajen saka sunan labari marubuci ya kula da alaƙar sunan da jigon, don haka wasu marubutan sukan ɗauki jigo a matsayin abin jinginar sunan, wasu kuma sukan ɗauki sunan ya zama abin jinginar jigon. Mu muna magana ne a kan sunan labari, don haka za mu ɗauki suna ya zama abin jinginar jigo.

  Sunan labari aji nawa ne?

  Sunan labari iri biyu ne;

  • Suna Tahaƙiƙi;
  • Suna Jimla

  Duk wani sunan labari da za a samar dole yana ɗayan biyun nan ne, imma ya zama mai ɗauke da jigo tahaƙiƙi ko ya zama mai ɗauke da jigo jimla. To su ɗin me suke nufi?

  Suna Tahaƙiƙi: Shi ne sunan labarin da ba za a taba gane me labarin ya ƙunsa kai tsaye ta hanyar ji ko karanta sunan labarin ba, har sai mai karatu ya karanta labarin gabaɗaya zai iya ganewa. Irin wannan sunan yana da wasu fa'idoji da za mu duba wasu daga cikinsu yanzu insha Allahu.

  Daga cikin fa'idojin suna tahaƙiƙi akwai;

  1- Manazarci ba zai san me labarinka ya ƙunsa ba sai ya karanta. Hakan fa'ida ce sosai, saboda wataƙila jigon labarin naka a kan karuwanci ne, shi kuma wanda zai sayi labarin ko kuma aka ba shi labarin zai karanta ba ya son labarin karuwanci. Kun ga kenan idan tun a suna ya fahimci na karuwanci ne ka yi asararsa a cikin waɗanda za su karanta labarin. Amma idan bai fahimta ba ya saya ya fara karantawa wataƙila kana iya canza masa ra'ayi ya karanta labarin musamman idan ya zamana akwai jan hankali a cikinsa.

  2- Ɗan adam yana da wata ɗabi'a, da a ce za ka samo kaza ka yi mata jar suya ka sako ta a faranti ka kai wa baƙonka, idan za ka kai masa sai ka haɗa da tuwo miyar kuka a cikin mazubi rufaffe mai kyau. Idan ba sa'a ba kafin ya fara taɓa kazar sai ya faki ido ya fara buɗe mazubin ya ga mene ne a ciki, saboda zuciyar shi ba za ta taɓa samun nutsuwa ba. Zai ga kamar abin cikin mazubin zai iya fin naman kazar daɗi.

  To haka ma sunan labarin da ya bayyana me labarin zai ƙunsa da wanda bai bayyana ba suke, sau tari manazarci ya fi zaɓar sunan labarin da ya ji shi tahaƙiƙi. Ko alƙalin gasa ne idan ya fahimci inda labarinka ya dosa tun a sunansa, to ba lallai ba ne labarin ya yi masa bazata, saboda tun farko da ma ya riga ya saka ran abin da zai ji a cikinsa kenan. Amma idan suna tahaƙiƙi ne tun lokacin da ya ɗauki labarin yana karantawa, zai yi ta ƙoƙari ne ya ga ina labarin zai dosa. To irin haka ne idan marubuci ya ƙware sai ka ga ya tafi da tunaninsa gabaɗaya.

  Kamar yadda na faɗa sunan labari yana da matuƙar muhimmanci, don akwai labaran da dayawansu sunansu kaɗai yana iya sayar da su. Ga wasu a matsayin misali.

  • An Kashe Mutuwa: Sunan wani labari ne na A. A. Bature. Da muna tattaunawa da shi game da labarin ya ce akwai wanda sunan labarin kawai ya ji ya ce zai ɗauki nauyin buga shi.
  • Tamanin Da Tara (89): Shin me hakan ke nufi kamar a ajin lissafi?
  • Mari Goma: Wa aka mara? Ko kuma wa za a mara har sau goma? Bari na fara da ba mu misalai don a fi gane bayanin da zan yi idan na tashi bayani.

  Dabarar da marubutan suka yi amfani da ita wajen samar da sunan labaran:

  Tamanin Da Tara (89)

  Sau biyu ina yunƙuri ba tare da samun nasara ba, sai a na ukun na iya miƙewa tsaye da ƙyar. Duk tsayina amma sai na gan ni iyakacin ƙirjin mutumin. A halin yanzu muna fuskantar juna. Daga inda nake tsaye ina iya jin hucin numfashinsa a saman goshina.

  Tsirarin sakanni sun samu damar shuɗewa kafin ya ɗan matsa baya kaɗan.

  “Za ka iya yin tafiya?”

  “Sai dai na gwada.”

  “To gwada mu gani.”

  Da ƙyar na iya yin taku uku. Ji na yi ƙafafuna sun yi nauyi kamar an ɗaura min sifirin ta baya.

  “Biyo ni.”

  Juya wa ya yi ya soma tafiya da zummar ficewa daga cikin dakin.

  “Dan Allah ɗan dakata.” Muryata ta suɓuce. Tsayawa ya yi ya waiwayo ya dube ni ba tare da ya yi Magana ba. Katuwar faffaɗar fuskarsa mai kama da fefen garmaho na fuskanta ta.

  “Wane ne kai?”

  “Ni?”

  “Eh,”

  “Kawai ka kira ni da suna wani.”

  “Wani?”

  “Eh…”

  “To ni kuma wane ne?”

  Sai da ya yi shiru kamar ba zai kuma yin magana ba.

  “Kai ma wani ne.”

  “Wani kamar ya ya?”

  “Ga sunanka a gaban rigarka.”

  Da sauri na dubi gaban rigata. Sai a lokacin na kula da irin tufafin da ke sanye a jikina. Kananan tufafi ne shuɗaye karamar riga iya kugu da dogon wando. Sai dai ban ga suna a gaban rigata ba face lamba da aka rubuta balo-balo.

  '89'

  “Ban ga sunan…”

  “Ga lamba a gaban rigarka.” Ya tari numfashina kafin ya dora da fadin,

  “A gidan nan ba a kiran kowa da ainihin sunansa face lamba…”

  “Lamba kuma?” A mamakance.

  “Shakka-babu.” A kagauce.

  “Lambar da ke manne a gaban rigarka ita ce sunanka…”

  Tamanin da tara?” Na furta yayin da na daga kai na dube shi bayan na sake kallon lambar karo na biyu.

  “Eh kwarai, tamanin da tara. Wannan ne sunanka.” Wani irin abu naga ya yi mai kama da gatsine. Wataƙila a tsammaninsa hakan murmushi ne.

  “Sannu malam tamanin da tara.”

  “Ka ce gidan nan ba a kiran kowa da ainihin sunansa.”

  “Eh, haka ne…”

  “To wanne gida ne wannan?”

  “Da sannu za ka san gidan da mutanen cikinsa. Yanzu dai zan kai ka wajen wanda ke da haƙƙin yi maka cikakken bayani.”

  Mu kalli wannan misalin don Allah, ta yaya wanda ya karanta sunan labarin daga farko zai iya hasaso cewa a inda aka samo sunan labarin kenan? Kuma shin marubucin ya samar da alaƙa tsakanin sunan labarin da labarin ko kuwa bai samar ba? Shin hakan bai zo wa mai karatu da bazata da kuma abin burgewa ba? Abdullahi Hasan Yarima shi ne marubucin labarin Tamanin da tara(89), shi ne ya zo na ɗaya a gasar marubuta ta Gusau Institute Kaduna a shekarar 2019.

  Bayan labarin 89 zan ƙara mana da wani misalin da labarina na Da Ma Sun Faɗa Mini. Kodayake suna ne da yake ba da ƙafa, dayawa sukan yi tunanin ko nadama jarumi ko jarumar labarin suke yi na wani abu da aka faɗa musu ba su ji ba suka yi watsi da shi. Sai mutum ya karanta labarin kuma sai a bayar da shi, sai a yi gabas shi ya yi yamma.

  Da Ma Sun Faɗa Mini

  Kamar yadda Zainab matar wanda ya yi shaɓaɓar take bayar da labari, cewa ta yi 'yan ƙungiyar asiri ne suke ta yi mata gizo da barazanar cewa sai sun shanye jinin duk abin da zata haifa, wanda kuma kai tsaye mijin nata ya nuna mata yana da masaniya a kan su.

  Rana ta farko da suka fara yi mata barazanar wai a cikin asibiti ne bayan ta fito daga ganin likita zata koma gida, tana tafe sai take jin kamar tafiya a bayanta. Tana waigawa kuwa suka yi ido huɗu da wani mutum mai mummunar halitta da yasa 'yar autar hantar cikinta ta kaɗa. Babu shiri ta kautar da kanta gami da ƙara sauri tana yi tana waige.

  Me zai faru? Ai tana ɗaga kai ta kalli gabanta bayan ta ji motsin tahowar wani ta gaban nata ta hangi wani irin mummunan mutumin da ke bayanta, don haka babu shiri ta sauya akalar tafiyarta zuwa ɓarin hagunta. Sai dai bata ci wani dogon zango ba taga kamar an jefo mata wani a gabanta, wannan karon ma bakinsa har dalalar da jini yake yi.

  Cikin tsananin firgici da matsanancin bugun zuci ta ja da baya turus bayan ta rusa kururuwa da nufin ta jawo hankalin jama'a kanta ko za a samu wanda zai kawo mata ɗauki. Sai dai kuma abin da ya sake firgita ta shi ne gani da ta yi gaba ɗaya jama'ar cikin asibitin sun rikiɗe mata sun koma dodonni. Kowa ta gani yana sanye da wata jar riga mai kama da alkyabba sai dai ba alkyabba ba ce, daga bayan rigar tana sharar ƙasa da kwatan-kwacin yadi uku, yayin da gabanta iya cibiyarsu take. Idan har bata manta ba ta taɓa jin wata ƙawarta na cewa irin rigar shaiɗan kenan. Launin rigar ja ne irin ja na jini, sannan akwai hoton baƙin ƙadangare an yi wani ɗan rubutu mai kama da watsal-tsalan yara a ƙasan ƙadangaren daga bayan rigar.

  Suna tahowa inda take suna kiran sunanta da wata irin murya mai ban tsoro. Kamar yadda ƙudaje ke bin mushen da ke fitar da turirin wari haka suke bin hangamammen bakinsu mai haƙora cako-cako da zasu yi saurin tuno maka da bakin manjagara ko tarko. Wani irin baƙin jini yana dalala daga bakin nasu babu kyan gani, duk ya ɓata musu ilahirin jikinsu tun daga kan wuya har ƙirjinsu irin yadda yaro mai timbiɗi ko yoyon baki kan yi da gaban rigarsa.

  "Zainaaaaaab.! Zainaaaaaaab.!! Zainaaaaaaab.!!!... Sai kin ba mu ɗan da ke cikinkiiii..." Maganar su ta fizgi hankalinta gami da sake dugutsuma tunaninta, sai a lokacin taga ashe gaf suke da ƙarasowa inda take suna masu ɗaga hannayensu masu ɗauke da farata cakar-cakar kamar takobi.

  "Ki gudu kada su hallakaki." Wani shashi na zuciyarta ya bata shawarar da ba ta yi wani dogon tunani ba ta karɓeta ta hanyar fakar numfashinsu ta runtuma a guje ta ɓarin damanta da taga 'yar faraga, tuni ta manta da batun tsohon cikin da ke jikinta haihuwar yau ko gobe.

  Sai dai hakan da ta yi shi ya ƙara ta'azzara mata lamarin, don kuwa zama ya yi kamar a tsokani kare a gudu, yadda karen zai bi mutum haka suma suka rufa mata baya kamar ƙurar mota a cikin babbar farfajiyar asibitin da taga ya rikiɗe ya koma fili fetal kamar dokar daji, suna tafe suna wani irin ƙara mai kama da ƙaran faifan injin markaɗe.

  Firgicinta ya daɗu ne lokacin da ta tabbatar da tazararsu da ita baifi tazarar da ke tsakanin liman da mamu ba, bugu da ƙari a lokacin ta gama gajiya babu abin da ta ke yi sai haki kamar wacce ranta zai fita, a ɓangare guda kuma hannunta na tallafe da tsohon cikinta da ta ji yana barazanar faɗowa don ciwo. Hakan ne ya tilasta mata rage gudun, tana yi tana waigensu gaf da ita sanadin da ya sa ba zato ba tsammani ta yi turuuusss...! Ta faɗi a cikin fasassun kwalaben magani da allurai tana tsala ihun kiran Muradinta ko zai taimaka mata. Duk da haka cikin tsananin ƙarfin hali ta sakeyin yunƙuri da niyyar ta tashi amma ina cikinta ya ce bai san zancen ba, lokaci guda kuma ta ji mararta tana wani irin ɗaurewa kamar zata fashe.

  Su kuwa dodonnin mutanen sai suka ɗauka da shewa cikin wani irin sauti mara daɗin ji, suna wani irin tanɗar baki irin na raƙumin da yaga ruwan jiƙaƙƙiyar kanwa, kana suna tunkararta kamar masu shirin daka mata wawa. Ganin haka yasa ta tattaro duka ƙwarin gwiwarta ta ci gaba da jan jiki da baya da baya don ganin ta guje musu, sai dai bata yi wani dogon zango ba bayanta ya ci karo da wani abu da ta fi kyautata zaton bishiya ce. Saɓanin tunaninta tana waigawa ta ga ashe ƙafar wani dodon ne wanda duk ya fi sauran dodonnin mutanen girma da muni.

  Ta sake tsandara ihu ta yi tsalle irin na sufurin ta dira a tsakiyarsu tana waige-waige da yi musu magiyar kada su cutar da ita. Aikuwa kamar busar sarewa haka magiyar ta zama, gani ta yi ma kamar ƙara zuga su take yi. Don haka kawai sai ta saduda ta rufe ido tare da dunƙulewa tana shirin jin saukan takubban faratansu.

  A dai dai wannan lokacin shassheƙar kukanta ya tsananta ta yadda har ya farkar da mijinta da suke kwance ya fara taɓa ta zai tashe ta yana tambayar ta ko lafiya take kuka. Ai kuwa tana farkawa ta tsandara ihu gami da ƙanƙame ɗan matashin mijin nata.

  "Mene ne? Me ya faru?" Ya shiga tambayarta a kiɗime kamar yadda itama take ba shi amsar a kiɗime tana waige-waige.

  "Bi..bi...biyo ni suka yi za su kashe ni." Jin haka ya ƙara jawo firgitacciyar matar tashi jikinsa bayan ya fahimci mafarki ta yi. Don haka sai ya fara yi mata addu'o'i yana tofa mata yayin da ita kuma take maƙale da shi kamar zata shige jikinsa, fuskarta ta haɗa gumi sharkaf kamar sabuwar kuturwa. Bai daina addu'ar yana shafa bayanta ba har sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ta dawo cikin hayyacinta ta nutsu sosai sannan ya tambayeta abin da ya faru.  Nan take ta kwashe labarin mafarkin nata gaba ɗaya na ganin dodonnin mutanen da ta yi da kuma ce mata da suka yi wai sai ta ba su ɗan cikinta sun sha jinin shi.

  Jin haka ya yi shiru alamun damuwa suka bayyana ƙarara a kan majigin fuskarsa, tuni ma ya saki matar tashi ya miƙe tsaye ya fara safa da marwa a cikin yalwataccen ɗakin nasu mai dishi-dishin hasken lantarki na bacci.

  "Murad.! Me ya faru?" Zainab ta tambaye shi tana mai ƙara yin nazarin shi ganin yadda a cikin ƙanƙanin lokaci yanayin shi ya sauya. "Da Ma Sun Faɗa Mini" ya ambata hakan dai dai lokacin da ya goya hannayensa a baya da alamar ƙololuwar damuwa a tare da shi.

  "Da ma sun fada maka?" Zainab ta maimaita furucin na shi ƙasa-ƙasa.

  "Su waye suka faɗa maka? Kuma me suka faɗa maka?" Ta yi mishi tambayar da ta dawo da shi hayyacinsa ya yi firgigit kamar ya tashi daga bacci, sai a sannan ya fahimci ya yi suɓutar baki zancen zuci ya fito fili, kamar yadda ita ma Zainab ɗin sai a lokacin ta gane cewa bai san lokacin da ya ce 'Dama sun faɗa min' ɗin ba...

  A matsayinka na marubuci, ko matsayin ki na marubuciya, kada ka ce lallai kai labarinka sai ya zama mai sunan abin da labarin ya ƙunsa, kamar dai yadda dayawan marubutanmu na yanzu, musamman na online suke yi.

  Sai Na Aure Shi

  Ba Na Son Kishiya

  Ya Yaudare Ni

  Ire-iren waɗannan sunayen za ka ga suna yawo ana tallata su a matsayin labari. Ba a ce kada a rubuta sunan da za a hakaito me labari ya ƙunsa ba, amma idan za a saka a ɗan saƙa ƙaƙƙarfan suna ba rarrauna irin waɗannan ba. Idan mun zo bayani a kan Suna Jimla insha Allahu za mu tattauna matsalar sosai.

  Za mu dakata a wannan gaɓa, kamar kullum ƙofar gyara, tambaya ko ƙarin bayani a buɗe take.

  Jibrin Adamu Jibrin Rano

  08132505026

Comments

1 comment