Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Ummu hani

Ummu hani

 • https://hikaya.bakandamiya.com/ummu-hani-babi-na-shida/

  Ummu hani ta nisa kamin ta ce, Yawwa Daman na ga yau Bakwau, shi ne na ce ko wazai ɗauki Muhammad ta nuna jaririn da ke hannunta, wanda tunda aka haifeshi babu wanda yai tunanin saka masa suna cikin dangin umman su da na Abbansu.

  Kawu Bala ya numfasa, sannan yace toni dai kinsan Mata ta tayi tsufan da ba zata iya rainon yaro...

  Kamin ya rufe baki, Inna Abu yayar ummansu ce data rasu, ta ce bare kuma ni, ga tsufa, ga masifaffen miji, innaje masa da jariri ai sai ya koren ya ce na kawo masa nauyi.

  Haka kowa yai ta bada uzirin sa.

  Ummu Hani ta share hawaye, gami da saɓa Muhammad dake kuka a kafaɗa, ta ce to shikenan, mu yanzu ya zakuyi ɗaukan namu, ɗai ɗai zaku rarrabamu, ko bibiyu, nidai duk wanda zai ɗauken sai ya haɗa da Muhammad ni zan kula dashi.

  Kamar ɗazun, haka sukai ta bada uziri naƙin ɗaukan su, ji take tamkar ta fashe da kuka, sai dai tanajin ita dinfa jaruma ce, intai kuka kannenta fa.

  To shikenan, yanzu shinkafar da Alhaji Badamasi da wadda Alhaji Bashir ya kawo, naga kun rarraba a tsakanin ku, nai muku shiru ne, dan nayi zaton ku zaku riƙe mu, yanzu sai ku aje mana, fatan kunsan marayu suka bawa ba dangin marayu ba.

  Nan guri ya ɗauka, ka gamin mara kunya mu ba iyayanki bane.

  Bata ce komai ba, ta mikawa Aisha Muhammad, ta hau shigar da shinkafar ɗaki inda sauran ƙannenta suka fara taya ta.

  Kawu Bala ne ya rike tasa, tasa hannu zata amsa yaƙi bayarwa, tace ka saki ko Wallahi tallahi in kaika ƙara gun hukuma, Ba shiri ya saki yayin da kowa ya watse.

  Ko da suka watse, toilet ta shiga tasha kukanta yanzu ita yaza tai da Muhammad, wanda ita tasa masa sunan, bayan haka sauran ƙannenta biyar ya za tai dasu, wato babu wanda yafi danginsu zalunci suna nufin kenan su kaɗai zasu rayu ko me.

  Yaya taji Aisha kira ta, wanke fuskar ta tai sannan ta fito, kinga Muhammad na kuka, ta amsheshi ta goya ta zari mayafi, ba inje in dawo, nan yan biyu suka sa kuka, ta rike musu hannu, sannan ta dubi Aisha, ki kula da su khairi, zan je in nemo abinda zamu dinga bawa Muhammad, A'isha tace to yaya sai kin dawo, ta ja su Hasana suka fice.

  Rimi ta wuce da yan kudin da suka rage mata, ta haɗo saiwar magunguna, wanda zasu sa ruwan mama yazo, dan ta yanke shawarar ita zata shayar dashi kawai, tunda basu da kuɗin madara.

  ********

  Ummu Hani kenan yarinya yar kimanin sheka goma sha shida, da rayuwa ta sauya mata ko ya zata kaya ku biyo ni

  Me kuke gani game da labarin

Comments

0 comments