Rubutu

Blogs » Tarihin Mutane » Sirrin samun nasarorin Alhassan Dantata

Sirrin samun nasarorin Alhassan Dantata

 • Al’hassan Dantata, fitaccen attajiri a fadin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga siyar da Goro, da Gyada.

  Hihuwa da Nasaba

  Alhassan Dantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani karamin kauye da ake kira Danshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar akalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan daya ne daga cikin ‘ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa.
  Shi Abdullahi da ne ga wani mutum mai suna malam Ali, wanda ake yiwa lakabi da Baba Talatin. Sun taso ne daga kasar Katsina da iyalansu kamar yadda suka saba, suka yada zango a garin Bebeji, bayan wani lokaci kuma sai Baba talatin ya koma Madobi da zama, wanda a nan Allah ya yi masa rasuwa. Wannan dalilin ne ya zaunar da su a garin, wanda shi Abdullahi ya ci gaba da kula da iyalan har zuwa lokacin da suka kimtsa don ci gaba da tafiyar a shekarar 1877. Bayan sun shirya tsaf don tafiya izuwa garin Gonja, babbar cibiyar hada-hadar Goro ta kasar Ghana, sai matarsa Amarya ta haifi Alhassan a sansanin da suka yada zango a nan garin Bebeji.
  Abdullahi mahaifin Alhassan ya rasu a shekarar 1885, lokacin Alhassan na da shekaru takwas a duniya, kuma yana da kanne kamar su; Malam Jaji, Malam Bala, Malam Sadi da sauransu. Duk suna kanana sosai a lokacin, don haka ba zasu iya juya dukiyar mahaifin nasu ba.
  Bayan an raba gado an ba wa kowa nasa kamar yadda shari’a ta tanadar, sai Amarya mahaifiyar Alhasan wadda dama ita ma tana kasuwanci kamar yadda mahaifiyar mijinta ke yi, ta yanke shawarar barin garin Bebeji inda ta bi ayarin fatake zuwa Accra ta kasar Ghana, inda a can ta ci gaba da yin kasuwancinta. Ta bar ‘ya’yanta a Bebeji.
  Shi Alhassan ya kasance a karkashin kulawar wata tsohuwar mata, wadda ta kasance baiwa ce, da ake kira da Tata. Alhassan ya samu duk wata kulawa da ake samu a wajen uwa, wannan dalilin ne ma ya sa tun a wancan lokacin ake kiransa da suna Alhassan Dantata.

  Neman Ilimi da gwagwarmayar rayuwar Dantata

  Alhassan Dantata ya yi karatun Alqur’ani (Allo) a nan garin Bebeji, makarantar da ke karkashin kulawar darikar Tijjaniyya. A matsayin almajiri yana da bukatar abinda zai taimakawa kansa, wannan ya sa ya fara tsakurar abinda ya samu na daga gado domin ya tallafi rayuwarsa. A matsayin Almajiri mai daukar nauyin kula da kansa ta bangaren abinci da suture, har ma da tallafawa malaminsa, abu ne mai matukar wahala, don haka ya kan yi bara wani lokacin, wasu kuma su kan sanya shi aiki ya yi a biya shi. Aikin hannu, ko aikin karfi kamar wata al’ada ce ta matasan zuri’ar Agalawa da Alhassan Dantata ya gada. Hakan kuma bai hana shi samun lokacin yin karatu ba. Alhassan ya yi nasarar tara ‘yan kudade a asusu, wanda Tata ke kular masa da shi.
  Yana dan shekaru sha-biyar a duniya ya bi ayarin fataken Gonja, da niyyar kai wa mahaifiyarsa ziyara. Ya sari kaya a nan garin Bebeji ya tafi da su, wadanda ya siyar da fiye da rabi a hanyarsu ta zuwa Accra.
  Ya yi farin cikin ganin mahaifiyarsa da yadda ya sameta cikin kwanciyar hankali, tare da bunkasar dukiyarta. Har ma ya yi fatan dukiyar zata wadacesu su rayu tsawon lokacin da zai dawo ba tare da ya nemi kudi ba. Sai dai kwanansa daya da zuwa sai ta dauke shit a kais hi wajen wani malamin addini domin ya yi karatun Alqur’ani, tare da umartarsa da ya zauna a wajensa kafin lokacin tafiyarsa ya yi.
  Dantata bayan karatun Qur’ani, a ranakun Alhamis da Juma’a yana fita neman aiki, ya yi sosai a Accra fiye ma da yadda ya yi Bebeji, haka kuma yana bawa malamin kaso mafi tsoka na duk kudin da ya samu. Sannan yana yin barar abinci domin ya ci kuma ya kai wa malamin.
  Bayan wasu ‘yan kwanaki sai Alhassan ya dawo garin Bebeji domin ci gaba da neman ilimi, yayin da Tata ta ci gaba da dorashi a hanyar yin adani, inda yaci gaba da ajiye kudi kullum a duk abinda ya samu.
  Yadda rikice-rikice suka ritsa da Dantata

  A shekarar 1893 rikicin mulki da na fataucin bayi suka barke a garin Kano, lokacin Dantata yana da shekaru sha-shida a duniya. A lokacin aka samu wasu gungun marasa rinjaye da suka balle daga Kano, suka yiwa garin Bebeji tsinke, inda suka kori mutanen garin, suka karkashe wasu da dama, sannan suka kame wasu a matsayin bayi. Alhassan da ‘yan uwansa Bala da Sadi, na daga cikin wadanda aka kama a matsayin bayi, daga baya Alhassan ya fanshesu da dukiya, suka shaki isakar ‘yanci. Yanayin ya zowa Alhassan da tsauri a lokacin, saboda karacin shekarunsa.
  Yana garin na Bebeji lokacin da turawan mulkin mallaka suka baro Zaria, suka kawo hari Bebeji, a ranar 1 ga watan February na shekarar 1903, suka kashe jagoran garin tare da wasu da dama na mukarrabansa.
  Sai kuma rikicin neman mulki, wanda ya biyo bayan rasuwar sarkin Kano Muhammad Bello, a shekarar ta 1893. Inda aka samu mutane biyu da ke son zama magadansa, wato; Tukur, da Yusufu. Tukur wanda da ne ga marigayin, ya yi ilimi mai zurfi a wajen malaman Tijjaniyya, hakan ya sa ya samu goyon bayan zuri’ar Agalawa. Shi kuma Yusufu wanda ya kasance ya yiwa Sarki Muhammad Bello mubaya’a lokacin da ya zama sarki, ya yi iliminsa ne a wajen malaman Qadiriyya. Sakamakon da ya biyo bayan wannan rikicin na cikin gida shi ne, Yusufu ya hakura ya janyewa Tukur.

  Fadada harkokin kasuwanci

  Bayan rikicin ya lafa, sai Dantata ya mayar da hankalinsa kan shirye-shiryen fadada harkokin kasuwancinsa. Ya fara amfani da sabbin hanyoyin kasuwanci, inda ya fara zuwa Ibadan da Lagos, tare da inganta dangantaka tsakaninsa da takwarorinsa ‘yan kasuwa. Ya kan sayi dabbobi ya yi musu shaida ya loda su a katon jirgin ruwa ya dinga kaiwa garuruwan; Accra, Kumasi, Sekodi, da Lagos, daga can kuma ya saro goro ya Kanoya rarrabawa kananan ‘yan kasuwa. Shi ne dan kasuwa na farko a arewacin Nigeria da ya fara habbaka wannan hanyar kasuwancin, kuma ya dauki shekaru da dama yana yi. Wannan kokarin nasa ya jawo hankulan kasashen turai wajen kulla dangantakar kasuwanci da shi.
  A shekarar 1906 ya fara zama hamshaki a sha’anin kasuwancin kasa da kasa. Inda yake siyo kananan duwatsun kwalliyar mata, da sarkokin mata, da suture daga kasashen turawa, da sauran kayayyaki yana siyarwa.
  A shekarar 1908, mahaifiyarsa wadda bata sake yin aure ba ta rasu a Accra. Bayan rasuwarta sai ya takaita harkokin kasuwanci tsakanin Kano da Lagos, sai dai lokaci zuwa lokaci yak an kai ziyara Accra.
  Dantata yana rayuwarsa ne a garin Bebeji, ya gina wani katon gida a garin, wanda aka yi ittifakin cewa kaf ‘yan kasuwar da ke fadin kano babu mai irin shi. Ya gina gidan ne kawai saboda saukar baki abokan kasuwancinsa na kasashen ketare. Bai wai ya gina ne don ya zauna a ciki ba. Yana zuwa garin Kano ne lokaci zuwa lokaci, ko kuma idan sha’anin kasuwancinsa ya taso.
  Dantata ya gina gidansa na farko a cikin birnin Kano ne a unguwar Sarari, da ke yankin Koki a shekarar 1903, bayan turawan Birtaniya sun nada Muhammad Abbas a matsayin Sarkin Kano, sai Sarki Abbas ya umarci Dantata da ya ginawa zuri’ar Agalawa gida a Kano.
  A shekarar 1912 ne kasashen turai suka nuna bukatarsu ta son kulla alakar kasuwancin shigar musu da Gyada, sun tuntubi manyan ‘yan kasuwa irin su; Umaru Sharubutu, da Maikano Agogo, ta hannun wakili sarki wato Adamu Jakada, wadanda dukkansu suka amince.
  A shekarar 1918, Alhassan da Royal Niger Company, suka cimma yarjejeniyar kulla alakar kasuwancin gyada, wanda dama tuni shi Dantata yana da tunanin neman mutanen da zai hada hannu da su domin fara shigar da Cocoa kasashen turai. Da yake yana da damarmaki fiye da sauran ‘yan kasuwar Kano, saboda yana iya yin magana da turanci, saboda cudanyarsa da ‘yan kasuwar kudancin Nigeria, da Accra, da ma na kasashen turai. Wannan ya taimaka masa sosai wajen bunkasar karfin jarinsa fiye da sauran ‘yan kasuwa.
  Duk da tarin dukiyar da Dantata ya mallaka, yana yin sassaukar rayuwa ne, yana yin aiki tukuru, kuma yana da kyakkyawar mu’amala da sauran mutane.
  Ya dauki wasu mutane biyu Alhaji Babba na Alhassan, da Alhaji Garba Maisikeli don su taimaka masa wajen gudanar da kasuwancinsa, wadanda suka yi aiki tare tsawon shekaru talatin da takwas. Cikin kankanin lokaci da fara kasuwancin na gyada, Dantata ya mamaye harkar, ya zama ya kere su Umaru Sharubutu da Maikano Agogo a fagaen kasuwancin, wadanda a das u ne na daya da na biyu. Ya tara manya-manyan dalar gyada guda sittin, yace “gaba daya wadannan nawa ne.”
  A shekarar 1929, da turawa suka bude reshen Bank of West Africa a kano, Dantata ne dan kasuwar da ya fara bude account, inda ya kawo Rakuma ashirin kowannensu dauke da lodin tsabar kudi na silver.
  Alhassan Dantata ya zama babban mai siyar da gyada na kamfanin Royal Niger Company, wanda daga baya ya zama United Africa Company.
  A shekarar 1932, ya nemi lasisin zama mai kai gyada kai tsaye zuwa ga kasashen turai, amma saboda wasu matsaloli bai samu lasisin ba, sa a shekarar 1953.
  Banda harkar gyada, Dantata yana siyar da abubuwa da dama, kamar; shanu, goro, dunwatsun kwalliya, kayan sa wa, farin dutse, da dai sauransu.

  Taimako

  Dantata ya taimaki mutane da dama rayuwarsa, ba iya kabilarsa ta hausa ba, har da Yarabawa, da inyamurai. Wadanda ya samar musu da aiki a kamfanunnukansa, da yake biyansu. Haka nan da yawa daga cikin ma’aikanta musamman Hausawa suna kwana a gidansa, haka nan yak an dauki dawainiyar ani sha’ani na ma’aikatansa idan ya taso, kamar biki ko suna. Snnan ya kan shiga cikin ma’aikatansu suyi aiki tare, haka ma idan watamatsala ko rigima ta tashi a tsakaninsu, yak an shiga ya sasanta, kuma ya kashe rigimar.
  Dantata ne mutum na farkon fara zuwa Makka a jirgin ruwa na kasar Ingila. Ya gina kananan masallatai a dukkan gidajensa. Yana girmama makaranta Alqur’ani, ya kan ware lokaci musamman don sauraron karatun Alhaji Abubakar (Mahaifin Malam Lawan Kalarawi). Dantata mabiyin darikar Tijjaniyya ne. Dantata baya yin huldar kasuwanci da mace duk matakin shekarunta. Matarsa hajiya Umma Zariya, ita ce mai taimaka masa a bangaren mata. Haka nan baya karbar kudin ruwa a kudaden ajiyarsa na banki.

  Sanadin rasuwarsa

  A shekarar 1955 Dantata ya kamu rashin lafiya, ganin yadda cutar ta tsananta, sai ya tara ‘ya’yansa, da mai kular masa da bangaren kudi, wato Garba Maisikeli, ya fada musu cewa shi fa rayuwarsa tazo karshe, babu abinda ya kamacesu suyi illa hadin kai. Ya ja hankalinsu da cewa, kar su bari wannan kamfanin na Alhassan Dantata and sons da ya gina, su bari ya rushe. Ya kuma rokesu da su riki auren danginsu, su taimaki mabukata, sannan suyi huldar arziki da sauran attajirai.
  Kwanaki uku bayan wannan hudubar da ya yi musu, Alhasan Dantata ya rasu, a ranar Laraba 17 ga watan August 1955. A ranar aka binne shi a gidansa da ke Sarari.
  Ya rasu ya bar mata biyu, Umma Zariya, da kuma Maimuna. Daga cikin ‘ya’yansa akwai; Mamuda Dantata, Ahmad Dantata, Sunusi Dantata, (wanda ya haifi Mariya, ita kuma Mariya ta haifi Aliko Dangote). Aminu Dantata, da kuma Mudi Dantata.
  Zaharadden Nasir, Kano Nigeria.

Comments

2 comments