Makalu

Sabbin Makalu

View All

Rai da kaddara 2: Shafi na ashirin da shidda

 • Duk labarun tashin hankalin da yake ji basu taya shi shiryawa zuciyar shi wannan da yake so wani ya girgiza shi yace masa mummunar mafarki ne yakeyi ba, ko a tarihi ba zai tuna kunnuwan shi sun tsinkayo mishi wani yana bada labari kwatankwacin abinda yake gani yanzun ba. A tsaye yake akan kafafuwan shi, har yanzun yana da tabbacin akan kafafuwan shi yake tsaye saboda yana jin sunyi sanyi. Duniyar da yake tsaye akanta ne ta birkice dashi tana nuna masa iyakarsa. Kamar awanni ba kasa da dakika ba haka yaji tsakanin rufe idanuwan shi da yayi ya sake bude su kamar yana son wani sashi na zuciya ko kwakwalwar shi su karyata masa abinda yake gani.

  Mintina nawa ne daga bangaren su zuwa nan din, duka anyi awa da fitar shi? Ya za'ayi ace gabaki daya duniyar ce tayi juyin waina dashi haka? Yaune fa, dazun nan, ya dawo daga wajen aiki a gajiye, ya wuce bangarensu kai tsaye yayi wanka ya sake kaya, maimakon ya kwanta yayi bacci, da cajar wayarshi da ya dauko danya makalata sannan ya kwanta ya baro bangaren su zuwa na Saratu, saboda yana son ganin Madina, sai dai guga takeyi daya kira wayarta. Takawa yayi daga falon yana karasawa har dakinta ya kwankwasa, sai da ta bashi izinin shiga sannan ya tura kofar. Dakin Adee ne ada, banda litattafan Madina da suke ajiye kan durowar gefen gado, kusan dakin yana nan yanda ya san shi.

  Haka kawai sai kewar Adee din ta saukar masa kamar basa waya kullum. Kusan rabin rayuwarta ita da Nawfal a makaranta sukayi ta, saboda itama har sakandire dinta makarantar kwana ce. Amman dan lokacin da take gida, yayi kewar wannan lokacin, fadansu saboda bata san yanda zatayi abu a hankali ba, ko zaune yake a falon saiya sani idan itace take wanke wanke, zai iya rantsewa cokali take dauka tana kwalawa a jikin kwanoni saboda ta saka shi magana, ko tafiya zatayi saita dinga jan kafafuwanta. Idan bai kai mata duka koya zageta ba batajin dadin. Adee ce duk a cikin kannen shi zata zauna kan kujerar da yake kai, ko mai zaman mutum dayace saita zauna a hannunta.

  Har tambayar Saratu yakeyi

  "Nanna anya baki haifo Adee bane don kawai ta takuramun?"

  Ko ita Adee din gab da bikinta da ya kai mata wata masga sai da tace

  "Na kusa bar maka gidan Hamma, sai kayi kewata"

  Gani yake kewarta na me zaiyi? Gashi kuwa yanzun, dakinta kawai ya gani amman zuciyar shi tayi wata irin matsewa a cikin kirjinshi. Kewarta yakeyi sosai. A bayan zuciyarshi ya adana cewar ya kamata ya biya yau ko zuwa gobe ya ganta. Tunda kwana biyu bata zo gidan ba

  "Na kusa gamawa... Saura guda biyar"

  Madina ta fadi tana masa murmushi, zaune take bakin gado tana gugar a kai, kofar Salim ya sake budewa sosai, wannan dokar Saratu ce tuntuni, in dai wani a cikinsu zai shiga dakin Adee to kofar a bude za'a barta, sannan kamar yanda tun suna hade waje daya, ba'a ware musu bangarensu ba, akwai kujeru a nasu dakunan, dakin Adee ma akwai. Babu mai hawar mata gado in dai sun shiga. Da aka ware musu bangarensu kuma, da hankalin shi dai zai kirga lokuttan da Adee ta taka bangaren su, sai dai su suzo na Saratun. Har yanzun kuma akwai kujerun guda biyu, daya daga ciki yaja yana zama.

  Yanajin yanda zuciyar shi ta nutsu da kusancin da yake da shi da Madinar

  "Bacci ya kamata ace kanayi Hamma"

  Kafadarshi daya ya makale mata saboda bayason yin magana, bayason cewa komai. Da zai samu, baccin zaiyi, daki daya da ita. Baccin da yafi kowanne yi masa dadi da nutsar dashi shine lokuttan da yayi su a kofar gidan Daada, a cikin motar shi, sanin tana gefen shi a zaune tana kallon shi, ko tana danna wayarta, ko tana karatu. Tana dai gefen shi, koma me ta zabi tayi kafin ya tashi, awa dayane, wasu ranakun awa biyu. Amman idan ya tashi sai yaji duk gajiyar da ya kwaso ya nemeta ya rasa. Madina na da wannan tasirin a rayuwar shi.

  "Ka ci abinci?"

  Kai ya daga mata, meatpie ne daya siya da daddare, guda biyu ya rage, shine ya ci da safen kafin ya baro asibiti, kuma bayajin yunwa. Kai ta daga masa, dankali da kwaine da shayi sukayi da safen, Khalid ma da nashi ya tafi don yace ya makara, Lukman kuwa a kitchen din ya tsaya yana ci da sauri-sauri, shima saida tace ta zuba masa ya tafi dashi ya girgiza mata kai. Ta zauna kenan a dining table zata karya Julde ya fito, haka kawai ta tsinci kanta da mikewa bayan ta fito, ta dauki plate din. Bayan sunanta daya kira ba zatace ga abinda yake fada ba, saboda yanzun idan ta ganshi sai taji zuciyarta na mata rawa. Ya dai miko mata wani lemo da ta amsa tana shigowa daki dashi.

  Yanzun ne ma ta hango shi ta mika hannu ta dauko, robar tayi mata kyau sosai, lemon na mangwaro ne, ta saka karfinta wajen kwance murfin, sai taga ya bude kamar a kwance yake daman, ko dan wasu robobin ba'a datse su da karfin nan. Kurba tayi

  "Wanne irin lemo ne?"

  Salim ya tambayeta, sai da ta hadiye ta kara saboda dandanon yayi mata dadi sannan ta amsa shi

  "Na mangwaro ne, Daddy ya bani dazun... Zaka sha?"

  Kai ya girgiza mata, yana dai kallo harta shanye duka robar a gefe suna cigaba da hira jefi-jefi

  "Bacci kake ji Hamma, kamata yayi ace ka kwanta"

  Ta furta ganin yayi hamma a tsakanin maganar da sukeyi tafi a kirga, bai amsa ba, kallonta kawai yayi. Itama kanta take ji kamar an dora mata dutse, ga wani lumshewar rashin dalili da idanuwanta sukeyi mata, ko bashin bacci taci baya mata haka, balle ta samu wadataccen bacci

  "Ke ma baccin kike ji, karatu kika tsaya jiya ko?"

  Kai ta girgiza masa, badon bata so ta tsaya karatun ba, sunyi waya dashi yana asibiti yace mata ta kwanta tayi bacci saboda tayo masa korafin kanta yayi mata nauyi. Kuma sai tayi abinda yace din

  "Kai kace in kwanta Hamma"

  Tayi maganar kamar bata da wani zabi daya wuce bin umarnin shi, hakan ya sanyaya wani bangare a cikin zuciyar shi

  "Kawai dai wani baccin ne ya kamani yanzun"

  Ta dora da fadi tana kara gyara zamanta. Saiya mike

  "Ki kwanta, nima bari inje in dan samu baccin... Mu fita yawo anjima?"

  Ya karasa maganar da alamun yana jiran amsarta, kai kawai ta iya daga masa. Shi yaja mata kofar daya fita daga dakin. Kuma kai tsaye bangaren su ya wuce ya kwanta a falo kan doguwar kujera, bayajin yayi baccin awa daya yaji ya bude idanuwan shi, dan ya dauki wasu mintina yana neman dalilin yankewar baccin nashi ya rasa. Wayar shi daya laluba don ya duba lokaci yaji bata gefen shi yasa shi tashi zaune yana tunanin inda ya ajiyeta. Saiya tuna ya barta dakin Madina, abinda yaso yayi, ya tura kofar a hankali, ya mika hannu ya dauko wayar shi, ya rufo mata a hankali, dan duka fatan shi yana kan ta samu baccin. Shisa har yanzun yake tuhumar kanshi ko mafarki yakeyi.

  Yake addu'a da yakinin da bai taba yi ba tunda yake a rayuwar shi, abinda yake gani a gabanshi ya kasance mafarki ne

  "Akwai macen da zata gifta ta gabanka baka bita ba Julde? Kana da wani layi in dai akan mace ne da ba zaka iya ketarewa ba?"

  Maganganun Saratu a wani dare kan fadan da suka saba ita da Julde suka dawo masa. A lokacin bai gane abinda take nufi ba, asalima kalaman sun tsaya masane saboda kamar basuyi masa dadi ba, kamar tunda yasa kafafuwan shi cikin takalmin Julden yake kokarin fahimtar shi, ya dauka zai tsaya kan mace dayane, duk sanda zai bi wata zai raya a zuciyarshi itace ta karshe, sai wani abu ya sake jan shi, wani abu mai wahalar fassarawa, wani abu da wanda ya tsinci kanshi cikin yanayin bukata irin tashi ce kawai zai fahimta. A lokacin sai yake ganin inda itama Saratun zata saka kafafuwanta a cikin takalman Julde data yi masa uzuri ko kadan ne, data gane abinda yakeyi abune mai wahalar bari, da ta gane akwai darare mabanbanta daya kudurci cewa shine daren shi na karshe tare da wata mace da bata halatta a wajen shi ba, amman saiya kasa. Sai wani abu ya sake mayar dashi, wani abu mai girman gaske.

  Wannan ne layin da take magana a kai daman? Layin da komin lalacewar da kayi bai kamata ace ka tsallaka ba? Ashe haram kala-kala ne? Girman wani ya kamata ace baka gwada dauka ba saboda ba danne ka kawai zaiyi ba, harda makusanta zai hada idan ya tashi.

  "Banyi mata komai ba"

  Julde ya sake fadi yana kallon Salim, a gefe daya kuma yana dawo da Salim din cikin hayyacin shi yana kuma tabbatar masa da ba mafarki bane ba, abinda yake gani gaskiya ne. Idanuwan shi Julde ya raba daga kan Salim yana mayarwa akan Madina da take kwance da alama batama san duniyar da take ba. Ya sake mayarwa kan Salim, jikinshi bari yakeyi, ba kuma waje ba, har cikin tsokar shi yakejin hakan, zuciyarshi na wani irin bugu da tun halittarta wannan ne karo na farko data taba yi masa haka. Ya dade yanajin shi kamar wanda wani abu yake bibiya, kamar bacci yake yana mugun mafarki, yanzun kuma da yaji ya farka saiya taradda mafarkin ya biyoshi har wannan duniyar ma.

  A karo na farko a tsayin lokaci da yaji ya furta

  "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

  A cikin kanshi, yana shirin sake karantowa sallamar da ta karade falon har suna ji daga inda suke ta hana shi

  "Madina!"

  Khalid ya kira da alamun murmushi a muryar shi, tun jiya Nawfal yace masa ya zauna cikin shirin zuwa dauko su daga airport don zasu kamo hanya a jiyan, zasu tsaya Abuja su kwana saboda Murjanatu, yau din zasu biyo jirgin Kano, amman karya fadawa kowa saboda suna son ba Madina mamaki. Saurin da yakeyi kenan da safe, ya karasa wajen aiki, akwai takardun da suke bukatar kulawar shi, ya kuwa gama akan gaba, dan yana fita daga office, kiran Nawfal din na shigowa wayar shi, ya kuma ga lambar shice ta Najeriya, alamar sun karaso.

  "Daada kamar dai kinje yawon shakatawa ba jinya ba, irin wannan karo haske da kiba haka? Gaskiya da na sani na biku"

  Ya furta cikin sigar tsokana, har ranshi yana jin dadin ganin saukin data samu, dariya kawai takeyi, da alama murnar dawowa da kuma ganin shi ta hana tsokanar tashi tasiri, ko da ya sake cewa

  "Bakinki yaki rufuwa Daada, nifa auren nan bawai inayi bane ba, duk kyan nan da kika kara"

  Hannu takai tana kamo kunnen shi hadi dayin dariya, shima dariyar yakeyi yana fadin zata cire masa kunne dan inya tashi kara aure ace ba za'a bashi ba

  "Batare da ita kuke ba?"

  Khalid yayi tambayar yana kallon Nawfal

  "Ita wa?"

  Nawfal ya bukata duk da ya gane cewa Murjanatu yake tambaya

  "Anty na"

  Dariya Nawfal yayi

  "Tare muke, zata karaso gobe ko jibi In shaa Allah, kasan ta dade rabonta da nan, to ta tsaya wajen yan uwanta a Abuja..."

  Daada taso su wuce da ita gidanta ne kai tsaye, Khalid yace

  "Daada so kike Madina ta dauki gaba damu? Ai mu biya mu dauketa kawai sai mu tafi mu sauke ku tare, bata fa walwala tunda kika tafin nan, sai kince a cikin bare kika barta ba 'yan uwa ba"

  Murmushi Daada tayi, itama kewar Madinar na danneta, dan kwanakin nan kullum sai tayi mafarkinta, ko safiyar yau dan baccin daya dauketa a cikin jirgi, mafarkin Madina ne ya farkar da ita, zuciyarta kuma sai tayi mata nauyi, lokacin daya rage a tsakaninsu take jin kamar yayi mata nisa fiye da kullum, kamar ba'a hanyar gida suke ba. Shisa suna shiga cikin gidan, Khalid ya kwala mata kira Daada taji kiran har cikin zuciyarta, ganin inda Khalid ya nufa, Nawfal na rufa masa baya yasa Daada dinma taji tana so ta karasa don ji tayi ba zata iya jira har Madina ta fito ba.

  "Madi..."

  Khalid ya soma, ganin Salim a tsaye yasa maganar koma masa

  "Hamma..."

  Ya kira da alamar tambayar me yakeyi a tsaye haka a wajen a cikin idanuwan shi, fuskar Salim din Khalid ya kalla yana ganin wani abu a shimfide akai da yasa karawa bugun zuciyar shi gudu, haka kawai kafafuwan shi suka soma yi masa barazanar kasa daukar shi ta hanyar yin wani irin sanyi

  "Me ya faru? Menene?"

  Nawfal yake tambaya yana wuce Khalid ya karasa inda Salim yake, sai lokacin Salim ya motsa tun bude dakin da yayi, sai dai ya motsa a makare dan har Nawfal din ya karasa, ya kuma ture hannun Salim da yake kokarin hana masa ganin meye a cikin dakin. Idanuwan shi ya fara runtsawa yana yo baya kamar an watsa masa ruwan zafi, yanda zuciyar shi take dokawa na saka shi neman taimakon bangon wajen don dai-daita tsayuwar da take neman gagarar shi

  "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

  Ya tsinci kanshi da furtawa, yana sake runtse idanuwan shi gam, yana maimaitawa cikin sallamawa ga Ubangiji da neman taimakon Shi wajen bacewar abinda yagani daga duniyar shi na har abada

  "Hamma"

  Khalid ya kira, tsoron da yake cike da zuciyarshi na bayyana a muryar shi, kai Salim yake girgiza masa, ba saiya karaso ba, ba sai yaga abinda zai canza duniyar shi na har abada ba, amman ya kasa kin karasawar, cikin dakin ya shiga gabaki daya, yana kuma yin abinda su duka suka kasa, karasawa har inda Madina take kwance yaja mayafin da yake kan gadon ya rufa mata a jikinta

  "Ban mata komai ba..."

  Julde ya furta yana kallon Khalid, rigar shi da take ajiye a gefe Khalid ya dauka ya mika masa, ganin bai karba ba yasa Khalid kallon shi, wani abune a cikin idanuwan Julden da ba zai fassaru ba, kamar shima neman wanda zai tambaya abinda yakeyi a tsaye a dakin yakeyi, kamar kuma neman wanda zai jijjiga shi yace masa mafarki yakeyi yake nema

  "Kasa rigarka..."

  Khalid ya fadi muryar shi na fitowa a raunane, karba Julde yayi yana mayarwa, sai yakejin nauyin rigar tare da wani abu daban na ratsa shi, tsikar jikinshi ta shiga mikewa, da fankar dakin ta kada, sai yaji saukar iskar a jikin shi da wani irin yanayi, kamar tun shigowarshi dakin wannan ne karon farko daya san da zaman fankar, sanyi yakeji, sanyi yakeji har baisan hakoran shi na haduwa da juna ba balle jikin shi da yake bari

  "Daddy"

  Khalid ya kira yana kai hannu ya rike damtsen hannun Julde dashi, amman yanayin da Julde yake ji na sanar dashi karshen komai yazo, ga numfashin shi ya daina kaiwa inda ya kamata, iskar fanka na kadawa tunda yanajin sanyinta na kara masa wanda yakeji, amman bata kaiwa hancin shi balle idan ya shaka ta wadace shi, rufe idanuwan shi yayi da niyar ya budesu, amman sai wani duhu na ban mamaki ya lullube masa komai. Khalid na rike da hannun shi yayi kasa yanajan har Khalid din da yake kiran sunan shi a wahalce. Salim na kallon su, yana kallon Khalid na jijjiga Julden amman ya kasa motsawa balle ya kai musu wani taimako.

  Daada data yi tsaye inda take ma batayi wani yunkuri ba, jikinta ya bata koma menene ba abinda zata so bane ba, zuciyarta tayi raunin da bakowanne tashin hankali zata iya dauka ba yanzun, tana kuma da tabbacin wannan tashin hankali ne da zai iya karasa abinda yayi saura a cikin kirjinta. Duk da wasu zasuce wanne dare ne jemage bai gani ba? Amman ita tasan baiga daren mutuwar shi ba, wannan kuma dai-dai yake da hakan a wajenta

  "Me yake faruwa ne Daada?"

  Saratu da ta shigo gidan take ta sallama harta karaso babu wanda ya nuna alamar yasan tanayi ma balle ya amsa ta tambaya, kallonta kawai Daada tayi da idanuwanta da batama san sun cika da hawaye ba taji wani tashin hankali na tasowa tun daga dan yatsan kafarta har tsakiyar kanta kafin ya tattaro ya samu wajen zama a cikin kirjinta, sai dai data karasa cikin dakin bata tsammaci zata ga Julde kwance kamar gawa ba, bata kuma sake tabbatar da shi din kacokan ne duniyarta ba sai yanzun da ta ganshi kwance haka, ba zatace a tsaye ko a zaune ta rarrafa inda yake ba, ta dai ganta a kasa, ta kuma ga kanshi a jikinta, hannuwanta na bin fuskar shi tana son tabbatar da karshen duniyar ta baizo tare da nashi ba.

  Da gaske ne wani tashin hankalin ya fi gaban kwatance...

  ***
  BARKAN MU DA SALLAH. ALLAH YA YAFE MANA YA AMINTA DA AYYUKAN MU YASA MUNA DA RABON GANIN WATA CIKIN LAFIYA DA AMINCI.

  *

  Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar acan, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku.

  Idan kana da account sai ka sake yin sign in zaka iya yin comment da like, sannan ka dawo ka danna kan link din.

  Whatsapp: 0903 572 3778

  #SonSo

Comments

20 comments