Makalu

Sabbin Makalu

View All

Rai da kaddara 2: Shafi na ashirin da biyar

 • Tun tasowarta, koya ta juya zata ga Daada a kusa da ita. A wautar tunani irin nata ko a mafarki bata taba hasaso nisa da Daada irin haka ba. Ace ba unguwa bace a tsakaninsu, ba gari bane ba, kasa ce kacokan a tsakaninsu. Awanni ne masu yawan gaske idan akace lissafasu za'ayi. Komai ba tajin dadin shi. Duniyarta tayi tsaye waje daya, tana zaune kawai sai taji hawaye na cika mata idanuwa. Duk da taji muryar Daada yafi a kirga yanzun, ta ganta a video calls din da Nawfal ya kirata yana hadasu. Ta tabbatar mata da cewar tana samun sauki, har anma kusan saka lokacin dawowar su. Ta wani bangaren hankalinta ya kwanta, amman kewar Daada fa?

  Abinda duk take so a gidan shi takeyi, banda Salim kowa na bata wajen da suke tunanin tana bukata, tunda Saratu tayi duk wani kokari na ganin ta saki jikinta da ita amman ta kasa. Tasan babu jituwar kirki tsakanin Saratu da Daada, a iya tunaninta da fahimtarta kuma akan Nawfal ne hakan ya faru. Duk yanda Saratu take faran faran da ita sai ta tsinci kanta da kasa sakewa da matar. Tana shiga kitchen ta tayata aiki sosai, haka su sharar gidan da mopping ma, wasu ranakun ita take dafa musu abincin gidan gabaki daya. Tunda Saratu ta kula ta iya girkin sosai, idan tace tabar mata bata musawa.

  Yau ma daya daga cikin irin ranakun ne, sai ta zabi ta dafa wake da shinkafa tunda miyar kifi ce tayi. Sabonta ne zama kitchen idan tana girki duk fadan da Daada zatayi, musamman yanzun da Khalid ya nuna mata wani waje da zata iya sauke litattafai a cikin wayarta, da kuma manhajar da ta dauko don bude litattafan, ta dai fi son taji littafi a hannunta, wannan yanayi ne da ba zai misaltu ba, ko kamshin takarda daban yake a wajenta. Nutsuwar da kamshin yake samar mata abune da ba zata iya amfani da kalamai wajen fassara shi ba. Sai dai ya saukaka mata ba saita dauki littafi zuwa ko ina ba, yanzun a kitchen da ta shiga a wayarta sai ta cigaba da karatunta tana zaune a kujerar robar da take cikin kitchen din.

  Hankalinta gabaki daya yana kan littafin da take karantawa mai suna Obsidian na Jennifer L. Armentrout. Tun daga shafin farko jiya littafin ya riketa, so takeyi kawai taji ya za'a kare. Shisa bataji shigowar Salim ba saida yasa hannun shi yana rufe mata screen din wayar da ta tattara nutsuwa a kai

  "Hamma..."

  Ta kira cikin kasalalliyar muryar da yaji kaman ya fito wanka an kunna masa fanka, yanda ta sauke idanuwanta a fuskar shi tana sauke numfashi a hankali yasa har gwiwoyin shi yaji sunyi masa sanyi. Mata da yawa, mata kala-kala da ya gani, ya taba, suka bishi. Babu wadda take da tasirin nan da Madina take dashi a rayuwar shi, yarinyar da ko shekara ashirin bata hadaba a duniya ce take sanyaya masa jiki har haka. Dan yatsa yasa yana tura mata gilashinta yana sa tayin dariyar nan tata da sautinta yake sa kaji kana son kasancewa cikin irin nishadin da take ciki.

  "Yunwa nake ji, me kike dafawa?"

  Ya furta yana jingina da kantar kitchen din ya harde hannayen shi a kirjin shi. Sai taga duk ya cika kitchen din

  "Wake da shinkafa da miyar kifi. Nanna tace za'ayi salad, amman wake da shinkafar bai dahu ba tukunna, yanzun ma na zuba shinkafar"

  Dan hade girar shi ya sakeyi yana sakata yin dariya

  "Ina miyar kifin?"

  Sai da ta kalli tukunyar, sannan ta kalle shi, ta bude baki, kafin tayi magana ya raba jikinshi da inda yake tsaye ya karasa ya bude, cokali ya dauka ya tsamo kifi guda daya

  "Hamma me kakeyi?"

  Inda zai saka kifin yake nema, wani kwano ya gani ya dauka ya saka kifin a ciki yana kara tsamo guda biyu

  "Inalillahi... Hamma kifin zaka tsame mana? Ka tsaya a kirga aga kowa nawa zai samu"

  Makale mata kafada yayi yana kara yanka daya sannan ya rufe tukunyar

  "Guda nawa ka dauka?"

  Madina ta fadi tana mikewa tsaye itama, sama yayi da kwanon hannun shi

  "Ni ki kyaleni yunwa nakeji"

  Dariya takeyi har lokacin

  "Ka kawo to inga guda nawa ka dauka"

  Yana sake sama da hannun shi Saratu ta shigo kitchen din

  "Me kake mun a kitchen Salim?"

  Tayi masa tambayar cikin harshen fulatanci

  "Yunwa nake ji"

  Ya amsa Madina na karbewa da

  "Shine ya kwashe mana kifi Nanna"

  Kallon shi Saratu tayi, sai ya sauko da kwanon yana nuna mata tare da turo labbanshi

  "Ba da yawa na diba ba Nanna... Yunwa nakeji"

  Lukman ne karami a cikin yaranta, amman babu mai nuna har yanzun shi yarone a wajenta kamar Salim din, duk da maganarshi bata cika tsawaita ba, dan ya shagwabe mata ko a gaban waye baya masa wahala. Yanda zai kalleta ya shagwabe fuska, ya juya ya canza fuska wa kannen shi yana basu umarni har mamaki da dariya yake bata. Sai dai ta kula da abu daya, dariyarshi ta karu tun dawowar Madina gidan, kamar akwai wata shakuwa a tsakaninsu da yanzun ne take sanin akwaita. Sannan ko baiyi magana ba idan yaga Madinar yanayin fuskar shi saiya canza, girarshi da bayason saukewa ko yaushe da kanta take sauka kafin karamin murmushi ya bayyana kan fuskarshi da tazo waje.

  Surutun kowa har da na Saratun kuwa yana nuna ya dame shi, amman banda na Madina, da kanshi zai fara janta da kananun hira. Kacokan ya dawo da zama a falonta duk saboda Madina din, shisa ita ta rage zaman falon dan suyi hirar su cikin kwanciyar hankali tunda ta kula Madinar bata sakewa yanda take so idan tana waje. Da tasan matsayin Yelwa a wajenta da ta sake da ita, da tasan yanda itace wadda taso a kusa da ita ba Nawfal na da ta bata dama fiye da wadda ta bata a filin rayuwarta. Ayar tambayar da yake zagaye da asalinta bai damu Saratu ba.

  Saboda tana jin abinda zata iya yiwa Yelwa shine kulawa da Madinar, fatanta shine hasashenta tsakanin Madina da Salim ya zama gaskiya. Saboda sirrinsu zaifi lullubuwa idan hakan ta faru, daga ita har Julde babu wanda zai bukaci wani tone-tone, sune dangin Madina, sune kuma iyayen Salim.

  Sai dai wani fatan zai iya kasancewa a hasashe kawai zai tsaya
  Kamar yanda wasu sirrikan da kansu suke bayyana kansu ba sai sun jira an tono su ba

  "Baka karya ba?"

  Wannan karin Madina ce ta amsa mata da

  "Yau laraba, aikin kwana yake da duka satin nan"

  Kai Saratu ta jinjina

  "Ka nemi wani abin kaci kafin a gama abinci"

  Kwanon ya ajiye yana karasawa wajen fanfo ya wanke hannun shi kamar ba dashi suke magana ba. Murmushi Saratu tayi tana fita daga kitchen din, wata kujerar Salim yaja ya zauna, saboda yasan Madina zatayi masa magana idan yaci kifin a tsaye. Kofi ta samu tana karasa ta bude fridge ta dauko ruwa ta zuba masa a ciki tana mika masa

  "Nagode"

  Ya furta a hankali bayan ya karba, itama taja kujera ta zauna, kamar hakan wayarta take jira ta fara ruri, tana dubawa taga Nawfal ne ya kirata video call. Dagawa tayi tana murmushi

  "Hamma..."

  Ta kira, lokaci daya Salim yaji dandanon kifin da yake bakinshi ya dauke gabaki daya. Zuciyar shi tayi nauyi a cikin kirjinshi, bayaso tana kiran kowa da wannan yanayin banda shi, wannan murmushin da yake fuskarta ya kamata ace bai kai haka girma ba tunda bashi take yiwa ba. Kishine yake damun shi, kishi da bai taba tunanin yanada irin shi ba, kishin da batama san yanayi ba

  "Kana ina haka? Ina Daada?"

  Ta tambaya

  "Jaan ta koroni, dole saina fito na sha iska wai, tana tare da Daada, bacci takeyi sanda na fito dai... Me kikeyi ke?"

  Juya camera din tayi tana haska masa kitchen din, kafin ta sake dawo da ita zuwa dubanta

  "Ina zaune a kitchen ni da Hamma Salim...ni ina girki, shi kuma yana cin kifi"

  Dariya Nawfal yayi

  "Aikin dare yayi ya dawo gida ya kwanta bacci maimakon ya nemi abinci ya tashi da yunwa ko?"

  Dariya Madina takeyi tana daga masa kai

  "Ina zaune a kitchen din Bajjo, ranka kuma zai baci"

  Dariya Nawfal ya sakeyi, Madina ta mikawa Salim din wayar, ya karba lokacin da ya sake kai wani kifin bakin shi, Nawfal kuma yana gaishe dashi, gira Salim ya hade masa a maimakon amsa gaisuwar yana sakashi sake yin dariya

  "Yaushe zaku dawo?"

  Salim ya tambaya bayan ya kara jin cewa Daadar ta samu sauki

  "Inajin nan da sati daya haka ko kwanaki goma idan Allah ya kaimu"

  Kai Salim ya jinjina

  "Ka kula da kanka..."

  Murmushi Nawfal yayi

  "Jaan na kula dani"

  Dakuwa Salim yayi masa yana yatsina fuska cikin yanayin da yasa Nawfal din yin dariya, yanke kiran yayi kafin ya mikawa Madina wayar. Karba tayi sai taji zuciyarta kamar batayi mata dadi da abinda Nawfal din ya fadi, duk da yayi maganar ne cikin sigar tsokana. Amman akwai gaskiya a kasan hakan, akwai kuma yanayin da yake nuna nishadin da fadin Murjanatu na kula dashi ya samar masa

  "Ki duba girkin nan koya totse"

  Salim ya fadi ganin tana jujjuya wayar a hannunta kamar tana jiran Nawfal din ya sake kiranta, ta kuwa yi masa murmushin nan nata tana sakashi sauke numfashi. Batayi masa musu ba ta tashi tana dubawa. Sai ta dauko lettuce din da ta wanke ta saka shi a kwando dan ruwan ya tsane ta fara yankawa. Ko da Salim ya gama cinye kifin shi bai bar kitchen din ba, komawa yayi ya zauna kan kujerar daya tashi yana sakata bashi labarin littafin da take karantawa, idan za'a karbi wukar hannunta a saka masa a wuya ba zai iya fadin me littafin ya kunsa ba. Hankalin shi yana kanta, amman kalaman da take fada basa karasawa kunnuwan shi, yanayin yanda labbanta ke motsawa, yanda takeyi da hannayenta idan tazo wajen da yayi mata dadi a labarin, da dariyarta sune abinda yake kallo.

  Baya ganin komai sai kyanta da ba kowa bane zai gani farat daya. Yana so rana daya, ya cire mata gilashin nan, ya rabata da kayan nan, ya ganta a cikin shigar atamfa, hannuwanta masu kyan nan da kunshi, ya ganta a cikakkiyar mace saboda a cikin kanshi daya hasaso tayi kyau, wani irin kyau mai sanyi. Ko da ta gama girkin ma sai dakyar ta samu ya bar kitchen din bayan ta zuba masa. Ta wanke yan kwanonin da ta bata, ta goge ko ina tana fitowa falon

  "Ke ba zaki ci ba?"

  Kai ta girgiza masa

  "Sai anjima, banajin yunwa ni kam"

  Da ya gama cin abincin ma ta kusan mintina sha biyar tana fama dashi kan yaje ya kwanta saboda yana bukatar baccin

  "Zan kwanta anan"

  Kai ta girgiza masa

  "Anayin kwakkwaran motsi tashi zakayi. Dan Allah ka kaje ka kwanta Hamma, nima baccin zanyi"

  A fuskar shi baiso ba, saboda ji yake kaman daga bangaren Saratun zuwa nasu yayi masa wani irin nisa, nisan da bayaso a tsakaninsu. Amman da gaskiyarta, ya gaji sosai, yana kuma bukatar baccin. Yana tafiya ta mike itama zuwa dakin daya zama nata yanzun a cikin gidan. Kai tsaye bandaki ta wuce ta watsa ruwa ta fito daure da towel, sai da ta shafa mai sannan ta saka kaya, sanin babu wanda zai shigo yasa tabar na jikinta, tunda lokutta da dama tana amfani dasune a matsayin na ciki, ta dora wasu akai, gara ta saka kaya hudu a jikinta komin zafin da akeyi in har ba zasu fito da wata alama ta halittarta ba.

  Sai dai abinda batayi tsammani bane ba ya faru, tana tsaye aka murda hannun kofar aka kuma bude duka cikin abinda bai shige dakika biyu ba, numfashinta ta dauke lokacin da idanuwanta suka sauka cikin na Julde. Shi ya fara sauke nashi yana kallonta, tun dawowarsu daga airport rakiyar Daada yake jin shi wani iri, yake jin shi kamar yana yawo a cikin wata kwalbane da baisan yanda zai fito daga cikinta ba. Baccin kirki baya samu, daya kwanta ya fara bacci sai yaji ya farka, idan za'a tambaye shi ba zai iya fadin dalilin farkawar tashi ba.

  "Ka kwantar da hankalinka Julde, ance ta samu sauki. Da yardar Allah babu abinda zai sameta"

  Saratu tace masa satin daya fita da ta farka tsakiyar dare ta ganshi a zaune. Kuma tanata kokari ya kula tun tafiyar Daadar wajen ganin ba suyi fada ba, watakila ta kula da yanda baya cikin hayyacin shi. Sai dai ya kalleta kawai, tunda baisan ya zai fada mata ba rashin lafiyar Daada bace kawai matsalar shi. Taya zai fara fada mata abinda shi da kanshi bai gama sanin menene ba? Yanajin kamar wani abu na sarke dashi, ko tuki yake yanajin abin gab dashi, idan ya sauka yana tafiya da kafarshi saiya waiga yafi a kirga saboda ji yake kamar abin na biye dashi. Ga wani irin tsoro da yake cike da zuciyarshi da baisan daga inda yake tasowa ba.

  Yanzun ma yana kasuwa yaji ya nemi yar nutsuwar da yake tare da ita ya rasa, yayi niyyar biyawa wani wajen kafin gida, inda zai samu wata nutsuwar ta daban, sai ya kasa. Saboda abinda yake nema yana da tabbacin ba zai samu a tare da kowacce irin mace bace zata fado masa. Kamar ya fasa ihu haka yake ji sanda ya shigo gidan, yaje dakin Saratu ya tura yaganta kwance tana bacci, sai ya karasa dakin Lukman ya tura yaji shi a kulle, hakan na tuna masa da kowacce rana ce, Lukman din yana da makaranta. Wani abune ya tuna masa Madina na gidan, kawai so yakeyi yayi magana da wani, wani wanda yake ji a zuciyar shi watakila ya samu nutsuwa.

  Ko idanuwanshi ya rufe da wahala ya lalubo hotunan Madina guda uku a cikin kanshi da ta saka wasu kaya na mata, tunda ta fara hankali kuma duk ganin da zaiyi mata banda hannuwanta da fuskarta baya iya tuna yaga wani abu. Sai yau da baisan yanda zai fara hana idanuwanshi yawatawa akanta ba. Ganin da yake mata gajera saiya dauka kamar Adee take itama, bambancin nasu yana tare da shigarsu da ta bambanta. Tunanin shine da bai taba yi mata kallo na biyu ba ko idanuwan shine bai sani ba, amman akwai abinda ya kange shi daga hasaso cewa abinda Madina take boyewa a karkashin shigarta kenan.

  "Daddy..."

  Muryarta dake rawa ta kutsa cikin tunaninshi tana saka shi dakyar ya dago da idanuwan shi ya kalleta

  "Ka dawo? Sannu da zuwa... Inzo in zuba maka abinci?"

  Rashin sanin abinda zai fada yasa shi daga mata kai

  "Barin saka kaya in fito"

  Ta furta tana murmushi, haka kawai taji zuciyarta na mata rawa, taji wani tsoro ya ratsata irin wanda bata taba tunanin zata jishi idan Julde yana tsaye a wajen ba. Yanda saida idanuwan shi suka sake yawatawa a jikinta kafin ya ja kafafuwanshi ya fita ya saka tsikar jikinta mikewa cikin yanayi marar dadi, sai taji kamar wata dauda ta manne mata. Kallo ne da baiyi mata dadi ba, kallo ne daya sake ninka tsoron da yake zuciyarta ya kuma raunana kallon da take yiwa Julde batare da ta sani bama. Yana fita jikinta har rawa yakeyi ta karasa ta kulle kofar tana murza mukulli, zuciyarta a makoshinta lokacin data gama saka kaya ta fito tana nufar kitchen. Abincin ta hada masa tana kai masa dining table, daga nan inda take tsaye tace masa

  "Daddy ga abincin naka"

  Tayi nufin komawa dakine sanda taji muryar shi na fadin

  "Ki bani ruwa"

  Ta manta da ruwa, kitchen din ta sake komawa ta dauko kofi da robar ruwa, ta ajiye robar tana shirin ajiye kofin taga ya mika mata hannu, batayi tunanin komai ba ta mika masa kofin, yanda hannunsu ya hadu kadan ya rage kofin ya subuce mata da Julde bai rike ba, zuciyarta taji ta sake yin wani tsalle kamar tana kokarin rabuwa da kirjinta. Da sauri ta juya tana barin wajen

  "Yanda ka kunyata ni Julde... Allah ya kunyata ka a idanuwan mutanen da suka fi komai muhimmanci a wajenka..."

  Julde yaji kalaman sun dawo masa lokacin daya bi bayan Madina da kallo kafin ta bacewa ganin shi, idanuwan shi ya runtsa ya sake bude su yanajin jikin shi ya dauki wani irin dumi

  Sai dai wata kaddarar yanzun ne shafinta zai bude...!

  *

  Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, ko da fatan alkhairi ne. Sai da data zan samu in sake update, data kuma sai da kudi. Idan babu comments da likes dinku anan ba za'a biyani ba.

  Idan kana da account sai ka sake yin sign in zaka iya yin comment da like, sannan ka dawo ka danna kan link din.

  #SonSo

Comments

28 comments