Rawar da zuciyar shi takeyi ce tasa har duka jikin shi na amsawa, ta waje da ta ciki, a zaune yake, sai yakejin kamar ya kwanta, ko zai samu sauki, ko zaiji wani abu ya zame mishi dai-dai ko da na dan lokaci ne, takarda ce a hannun shi, kwara daya da take lankwashe, bai kamata ace tana da nauyin da ...